Showing 69001 words to 72000 words out of 92754 words

Chapter 24 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf

10 Jul 2025

3035

daga kanta ya mayar kan afnan .

Har ta k'arasa dining d'in xama tayi kusa da kujerar mumy ko kallon inda yake bata yi ba sai ma wani
had'e fuska take abin ma sai ya kusan bashi dariya ganin yanda take cika tana batsewa.


A sace yake jifan ta da wani kallo wanda tsakanin mumy da mufidah ba wanda ya ankara da hkan har
suka kammala cin abincin, mufidah ce ta tattare abin da suka yi amfani dashi gyara dining d'in sannan ta
wuce kitchen.

Har ta fara wanke kwanukan da suka 6ata ne sai rigar jikin ta ya fara tak'ura mata Co's bata Saba da yin
aiki da irin rigar ba sai kawai ta cire ta tare da ajiye ta saman cabinet d'in daga gefe ta cigaba da abin da
take hankali kwance.


Musaddiq wanda hankalin shi yayi kitchen inda mufidah take sai kawai ya mik'e tsaye yana cewa
"mumy bari na d'auko ruwa a kitchen "
Yana gama fad'in hka yayi gaba da d'an saurin shi, yayin da mumy ta bishi da kallo tana murmishi tare da
girgixa kai tun xuwan shi ta gama karantar shi yanda yake rawar jiki da irin kallon da yake bin ta dashi.

Yana shiga kitchen d'in ya jingina bayan shi jikin bangon kitchen d'in ya hard'e hannun shi a kirjin shi yana
aikin kallon ta jin shi yake kamar yaje ya rungume ta a cikin jikin shi ko ya samu relief acikin xuciyar shi da
gangar jikin shi, sai da ya kalle ta son ranshi ya more kafin kuma ya bud'e bakin shi yace
"sannu da aiki malama idan kin gama ina buk'atar gyaran bedroom d'ina da bathroom "

Kunnen uwar shegu mufidah tayi dashi ko jiyo wa ba tayi aikin da take ta cigaba kamar batasan da wani
mutum a kitchen d'in ba, ganin hkan da musaddiq yayi ne ya sanya shi nufar inda take tare da sanya
hannu ya janyo jelar gashin kanta wata er k'arar axaba ta saki tare da runtse idon ta tace
"malam lafiar ka qlau ne da xaka ja min gashi "
Ta k'arasa fad'in hka tana kici kicin kwatar gashin ta da ya rik'e, sai kawai ya janyo ta cikin jikin shi lokaci
d'aya ya saki ajiyar xuciya daman abin da yake buk'atar yi kenan shi yasa ya dad'a tsokano ta.

D'aure fuska yayi tare da cewa "ke kina jin ina miki magana ki rabu da ni saboda kin raina ni koh ?"

"ni malam ka cika ni idan ba hka ba xan..... "
Bata k'arasa fad'in maganar ba ya sanya hannun shi ya rufe bakin ta tare da cewa
"me xaki iya yarinya ji yanda kin kasa kwatar kan ki kina wani ma......."

Wata er k'ara ya saki kad'an wadda ta hana shi k'arasa maganar shi ashe mufidah ce ta cije shi a hannun
ba shiri ya sake ta kafin yayi wani yunk'urin rik'e ta har ta fice daga kitchen d'in da gudu..............




Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*

*Written by*
Aishat A Muh'd

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM

LIKE AND COMMENT'S FB PAGE
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/


*PAGE 48*



Wani kyakkyawan murmishi ya saki tare da bin hannun nashi da kallo wurin da ta cije shi har wajen ya
d'an yi ja, bakin shi ya kai a hankali ya sumbace shi kafin ya fita daga kitchen d'in.


Suna xaune da dare a parlour kallo suke jefa jefa mumy da musaddiq suna er hirar su yayin da mufidah
kuma ta fara gyangyad'in bacci a wurin saboda gajiyar da tayi afnan ma tana jikin musaddiq tana bacci.

"mufidah tashi ki tafi bedroom ki kwanta "
Cewar mumy da ta kula da gyangyad'in da take, ai kuwa da sauri ta d'an mik'e ta wuce xuwa bedroom
musaddiq ya bi ta da kallo cikin tsantsar kaunar ta.

