Showing 90001 words to 92754 words out of 92754 words
Chapter 31 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf
take, tana bashi duk wata kulawa da ta kamata, shafa fuskar ta yayi da hannun shi yace
"Ngde da wannan kulawar take habibty "
Kafin ya cigaba da cewa
"wanne suna kike ganin zamu sanya wa yaran mu? "
D'an murmishi tayi tana cewa
"Ni ban da wani za6i sai naka, duk sunan da ka sanya musu yayi min "
Wani murmishin jin dad'in abin da tace yayi, sake rungume ta yayi a jikin shi yana shak'ar daddad'an
k'amshin turaren yace
"sunan da nake son sanya musu shine, babban zai ci sunan Abubakar sadeeq d'ayan kuma sunan Muh'd
ko ya kika gani idan bai yi ba sai ki fad'i wanda kike so"
Wasu hawaye masu zafi ne suka zubo wa Mufidah, tabbas daman kudurta cikin zuciyar ta idan Allah yasa
ta samu d'a namiji sunan Sadeeq zata mayar shi, sai gashi Musaddiq ma hakan ne cikin zuciyar shi.
D'ago kanta yayi yana girgiza kanshi tare da sanya hannun shi yana goge mata hawayen fuskar ta yace
"Kiyi hak'uri Mufidah addu'a kad'ai zaki na yiwa Yah sadeeq, don ita kad'ai ce zamu yi mishi mu nuna
kaunar shi a gare mu, bana son ganin kukan ki, ki daina please"
Cikin sanyin murya yake maganar, gid'a kanta tayi kafin tace
"na daina, Allah ya jik'an shi da rahma "
"Amin "
Ya amsa, ganin ta shiga damuwa ne yasa shi rarrashin ta har ta dawo normal, kafin su cigaba da hirar har
zuwa lokacin da Mumy tazo ta kore shi, don ya bar ta ta huta, haka ya tafi yana mitar hana shi sake wa da
matar shi da 'ya'yan shi.
Haka aka cigaba da hidindimu har zuwa ranar suna, lokacin dasu Mumy da Muh'd suka ji sunan yaran
sosai sun yi farinciki ba k'arami ba, don sunan da Musaddiq ya sanya musu yayi dai dai, sai fatan Allah
yasa su gado masu sunan.
Muh'd a daren sunan ya shirya dinner sosai, ba wanda ya sani tsakanin Musaddiq da Mufidah sai da
daren hatta kayan da za su yi amfani dashi ya tanadar musu, Musaddiq sam bai yi musu ba suka shirya
suka tafi tare da twin's d'in su.
Wow gaskiya wurin dinner d'in ba k'aramin had'u wa yayi ba, don mutane sosai Muh'd yayi gayyata, har
da en Exclusive writer forum, ga en group d'ina Aishat A Muh'd fan's, can na hango momma na ta kaina
(Aunty maijiddah) tare da twin's d'in ta, mutane sun yi k'ara wajen zuwa, ga fan's d'in Musaddiq da
Mufidah (Musfeedah) nan duk sun zo na hango su gaba d'ayan su a wurin, sun sha gayu sai zuba iyaye
ake, lol.
Anci ansha anyi musu addu'ar Allah ya raya su, kafin kuma a tashi kowa ya kama gaban shi, Mufidah
kuwa ta cika fam da fushi da kishi saboda yanda 'yammata suka dunga kula wa Musaddiq suna wani
shishshige mishi, dakyar ya shawo kan kayar shi suka shirya, don sam bazai iya zaman second's ba da
kwanciyar hankali ba idan Mufidah na fushi dashi.
Sun cigaba da rainon twins d'in su har zuwa lokacin da suka yi arba'in, twin's sun yi wayo sosai, sun k'ara
girma gasu da wayo yaran, dakyar Musaddiq ya yarda taje gidan su kwana uku tayi ta dawo shima
kwanakin ukun kusan dashi aka yi kwanan, don zaman shi yayi ya kasa tafiya ko kunyar su Umma baya yi,
Mumy dai taga rashin kunya kam ganin yanda Musaddiq ya tafi gidan surukai kwana................
Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page*
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com
_Wannan shafin kyauta ne da duk wani masoyina da masoyin wannan littafin, ina muku fatan alkhairi_
*K'ARSHE* (LAST PAGE)
*PAGE 60*
Suna dawo ne ko kwana d'aya basu k'ara yi a side d'in Mumy suka wuce nasu part d'in, daman tuni
Mumy ta gyara d'iyar ta ta don ya taga yanda d'an nata yake rawar jiki, haka ma Umma ta tsaya tsayin
daka wajen gyara ta sosai, tanan 6angaren Mufidah bata da matsala.
