Showing 6001 words to 9000 words out of 92754 words

Chapter 3 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf

10 Jul 2025

2467



Yah sadeeq ya tuntsire da dariya kafin yace "tabbb mumy wannan doctor d'in idan matan suka ganshi
guduwa ma xasu yi saboda fuskar ba fara'a "

Cikin shagwa6a yace "Mumy ko kiyi wa brother magana idan ba hka ba xan mishi allura yanxu nan kuwa "
Don Yah sadeeq Akwai shi da tsoron allura kamar mace nan kuwa ya marairaice fuska yana cewa "Haba
d'an k'anina na dai na wuce mu je ni don Allah kada yi min xancen wata injection ina xama na lafia"

Nan musaddiq da Mumy suka tuntsire da dariya shi kuwa Yah sadeeq da sauri ya fice daga falon yana
cewa "ni nayi gaba ina jiran ka a mota "

Musaddiq ne ya kalli mumy cikin murmishi yace "mun tafi sai mun dawo "
Ya K'arasa fad'i yana bata peck a kumatu ita ma cikin murmishi xuciyar ta cike da k'aunar d'an nata tace
"Allah ya dawo min daku lafia Allah ya tsare min ku "
"Ameeen mumyn mu thanks for your du'a,bye"

Daga hka ya juya ya fita mumy ta bishi da kallon k'aunar 'ya'yan ta, su kad'ai Allah ya mallaka mata ba
K'aramin so take musu ba.

A parking space ya tarar da Yah sadeeq xaune cikin mota yana jiran shi don hka shima shiga yayi ba tare
da 6ata lokaci ba Yah sadeeq yayi wa motar key sannan suka fice daga gidan duk wanda ya gansu sai sun
bashi sha'awa saboda yanda suka yi matuk'ar yin kyau gasu kyawawa tubarkallah, motar da suke ciki ma
kanta abar kallo ce.

Cikin mintuna da basu gaxa 50 ba suka K'arasa wajen partyn, waje Yah sadeeq ya samu yayi parking
sannan suka fito jerawa suka yi kamar wasu tagwaye suka nufi wajen sam baxa kaji irin tashin sautin
kid'an nan ba wanda xai dami mutane, slow music ne yake tashi a wajen.


Shigowar su wajen shi ya janyo hankalin mutanen wajen kansu don ba k'aramin burge su suka yi ba
musamman ma musaddiq yawancin matan wajen suka raja'a da kallon shi, irin kallon nan na daman kace
kana so na.

Yah Omar yana tsaye gaban cake mufidah na gefen daman shi yayin da nabila tana hagun shi kenan sun
sashi a tsakiya,xai yanka cake din kenan yaga shigowar su musaddiq don hka ya dakata da yankawar
wajen su ya k'arasa suka rungume junan su cikin farinciki Kafin su saki juna Yah Omar ya kalli sadeeq yace
"abokina musaddiq fah ya girma nema ma yake yafi mu girma ya kamata mu ajiye iyalai mun girma "
Dariya ya sadeeq yayi suka tafa da Yah Omar sannan yace "k'warai da gaske abokina ka kawo shawara
mai kyau "
Shi kuwa musaddiq murmusa wa kawai yayi, suna cikin tafiya xuwa gaban cake din ya Omar ya cigaba da
cewa
"gwara mu yi mu bawa k'annan namu fili su ma su yi "

Dai dai lokacin sun k'araso wajen don hka Yah Omar ya kalli mufidah yace
"sadeeq ka gane wannan kuwa?"
Ya fad'i yana nuna mufidah da hannu, d'ago kan shi yayi ya kalli mufidah ita ma anyi sa'a ta d'ago kanta
nan idanun su suka sark'e da na juna take Yah sadeeq yaji wani abu a tattare shi yana bin ilahirin jikin shi,
lokaci d'aya sadeeq yaji wani son mufidah a cikin xuciyar shi wanda ake cewa love at first sight gaba d'aya
ya mance a inda suke ya kasa janye idanun shi a kanta.

