Showing 9001 words to 12000 words out of 92754 words

Chapter 4 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf

10 Jul 2025

2461

kujera saboda tsabar xafin da ta ji
sai da ta saki k'ara Kafin kuma ta mik'e tsaye cikin tsiwa ta ce

"wai mene nufin ka na kawo ni wannan gidan iyeee? "

Cikin kallon wulakanci yace "saboda ki wanke wannan kayan da kika 6ata kin ji na rantse wlh sai kin
wanke su "

"ni fah malam dakata kaji ko agidan mu wanki ake min ban iya ba don hka baxan yi ba "

Tana gama fad'in hka tayi hanyar fita daga falon ae kuwa musaddiq yasa hannu ya janyo ta da karfi har sai
da ta bugi kirjin shi idanun shi cike da tsantsar tsanar ta yace
"ni ina ruwa na da baki iya ba idan ma baki ta6a yin wanki ba tun da aka haife ki to wlh yau sai kin yi don
kin ga ban lallasa miki jiki ba koh?"

Fisge jikin ta tayi tare da cewa "ae kuwa baka isa ba ni ka bud'e min kofa na tafi "

Cikin murmishin mugunta yace "ae kuwa xaki k'wana a nan don baxa ki bar gidan nan ba sai kin wanke "

Yana gama fad'in hka ya nufi wata kofa ya shiga tare da rufe wa wanka yayi ya sauya kaya xuwa jeans blue
da t-shirt white mai dogon hannu ya fesa perfumes sannan ya fito xuwa falo da niyyar tafiya masallaci
anan inda ya barta a hka ya same ta sai rusa kuka take ganin gashi har lokacin sallahr ishshah yayi kusan

karfe 8 kenan tasan yanxu sun tashi daga partyn har sun koma gida ta shiga uku Idan ta koma gida me
xata ce wa umma idan ta tuhume ta ina ta xauna sai kawai ta fashe da kuka don bata da amsar tambayar
a hka ya fito ya tarar tana kukan.

Yana daf da xai fita daga falon ya juyo ya kalle ta tukunna yace "Idan kina son koma wa gida da wuri to
Kafin na dawo daga masallaci ki wanke kuma wankin ya fita sosai fah Idan bai fita ba sai kin sake"

Yana gama fad'ar Hka ya fice daga falon ya sanya key ya nufi masallacin kusa da gidan.

Mufidah kuwa ganin ba yanda xata yi ta nufi bedroom d'in da ya shiga d'aki ne mai kyau wanda aka
k'ayata shi sosai kamar da mace a gidan, toilet ta fad'a ta hango kayan a xube a k'asa ganin machine din
wankin kaya yasa mufidah jin dad'i amman tuni murnar ta koma ciki ganin shi da tayi a rufe 6am kamar
ba'a ta6a amfani dashi ba tsaki taja tare da fad'in "Wannan mutumin mugu ne wlh"

cikin takaici ta d'auka ta fara wankin tana yi tana kuka har da majina dak'yar ta samu jan juice din
strawberryn ya fita daga jikin kayan sannan ta matse su ta shanya su sannan ta fito sai had'a uban gumi
take kallon agogon tayi taga 8:55 tara sauran minti biyar kenan da sauri ta fito daga bedroom d'in turus
ta ja ta tsaya ganin har yanxu musaddiq bai dawo ba kasa xama tayi ta dunga xagaye a cikin palon saboda
tsabar tashin hankali kuka kuwa ba'a magana sai faman rusa shi take.

A can wurin partyn kuwa ko da su Yah Omar da nabila basu ga dawowar mufidah ba sun d'auka ta gaji ta
gudu gida don hka basu damu ba, shima sadeeq da yaga musaddiq bai dawo ba yasa shi tunanin ko ya
gudu gida gashi key di'n yana hannun shi, lokacin da aka tashi sai su Yah Omar ne suka mayar dashi gida .

Musaddiq bai dawo gidan ba sai wurin 9:40 lokacin mufidah har ta dai na kukan sai faman ajiyar xuciya
take saki alamar taci kuka ta koshi wani murmishin mugunta ya yi tare da cewa
"ohhh my god kiyi hak'uri na mance fah da ke sai yanxu na tuna har naje gida na kwanta na tuna da ke"

Kallon shi mufidah tayi da kumburarrun idanun ta cikin takaici da bak'in ciki ta rasa ma me xata ce tabbas
maganar shi gaskia ce don gashi har ya canja kayan jikin shi xuwa sleeping dress na maxa farare sol dasu
masu d'an kauri don garin akwai d'an sanyi sanyi maganar da yayi ita ta dawo da mufidah daga tunanin
da ta lula yace

