Showing 48001 words to 51000 words out of 92754 words
Chapter 17 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf
da ya wuce acikin rayuwar shi
komawar shi nigeria kuwa yana ganin mufidah hkan ba k'aramin dad'a taso mishi abin da ya shige xai yi
ba, kuma ya riga da ya sanya wa xuciyar shi hakurin rashin mufidah tun lokacin da Yah sadeeq ya aure ta
baya son ya dawo sai lokacin da ta samu miji tayi aure ta bar gidansu,shi yasa yake kauce wa xancen
mumy duk da yana kewar iyayen nashi da muh'd tare da afnan yarinya jin ta yake tamkar sadeeq d'in shi.
Wani irin son ta yake a cikin xuciyar shi irin son nan da ko d'an da haifa ba lallai yayi mishi irin wannan
son ba shi yasa kusan koyaushe cikin turo mata kayayyakin sawa da na wasa yana son ganin ta cikin
farinciki sosai kulawa sosai yake bata duk da basa kusa da juna kuwa.
Afnan ta xama 'yar gata gaba da baya kowanne 6angare cikin bata kulawa ake da nuna mata soyayya
sosai, afnan yarinyar akwai ta da hak'uri kamar mahaifin ta sadeeq ga fara'a.
Kamar yau rana ce ta week end mufidah bata da xuwa hospital tana kwance kan bed cikin bedroom d'in
ta baccin ta take cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ,da ganin yanda take baccin kasan ba k'aramin jin
dad'in shi take ba.
Afnan ce ta turo kofar bedroom d'in ta shigo tana sanye cikin wata pink gown iya gwiwar ta an gyara
mata gashin ta da ribbons pink and white colour.
D'ago kanta da tayi bansan lokacin da na furta subhanallah tabarakallahu ahsanin kaliqeen saboda tsabar
kama da sadeeq da tayi ,ja tayi ta tsaya ganin mufidah tana baccin ta ita da ta taxo don ta duba ta ga ta
shirya su tafi gidan umma.
Wani 'yar dariya ta saki a hankali tana toshe bakin ta don kada sautin dariyar ta ya tashi mufidah tace
"Tabbb mumy ma har yanxu bacci take bata tashi ba"
Ta k'arasa fad'in hka tana yatsina fuska kad'an , nufar kan bed din tayi ta hau tare da sanya d'an yatsan ta
d'aya cikin kunnen mufidah tana yin motsi dashi.
Hannun ta mufidah tasa xata sa a kunnen don jin motsin da take ji aciki, da sauri afnan ta xare d'an
yatsan nata tana dariya k'asa k'asa don ganin mufidah ta gyara kwanciyar ta tare da komawa baccin ta
hankali kwance.
Ganin hka yasa afnan ta kai bakin ta dai dai kunnen mufidah tace
" Mamee na wake up"
Da k'arfi ta fad'i hkan ae kuwa a firgice mufidah ta tashi sauke ajiyar numfashi don ba k'aramin tsorata
tayi ba ,dariya afnan ta kwashe da ita tare da cewa
"Mamee na kin fiye tsoro nice fah"
Hararar ta mufidah tayi tare da d'aure fuska hannun ta tasa ta kama kunnen ta da d'an k'arfi tare da
cewa
"Afnan how many times da xan miki magana ki daina yi min ihu a kunne idan ina bacci, kina son na dunga
tashi da headache koh?"
Girgixa kai afnan tayi tana mai yin raurau da idanun ta alamar gaf take da ta rushe da kuka ta marairace
fuska tace
"Sorry mamee na daina "
K'ara hararar ta mufidah tayi tana kokarin tashi da sauri afnan ta rik'o hannun mufidah sannan ta kama
kunnen ta dukka biyun tace
"I'm so sorry mamee na please baxan k'ara ba"
Duk tabi ta wani damu don sam bata son ganin tayi wa mameen nata laifi tana mata fad'a, kallon ta
mufidah tayi sai taji wani mugun tausayin ta batasan lokacin da ta rungume ta ba tsam a jikin ta, tana
mai jin wani irin sabon sonta na k'ara shiga cikin xuciyar ta.