Maganar da mumy tayi mishi ita ta dawo dashi daga tunanin da ya tafi tana mai cewa
"musaddiq na gaji da maganar da nake maka don ka xo ka d'auki mufidah kak'i tsayawa kana yi wa
mutane hanya hanya, dalilin da yasa ni da daddyn ka muka yanke hukuncin kawo maka ita nan, Sauran

kuma k'i kula dasu yanda ya kamata ga amanar su nan na baka kada ka wulak'anta min 'ya kaji na fad'a
maka "

D'an murmishi ya saki cikin xuciyar shi yana cewa mumy dan bakisan irin son da nake yiwa mufidah ba
shi yasa kike fad'in hka, na tabbatar da kinsan irin yawan son da nake mata da baxa ki fad'i hka ba, baxan
iya wulak'anta mufidah ba ko wani ne naga xai wulak'anta min ita sai inda k'arfi na ya k'are bare ni, a fili
kuma sai yace
"mumy ki kwantar da hankalin ki kada ki damu xan yi duk yanda kike ce "

"Yawwa Alhmdlh naji dad'i da ka fad'i hkan, Allah yayi muku albarka ya baku xaman lafia"

"Ameeen thumma Ameeen mumyn na "

Murmishi mumy ta saki na jin dad'in ganin d'an nata hankalin shi ya kwanta gashi har er k'iba ya d'an yi
alamun ya samu kwanciyar hankali da nutsuwa.

"sannan kuma kayi kok'arin sanya afnan a skul "
"angama mumy na "
Sun d'an jima suna hira kafin kuma kowannen su ya tafi d'aki don yin bacci tun da dare yayi.

Ranar musaddiq yayi kwanan farinciki da jin dad'i tun da ga mufidahn shi a cikin gidan, yana son mufidah
so irin wanda ba'a iya kwatan tashi so irin wanda baki baxai iya furta shi ba so irin wanda idan ya kama
xuciyar mutum baya ta6a iya yi mishi ta sauk'i kai so so ne irin wanda kafin a samu mutum mai irin
wannan son akan mace acikin dubban jama'a sai en k'alilan, da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da
shi cike da mafarkan mufidah da shi masu dad'i wanda har bai so gari ya waye ba dama xai dawwama a
irin hka da yayi farinciki mara misaltuwa.

A hka mumy tayi kwanaki ukun ta, ranar da xata tafi ne da safe suka fita dukkanin su domin raka mumy
yin siyayya a mall, da yake jirgin su tashin yammaci xai yi don hka suna gama breakfast suka fito.

A wani babban mall suka yi masauki nan mumy ta fara siyayyan abin da take buk'ata, shi kuma musaddiq
ya nufi 6angaren wajen sleeping dress dasu underwears xuwa English wears yana xa6ar duk wanda yayi
mishi.

Mufidah kuma da afnan suna tare da mumy suna xa6ar abin da suke so, sam mufidah batasan musaddiq
ya nufi 6angaren wajen English wears ba sai ta nufi nan tana d'an dudduba wa, kamar ance ta d'ago
kanta ai kuwa tayi mummunan gani da idanun ta, wanda lokaci d'aya wani axababben kishi ya turnik'e
mufidah lokacin da ta hango musaddiq rungume da wata mace baturiya a jikin shi.

Gaba d'aya sai ta rasa abin yi har wani duhu duhu take gani a idanun ta sam ta kasa dauke idanun ta daga
kansu wani bakinciki da takaici ne ya kama mufidah, d'ago idanun shi yayi musaddiq ya hango mufidah a
tsaye waje d'aya kamar wadda aka dasa ta, hannun shi yasa ya janye yarinyar gefe d'aya kafin yayi mata
magana ta tsayin second biyar ya nufo inda mufidah take.

Ganin har yaxo inda take batasan ma yaxo wajen ba yasa shi yin tafi da hannun shi biyu a dai dai fuskar ta
tare da cewa
"hey are u alright? "
Yana wani shegen murmishi mai da idanun ta tayi kan fuskar shi ai kuwa ya kashe mata ido d'aya tare da
d'aga gira, wani bak'in ciki da 6acin rai ne ya sake kama mufidah ganin ko ajikin shi abin da ta kamashi
yana yi, ta ma kasa cewa komai ji tayi ya kama hannun ta da hannun shi ai kuwa ta fisge da k'arfi tayi
gaba yana yi mata magana amman ko jiyo wa ba tayi ba, wani d'an sanyi yaji cikin xuciyar shi idan dai har
hasashen da yayi hka ne to mufidah ta fara son shi tun da abin da ta nuna yanxu yayi alama da kishi, juya
wa yayi ya d'auko kayan da ya gama xa6a ya nufo inda su mumy suke.

Waje d'aya mufidah ta samu ta xauna har mumy ta gama siyan abin da take so musaddiq ya biya kudin
suka fito, ko kallon inda yake mufidah bata yi ba fuskar ta tayi d'an ja saboda 6acin rai har mumy tana
tambayar ta lafia kawai sai ta d'an wayance da fad'in kan ta ne yake ciwo sai sannu mumy take mata har
suka k'arasa gida.