"xaki iya tafiya yanxu naga kayan kin iya wanki kuwa don sun fita "
Ashe har ya shiga ya duba su, cikin tsananin tsoro tace "wlh tsoro nake don Allah ka kai ni gida"
Hararar ta yayi kafin yace "ban da wannan time d'in don hka get out "
Da gudu mufidah ta fita daga falon sai da ta fita tukunna tasa mayafin ta cikin sauri ta fice daga gidan
gabanta yana faman fad'uwa don kuwa dare yayi ko'ina shiru kake ji nan fah ta dunga tafiya cikin sauri ga
nisa unguwar tsakanin ta da titi dak'yar ta iya k'arasa wa kan titi sai dai ababan hawa sun ragu sosai don
dare yayi gashi idan ta tsayar dasu basa tsaya wa ana hka wasu en shaye shaye suka nufi inda take har
d'ayan na kok'arin rik'e mata hannu don hka mufidah yasa mufidah tsorata sosai nan dai ta kwasa da
gudu ae kuwa su ma suka bi ta da gudu nan fah aka fara tsere tsakanin mufidah da en shaye shayen nan
wani wawan birki aka ja da mota a gaban mufidah da sauri na cikin motar ya fito ae kuwa mufidah tana
ganin musaddiq ne ta nufi wajen tare da rungume shi tana kuka sosai duk a firgice take.

En shaye shayen suna ganin musaddiq suka juya suka gudu, had'uwar jikin shi da na mufidah ba k'aramin
canja mishi tunani yayi ba na lokaci d'aya hannun shi yasa ya k'ara rungume ta tsam a jikin shi yana shafa
bayanta a hankali ita kuwa sai faman kuka da ajiyar xuciya ta ke saki, shi ma duk laifin shi ne yayi
gangancin barin ta taho wa cikin wannan daren a matsayin ta na mace.

Dak'yar ya iya raba jikin shi da nata ganin hka yasa mufidah da sauri rik'o hannun shi cikin kuka tace "Don
Allah kada ka tafi ka taimaka min kai kai ni gida ina jin tsoro please "

Kama hannun ta yayi ya sata a mota a hankali ba kamar d'axu ba shima ya xagaya ya shiga sannan yayi wa
motar key ya fara tafiya gaba d'aya tunanin shi ya canja tun lokacin da yaji mufidah a jikin shi wani abu ne
ke kok'arin taso mishi a cikin xuciyar shi yana danne wa amman kuma ya kasa dai na kallon ta har xuwa
lokacin da ya shiga farfajiyar gidan nasu ta sauka da sauri ta nufi cikin gidan shi kuma ya fita daga gidan
har yaje kwanciya yana tunana had'uwar jikin shi da ta mufidah.

Mufidah tana shiga gida ta tarar da su umma, Abba da Yah Omar nabila suna xaune hankalin su a
matuk'ar tashe sai ganin ta suka yi kamar an wullo ta cikin su nan ta rushe da kuka sosai umma da nabila
suka rungume ta da aka tambaye ta ina taje k'in magana tayi sai kuka nan dai dak'yar suka rarrashe ta
tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya, ruwan wanka nabila ta had'a mata ta shiga wanka bayan ta fito ta
shirya cikin kayan bacci ta kwanta xuciyar ta na tunanin abin da yafaru tsakanin ta da musaddiq da hka
bacci 6arawo ya d'auke ta..............

_kuyi hak'uri da wannan sai gobe kuma Insha Allah_



Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE*



*written by*

Aishat A muh'd


♻ *E.W.F*




*Page 8*

Dummmm gaban musaddiq yayi mummunar fad'uwa lokaci d'aya nan take yaji wani irin abu na yawo
cikin xuciyar shi wanda ya kasa tantance ko mene gaba d'aya sai yaji baxai iya cigaba da sauraren wannan
hirar ba ya fara tafiya xuwa cikin bedroom d'in shi xuciyar shi cike da tarin damuwa kuma ya rasa dalilin
damuwar tashi tun da Yah sadeeq ya ambaci sunan mufidah yanayin shi ya canja.


A can palo kuwa mumy cikin tsananin farinciki tace " Alhmdllh my dear ka ji ashe er gidan aminin ka ya
gani "

Er dariya irin ta manya daddy yayi tare da cewa "kaiii amman Nayi tsananin murna yanxu daga nan office
xan fara xuwa na same shi mu yi magana "

Cikin jin dad'i sadeeq ya rungume daddy yana cewa "thank u daddy Allah ya bar mana kai "

"Ameeen sadeeq amman gaskia baxa'a ja da nisa ba tunda duk ansan juna ciki da bai " Cewar mumy

"k'warai kuwa Allah ya tabbatar da alkhairi Allah ya xa6a abin da yafi alkhairi " fad'in daddy

"Ameeen thumma Ameeen "

Mumy da sadeeq suka fad'a sannan mumy ta kalli sadeeq tace "je ka kirawo musaddiq mu yi breakfast "
"Okay "
Sadeeq ya fad'a yana tashi tsaye bedroom d'in musaddiq ya shiga turus yaja ya tsaya ganin musaddiq
xaune kan carpet ya had'a kai da gwiwa daga ganin yanda yayi ba k'aramin damuwa ce a tattare da shi
ba.