Ansha soyayya sosai a wannan daren tsakanin Mufidah da Musaddiq, sun kasance cikin farinciki sosai, ji
suke tamkar don su aka hallaci duniyar saboda tsantsar farincikin da suka tsinci kan su a ciki, sun yi
baccin su cikin kwanciyar hankali.
Washe gari da safe Mufidah ce ta fara kok'arin tashi daga bacci da safe, bayan ta tashin ne ta fara kok'arin
gyara gidan, cikin en mintuna ta tsaftace ko'ina ta sanya turaren wuta masu k'amshi tare da air freshener,
tana gama wa ta wuce bedroom wanka ta fara yi wa twin's ta gyara musu cikin su tsaf, sannan ta basu
abincin su suka sha, bayan ta d'ora su a kafad'a ne tana d'an shafa bayan su har sai da suka yi gyatsa
tukunna ta kwantar da su.
Toilet ta wuce wanka tayi sannan ta fito ta gyara jikin ta tare da yin light make up, wata atampha ta
dauko tare ta sanya d'inkin riga da siket ne sun zauna a jikin ta sosai, tayi kyau tana cikin fesa perfumes
ne Musaddiq ya shigo d'akin ko wanka bai yi ba sleeping dress ne kawai a jikin shi.
Rungume ta yayi ta baya tare da kar6ar turaren hannun ta yana cigaba da fesa mata bayan ya gama ne ya
ajiye akan dressing mirror, sannan ya cusa kanshi tsakanin wuyan ta yana shak'ar k'amshin daddad'an
turaren ta har wani ajiyar zuciya ya ke saki.
"Baby nah shine kika gudu koh, kika yiwa twin's wanka kema kika yi, aka mance da ni "
Murmishi ta saki cikin k'ara kaunar mijin nata tace "Haba nawan ni na isa, yanzu zan zo na shirya ka, yau
akwai zuwa hospital "
D'an yatsina fuska yayi tare da cewa " ni yau hutu nake ba inda zan je"
Cikin mamakin abin da yace d'ago kanta suna kallon face d'in junan su tace
"Saboda me? "
Hannun ta ya rik'o yana shafa su a hankali yace
"dalili kike son sani uhm"
Bai k'arasa fad'i ba ya kashe mata ido d'aya, tuni ta fuskan ci abin da yake nufi, d'an dukan wasa ta kai
mishi a gefen kafad'ar shi ya goce yana mata dariya, nan suka fara wasannin su suna ta dariya daga
k'arshe suka zube kan bed kusa da twin's suna mayar da numfashi, kafin daga bisa ni ta raka shi toilet yayi
wanka, ta taimaka mishi ya shirya, sannan suka zauna yiwa twin's wasa.
A ranar Musaddiq ba inda ya fita sai zuwa gaida su Mumy da suka je, acan ma suka yi breakfast suna
gama wa,shima basu wani jima ba ya tak'ura mata suka tafi side d'in su aka bar Mumy da twin's, daman
Afnan ta tafi school.
*** *** ***
*AFTER 7 YEAR'S*
A cikin wad'annan shekaru da wuce zaman lafiya sosai ake tsakanin Mufidah da Musaddiq, haka ma ta
6angaren Mumy babu abin da ya sauya daga soyayyar da take nuna wa Mufidah.
Haka amintakar da ke tsakanin Musaddiq da Muh'd kullum sake kaunar junan su suke, ta 6angaren
Mufidah da Nabilah tare da Nafisat su ma kawancen su sosai suke yi sun zama tamkar 'yan uwa.
A cikin wad'annan shekaru Nabilah ta sake haihuwar yara biyu, sun ci sunan Umma da Abba, haka Nafisat
matar Muh'd ita ma ta sake haihuwar wasu yaran har guda biyu duk mata.
Mufidah ma ta sake haihuwar namiji yaci sunan daddy ga kuma wani tsohon cikin da yake jikin ta
haihuwa yau ko gobe.
Musaddiq da Mufidah kullum k'ara kaunar junan su suke, tattalin juna da kulawar da suke yiwa junan su
shi yayi musu jagora wajen shimfid'a kyakkyawar rayuwar su mai cike da jin dad'i da kwanciyar hankali.
Ga kuma kula da yaran su da suke, suna kok'arin gaske wajen basu tarbiyya tare da basu ilimi na addini
dana boko, yaran sun girma gashi sun taso cikin soyayyar iyayen su da kakannin su ta kowanne 6angare,
amman duk da wannan soyayyar da suke nuna musu hakan bai hana su basu tarbiyya mai kyau ba.