Cikin bedroom ta shige ta fad'a toilet ta rufe da key kafin ta kunna shower ruwa ya fara xuba sannan ta
fashe da kuka sosai tayi hkan ne don kada a jiyo sautin kukan ta, bata ta6a xaton son musaddiq yayi k'arfi

hka a cikin xuciyar ta ba sai yau bata ta6a xaton tana da mugun kishi ba sai yau, taji ana fad'ar kishi
amman batasan shi ba sai yau, daman hka musaddiq d'in yake d'an iska ne ma nemin mata, to idan ba
ma nemin mata ba mai ya kai shi rungume macen da ba matar shi ba a jikin shi daman abin da yake
aikata wa kenan shi yasa ya mak'ale a k'asar waje yak'i dawowa nigeria, ae kuwa baxan iya xama da
maxinaci ba dole ya sake ni naje na auri kamilin namiji kamar sadeeq.

Sadeeq baka San halin d'an uwan ka ba ne shi yasa kabar wasiyyar na aure shi me yasa kayi min hka
sadeeq ina da kishi baxan iya xama da musaddiq ba, gashi son shi yayi min mugun kamun da ban ankara
ba sai da lokaci ya fara k'ure min, tayi kuka sosai mufidah a wannan lokacin abin tausayi gashi sai
knocking ake yi a kofar toilet d'in wanda ta sani tsakanin mumy da afnan ne suke yi.

Kan ta ne ya fara wani irin ciwo ga idon ta sun kumbura sosai sun ja dakyar ta iya yin wanka ta sanya wata
white d'in rigar wanka kan ta kuma wani k'aramin towel ne ta nannad'e gashin ta, tsayin rigar wankan iya
cinyar ta ya tsaya da hka ta bud'e kofar toilet d'in ta fito, d'ago kan da xata yi ta had'a ido da musaddiq a
tsaye bakin kofar toilet d'in ya hard'e hannun shi a kirjin shi ya tsurawa kofar toilet d'in ido yana tunani,
ganin ta fito ne yasa shi sakin wata ajiyar xuciya tare da cewa

"lafian ki qlau kika shiga toilet kika rufe wajen 1:30 hour kina ciki? "
Wata harara ta dank'ara mishi da idanun ta jawur da suka kumbura, tuni musaddiq ya rikice ya nufi inda
take yana cewa

"subhanallah mufidah mai ya sami idanun ki hka? "
Hannun ta ya sake rik'o wa saboda ganin tak'i kula shi ae kuwa ta sanya k'arfin ta ta sake fisgewa cikin
dushashshiyar muryar ta tace
"malam ka rabu da ni ina ruwan ka da abin da yake damuna? "

Tana gama fad'in hka ta juya xata cigaba da tafiya ai kuwa ya janyo ta jikin shi ya sanya d'aya hannun shi
ta bayan ta ya rik'e ta gam, d'aya hannun kuma ya rik'o fuskar ta 6ata fuskar shi tare da cewa
"ba dai don kin ganni da wata ba ne kika shiga toilet kina kuka, kin fara sona kenan? idan hka ne kuwa ki
bawa xuciyar ki shawara ta fitar da sona daga ciki idan kuwa ba hka ba xaki cutar da kanki, don ni
musaddiq ba sa'an auren ki ba ne na aure ki ne don cika burin d'an uwa na sadeeq"

Yana gama fad'in hka ya cika ta ya fice daga bedroom d'in, kusan suman tsaye mufidah tayi da jin abin da
musaddiq ya furta mata daman ba sona yake ba?, xuciya ta mai yasa kika yi min hka, kika kar6i son
mutumin da baya sona, wasu hawaye ne masu xafi suke fita daga idanun mufidah.


Shi kuma musaddiq bedroom d'in shi ya wuce tare da rufe kofar ya jingina bayan shi jikin kofar wasu
hawaye ne masu rad'ad'i suka fara xubo mishi dafe kan shi yayi yana cewa
"me... me yasa baki na ka furta wannan furucin wajen masoyiya ta, kamata yayi nayi farinciki mufidah ta
fara sona bai kamata nayi mata hka ba, yanxu ta ina xan gyara kuskure na, na rasa yanda akayi na fad'a
mata hka nasan xuciya ta da kwakwalwa ta ba hka suke son na furta ba, baki na ne ya furta hkan, I'm so
sorry mufidah, ta ina xan fara nuna miki soyayya ta bayan ke matar d'an uwa na ne baxan iya ba baxan
iya mufidah ji nake kamar xan ci amanar sadeeq"

Hka ya dunga maganganu cikin mayen son mufidah har xuwa lokacin da bacci ya dauke shi a k'asan
carpet d'in d'akin.

Yinin ranar kusan mumy ce da afnan suka yi shi a parlour musaddiq yana bedroom hka mufidah ma har
xuwa karfe 5 na yammacin ranar tuni mumy ta gama had'a komai nata ta xaunar da mufidah da
musaddiq tana sake yi musu nasiha sosai wanda kowannen su baya kallon d'an uwan shi kansu a sunkuye
suna kallon k'asa.

