Showing 33001 words to 36000 words out of 92754 words

Chapter 12 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf

10 Jul 2025

3048

shi Doctor da kaina idan ya tashi"

"Yawwa kin kyauta"

Daga hka suka yi sallama ya tafi, mufidah ta xube kan kujera tare da xabga tagumi tana tunani, ta d'an
jima da hka kafin taji cikin ta yana murd'a wa atake ta fahimta yunwa take ji.

Kitchen ta shiga ta had'a tea a cup ta sha sannan ta dawo d'akin har yanxu sadeeq bacci yake kallo d'aya
xaka yi mishi kasan ba k'aramin wahala ya sha ba duk ya dad'a rame wa, xama tayi kusa dashi ta rik'e
mishi hannun shi tana murxawa a hankali.

Sai after la'asar sadeeq ya farka da mufidah ya fara had'a ido murmishi suka sakarwa junan shi cikin jin
dad'i mufidah tace
"Sannu sadeeq ya kake jin jiki"

Murmishin yak'e ya saki don shi kadai yasan abin da yake ji a jikin shi, hannun ta ya rik'o tare da cewa
"My wife kwantar da hankalin ki, jiki na da sauk'i ya lafiyar baby na dafatan kin bashi kulawa?"

Da kai tayi mishi alamar ehhh, taimaka mishi tayi yayi wanka ko abinci ya kasa ci sai coffee yasha tukunna
suka tafi hospital, mufidah ce take driving sadeeq na gefen ta hannun shi d'aya dafe da cikin shi ya
lumshe ido, da hka har suka k'arasa asibitin bayan mufidah tayi parking ne ta fito tare da bud'e wa
sadeeq kofar motar ita ta taimaka shi ya fito tukunna ta rufe motar.


Tana rik'e dashi suka k'arasa cikin asibitin kai tsaye office d'in muh'd suka nufa sai da mufidah tayi
knocking, muh'd dake xaune kan kujera yace

"Yes come in"
Nan mufidah ta tura kofa suka shigo ganin sune yasa muh'd mik'e wa da sauri ya taimaka wa sadeeq ya
xauna tukunna ita ma ta xauna
"Babban yaya ya jikin na ka?"
Cikin yak'e sadeeq yace " jiki da sauk'i muh'd"

Nan babu 6ata lokaci Dr muh'd da wani likitan daban suka shigar da sadeeq room d'in scanning mufidah
tana xaune a gefen shi da yake kwance hannun ta cikin nashi suna kallon komai da ake ta jikin nau'orar
computer d'in.


Sun d'auke tsawon mintuna arba'in xuwa hamsin suna scanning d'in, bayan sun gama suka koma
6angaren yin test d'in urine test da blood test har xuwa lokacin da aka kammala had'a result gaba d'aya.

Lokacin da Dr muh'd ya duba dukka result d'in sai da wani gumi ya yanko mishi sakamakon ganin abin da
yake damun sadeeq, tuni idanun shi sun yi ja kamar xai yi kuka hankalin shi yayi matuk'ar tashi yana
tunanin ta yanda xai sanar da su wannan hargitsatsan labarin.



Sam ya kasa d'aga kanshi ya kalli sadeeq da mufidah, ganin yanda ya koma yasa sadeeq yin murmishi
yace

"Muh'd lafia kuwa, me ke faruwa tell me please?"

Cikin wani irin yanayi ya xuba wa sadeeq ido, gaba d'aya mufidah ta gama tsorata jikin ta har rawa yake,
shi kuwa sadeeq cikin shi ne ya cigaba da yi mishi ciwo sosai amman sai ya daure yace

"Nasan ciwo na ne yayi worst da yawa ko?"
Da sauri muh'd ya d'ago kanshi ya kalle shi cikin mamakin abin da yace,lumshe ido yayi tare da cije le6en
shi saboda yanda cikin shi yake mishi ciwo sai da ya d'an lafa sannan ya kamo hannun mufidah ya rik'e shi
gam tare da cewa

"Kiyi hak'uri my wife na rufe miki bansanar dake wani abu ba, wanda bana son tashin hankalin ki shi
yasa"

Kallon Dr muh'd yayi tare da jiyo wa ya cigaba da kallon mufidah wadda gaba d'aya hankalin ta Yayi
masifar tashi jin abin da sadeeq yake fad'a.