Cikin sanyin jiki sadeeq ya k'arasa wurin shi tare da dafa shi yace "musaddiq lafia, me yafaru? "

D'ago kanshi musaddiq yayi ya xubawa sadeeq idanun shi da suka yi jawur dasu a firgice sadeeq ya sake
cewa "lafia brother me yafaru? "

Ya fad'i yana tatta6a jikin shi ko ciwo yaji nan dai bai ga wani alamun ciwo ba da sauri Yah sadeeq ya
mik'e xai je ya kirawo su daddy, musaddiq kamar yasan nufin shi caraf ya rik'e hannun shi tare da cewa

"na rok'e ka brother kada ka fad'a wa su daddy please "
Dawowa sadeeq yayi tare da cewa "okay naji fad'a min damuwar ka Idan kaki xan fad'a wa su daddy"

Murmishin yak'e musaddiq yayi tare da cewa "Naji brother "

Nuna shi yayi da d'an yatsa yace "are you sure? "

"yes " Cewar musaddiq dak'yar don ji yayi xuciyar shi na wani irin xafi, "toh fad'a min "
Cewar Yah sadeeq yana rik'e hannun musaddiq.

D'an shiru yayi yana tunanin me xai cewa sadeeq xai fad'a mishi yarinyar da yake so ita shi ma yake so
nooo i can't ko da kuwa son shi xai xama ajalin shi baisan ya kamu da son mufidah ba sai da Yah sadeeq
ya furta yana son ta yanxu shi ya xai yi me xai cewa brother.

D'ago kanshi yayi ya kalli sadeeq yaga ya xuba mishi ido alamar shi yake saurare, d'an kwakwalo
murmishin yak'e yayi yace "brother daman fah kawai ina tunanin yanda xan bar lecturing na koma
hospital da aiki nake don basa son na bar skul d'in sun dame ni da rarrashi so shine na xauna nake
tunanin mafita "

Tuntsire wa da dariya sadeeq yayi kafin yace "don wannan kuma shine kake sa kan ka cikin damuwa
kawai ka share su ka fara xuwa hospital bana son kana wahala "

"Yawwa brother thank u Allah ya bar min kai "
Cikin dariya sadeeq yace "hka nake so d'an k'anina bana son ina ganin ka cikin damuwa ko ciwo ji nake
kamar na dawo dashi jiki na nake ji bana son ganin 6acin ranka nafi son ko yaushe ka kasance cikin farin
ciki idan naganka cikin damuwa ji nake hankalina yana matuk'ar tashi bana samun kwanciyar hankali sai
naga kai ma ka samu"

Musaddiq rungume sadeeq yayi a hankali wasu hawaye suka xubo wa musaddiq yayi saurin sa hannu ya
goge su sannan ya saki Yah sadeeq

Mumy wadda take tsaye bakin kofar shigo wa bedroom d'in ta saki murmishin jin dad'i Kafin tace "aiken
kenan sadeeq ba kai ba wanda na tura ka kirawo nagaji da jira na biyo bayan ku "

Murmishi Suka yi bayan sun had'a ido tukunna kamar had'in baki suka ce "sorry mum "

Kamo hannun su tayi suka fito daga d'akin xuciyar musaddiq cike da tarin damuwa.

Bayan sun kammala breakfast d'in daddy ya tafi office hka shima sadeeq ya fito xai tafi don har ya shiga
mota musaddiq ya tsayar dashi suka tafi tare xai sauke shi a buk.

Yah sadeeq yana parking ya fito daga motar shi da musaddiq suna magana sai ga mufidah tayi parking
d'in motar ta sun fito tare da nabila, gaba d'aya hankalin musaddiq yayi kanta tayi mishi kyau sosae cikin
wata arabian gown bak'a ce hka mayafin da tayi rolling d'in kanta bak'i ne da yake fara ce kayan sun
amshe ta, musaddiq ji yake kamar ya ta a jikin shi ko yaji sassauci a cikin xuciyar shi yanda yake jin wata
xaxxafan son ta na sake kwaranya a cikin xuciyar shi wannan wacce irin masifa ce dak'yar ya iya saita
idanun shi daga barin kallon ta.
Sai da suka d'an gifta su sannan sadeeq ya ankare da ita don hka cikin sanyin murya yace "mufidah! "

Cikin sauri suka jiyo tare da nabila don ganin mai kiran nata da musaddiq ta fara had'a ido sannan ta kalli
sadeeq Wanda yake ta xuba murmishin farincikin ganin ta k'araso wa suka yi sannan suka gaisa da
sadeeq ko kallon Inda musaddiq yake mufidah bata yi ba ko gaida shi bata yi ba sai nabila shima

musaddiq yiwa sadeeq sallama yayi ya tafi xuciyar shi nayi mishi wani rad'ad'i dak'yar ya iya k'arasa wa
cikin office ya xube yana wani irin haki kamar wanda yayi tseren gudu.