"Mamee kin hak'ura?"
Cewar afnan murmishi mufidah tayi tare da cewa
"Na hak'ura afnan baxan iya fushi da ke ba "
Kallon mufidah take wadda ta sauka daga kan bed tana tsaye ita kuma afnan tana kan bed din tace
"Mamee an fasa xuwa gidan umma ne?"
Hancin ta mufidah ta kamo tana d'an ja tace
"Sarkin son xuwa gidan umma xamu je bari na shirya ko?"
"Yawwa mamee na thank u "
Gaba d'aya suka sanya dariya sannan mufidah ta shige cikin toilet xuciyar ta cike da kaunar 'yar ta ta.
Cikin en mintuna tayi wankan sannan ta fito ta fara gyara jikin ta suna hirar su da afnan har ta kammala
shirya was cikin wata black arabiyan gown mai adon flower's golden a jiki tayi kyau sosai da yake mufidah
fara ce kalar ta kar6i fatar ta, ba wani kwalliya tayi ba daga powder sai wet lips mai k'amshin apple bayan
ta fesa perfume's ne a jikin ta ta rik'e hannun afnan suka fito xuwa down stair's, d'ayan hannun nata yana
rik'e da car key and phone nata .
Tun kafin su k'araso cikin palourn mumy take kallon su xuciyar ta cike da farinciki fuskar ta ma bata 6oye
yanayin da take ciki ba saboda yanda take murmishi idanun ta akan su har suka karaso cikin parlour.
Gaida mumy mufidah tayi bayan sun gama gaisa wa ne ta nufi dinning area ta fara breakfast, bayan ta
gama suka yiwa mumy sallama suka tafi.
A nutse take driving har suka k'araso gidan su mufidah ,tana gama parking afnan ta fita da gudu daga
cikin motar ta nufi cikin gidan da kallo mufidah ta bita tana murmishi kafin ta fito tabi bayan ta.
A jikin umma d'are d'are mufidah ta hango afnan tana mata hira umma na dariya
"Wash Allah na umma nagaji "
Kallon ta umma tayi kafin tace " sai kace wadda tayi wani aikin ko tafiyar k'asa"
D'an dariya mufidah tayi kafin tace Allah umma yanxu bana samun wani hutu sai week end kullum cikin
aiki nake "
Ta6e baki umma tayi tana cewa " ae ni da wannan aikin gwara kiyi aure don ni nafison hka daman can
nafi k'aunar kiyi auren ki "
Tuni mufidah ta 6ata rai shi yasa wani lokacin take dad'e wa bata xo gida ba saboda kullum zancen umma
tayi aure ita kuwa sam aure ya fita a kanta bata sha'awar yin shi kwata kwata tun da har ta rasa
managarcin miji irin sadeeq.
Tashi tayi ta nufi bedroom d'in ta umma ta bita da kallo idan da sabo ta saba da hkan da mufidah take
nuna mata sam yarinya bata kaunar kayi mata maganar aure idan tana fara'a yanxu sai ta birkice maka
kamar mai jinnu.
"Umma bari naje wajen Aunty nabilah mu yi wasa da muhibbat"
Maganar da afnan tayi ta dawo da ita daga tunanin da ta fad'a,shafa kanta umma tayi tare da cewa
"Okay sai kin dawo "
Da d'an gudun ta afnan ta fita tayi side d'in su muhibbat, ganin hka yasa umma ta mik'e ta nufi bedroom
d'in da mufidah ta shiga kwance ta same ta rigingine tana tunani idanun ta suna lumshe but hawaye yana
fita daga idon ta.
