Showing 3001 words to 6000 words out of 92754 words

Chapter 2 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf

10 Jul 2025

2466

me yake faru wa ? "
Ganin yanda yake kakarin amai da rik'e ciki.

Ina musaddiq bai masan me yake cewa ba don gaba d'aya ya fara fita a hayyacin shi saboda kakarin aman
da yake, gaba d'aya Yah sadeeq ya rud'e nan fah hankalin mutanen da suke xaune ya dawo kansu sai
kallon su ake cike da tausayi a fuskar su suna tunanin ko bai da lafia ne.

A hankali aman ya lafa mishi Yah sadeeq ya taimaka mishi ya xauna kan kujera yana mishi sannu sake
had'a ido musaddiq yayi da abincin ai baisan lokacin da wurgar da plate di'n ba abincin ya xube a k'asa
plate di'n ma bai tsira ba sai da ya fashe,ruwa Yah sadeeq ya miko wa musaddiq ya kar6a tare da sha sai
da ya shanye ruwan sannan ya ajiye cup d'in tare da lumshe ido yana faman sauke ajiyar xuciya gaba
d'aya fuskar shi da idanun shi sunyi ja saboda wahalar da yasha wajen kakarin aman.

Sai lokacin Yah sadeeq hankalin shi ya kwanta har ya fuskanci abin da yasa musaddiq cikin wannan
yanayin dariya ya tuntsire da ita saboda yasan sarai k'anin nashi akwai shegen tsantsami cikin dariya yace
"Haba musaddiq akan wannan abin ka wahalar da kan ka ji yanda ka koma "

Kafin musaddiq yayi magana wanda ya kawo abincin nan ya xo wurin ae kuwa Kafin ya ankara musaddiq
ya kife shi da wani wawan mari Wanda har yasa ki kusan fad'u wa k'asa tuni mutumin ya rikice durkusa
wa yayi a k'asa yana cewa

"I'm sorry sir wlh sa ni akayi "
Da yake ya gama tsorata da marin da musaddiq yayi mishi, da har ya d'aga hannu xai sake marin shi sai ya
dakata jin wannan maganar da yayi cikin 6acin rai musaddiq yace
"what! uban wa ya saka? "
Cikin rawar jiki ya nuna Inda mufidah take tsaye tana shek'a dariyar mugunta amman sai dai me wayam
ba kowa, da sauri musaddiq ya tashi tare da fita a wajen don da alama wanda yasa a yi mishi wannan
iskancin bai yi nisa ba, da sauri shi ma yah sadeeq ya rufa mishi baya cike da tarin tambayoyi a xuciyar shi
to shin wane yasa ayi wa k'anin shi wannan wulakancin.

Suna fito wa farfajiyar restaurant d'in nan ma basu ga kowa ba hkan ya tabbatar da wanda yasa ayi hkan
ya gudu daga wurin nan fah bak'in ciki ya rufe musaddiq yaso ace ya ga d'an iskan da yasa ayi mishi hka
da yau kashe shi ne kawai baxai yi ba, nan dai Yah sadeeq ya lalla6a shi suka bar wajen.

Mufidah kuwa duk abin da ke faruwa ta na gani kuma taci dariya har da hawayen ta ganin a mari wannan
mai kawo abincin yasa ta 6uya don hka shi yasa lokacin da ya nuna wajen musaddiq bai ga kowa ba, tana
ganin sun fita ita ma ta fito daga wurin motar ta ta shiga kai tsaye gidan su nabila k'awar ta ta nufa bayan
tayi parking ne ta nufi ainahin kofar da xata sada ka da cikin gidan.

Da sallama ta shiga umman nabila da take tsaye 6angaren dinning table tana shirya abinci akai ta jiyo
tare da amsa sallamar ganin mufidah ce yasa ta fad'ad'a fuskar ta da fara'a tare da cewa
"Oyoyo my daughter, baki da kirki mufidah yaushe rabon ki da shigowa cikin gidan nan sai dai ki sauke
nabila a bakin gate "

Umman nabila ta fad'a cikin wasa, Murmishi mufidah tayi tare da kama kunnen ta tace "sorry ammin mu
na tuba na dai na"
Dariya umman nabila tayi tare da cewa "Okay shikenan ya wuce sauran ki k'ara "
Da sauri mufidah tace "baxan ma k'ara ba Insha Allah ammi "
Dariya suka yi gaba d'ayan su sannan umman tace "Allah yasa hka ne, ina umman taki ?"