Mufidah ce ta janye idanun ta a cikin xuciyar ta tace wannan ya fiye kallo da yawa ta d'an murgud'a bakin
ta Kad'an hkan da tayi sai sadeeq ya ji ta k'ara shiga xuciyar shi, ya Omar da ya ankare da kallon da yake
yiwa mufidah sai yayi Murmishi tare da dafa kafad'ar sadeeq yayi gyaran murya tare da cewa
" uhm uhm abokina ko er gida xa'a yi NE? "
Ya fad'i hkan saitin kunnen sadeeq, firgigit sadeeq yayi kamar wanda ya tashi daga bacci d'an sosa k'eya
yayi tare da cewa
"da xaka ba ni ae da naji dad'i "
Sannan kuma ya jiyo ya sake kallon mufidah tukunna yace "gaskia ba don ka fad'a min ba baxan ta6a
gane ta ba "
Yah Omar yayi dariya tare da cewa "sadeeq musaddiq wannan ita ce k'anwa ta mufidah, ke kuma
mufidah wad'annan sune sadeeq abokina musaddiq kuma k'anin shi, kuma nasan kin san Alhj Abubakar
daddy aminin abba "
Gid'a kai tayi alamar ehh ta gane sannan cikin sanyin murya tace
"ina yinin ku"
Sam bata kula da musaddiq ba shi ma hkan jin wata murya mai shegen dad'i tana gaida su yasa shi jiyo
wa ya Kalli wajen nan kuwa suka had'a ido da musaddiq tuni annurin fuskar shi da annurin fuskar ta suka
d'auke lokaci d'aya ta wani juyar da kanta gefe, sai yah sadeeq ne ya amsa gaisuwar ta ta cikin murmishi,
nabila kuwa cikin mamaki take kallon musaddiq sai dakyar ta iya bud'e baki tace
"malam ina yini?"

Dak'yar ya iya bud'e bakin shi yace "lafia " daga hka yaja bakin yayi shiru, yah Omar kallon nabila Yayi
yace
"ashe kun san shi? "
"ehhh malamin mu ne "
Cikin mamaki Yah Omar yace "malamin ku kuma shi da likita ne kuma, mene gaskiyar xancen sadeeq? "
"wlh Omar ra'ayin musaddiq ne amman naji yana cewa ya fara gaji da koyarwar, xai fara aiki a wani
hospital kafin a kammala gina nashi "

"okay hkan yayi kyau mu yanka cake din don idan muka biye wa hirar nan xamu iya 6atawa mutane lokaci
"

"alright hkan yayi kyau"

Matsawa suka yi daf da cake din wad'annan xaratan maxajen su uku da kyawawan enmatan nan su biyu,
amman musaddiq da mufidah babu fara'a akan fuskar su idan ka d'auke Yah Omar, Yah sadeeq da nabila
k'ayataccen murmishi ne shimfid'e a fuskar su, da hka Yah sadeeq ya d'auke knife din yanka cake din
tukunna ya kalli su sadeeq yace
"ku matso en uwa na mu yanka tare "
Gaba d'ayan su suka matso sannan yah Omar ya bawa nabila wuk'ar ta rik'e ya d'ora hannun shi kan nata
sannan ya sadeeq yasa hannun shi kan na Yah Omar sai mufidah sannan musaddiq shine na K'arshe ya
axa hannun shi kan mufidah lokaci d'aya suka ji wani shock but sai suka maxe kawai nan aka kirga 3
sannan suka yanka a tare nan fah aka dunga watso musu wasu kyawawan red flowers masu d'aukan
pictures da video suka cigaba da aikin su, nan yah Omar ya yanka cake ya bawa mufidah, nabila, sadeeq
sannan musaddiq hka su ma suka gutsuro suka bashi sosae sun burge mutane a wajen har wasu na
tunanin ko en gida d'aya ne saboda ganin su farare kuma kyawawa dasu.