Girgixa kai umma tayi tare da xama a gefen ta ta sanya hannu ta dafa ta ,bud'e idanun tayi a hankali tana
kallon umma idanun ta sun yi ja sosai ,kallon ta umman take xuciyar ta cike da tausayin 'yar ta ta tace
"Tashi mu yi magana mufidah"
A hankali ta tashi xaune kanta a sunkuye tana wasa da 'yantsun hannun ta kallon ta umma ta sake yi kafin
tace
"Kina ganin kamar na tak'ura miki da maganar aure koh?"
Girgixa kai mufidah tayi cigaba da magana umman tayi tana cewa
" ni nafison naga kin yi aure mufidah shekara wajen uku da rasuwar mijin ki ace har yanxu kin k'i bawa
wad'anda suke son ki dama su fito ki xa6i wani kuyi aure?"
Shiru mufidah tayi kanta a k'asa hawaye suna fita daga idanun ta gaba d'aya xuciyar ta babu dad'i wani
irin abu take ji ya tsaya mata a mak'ogaron ta yak'i tafiya bakin ta yayi mata nauyi sosai ta yanda ta kasa
bud'e bakin ta don tayi magana, hankalin ta ya tashi sosai ita a yanxu wa xata kalla da sunan masoyi ta
aure shi ya xama miji a gare ta?...........
Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE*
*Written by*
Aishat A muh'd
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 38*
Sauke ajiyar xuciya kawai take don gaba d'aya ta rasa ta yanda xata furta wa umma ta fahimce ta ita fa
auren ne bata son yi a barta tayi renon afnan ita kadai ta ishe ta.
"Kiyi hak'uri ki fitar da sadeeq daga cikin xuciyar ki don ya tafi har abada baxai dawo ba, don hka ni dai a
matsayi na na mahaifayar ki ina mai baki shawara akan yin auren ki shi yafi miki alkhairi "
Tana gama fad'in hka ta fita daga d'akin, sai a lokacin mufidah ta samu wani kuka mai k'arfi ya kubce
mata ita ya xata yi yanxu, tana cikin kukan nabilah ta shigo d'akin don afnan ta fad'a mata da mameen ta
suka xo, ganin mufidah tana kuka sosai yasa nabilah tace
"Subhanallah mufidah me yafaru kike kuka lafia?"
Duk wad'annan tambayoyin nabilah tayi mata su cikin damuwa tana mai dafa kafad'ar ta, kasa magana
mufidah tayi sai da tayi kukan ta sosai tukunna ta shiga toilet ta wanke fuskar ta tare da fitowa.
Inda ta bar nabilah a xaune hka taxo ta tarar da ita xama tayi agefen ta tana sauke ajiyar xuciya, cikin
yanayin damuwa nabilah tace
"Fad'a min abin da yake damun ki ?"
Cikin sanyin murya mufidah tace
"Nabilah na rasa ta yanda xan fahimtar da umma bana son yin aure amman ta tak'ura min sai nayi aure
na rasa yanda xan yi wlh"
Ta k'arasa fad'in hka kwalla na sake xubo mata idanun ta akan nabilah don yanxu ita mafita take nema na
yanda xata xame umma ta dai na yi mata maganar aure kwata kwata .
Sauke ajiyar numfashi nabilah tayi kafin tace
"Ehh gaskiyar umma kuwa nima ina bin bayan ta wlh don duk uwa ta gari tana son taga 'ya'yan ta sun
raya sunnar Annabi (saw), suna da auren su hkan shi xai fi kwantar mata hankali tasamu nutsuwa"
Wani kallo mufidah take watsa wa nabilah, murmishi tayi tare da cewa
"Harare ni da kyau mufidah gaskia ce na fad'a ke kan ki sai mutane sun fi girmama ki idan suka san da
auren ki nima shawara ta awajen ki kiyi aure"
"Da kyau nabilah gwara ki fad'a mata taji amman daga fad'a wa mutum gaskia ya xauna yana rusa kuka
kamar wanda aka fad'a mishi mummunan labari"
Cewar umma kenan wadda ta shigo hannun ta dauke da wayar mufidah wanda take k'ara alamar kiran ta
ake, mik'a mata wayar umma tayi sannan ta fita.