"tana gida "

Sai a lokacin suka gaisa tukunna ta nufi bedroom d'in nabila a gaban dressing mirror ta same ta tana
shirya wa alamar fitowar ta daga wanka kenan nan fah suka sakar wa junan su murmishi sannan mufidah
ta xauna gefen bed tana cire mayafin da tayi rolling d'in kanta ta furta
"wash Allah na nayi matuk'ar gajiya yau "
Cikin mamaki nabila tace "gajiyar me kuma? "
"yanxu dai ya jikin na ki? "
"ah na samu lafia daman fah ciwon kai ne na tashi dashi "
"Ayyah Allah ya k'ara sauk'i sannu " Cewar mufidah
"Ameeen ya rabbi "

Cikin tsokana nabila tace "kin had'u da mutumin na ki ne yau? "
cikin rashin fahimta mufidah tace "wa kike nufi? "

"musaddiq Abubakar man "
Wata dariya ce ta kubce wa mufidah ta dunga yi yayin da nabila ta saki baki tana kallon ta kawai cike da
mamaki sai da tayi dariyar ta ta gama har da hawaye sannan ta bawa nabila labarin abin da tayi mishi,
nan fah nabila me xatayi ban da dariya daman tasan mufidah baxa ta kyale shi ba sai tayi mishi wani
abun.

"Allah k'awata baki da kirki amman ina rok'an ki ki rabu dashi a matsayin ki na 'ya mace ki rabu dashi
kuma ki kiyaye abin da xai sake had'a ku a gaba"

D'an hararar ta mufidah tayi tare da cewa Kina nufin ya ci bulus kenan marin da yayi min ?"
"Haba k'awata ban sanki da wannam halin ba ki rabu dashi please "
"Okay naji na yarda amman da sharad'i guda idan yayi min xan rama"
Mufidah tana rufe bakin ta umman nabila ta shigo d'akin tana cewa "ku dai idan kuka shigo d'akin kuna
surutu mance wa da komai kuke toh lokacin cin abinci yayi don hka oya ku fito mu ci"

"toh ummah " suka fad'i sannan suka fito daga d'akin dinning table suka nufa nan suka ci abinci sannan
suka dawo falo suna ta6a hira sai yamma sannan mufidah ta tafi gida...............



Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:03 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE*



*written by*
Aishat A muh'd

♻ *E.W.F*



_Wannan shafin na kine k'awata sadeey S Adam (SaNaz), ngde da k'aunar da kike nuna min Allah ya bar
xumunci ya k'are min ke a duk inda kike, ina miki fatan alkhairi_



*Page 4*


*WACE CE MUFIDAH*

Mufidah El Hussaen 'yace a wajen Alhj EL Hussein da hajia Aisha, mahaifin ta haifaffen garin d'ambatta
ne sana'a ce ta dawo da mahaifin shi cikin garin kano iyayen shi ba wasu masu kud'i ba ne rufin asirin
Allah ne da hka yayi karatun boko dana addini da yake shi kad'ai suka mallaka akan fannin Shari'ah yayi
karatun cikakken alk'ali ne Wanda yasha gwagwarmaya Kafin kuma yayi ritaya ya koma harkar kasuwanci
ta siyar da motoci.

Alhj El Hussaen baxa ka kirawo shi da mai dukiya sosai ba yana da arxikin shi dai dai gwargwado yana
xaune a sultan crescent, matar shi hajia Aisha uwar 'ya'yan shi bafulatana ce amman ta samu karatu sosai
don ita ma k'wanan nan ta bar aiki tana matsayin babbar lecture da ake damawa dasu a makarantar buk.