Musaddiq ne ya xame daga wajen yaje ya samu waje d'aya ya xauna yana danna wayar shi nan fah
enmata suka dunga xuwa inda yake amman ko kallon arxiki baya yi musu hka xasu karaci surutun su
Amman kamar da dutse suke dole hka xata tashi ta bar wajen.
Ashe mufidah tana kula da yanda yake nan fa ta k'ulu kamar itace enmatan da yake wulak'anta war, tsaki
taja tare da cewa "ji be shi kamar wani sarki sai kallon mutane yake d'ai d'ai "
Nabila wadda ta ji ta sai ta harare ta, yana cikin danna wayar tashi ne aka kirawo shi don hka ya mik'e xai
fita daga wajen, a lokacin mufidah ta tashi daga kan kujerar hannun ta rik'e da cup Wanda yake cike da
juice din strawberry xata guje wa kallon da sadeeq yake yi mata, taxo wajen kofar dai dai fita daga wajen
shi kuma musaddiq ya taho sai ya take mata kafa da takalmin shi "washhh Allah " abin da mufidah ta
fad'a tana runtse ido saboda tsabar xafin da taji ko kallon Inda take bai yi ba bare yayi mata sannu kuma
yana sani ya take ta ganin yanda ya takata ko sannu bai ce mata kamar ya taka dutse yasa mufidah fusata
ranta yayi mugun 6aci da abin da yayi mata a fusace ta bishi wajen.

Yana tsaka da amsa waya ne ya juya bayan shi bai ankara ba yaji saukar wani abu mai sanyi a jikin shi tun
daga saman kafad'ar shi har xuwa cikin rigar shi da sauri ya juyo ae kuwa suka had'a ido da mufidah
hannun ta rik'e da cup d'in lemo alamar shi ta xuba mishi, kallon jikin shi yayi yaga gaba d'aya kayan sun
6aci don lemon ja ne tuni fuskar musaddiq tayi ja saboda tsananin 6acin rai da takaicin wannan abin da
yarinyar nan tayi mishi don hka a fusace yayo kan mufidah...........

Wayyo mufidah yau ta ta6o mutumin nata fiye da ko yaushe.


Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*




*written by*

Aishat A muh'd


♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*




_wannan page d'in naki ne k'awata ta arxiki Aishat Aliyu garkuwa tare da sadiya bashir (Sardy bash), ku
sani kuna rai na ngde sosae da k'aunar da kuke nuna min Allah ya k'ara basirah Allah ya bar xumunci, ina
muku fatan alkhairi en uwa_



*Page 7*

*WASHE GARI*



A hankali yake bud'e idanun shi daga wani nauyayyen bacci da ya d'auke shi bayan sallahr asuba da ya
dawo daga masallaci sai lokacin ya samu cikakken bacci, d'an bud'e idon shi yayi Kad'an sai yaga wani abu
kamar maciji a saman blanket din da yake rufe dashi yana kallon shi har da d'an xaro harshen nan da
yake.

Lokaci d'aya ya k'arasa bud'e idanun shi gaba d'aya tare da murxa su ae kuwa ba mafarki bane gaske ne
maciji ne akan blanket din yana taho wa xuwa kanshi gashi bak'i wuluk sai xare harshe yake ae kuwa
musaddiq a firgice ya tashi daga kan bed d'in ya mik'e tsaye cikin matuk'ar tsoro da tashin hankali ganin
micijin again wurin shi yake taho wa yasa shi daka wani uban tsalle ya diro daga gadon yana furta
Innalillahi don ba k'aramin tsorata yayi ba gaba d'aya ya fara had'a wani uban gumi.