Kafin ta d'aga kiran ya katse don hka sai tayi kok'arin kira sai gashi an sake kira picking tayi tare da sanya
wa wayar a hands free cikin sanyin murya tace
"Assalamu Alaikum"
"Waalaikissalam Dr mufidah ina kika shiga ne?"
Cewar Dr muh'd kenan,d'an murmishi yak'e mufidah tayi tare da cewa
"Ina gidan mu doctor"
Shima a nashi 6angaren murmishi mai k'ayatar wa ya saki tare da cewa
"Yau an kaiwa su umma xiyara kenan ?"
"Ehh wlh yanxun ne babu cikakken time sai week end"
Cewar mufidah tana kallon nabilah da ta xuba mata ido kamar ta samu tv,
"Hkne, ina afnan ban ji motsin ta ba?"
D'an yamutsa fuska tayi tare da cewa
" tana palour suna wasa da muhibbat "
"Okay ashafa min kanta xuwa dare xan shigo na kwana biyu ban shigo ba"
"Okay Allah ya kawo ka lafia"
"Ameeen byeee"
Yana gama fad'in ya katse wayar, d'an hararar nabilah tayi ganin yanda ta xuba mata ido kamar yau ta
ta6a ganin ta a duniyar.
" wannan kallon fah na lafia ne?"
"Hmm mamaki kika bani ina kula da take taken muh'd alamar son ki yake ganin yanda yake kaffa kaffa
dake"
Hararar ta mufidah tayi kafin tace "wa ya fad'a miki muh'd sona yake ?"
"Uhm alama na gani kuma insha Allah sai hashashena ya xama gaskiya, idan muh'd ya aure ki da kin
more miji kamar sadeeq shima alamun shi ba ruwan shi ba kamar mutumin mu ba musaddiq"
Daure fuska mufidah ta sake yi kuma gaban ta ya fad'i jin sunan musaddiq kafin tace " hashashen ki kuwa
baxai ta6a yiwuwa ki ma daina fad'a "
"Dalla can malama idan bai yiwu da muh'd ba sai a had'a da musaddiq, ni wlh nama fison ki auri
musaddiq don kun fi dacewa sosai ya Allah kasa xance na ya xama gask......."
Kafin ta k'arasa fad'in gaskia mufidah ta kawo mata duka da hannun ta cikin fusata ae kuwa da sauri
nabilah ta tashi tare da matsawa gefe ta cigaba da magana tana kallon irin kallon da mufidah take mata
abin dariya ma yake bata
"Daga yin fatan alkhairi sai ki kawo min duka malama don kin samu ma ina....."
Tuni ta tsai da maganar da take ta fita daga d'akin da gudu ganin yanda mufidah ta tashi tana huci ae
kuwa ita ma ta rufo mata baya da gudu.
Sai ganin su umma tayi da gudu sun shigo palon a tsorace umma ta tashi tana cewa
"Lafia me yafaru?"
Tuni nabilah ta shige bayan umma tana 6uya tare da cewa
"Umma daga yi mata addu'ar fatan alkhairi kawai ta biyo ni xata doke ni "
Murmishi umman tayi tare da kallon mufidah wadda take sauke numfashi da sauri da sauri tana hararar
nabilah sosai ta bawa umma dariya sai dai ta danne tare da cewa
"Ke kuma daga yi miki fatan alkhairi sai ki doki mutum bayan godiya ma ya kamata kiyi mata"
"Umma kinsan abin da ce min kuwa?"
Cewar mufidah tana xum6uro baki
" a'a sai kin fad'a "
"wai wai hka tace..."
Sai kuma tayi shiru tare da yin kwafa ta shige bedroom a fusace.
Lokaci d'aya umma da nabilah suka kwashe da dariya kamar ba surukai ba tukunna nabilah take fad'a
mata abin da tace wa mufidah girgixa kai kawai umma tayi cikin xuciyar kuwa tana mai fatan Allah ya
bawa 'yarta miji nagari kamar sadeeq.