"Ba wani abu na rufe miki ba my wife ina da ciwon hanta tun kafin na aure ki, na kasance ina yawan fama
da ciwon ciki sosai ganin hka sai na yanke shawarar xuwa ganin likita a k'asar london anan yake fad'a min
ciwon hanta ne ya kama ni har sai da suka yi min aiki a can"

Gaba d'aya kallon shi suke da idanun su da ya firfito na tsabar kidima, duniyar tunani mufidah ta fad'a
don akwai wani lokaci da tana xaune gefen bed ya fito daga wanka d'aure da towel tana cikin shirya shi
taga wani siririn yanka a gefen sam bai yi kama da operation ba a gefen cikin shi har tana tambayar shi
mene wannan sai yake fad'a mata yana k'arami ne ya ta6a jin ciwo awajen.


Maganar da sadeeq ya cigaba da yi ita ta dawo daga duniyar tunanin da ta fad'a ya cigaba da cewa " ban
fad'a wa su mumy da daddy ba saboda kada su d'aga hankalin su su shiga damuwa balle uwa uba d'an
uwana rabin jiki musaddiq bana jure ganin shi cikin damuwa shi yasa na 6oye musu, sauran kad'an
musaddiq ya gane don ya kamani da magungunan sai na wayance da na aboki nane dak'yar ya yarda da
hkan don har yaso dubani na nuna mishi 6acin raina shine ya hak'ura, bayan na warke na cigaba da xuwa
ganin likita ina kar6ar magani daga k'arshe da naga na samu sauk'i sai na watsar da xuwa ganin likitan
kwata kwata, sai k'wanan na fara jin ciwon ya dawo min amman na kasa tafia ganin doctor saboda bana
so nayi nesa da mufidah"

K'ara rik'o hannun mufidah yayi cikin sanyin murya ya cigaba da cewa " kiyi hak'uri my wife tashin
hankalin kune bana so shi yasa ban fad'a muku ba, ki yafe min don Allah"

Wani kukan tausayin sadeeq ya kamata ta fad'a jikin shi tare da sakin kuka mai ban tausayi, hak'uri da
rarrashin ta sadeeq kawai yake.

Dr muh'd kuwa hawaye ne kawai suke xuba a idanun shi, yanxu ta ina xai fara fad'a wa su mumy labarin
nan dukka 'ya'yasu biyu Allah ya basu a duniya kowannen su Allah ya jarabce shi da babban ciwo,
musaddiq ciwon xuciya sadeeq kuma ciwon hanta ciwon da ya gama cin k'arfin shi sosai ta ina xai fara,
hawaye kawai yake yi yana kallon sadeeq kanshi na wani irin juyawa.

Dak'yar sadeeq ya rarrashi mufidah tayi shiru amman still tana jikin shi sai faman ajiyar xuciya take sauke
wa, kallon muh'd d'in sadeeq yayi ganin ya xuba mishi ido yana kallon shi ga hawayen da yake yasa shi
sakin murmishi tare da cewa
"Haba muh'd ae ba kuka ya kamata kayi ba, sanar da ni naje last stage koh?"

Wasu hawaye masu d'umi suka fara xuba cigaba da xuba a idanun muh'd, shima sadeeq d'in dauriya
kawai yake ga ciwo yana jin shi sosai ga tashin hankalin shi mufidan shi cikin damuwa.

Sun dad'e a hka kafin muh'd ya bud'e bakin shi cikin rawar murya yace
"I'm sorry to say babban yaya gaskia ciwon ka ya kai matakin k'arsh......"
Kasa k'arasa fad'a yayi saboda kukan da ya kubce mishi, mufidah ma sai ta fashe da kuka ganin likita guda
yana gurxar kuka ya had'a kai da table d'in dake gaban shi.