Yah sadeeq da yake bakin kofa yana danne dariyar shi hannun shi rik'e da remot yasa ni asashen shine
yasa wa musaddiq micijin ga remot a hannun shi yana control din shi danna wani gefe yayi acikin remot
din ae kuwa da sauri micijin yabi musaddiq inda yake tsaye yana karkarwa don baxai iya fita ba tun da
micijin bayan shi yana kallon kofar shigo wa iya tsorata musaddiq ya tsorata ba Kad'an ba ganin micijin
yayo kan shi da sauri ya sashi fara tsalle tsalle yana ja da baya kok'arin shi ya shige toilet ya rufe don yana
ganin Idan ya shiga toilet ya tsira.
Yah sadeeq da ya kasa danne dariyar shi ya kyalkyale da dariyar mugunta jin dariya yasa musaddiq kallon
bakin kofar yana kallon Yah sadeeq cikin tsorata yace

"Yah sadeeq don Allah ka taimaka min micijin ne kada ya harbe ni please "

Yah sadeeq ne ya shigo cikin d'akin sosai ya nufo inda micijin yake cikin tashin hankali musaddiq yace
"kada ka taho min brother xai harbe ka "

K'arasa wa yayi Inda micijin yake ya d'auke shi da hannu cak tuni musaddiq ya runtse idon shi saboda
kid'ima amman jin Yah sadeeq yana kyalkyala dariya yasa shi bud'e idon da sauri ganin shi yayi ya rataya
micijin a wuyan shi yana cewa "Kaiii matsoracin likita na roba ne fah wasa nake ma kada ka sume min "

Shiru musaddiq yayi ya xuba wa micijin idanu sosai don ya tabbatar da abin da Yah sadeeq ya fad'a ae
kuwa nan ya duba tare da tabbatar wa na roba ne kamar yanda ya fad'i .

A fusace musaddiq ya nufi wurin da Yah sadeeq yake yana tuntsira dariya ganin hka yasa sadeeq ya fara
gudu don hka shi ma musaddiq yabi shi a baya nan suka fara gudu cikin d'akin suna tattaka kujerun d'akin
da kan bed d'in nan suka dunga xagaye d'akin sadeeq yana yiwa musaddiq dariya don ganin yanda yake
huci da hka suka fice daga d'akin suna gudu kamar wasu yara k'anana.



Mumy tana 6angaren dinning table tana shirya kan table da kayan breakfast ta ga Yah sadeeq ya fito daga
bedroom d'in musaddiq da gudu sakin baki tayi tana kallon su bata ankara ba taji sadeeq ya xagayo ta
bayanta yana cewa

"Mumy Ki taimake ni na tsokano likita "
Cikin dariyar manya Mumy tace "ina ruwa na kai dashi Idan yayi maka allura ba ruwa na "

Yana k'araso wa kusa da mumy ta rik'e shi tare da cewa "d'an lele na mai wannan yayan naka sarkin
tsokana yayi maka da safen nan? "

Sai da ya watsa wa Yah sadeeq harara sannan yace "mumy ina cikin bacci yaxo ya samin miciji a jikin
blanket yana tsorata ni"

Sadeeq bai ankara ba yaga mumy ta xame daga tsakiyar su daman shi yana bayanta ya lafe musaddiq
kuwa yana gaban ta cikin dariya tace
"ba ruwa na musaddiq gashi nan yi mishi allurar rashin ji "

Ta fad'i tana mik'a wa musaddiq wani k'aramin first aid box wani fari ae kuwa da sauri Yah sadeeq ya rik'e
tare da cewa "sorry brother baxan k'ara ba na daina "

Yanda Yayi maganar ba k'aramin sa musaddiq da mumy dariya ba don hka baisan sanda ya tuntsire da
dariya ba shi ma sadeeq dariyar yake nan suka rungume junan su cikin k'aunar junan su, mumy tana
kallon su cikin so da k'aunar su tana addu'ar Allah ya k'ara had'e mata kan yaran nata ya dawwamar
musu da farinciki.

Musaddiq ne ya cika sadeeq tare da kama kunnen shi kamar shi ne babba ya d'an murd'a tare da cewa
"sauran ka k'ara kuma "
Kama kunnen shi yayi tare da cewa "baxan k'ara ba ma brother wannan ma tsautsayi ne "

"Allah ya kyauta kullum ku dunga wasa kamar wasu k'ananan yara kun k'i fito da matar aure "
Cewar daddyn su yana sakkowa daga kan stairs yana dariya da sauri suka K'arasa wajen shi tare da
rungume shi suka bashi peck a kumatun shi ,mumy kuwa cewa tayi "ae kai ne kake shagwa6a su shi yasa
suka kasa fitar da matar aure "

Cikin shagwa6a musaddiq yace " ni har yanxu am a very young nake sai dai Yah sadeeq ".