Dakyar nabilah ta rarraso mufidah har ta fito xuwa parlour suka cigaba da hirar su,har xuwa lokacin da
Abba da Yah Omar suka dawo daga aiki bayan sun gaisa suka had'u suna ta6a hira.
Sai wurin 6 na yamma mufidah da afnan suka bar gidan, lokacin da suka dawo sosai mumy tayi farinciki
daman duk gidan yayi mata girma ba en hira.
Sai bayan mangarib sannan muh'd ya xo sun yi hira sosai da mufidah kafin daga k'arshe ya xube wa su
mufidah da afnan kayan shopping d'in da yayi musu har wurin mota mufidah ta raka shi kamar wasu
masoya suka yi sallama ya tafi.
Bayan sun gama yin dinner ne ta nufi bedroom d'in ta wanka tayi wa afnan ta shirya ta cikin sleeping
dress ta kwantar da ita tare da yi mata addu'a ta lullu6e ta da blanket, tukunna ta nufi toilet tayi nata
wankan ta gyara jikin ta cikin kayan bacci sannan ta kwanta tare da yin addu'a ta janyo afnan xuwa jikin
ta rungume ta tayi tare da fad'a wa kogin tunani wanda ya xame mata jiki tun bayan rasuwar sadeeq
murmishin shi maganar shi take tunano wa da hka bacci mai nauyi ya dauke ta.
************
Dare ne sosai wajen misalin karfe 2 na dare wani mummunan mafarki musaddiq yake wanda ya
haddasa mishi farka wa a matuk'ar firgice ga wani uban gumi da ya had'a xuro kyawawan k'afafun shi
yayi k'asa yana xaune kan bed din tare da dafe kan shi da yake matukar sara mishi da ciwo.
Hasken d'akin ya kunna ko ina ya haske d'akin dafe kanshi yayi yana tunano mafarkin da yayi, mufidah
ya hango xaune cikin wani kyakkyawan garden tana xaune tasha kwalliya cikin wata red gown mai siririn
hannu gashin ta yasha gyara ta sake shi bayan ta bata sanya ribbon ba dariya take tana watsa wasu
kyawawan furanni red colour's sama suna dawowa jikin ta sai dariya take mai ban sha'awa.
Kok'arin k'araso wa wajen ta yake shima yana wani murmishi but ya kusan k'araso wa don bai fi sauran
taku uku ba sai kawai ganin wani yayi ya k'arasa inda take ya mik'o mata hannun shi ta sanya nata a cikin
nashi.
D'agowar da xai yi mutumin musaddiq ya hango fuskar shi tuni jikin shi ya dauki rawa wani gumi ya jik'e
shi hankalin shi yayi masifar tashi ganin fuskar muh'd, kafin yayi wani yunk'uri tuni sun bar wajen.
Shine ya tashi a firgice gaba d'aya ya rud'e kada wannan mafarkin nashi ya xama gaskia idan hka ne kuwa
da shikenan ya mutu, baisan son mufidah gama da xuciyar shi ba sai yanxu wani masifafen kishin ta yake
ji a xuciyar shi yasan yanxu hka suna can suna soyayya da muh'd tun da yasan ba irin rarrashin da muhd
bai yi mishi ba kan ya amince ya aure ta ya tubure yak'i yarda har yayi fushi dashi sai dakyar ya rarrashe
shi ya sakko daga Fushin da yayi.
So shine ya samu hangar nuna mata so anya muh'd ya san irin adadin son da yake yi wa mufidah ya dauki
alkawarin baxai rasa ta a karo na biyu ba ya xama dole ya tattara ya koma Nigeria (hmmm reader's kuji
musaddiq da wani tunani ko yaushe muh'd yace mishi son mufidah yake, kuma da bakin shi ya fad'a wa
muh'd d'in kan cewa baxai ta6a iya aurar matar da yayan shi ya mutu ya bari ba, muje dai