Yaran su biyu Omar da mufidah sune yaran da Allah ya basu Yah Omar yana k'asar london yana karatun
shi ya ma kammala karatun cikin wannan watan suke sa ran dawowar tashi.

Mufidah itace mai bin Yah Omar ya bata wajen shekara 4, ita ma ta kammala karatun ta na primary da
secondary yanxu tana buk ta d'ora karatun ta, tana masifar son karatun na ta bata k'aunar abin da xai
ta6a neman ilimin nata, kuma ba iyakar ilimin boko ta tsaya ba har da na addinin islam ta ma yi saukar
alqur'ani da sauran mahimman littatafai na addini dai dai gwargwado tana da ilimi anan 6angaren.

Kuma ta kasance kyakkyawar yarinya mai kama da mahaifin ta amman farin umman ta ta d'auko duk da
uban shi ma ba bak'i ba ne, gashi akwai ta kirki bata shiga harkar da bata shafe ta ba akwai hankali da
nutsuwa sai dai aka ta6a ta bata kyale wa kamar yanda musaddiq Abubakar ya ta6o ta.


*WACE CE NABILA K'AWAR TA*?

Nabila yarinya mai hankali da nutsuwa ga hak'uri maman ta hajia Amina k'awa ce ga hajia Aisha umman
mufidah tare suka yi koyarwa a buk k'awaye ne sosai shi yasa mufidah da nabila suka xama k'awaye
sosai, sai dai ita nabila mahaifin ta ya rasu kuma ita kad'ai ce ta rayu cikin 'ya'yan ta da take haihuwa duk
mutuwa suke, gashi ita ma nabilan kyakkyawa ce sai dai mufidah ta fita kyau, duk tare suka yi karatun su
kan su a had'e yake.

_mun dawo labari_

Tun da suka shiga mota musaddiq Ko magana ya kasa saboda tsabar takaici har suka k'araso gida, Yah
sadeeq yana parking da mota musaddiq ya fito ya nufi cikin gidan d'akin shi ya shige ya cire kayan jikin
shi ya shiga toilet wanka yayi sannan ya fito ya shirya cikin wata riga mara hannu red colour da ash d'in
3quater bayan ya fesa perfumes ya fito xuwa babban palon gidan, anan ya tarar da mumy da Yah sadeeq
a xaune suna hira xama yayi kusa da mumy yace
" I'm hungry Mumy "
Har Yah sadeeq ya bud'e baki xai yi magana kamar musaddiq yasan abin da xai fad'a wa mumyn aikuwa
yayi mishi alamar kada ya fad'a mata don hka yaja bakin shi yayi shiru kawai.

" my son me xa'a kawo maka?" Cewar mumy

D'an yatsina fuska yayi tare da cewa " Duk abin da kika dafa mumy, amman a had'a min da fura mai
sanyi"

"kaje dinning table xaka samu komai acan akwai kuma fura cikin frige din kusa da dinning table, maxa
tashi kaje ka ci"

Tashi yayi ya nufi 6angaren dinning table d'in yana yatsine fuska, shi kuwa Yah sadeeq yana danne dariyar
da taxo mishi.

Cikin nutsuwa ya d'ebe abincin yaci Kad'an sannan ya sha furar nan da yawa, bayan ya gama sai ya dawo
palon amman bai xauna ba ya kalli mumy da Yah sadeeq yace
"ni xan je na kwanta na huta "
"Okay son ae gwara ka huta " Cewar mumy yayin da Yah sadeeq yace
"ae dole ma ka huta brother saboda ka sha........... "

Kafin ya K'arasa fad'i musaddiq ya harare shi yayi gaba shi kuwa Yah sadeeq dariya ya tuntsire da ita
mumy kuwa cewa take
"je ka huta son ka rabu da yayan nan naka sarkin tsokana "
"auuu hka xaki ce mumy "
Cikin murmishi mumy tace "Ehhh mana "
Nan dai suka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali.