Shi kuwa Yah sadeeq cewa yayi "ni daddy na samu Matar aure wlh"
Cikin jin dad'i Mumy da daddy suka ce "da gaske sadeeq? "
Har suna had'a baki wajen fad'i cikin murmishi sadeeq yace "Allah da gaske jiya partyn da muka je na
Omar anan naga yarinyar "
Kama hannun shi mumy tayi sannan tace "Yawwa hka nake son ji a ina take ya sunan ta kuma? "

"Kaiii mumy wad'annan tambayoyin hka " Cewar daddy yana dariya don yasan yanda ta damu k'warai da
k'in tsayar da matar aure da sadeeq yak'i.

"uhm uhm da xafi xafi ake dukan karfe dear " Cewar mumy kenan sannan ta cigaba da cewa "sadeeq
fad'a min "
Cikin murmishi sadeeq yace "Mumy kanwar Omar ce mufidah"

Dummmm gaban musaddiq yayi mummunar fad'uwa lokaci d'aya...............





Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*



*written by*

Aishat A muh'd


♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*

_Wannan page d'in sadaukar wa gare ku admins din exclusive writers Ummiey xeey,Amnoor, neena cool,
Aunty haliloss, nafisat anka, ruksad, Aishan umma and aunty Queen mermue, dukkanin ku ina muku
fatan alkhairi Allah ya k'ara basirah ya k'ara mana had'in kai Ameeen i really luv u guys_❤



*Page 6*





Saboda tsananin 6acin rai a fusace yayo kan mufidah kamar wani mayunwacin xaki jikin shi har rawa
yake, tuni mufidah ta fara ja da baya tana da nasanin abin da ta aikata mishi ga wani uban tsoro da ya
lullu6e ta lokaci d'aya.

Kafin ta ankara ta ganshi a gaban ta cikin tsananin 6acin rai ya d'aga hannu ya wanka mata mari a fuska
marin da yayi matuk'ar gigita mufidah, hannun ya kamo ya murd'e shi er k'ara ta saki saboda axaba Kafin
kuma yace "yanda kika 6ata kayan nan wlh sai kin wanke su "

Yana gama fad'in hka yaja mufidah har cikin mota ya cilla ta ciki da k'arfi har sai da ta buge nan ya shiga
ya ja motar a fusace duk mufidah ta gama tsorata jikin ta har 6ari yake tayi da nasani yafi sau ba iyaka
gashi batasan inda xai kai ta ba ga mangarib tayi addu'a ta dunga yi Allah ya ku6utar da ita daga hannun
shi ko kwakwkwaran motsi ta kasa yi saboda firgici.


Wata unguwa ce mai Kyan gaske suka shiga yanayin unguwar mai kyau ko'ina tsaf dashi ga haske ta ko'ina
kamar duhu bai yi ba gashi babu yawaitar mutane sosai, a gaban wani kyakkyawan gida flat house ya
danna horn tuni mai gadi ya bud'e kofar gate di'n nan ya shige da motar shi har xuwa wurin da ake

parking sannan ya fito ya bud'e kofar 6angaren da mufidah take ya fisgo ta sannan yaja ta xuwa cikin
gidan.

Gaskia gidan ba k'aramin had'uwa yayi ba kamar da mutane a ciki komai na more rayuwa akwai a gidan
musaddiq ya siya gidan ba don komai ba sai hutawa idan yayi ra'ayi don sai yafi 2 weeks bai xo ba gashi
ko'ina tsaf dashi da yake akwai masu gyara mishi gidan.

Suna shiga palon ya wurgar da mufidah har sai da ta sake bige wa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login