Showing 87001 words to 90000 words out of 92754 words
Chapter 30 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf
xaki guje ni ba"
Bakin ta takai saman le6en shi ta sumbata kafin ta d'ora hannun d'aya cikin nashi tace
"nayi alk'awarin kasance wa da kai my man har k'arshen rayuwa ta i luv u musaddiq "
"i luv u too habibty "
Ya k'arasa fad'i yana shigar da bakin shi cikin nata soyayya sosai suka gwada wa junan su a wannan
lokacin don Mufidah ma ta mance da wani ciwo sai da ta dawo dai dai tukunna ta sanya mishi kukan
shagwa6a ai kuwa ya dunga yi mata dariya kafin daga bisa ni ya 6ige da rarrashin ta.
Su Mumy sunyi matuk'ar farin ciki da wannan albishir d'in da Musaddiq yayi musu na samun jika, daman
tuni ta dauke Afnan daga wurin su tana hannun ta duk da kuwa gida d'aya suke zaune, su umma ma
sunyi farinciki sosai, amman babu wanda ya kai Muh'd farinciki abokin shi ya samu matar da yake so
gashi har zuri'a zata fara shiga tsakanin su, lokacin da Musaddiq yake sanar da Muh'd d'in bayan ya gama
taya shi murna ne yace
"aboki wai ina ciwon xuciyar taka ne? "
"yaro tun da zuciya ta samu abin da take so, ai kuma shikenan "
Dariya Muh'd yayi kafin yace
"Toh Allah ya k'ara lafia "
"Amin, don wani time d'in fah sai a hankali tana yi min ciwo, sai dai ina kok'ari wajen kiyaye abin da zai
taso min da ciwo, kaddara tawa kenan Muh'd "
Wani mugun tausayin shi ne ya kama Muh'd, nan ya yi mishi addu'ar Allah ya bashi lafia, kafin su yi
sallama da junan su............
Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page*
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com
*PAGE 59*
Cikin kwanciyar hankali suka cigaba da rainon cikin Mufidah, su Musaddiq sai rawar kai ake za'a
samu baby, kula da soyayyar Mufidah kullum k'ara k'aruwa take cikin zuciyar shi.
Ta 6angaren Mufidah duk wani kyautata wa tana yi mishi sosai, bata yi duba da irin son da yake mata ta
wahalar dashi ba, biyayya sosai take mishi duk wani abin da yake so take yi mishi, tana kok'arin kiyaye
abin da zai d'aga mishi hankali har ciwon shi ya tashi.
Duk lokacin da ta tuna sanadiyyar son ta ne, ya kamu da ciwon zuciya har kuka take yi mishi na tausayin
shi, a haka cikin ta yake ta girma sosai, gashi babu wani laulayi sosai, sai dai yana sanya ta kwad'ayi.
Ana cikin haka nafisat matar Muh'd ta haihu an samu baby boy, waiii murna wajen Musaddiq ba'a
magana, kamar Mufidah ce ta haihu haka yake jin shi.
Ranar suna sun yi hidimar suna sosai inda jaririn yaci sunan Musaddiq, rasa inda Musaddiq zai sa kanshi
yayi don farinciki hak'k'a Muh'd aboki ne na gari, ya d'auke shi tamkar Yah sadeeq d'in shi, ya kashe kud'i
sosai Musaddiq a wannan sunan,komai yak'i yarda Muh'd yayi sai shi, Mumy, daddy da Mufidah ma sun
yi hidima sosai,sai dai fatan Allah ya raya lil Musaddiq.
*AFTER 2 MONTH'S*
Mufidah zaune take a parlourn Mumy akan kujera, ta mik'e k'afafun ta saman centre table, tana cin
wani gashashshen nama ya sha cabbage, tomatoes and onions akai ga yaji mai dad'i a gefe tana
dangwala dashi, gefe d'aya kuma ga coconut drink wanda yasha milk gashi yayi sanyi, cin abinta take
hankali kwance.
Duk wannan hidimar Mumy ce tayi mata, don ta hana ta yin wani aiki ko girki, kuma duk abin da tace
tana so Mumy na kok'ari wajen sama mata shi, gaba d'aya ta duk'ufa wajen cin naman, batasan
Musaddiq ya shigo parlourn yana tsaye sai kallon ta yake dawowar shi daga hospital kenan.