A 6angaren musaddiq kuwa ba hutawar xai yi ba kawai tunanin Wanda yasa aka kawo mishi wannan abin
kaxantar yake amman duk tunanin shi ya rasa gano ko wane, amman lallai xan bincika, da hka bacci ya
d'auke shi.


*WANE NE MUSADDIQ ABUBAKAR*?

Dr Musaddiq Abubakar kyakkyawan saurayi ne hadadden guy wanda ilimin addini dana boko suka ratsa
shi nutsatstsan mutum ne ma'abocin miskilan ci da rashin son hayaniya, bai dad'e da kammala karatun
likita ba, mahaifin shi yana gina mishi asibiti, sai dai kuma musaddiq don ra'ayin kanshi yake koyarwar
amman shi cikakken likita ne.

Iyayen shi kuwa Alhj Abubakar da hajia khadija su biyu ne 'ya'yan su daga Abubakar sadeeq Wanda yaci
sunan uban nashi suna ce mishi sadeeq sai kuma musaddiq ,suna xaune cikin xaman lafia da kwanciyar
hankali gashi suna k'aunar junan su sosai har baxa ka iya banbance tsakanin sadeeq da musaddiq wanne
yafi k'aunar d'an uwan shi ba, mahaifin shi d'an kasuwa ne hka shima sadeeq sana'ar mahaifin nashi
yake.

Alhj Abubakar da Alhj El Hussaen abokanan juna ne na k'ut da k'ut,amintaka ce a tsakanin su sosai hka
ma matan su.


_mun dawo labari_

Tun daga lokacin mufidah take xuwa skul da wuri idan ta fuskanci ranar musaddiq yana da lecture a ranar
don hka bai k'ara korar ta ba, sai dai fah har yanxu haushin yarinyar yaji sosai, ita kuwa bata k'ara bi ta
kanshi ba gashi duk test d'in da yake musu da assignment kusan ita ce kan gaba wajen ci,kuma yaga
kusan lecture's din makarantar suna yaba ma yarinyar sosai.


Ana cikin hka Yah Omar yayi waya xai dawo nan da k'wana 2 don Allah mufidah ba xama ita da nabila
suna kok'arin had'a mishi partyn murnar kammala makarantar shi da kuma murnar xagoyowar shekarar
haihuwar shi, sosai suke shirya Inda xa'a yi partyn da a abubuwan da xa'a buk'ata a wajen.


Ranar Friday da misalin karfe 7 jirgin su Yah Omar yayi landing a airport d'in malam aminu kano, mufidah
da nabila ne suka d'aukar shi yana fito wa daga cikin jirgin mufidah ta nufi inda yake da gudu ta rungume
shi cikin tsananin farincikin ganin d'an uwan nata ,nan shima ya rungume ta cikin murnar ganin kanwar
tashi xuwa can ta sake shi tare da kallon shi cikin murmishi tace
"Yah Omar ka ga yanda ka koma lallai london ta kar6e ka"
"lallai yarinyar nan kin rainani daman can da Kyan nawa "
Ya Omar ya fad'a cikin dariya a lokacin kuma nabila ta k'araso tana gaida shi tare da yi mishi sannu da
xuwa rik'e baki yah Omar yayi tare da cewa
"kai kai wannan ba dai itace nabila ba?"

"ita ce mana "
Cewar mufidah, cikin tsokana yace "lallai yaran nan kun girma da yawa wannan ae Kun kusan kamo ni
"mufidah dariya tayi yayin da nabila take sunkuyar da kanta k'asa ganin irin kallon da Yah Omar yake
mata.

Nan fah ya dunga tsokanar su har suka k'araso gida, iyayen shi sunyi matuk'ar jin dad'in dawowar yaron
nasu lafia.

Kuma a ranar su mufidah suka dunga gayyatar mutane suna fad'a musu ranar asabar ne partyn da suka
shirya wa Yah Omar, ta 6angaren Yah Omar ma ya sanar da abokanan shi na nan har dasu sadeeq da
musaddiq 'ya'yan abokin mahaifin nashi kuma sun bashi tabbacin xasu xo...........