A cikin wani daren alhamis Allah ya sauki Mufidah lafiya, ta haifi baby girl d'in ta, farinciki wajen
Musaddiq kamar bai ta6a samun 'ya'ya ba, daman burin shi kenan ya samu mace mai kama da Mufidah,
sai gashi duk cikin yaran nan nata ita ce mai kama da ita sosai.
Ansha shagalin suna sosai an kashe kud'i, inda yarinya taci sunan ta Nauwara, haka Mufidah ta cigaba da
kula da 'ya'yan ta tare da taimakon jarumin mijin ta Musaddiq, wanda a kullum cikin bata dukkanin wata
kula wa yake, baya gajiya da hidimar Mufidah kamar yanda ita ma bata gajiya da tashi hidimar.
Duk hausawa sunce zo mu zauna zo mu sa6a, amman tsakanin Mufidah da Musaddiq akwai fahimtar
juna sosai a tsakanin su, duk da wani lokacin daman sai anyi hak'uri da juna, domin ance ko tsakanin
harshe da hak'ori ana sa6awa, ko da sun yi fad'a a tsakanin su baya kaiwa wani tsawon lokaci ba tare da
sun yi shirya kan su ba don basa jure yin fushi tsakanin su.
*** *** ***
Misalin k'arfe 8 na dare bayan an idar da sallahr ishsha ne, Musaddiq da twin's tare da lil Daddy suka
shigo parlourn da sallama dawowar su daga masallaci kenan.
Hannun su d'auke da robar ice cream da chocolate masu dad'i, saboda sun biya yiwa Mumy sallama sai
da safe shine ta basu, Afnan ce zaune a parlourn tana rik'e da Nauwara tana yi mata wasa ta amsa
sallamar su cikin nutsuwa.
Gaida Daddy Musaddiq tayi cikin ladabi da girmama wa, yayin da k'annan nata suka gaida ita suma, zama
suka yi ana hira cikin so da kaunar junan nasu.
Mufidah ta fito parlourn cikin wata gown ta atampha d'inkin yayi mata kyau sosai, k'amshin turaren ta da
Musaddiq ya ji shi ya sashi lumshe idanun shi yana saukar da ajiyar zuciya a hankali, kafin ya ware idon
shi kan Mufidah sanyayen murmishi suka sakarwa junan su, da hannu yayi mata alamar tayi kyau ta amsa
mishi da ido ta gode.
"Oya ku tasu aci abinci a kwanta gobe da school "
Mufidah ta furta hakan ganin yanda yanayin mutumin nata ya canja, tashi suka yi gaba d'ayan su suka
nufi dining table suka zauna, Mufidah tayi serving d'in su.
Nan suka yi bismillah cikin nutsuwa suka fara cin abincin su, ba wanda yake magana a cikin su sai dai
Musaddiq da Mufidah da suke aikawa junan su murmishi tare da wani irin kallo wanda su kad'ai suka san
ma'anar shi.
Bayan sun gama ne Afnan tayi musu sallama ta tafi side d'in Mumy da yake daman acan take sai dai
kusan yini take a part d'in Mufidah, Musaddiq bai barta ta tafi ita d'aya ba saboda dare ya d'an yi don 9
ta kusa, yana rik'e da hannun ta har suka zo part d'in Mumy sannan ya bata peck a kumatun ta yace
"Good nyt sweet dgter and sweet dreams "
Cikin murmishi tace
"Okay daddy good night "
Daga haka ta wuce ciki shi kuma ya juyo ya dawo, zuciyar cike da kaunar Afnan yarinyar da kullum
kamannin ta da Yah sadeeq yake k'ara fito wa, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mishi tare da furta
"Allah ya jik'an ka Yah sadeeq, ina cikin kewar ka nasan har na mutu bazan dai na zubar da hawayen
rashin ka ba "
Kok'arin saita kanshi yayi don kada Mufidah ta fahimci halin da ya shiga, lokacin da ya shiga part d'in nasu
ya rufe ko'ina tare da kashe hasken ko'ina, sannan ya lek'a bedroom d'in yaran shi ya tarar sun yi bacci,
murmishi ya saki yasan wannan duk aikin Mufidah ne, wajen sa yara bacci da wuri bin su yayi d'aya bayan
d'aya ya basu peck sannan ya k'ara yi musu addu'a ya kashe hasken d'akin, tukunna ya fito yana rufe
musu kofa.
Bedroom d'in shi ya wuce ya tarar da Nauwara kwance kan k'aramin bed d'in su na yara tayi bacci abin
ta, ita ma kissing d'in ta yayi, sannan ya wuce toilet don yasan Mufidah na can tana had'a musu ruwan
wanka.