Dafa mishi kafad'a sadeeq yayi tare da cewa " be a man haba muh'd kamar ba likita ba, ni daman jiki
yana bani baxan yi tsawon rai ba don ni kadai nasan me nake ji ina rok'on Allah kafin na mutu naga d'an
da mufidah xata haifa min wannan shi kad'ai ne buri na"






Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*

*Written by*

Aishat A muh'd

♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM



_this page dedicated to my lvly friend's nafisat anka dear, sardy bash dear, billy ladan dear, ina matuk'ar
alfahari da ku sister's, Allah ya k'ara muku lafia, Allah ya bar xumunci ina muku fatan alkhairi a duk inda
kuke_❤




*PAGE 25*




Haka rayuwa ta cigaba da tafia suna renon cikin su cikin kwanciyar hankali, wanda watannin shi
bakwai da en kwanaki ya girma sosai, sadeeq dasu mumy suna matuk'ar ji da wannan babyn da bai xo
duniya ba tukunna,ko da yaushe cikin yiwa mufidah addu'ar sauka lafia suke mata.


Duk wannan abin da ake ciki ba wanda ya fad'a wa musaddiq, sam baisan mufidah tans da ciki ba,
sadeeq bai fad'a mishi ba hka ma mumy saboda tana tsoron halin da d'anta xai shiga idan yaji labari shi
yasa ta ja bakin ta tayi shiru duk kuwa da wayar da suke yi kusan ko dayaushe.

Yau garin ya kasance cikin wani yanayi mai dad'in gaske sakamakon ruwan da aka dunga yi tun after
isha'e, garin ya d'auki sanyi sosai irin wannan yanayin ne yawancin xaka samu mutane sun yi bacci da
wuri, hka ta faru dasu mufidah da sadeeq su ma tun wurin 10 na dare suka kwanta bacci sun k'udundune
cikin blanket saboda sanyin garin.




Can wurin 2 na dare sadeeq ya tashi tare da xama saman bed yana kallon mufidah wadda take baccin ta
cikin kwanciyar hankali, ido ya xuba mata yana kallon ta sam ya rasa abin da yake damun shi a cikin
wad'annan kwanaki, jikin shi ya bashi akwai wani abu da xai faru but bai san kome ne ba.


Kallon mufidah kawai yake tare da sanya hannun shi kan cikin ta yana shafa babyn shi, lokaci d'aya kuma
wasu hawaye masu xafin gaske suka fara xuba daga idanun shi, wanda ya rasa hawayen mene, ya dad'e a
hka sosai duk idanun shi sun yi ja kan shi ya d'auki wani irin ciwo, tashi yayi dak'yar ya shige bathroom
alwala ya d'aura tare da fitowa praying mat ya shimfid'a ya fara nafila after ya gama sai ya fara yin
addu'o'i na neman gafarar ubangiji akan ya yafe mishi xunuban shi tare da addu'ar Allah ya sauki mufidah
lafia.


Bai tashi daga nan ba sai da yaji kiran sallahr asuba, sai da yayi raka'atul fijir sannan ya tashi mufidah ya
tafi masallaci jikin shi gaba d'aya ba k'arfi haka yake ji.

Tun da ya dawo daga masallaci wani bacci ne ya d'auke shi mai dad'i, har mufidah ta kammala had'a
breakfast ta gyara ko'ina tayi wanka amman bai tashi ba, xama tayi a palour tare da fad'a wa tunani tana
mai mamakin yanda sadeeq ya koma.


Gaba d'aya ya canja mata,na farko ya sake mata wani irin kyau da kwarjini na biyu kuma gaba d'aya yayi
sanyi sosai duk da sadeeq daman akwai shi da sanyi but na yanxu yafi na da, tana yawan farka wa a bacci
ta ganshi yana kallon ta ko yana shafa mata ciki, magana yanxu bata dame shi ba abinci ma baya iya ci
sosai.