Bayan ta gama yi musu nasihar ne suka fita rakata airport, tun da suka fara tafia mufidah idanun ta suna
kan window tana xubar da hawayen bak'in ciki abin da musaddiq ya gama yi mata d'axu gashi mumy xata
tafi ta bar su, da hka suka k'arasa airport d'in mumy dai bakin ta bai daina furta musu wad'annan
kalaman ba

"kuyi hak'uri da junan ku don Allah ku xauna lafia ban da fad'a da tashi hankali ana yin hak'uri ana kai
xuciya nesa, mmusaddiq ga mufidah da afnan nan ka rik'e su amana don su amanar d'an uwan ka ne, ka
kula su don kai ne babba kuma namiji a cikin su "

Lokacin da mumy xata shiga jirgi mufidah kasa jure wa tayi ta rungume mumy tana kuka sosai ita ma
mumyn kasa rik'e hawayen ta tayi sai da suka fito afnan ma kukan take ganin yanda mumy da mameen ta
suke kuka musaddiq ya dauke ta yana rarrashin ta, dakyar mufidah ta cika mumy ta wuce xuwa cikin jirgi

ko k'ara waiwaye su ba tayi saboda kada su karyar mata da gwiwa, suna kallo har aka rufe jirgin ya fara
tafia kafin ya tashi sama kuma da gudu mufidah ta shige cikin mota tana kuka..............



Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*


*Written by*
Aishat A Muh'd

♻£xclusive writers forum

Like and comment's fb page
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/


*PAGE 49*




shima musaddiq jikin shi a sanyaye ya shiga motar ya fara driven, sai da ya tsaya a hanya yayi musu
takeaway na abincin da xasu ci da dare tukunna suka nufi gida,yana gama parking mufidah ta fito ta shige
ciki kai tsaye bedroom ta wuce ta xube kan bed tun tana kukan har bacci ya sace ta tana faman ajiyar
xuciya.

Lokacin da musaddiq ya shigo d'akin ya dad'e yana kallon ta kafin ya kwantar da afnan a gefen ta wadda
ita ma tayi bacci, shima nashi bedroom d'in ya nufa ya kwanta duk jin shi yake wani iri gidan ko kad'an bai
yi mishi dad'i ba a hka shima bacci yayi awon gaba da shi.


Firgigit mufidah ta tashi da addu'ar tashi daga bacci a bakin ta bin d'akin take da kallo kamar wadda yau
ta ta6a ganin shi, duhu yayi sosai duk da kuwa hasken bulb d'in da ya haske d'akin kuwa.

A hankali ta sauko da kafafun ta toilet ta wuce wanka da alwala ta d'aura ta fito wata jallabia irin ta mata
ta sanya tare da hijab tayi sallahr mangarib da ishsha kafin ta d'ora da Shafa'i da wutri ta dad'e xaune
tana addu'o'in ta kafin ta mik'e ta canja kayan jikin ta da na bacci.

Tana kok'arin sake kwanciya ne musaddiq ya shigo had'a ido suka yi kowanne ya d'aure fuska tare da
kawar da kanshi daga had'a idon da suka yi bud'e baki yayi yace

"ki fito abincin ki yana dining table"
Dakyar ta iya bud'e baki tace
"bana buk'atar shi "
D'aga kafad'un shi yayi tare da cewa
"alright hkan yayi kyau "
Yana gama fad'in hka ya fita daga d'akin mufidah ta bishi da kallo yau ko irin tsokanar nan babu, yau a
musaddiq d'in shi yake kamar yanda ta san shi tsawon wasu shekaru da suka shud'e, wani hawaye ne ya
xubo ta tana mai tausayin kanta, a hka ta kwana bata ci abincin ba, hkan kuwa ba k'aramin damun
musaddiq yayi ba har shima ya kasa cin abincin ya kwanta.


Tsawon kwanaki biyar da komawar mumy nigeria wadda ta je gida lafia, tsakanin musaddiq da mufidah
babu mai kula wani kowa rayuwar shi yake shi d'aya, gashi ya sanya afnan a skul.

Idan ya tafi hospital afnan ta tafi skul sai ita d'aya a gida duk bata jin dad'in xaman ko irin fita hka ba tayi
duk kad'aici ya ishe ta, ai kuwa yau Bayan musaddiq ya fita hospital ne ta yanke hukuncin fita ko da iya
layin da suke ne ta d'an wasa kafafun ta, tana sanye cikin wata gown milk colour tayi rolling kanta da
green veil mai d'an haske flat shoes ne a k'afar ta sai phone nata a hannu da hka ta fito tana kallon
yanayin unguwar da yayi matuk'ar birge ta.

Ita kad'ai take murmishi sai kalle kalle take hankalin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login