Bayan sun yi wanka sun fito ne, suka kwanta kan bed tare da rage hasken d'akin, cikin wata irin muryar
shauk'i Musaddiq ya ce
"ina son ki Mufidah, kullum son ki k'ara ratsa zuciya ta yake, ina miki son da baki na bazai iya furta miki
adadin shi ba, ina alfahari da ke matsayin mata ta"
Cikin sanyin murya tace
"Nima a kullum cikin gode wa Allah nake da ya azurta ni da samun managarcin jarumin namiji kamar ka,
ina son ka Musaddiq with all my heart, i luv u so much sweetie darling "
Sake k'ank'ame ta yayi a jikin shi tare da had'a bakin su waje d'aya ya fara bata wani zafaffen sak'onnin
shi mai mata wuyar fassara, kullum cikin gode wa Allah take da ya bata Musaddiq, da fari Allah ya bata
Sadeeq salihin mutum mara son hayaniya babu ruwan shi, Allah ya d'auki abin shi daga k'arshe ya sake
bata wani mijin abin alfahari mai son ta tsakani da Allah, ga nutsatstsun yara da ya bata, shi yasa kullum
cikin gode mishi da take da tarin ni'imomin da yayi mata take.
Bayan komai ya kammala sun yi wanka suka kwanta rungume da junan su kowanne yana fad'a wa d'an
uwan shi irin yanda yake son shi, kafin daga k'arshe bacci mai dad'i yayi awon gaba da su.
*_ASUBA TA GARI MUSFEEDAH_*
*ALLAHAMDULILLAH*
_K'ARSHE_
*DUKKAN GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH (S. W. A), DA YA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFIN
LAFIA, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU K'ARA TABBATA GA ANNABIN MU,SHUGABAN MU ANNABI
MUHAMMAD (S. A. W), KUSKUREN DA SUKE CIKI ALLAH YA YAFE MIN, FAD'AKARWAR DAKE CIKI ALLAH
YA BAMU LADAN GABA D'AYA*
*NOTE* _wannan littafin nayi shine don fad'akarwa da nishad'antar wa, kuma k'irk'iran labari ne, abin da
yake ciki mai kyau da amfani ayi aiki dashi, mara kyan kuma a watsar dashi_
*KE TA DABAN CE*
_My sweet sadeey ke ta dabance cikin zuciya ta, baki na bazai iya furta miki yanda kike a wuri na, fatana
shine Allah ya bar xumunci mu kasance tare har abada,Amin._
*INA YIN KU IRIN SOSAI D'IN NAN ADMINS OF EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
_Aishan umma_
_Dgter ummiey xeey_
_Meelat dear_
_Aishat A Muh'd_
Allah ya bar mu tare 4 sister for ever, Amin.
*GODIYA DA FATAN ALKHAIRI GARE KU SISTER'S NA EXCLUSIVE WRITERS FORUM, HOME OF PEACE
HONOUR AND SUPER WRITERS, INA SON KU IRIN SOSAI D'IN NAN WANDA BAKI BA ZAI IYA FAD'A BA,
ALLAH YA BAR MU TARE EN UWA*
*INA ALFAHARI DA KU*
_My momma (Aunty maijiddah)_
_My billy ladan_
_My biebie deee_
_My Amnoor dear_
_My queen mermue_
_My zahra ( sister d'in halilos)_
_My halilos_
_zee yabour_
_My Asy khaleel_
_Namecy Ayusha_
_Namcey Aysha Ali Garkuwa_
_Miss zahra mansur_
_ummu safwan_
_khadija neenah cool ke ta dabance_
_Aunty fauxah_
Kaiii gaskiya baxan iya rubuto ku gaba d'aya saboda yawan da kuke dashi, amman ku sani Aishat A Muh'd
na matuk'ar kaunar ku da alfahari da ku,Allah ya bar xumunci ina muku fatan alkhairi.
Jinjinar ban girma gare ku en cikin *IDON MIKIYA WRITER'S ASSO*, ina yin ku guy's Allah ya bar xumunci.
*GARE KU MASOYA NA*
_kune abin alfahari na, ina son ku duk inda kuke Allah ya bar mu tare musamman en grp d'in Aishat A
Muh'd fan's ina yin sosai guy's_
*GROUP'S D'IN DA NAKE BAZAN IYA LISSAFO KU BA, AMMAN NASAN KU MASOYA NA NE, INA MUTUM
FATAN ALKHAIRI TARE DA GODIYA GARE KU, MUSAMMAN ADMINS D'IN SU*.
*_ina kuke masoya na ina muku albishir d'in new nvl d'ina mai zuwa nan babu dad'e insha Allah_*
Aishat A Muh'd ✍