Abin yana d'aure mata kai tare da damunta, tayi mishi tambaya ko wani abin yana damun shi sai yace ba
komai, k'arshe idan ta dame shi da tambaya sai ya fara neman gafarar ta tare da sako xancen mutuwa
nan sai ta fara kuka sai kuma ya hau rarrashin ta, wani lokacin kuma sai ya xuba mata ido yana kallon ta
duk inda tayi akan idanun shi duk sai tabi ta tsargu.



K'arar wayar ta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta fad'a, hannu tasa ta goge hawayen da suka
xubo mata sannan ta dauki wayar umman tace bayan sun gaisa tare da yin hira ta tsawon mintuna 15 ne
ta ajiye wayar tare da kallon agogo taga har 10:30 tayi sadeeq bai fito ba gashi kuma yau akwai aiki, tashi
tayi tare da nufar bedroom d'in shi.


Tura kofar tayi tare da shigo wa lokaci d'aya mufidah ta xaro ido tare da furta "sadeeq!"
Da k'arfi tukunna ta k'arasa wajen da yake kwance akan bed yana murkususu kamar macen da take
nakuda, cikin sauri ta hau kan bed din tare da janyo shi jikin ta tana jijjiga shi cikin kuka tana cewa
"Sadeeq me yake damun ka, tashi ka fad'a min please?"

Ya bud'e baki xai yi magana amman ya kasa, sai wasu hawaye masu xafi da suke xubo mishi, cikin gigice
wa da firgita mufidah ta yunk'ura xata tashi don taje ta fad'a wa su mumy amman sai ya rik'e ta k'am

yana yi mata wani irin kallo wanda ya tsurar da mufidah ta kusan fara nakudar tashin hankali saboda
yanda taji d'an cikin ta ya wani irin juyawa lokaci d'aya marar ta ta d'auki ciwo.

Cikin wata murya taji sadeeq ya bud'e baki dak'yar yace
" my wife kada ki sanar dasu mumy hankalin su xai tashi, ciki na ne yake ciwo ki kira min muh'd ya duba
ni"

Cikin sauri jiki na rawa mufidah ta d'auki wayar shi ta lalibo number d'in muh'd sai da ta kirawo shi sau
biyu bai d'auka ba sai ana ukun ya d'auka yana cewa
"Sorry babban yaya ina room's d'in patients ina duba....... "
Kafin ya k'arasa fad'i yaji muryar mufidah cikin kuka tana cewa " muh'd don Allah kayi sauri ka xo sadeeq
bashi da lafia"
Cikin tashin hankali yace " me ya same shi?"
"Ni dai kayi sauri kaxo please ina tsoro"
Ta k'arasa fad'i tana shashshak'ar kuka, da sauri yace
" kiyi hak'uri mufidah gani nan xuwa yanxu"

Yana gama fad'in hka ya katse wayar hankalin shi a tashe ya shiga mota ya taho, yayin da mufidah kuma
ta cigaba da kuka sosae ganin yanda sadeeq yake shan wahala, lokaci d'aya ya fara jan wani irin numfashi
da ya k'ara rud'a mufidah..............





Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*

*Written by*

Aishat A muh'd

♻ E.W.F




*PAGE 27*





Da k'arfi mufidah ta tashi tare da fad'in "stop it sadeeq"
Kafin kuma ta rushe da wani irin kuka ta xube k'asa tare da rik'e kafafun shi tana cewa
"Baxa ka mutu ba sadeeq xamu rayu tare da kai har abadan, xan haifa maka yaran da kake so da yawa ka
cika wa su mumy burin su na ganin jikoko da yawa xan mutu sadeeq idan ka mutu ina son ka baxan iya
rayuwa ba kai ba"

Kamo ta yayi tare da xaunar da ita shima idanun shi duk sun ciko da hawaye cikin muryar rarrashi sadeeq
yace

"Kiyi hak'uri mufidah mutuwa tana kan kowa idan lokacin ta yayi ni nasan ciwon nan bana tashi ba n....."