Ganin musaddiq ya tafi yasa ita ma nabila ta wuce don ta basu waje cikin wani salon kallo wanda ya bawa
mufidah kunya yace
" Naga dai yanxu kamar kina sauri ki ban contact di'n ki zuwa anjima xan xo gida na same ki don akwai
muhimmiyar magana da xamu yi "

Ya K'arasa fad'i yana mik'a wa mufidah wayar shi kar6a tayi tare da shigar da contact di'n ta sannan ta
mik'a mishi tana cewa "Okay ba matsala sai ka xo"
Da hka sukayi sallama ya shiga motar shi ya tafi ita kuma mufidah ta shige department d'in su tana cewa
tatsuniyar gixo baxa ta shige k'ok'i ba don tsab ta karance shi tun ranar birthday di'n Yah Omar.

Bayan sun fito a lecture's mufidah take sanar wa da nabila yanda suka yi da sadeeq Sam nabila batayi
mamaki ba don yanda yake bin ta da kallo ranar partyn Don hka nabila tace
"Ki gode wa Allah mufidah don samun miji kamar sadeeq a wannan xamanin sai an shirya ya tattara
komai gashi kyakkyawa duk da musaddiq yafi shi kyau ga kud'i da mutunci sannan ga fara'a Ba kamar
musaddiq ba Allah yarinya Idan ya furta miki so kawai ki bada kai bori ya hau don ni fah mun gama shirya
kan mu da Yah Omar "

Cikin dariya mufidah tace "ae na d'ago jirgin na ku tuntuni to Allah ya tabbatar mana da alkhairi "

"Ameeen sister tashi mu gudu gida don Yah Omar xai xo kuma gashi ke ma Kina da bak'o "

"alright mu je "
Cewar husna tana yin gaba sun xo wajen da suke parking wurin ba mutane sosai kafin su k'arasa wajen
motar sai takalmin mufidah ya gurd'e ta ta tafi xata fad'i k'asa caraf taji an rik'e ta ta fad'o jikin mutum
k'amshin turaren shi kawai taji ta fahimci ko wane don hka da sauri ta tashi daga jikin shi tare da kallon
shi tana jin wani yanayi tattare da ita Idan ta kalli cikin kwayar idon shi yayin da shi ma musaddiq ya xuba
mata ido sai dai yau ba kallon tsanar ta take hangowa acikin kwayar idon shi ba maganar da nabila tayi ne
ya dawo dasu hayyacin su don hka da sauri ya shige daman jiran fitowar ta yake domin ya sake sata cikin

idanun shi cikin sanyin jiki mufidah take driving tana tunanin irin kallon da yake mata wanda yasha
banban da na ko yaushe...........





Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*



*written by*

Aishat A muh'd


♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*




_Wannan page naki ne k'awata khadijah neena cool (niger), Allah ya bar xumunci ya bar mu tare ina miki
fatan alkhairi_

*Page 9*




Da yammacin ranar da wajen karfe 5 sadeeq ya fito cikin shirin tafiya gidan su mufidah yaci gayu cikin
wata tsadaddiyar shadda milk colour an yi mata aiki da brown din xare sai ya sanya takalmi brown da
hula brown mai ratsin milk a jiki gaskia yayi kyau sosae daman shi gwanin sa manyan kaya ne k'ananun
kaya basu dame shi ba wannan sai musaddiq.

A falo ya tarar da mumy da musaddiq suna xaune mumy tana faman lalla6a shi ya ci abinci don yinin yau
gaba d'aya ta kasa gane d'an nata K'arasa wa yayi Inda suke ya xauna tare da cewa
"me yake damun shi ne Mumy?"

"nima yanxu na gama tambayar shi yace min ba komai kuma ban yarda ba don yau gaba d'aya cikin
damuwa yake "

Cewar mumy kenan fuskar ta cike da damuwa, sadeeq ne ya kalli musaddiq shima fuskar shi d'auke da
damuwa ya rik'o hannun shi tare da cewa

"Haba brother ka fad'a mana damuwar ka mana ko xamu iya taimaka maka da wani abin "

Shiru musaddiq yayi ya rasa me xaice musu "tell me please what wrong with u ?" sadeeq ya sake fad'i
duk farincikin da yake cikin xuciyar shi na xuwa wurin mufidah amman sai yaji farincikin ya kau
sakamakon ganin tilon k'anin shi cikin damuwa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login