Aishat A muh'd
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*




*written by*
Aishat A muh'd

♻ *E.W.F*




*Page 5*



_Washe gari_

Mufidah da nabila ba xama ranar sai shirye shirye suke har xuwa lokacin da xa'a gabatar da partyn,
hatta kayan su iri d'aya ne da nabila komai da komai shima Yah Omar kayan da xai sanya colour d'in su
d'aya da na su mufidah sai dai shi na maxa ne abin da ya banbanta kenan.

Har xuwa lokacin da suka sanya karfe 4 na yamma xuwa karfe 7 na dare xa'a tashi, don hka xuwa karfe
hud'un duk friend's din su mufidah sun xo na skul, Wow! masha Allah na furta lokacin da na hango
mufidah ta gama shirya wa cikin had'ad'd'an lace green colour nd touch d'in flowers red d'inkin riga da
siket ne sun yi matuk'ar yi mata kyau sosae, mai make up suka d'auko ta tsantsara musu kwalliya, hka ma
nabila tayi kyau sosae xuwa karfe 4 sun bar gidan sun tafi wajen da suka kama don yin partyn.

Cikin hall di'n ya had'u iya had'uwa ya sha decoration da kwalliyar flowers ga k'aton birthday cake mai
hawa uku, friend's din Yah Omar ma sun xo sosai duk inda mufidah ta gifta idanun mutane na kanta har
da mata kuwa en uwanta don ba k'aramin had'uwa tayi ba, wani abin mamakin shine duk inda Yah Omar
ya d'auke kafar shi to nan nabila xata ajiye ta ta sai bata kulawa yake alamun dai sun bayyana wa kansu
soyayya, mufidah na ankare dasu sai dai tayi murmishi kawai kuma tayi farinciki sosai da hkan sun dace
da junan su.

"Haba musaddiq don Allah kasan mun yiwa Omar alk'awarin xamu je gashi kace ka fasa xuwa "
Cewar Yah sadeeq kenan lokacin da ya gama shirya cikin wata tsadaddiyar shadda purple ce tayi mishi
kyau sosae, ya shigo d'akin musaddiq don ganin ko ya shirya sai yayi turus ganin musaddiq a xaune yana
sarrafa laptop ko alamar shirya wa bai yi ba
"lafia musaddiq baka shirya ba gashi karfe 5 ma ta wuce? "
Cikin yatsina fuska yace "Yah sadeeq na fasa xuwa fah "
So shine sadeeq yake fad'a mishi sun yiwa Omar alk'awarin xuwa,nan dai dakyar Yah sadeeq yake lalla6a
musaddiq ya yarda xai je, ajiye laptop d'in yayi bayan ya kashe ta ya mik'e tsaye tare da cewa
"amman baxa mu dad'e ba ko brother don ni fah banson hayaniya? "

Murmishi sadeeq yayi tare da cewa "Haba musaddiq ka d'aure mu xauna xuwa a tashi kasan yanda muke
dasu Omar kamar en uwan jini "
"alright bari na shirya amman idan hayaniya ta dame ni xan gudu na bar ka " Dariya Yah sadeeq yayi yana
cewa "Ehhh na dai ji ".

Toilet musaddiq ya shige shi kuwa Yah sadeeq ya fita daga bedroom d'in nashi, cikin mintuna talatin
musaddiq yayi wanka a gurguje ya shirya cikin wani yadi blue colour yayi matuk'ar kar6ar shi yadin don
bai fiye sa manyan kaya ba sai ta kama, bayan ya taje sumar kanshi ya shafa mata mayuka sannan ya
d'aura tsadadden watch di'n shi tare da fesa perfumes masu matuk'ar k'amshi, sannan ya fito xuwa falo
inda Yah sadeeq yake jiran shi.

Yana fito wa palon mumy da Yah sadeeq suka bishi da kallo yaushe rabon su ganshi da manyan kaya gashi
kuma suna mishi kyau Idan ya saka mumy ce ta fara cewa
"Masha Allah d'an nawa yayi kyau Allah yasa idan aka je a sama min suruka"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login