Kafin ya k'arasa fad'i mufidah ta damk'e bakin shi cikin kuka tana girgixa kai tace "kayi shiru sadeeq don
Allah na rok'e ka wadannan maganganun suna rikita ni hankali na yana tashi sosai"

Cikin Murmishin yak'e yace "okay shikenan na bari my wife"

Kallon shi take ko kifta idanun ta ba tayi tana ganin idan ta kifta idon ta kafin ta bud'e sadeeq ya mutu,
don sai yanxu taji wani masifaffan son sadeeq yana ratsa jijiya da xuciyar jikin ta batasan tana mishi
wannan son ba sai hka, shi kuwa Dr muh'd kasa k'arasa magana yayi sai ajiyar xuciyar da yake sauke wa
akai akai.


Suna cikin hka ciwon ciki ya dad'a tasar wa sadeeq irin yanda yake yi kamar numfashin shi xai d'auke tuni
suka rud'e kuka sosai mufidah take tana rik'e dashi.

Da gudu muh'd ya mik'e yaje ya kirawo wasu likitoci biyu suka d'auki sadeeq suka shigar dashi wani daki
da gudu mufidah taxo xata shiga but d'ayan likitan ya rufe kofa wata nurse ce ta janye mufidah xuwa cikin
office d'in Dr muh'd tana rarrashin ta don muh'd shi kasa ce mata komai yayi.

Dak'yar ta nutsu ta daina kukan ta kirawo mumy tana fad'a mata cikin kuka, a matuk'ar firgice mumy ta
taho asibitin bayan ta sanar da daddy shi ma.


Kusan tare suka shigo asibitin da mumy da daddy office d'in Dr muh'd suka tarar da mufidah tana shar6ar
kuka wiwi gaba d'aya sai suka dad'a tsurewa ganin yanda mufidah ta koma lokaci d'aya gaba d'aya ta fita
daga hayyacin ta, janyo ta jikin ta mumy tayi tana rarrashin ta duk da ita ma daurewa take, daddy kuwa
tagumi ya xabga shi kad'ai yasan yanda yake ji a cikin xuciyar shi.

Wajen awa biyu suka yi kan sadeeq tukunna ya fara dawowa cikin hayyacin shi yana numfashi da taimako
oxygen tube, special room suka kai shi tare da sanya mishi drip bacci yake saboda allurar da suka yi mishi
kallo d'aya xaka yi mishi ka tausaya mishi ya yi wani irin rame wa sosai.



Dak'yar muh'd ya iya yiwa su mumy bayanin halin da sadeeq yake ciki don mufida ta kasa magana, ba
k'aramin rud'e wa da gigice wa suka yi ba wad'annan bayin Allah, jagwab mumy ta xube kan kujera tana
kuka sosai daddy kuwa idanun shi ne suka yi ja sosai daurewa kawai yake yi saboda shine namiji mai
rarrashin mumy da mufidah don kuwa Dr muh'd gudu wa yayi daga office d'in don baxai iya cigaba da
kallon kayan tausayi ba don xuciyar shi xata iya buguwa.




Har dare yayi sadeeq bai farka ba daddy yace mumy da mufidah su koma gida shi xai k'wana dashi da Dr
muh'd, dak'yar ya shawo Kansu suka yarda, koda suka je gidan ko takan abinci basu nema ba, k'arshe
mufidah a bedroom d'in mumy ta k'wana ko runtsa wa basu yi ba sallah kawai suke suna nemar wa
sadeeq samun lafia, har gari ya waye babu wanda ya runtsa a cikin su, K'arfe bakwai suka yi gaggawar yin
wanka simple gown suka sa kamar had'in baki mufidah da mumy suka sanya hijab ko mai basu shafa ba
saboda tashin hankali.


Abincin da en aiki suka yi na breakfast suka d'auka tare da tafia hospital d'in, sai ganin su daddy Yayi
kawai sun shigo room, koma wa gida yayi daddy don ya samu yayi wanka shima.



Kamar yanda suka barshi hka suka dawo suka ganshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login