Ta d'auka naman a jikin fork tana kok'arin kai wa bakin ta, taji an rik'e hannun ta da ta da yake d'auke da
fork d'in, da d'an sauri ta juya kanta baya suka had'a ido da Musaddiq, sakarwa junan su murmishi suka yi
cikin so da kauna, kafin Musaddiq ya juya hannun ta zuwa wajen bakin shi ya sanya naman har da wani
lumshe idanun shi saboda dad'in shi, kafin ya bud'e su ya watsa kan fuskar Mufidah.
Wadda ta ta6e fuska tana shirin yin kukan shagwa6ar da ta saba yi mishi, ya bud'e bakin shi yace
"Wow gaskiya Mumy tana ji da ke, irin wannan cin dad'i haka, sai an bari na tafi hospital take shirya miki
abin dad'i don kada na ci koh, aikuwa wannan ya zama rabo na daman yunwa nake ji "
Ya k'arasa fad'i yana d'aga mata gira, turo bakin ta tayi gaba tare da cewa
"ni dai gaskiya a'a, ai ba laifi na ne ba, babyn kane yake son ci "
Mak'e kafad'a yayi tare da cewa
"uhm uhm ni ban yarda ba, kullum ai tace wa baby na yake son abu don dai bashi da bakin magana "
Yana gama fad'in haka ya kar6e plate d'in hannun ta, zama yayi kusa da ita sannan ya fara ci ,ganin haka
yasa Mufidah fara tuttura k'afa zata fara kukan shagwa6a, dariya ya fara yi mata tare da sanya hannun shi
ya d'an ja kumatun ta yace
"sweet baby rigima ko Afnan kin fita rigima, toh dai wannan duk kukan shagwa6ar ki sai na cinye "
Ya k'arasa fad'i yana mata gwalo, ai kuwa ta saki kukan shagwa6ar da babu hawaye sai goge idon da ake,
shi kuwa Musaddiq sai tsokanar ta yake yi, gefe d'aya kuma yana cin naman tare da shan coconut drink
d'in nan.
Ana cikin haka sai ga Mumy ta shigo parlourn, ta tarar da Musaddiq yana faman tsokanar ta, girgiza kanta
tayi tana murmishi idan da sabo ta saba da rabon wannan rigimar kullum, k'arasa wa tayi cikin parlourn
tare da kallon Musaddiq tace
"Ohhh ni, Musaddiq me yasa ka fiye tsokanar ta ne? "
Turo bakin shi yayi irin na shagwa6ar nan yace
"Mumy kullum sai kin nuna son kai, idan na tafi hospital sai ki ta bata abin dad'i tana ci ni ba'a ajiye min "
Murmishi Mumy tayi tare da cewa
"kai ai babba ne kuma kaga abin da take d'auke dashi, dole ana bata abin da take so, ina ce jiya wurin
karfe 10 na dare ka fita samo mata shawarma da take son ci"
D'an sosa kai yayi yana kallon ta, don ya tuna rigimar da tayi mishi jiya da dare, sai da suka kwanta bacci
ta tashe shi ita shawarma take son ci, jiki na rawa ya tafi siyo mata, ko da ya dawo rabin d'aya ta iya ci a
duk yawan da ya siyo mata, kafin yace
"Ehemm na tuna Mumy, but ni ana ajiye min komai aka yi mata tun da ina taya ta rainon babyn "
Murmishi Mumy tayi tare da cewa "shikenan za'a ajiye maka, amman na yau a hak'ura a bar mata"
Mik'a wa Mufidah plate d'in yayi yana wani langa6e kai, kallon shi tayi sai taji ya bata tausayi, cikin murya
k'asa k'asa don kada Mumy taji tace
"My M, na bar maka kaci, daman na k'oshi "
Ta k'arasa fad'i tana yatsina fuska, murmishi yayi tare da jan karan hancin ta yana cewa
"Hmm da gaske kike habibty? "
D'aga mishi gira tayi, nan ya d'an huro mata kiss da bakin shi, aikuwa ta lumshe idanun ta tare da bud'e
su alamar ta kar6i sak'on nashi, lokaci d'aya suka sakarwa junan su murmishi.
Mumy ma murmishin ta saki, zuciyar ta fal farinciki da kwanciyar hankalin d'an nata, kuma tana jin
dad'in yanda Mufidah take bashi kula wa sosai.
"Mumy ta bar min ba ashe ta k'oshi ma ta tsaya yi min rigima gashi har ya fara sanyi "
"Hmm ka dai dame ta shi yasa ta bar maka "
"Da gaske nake fah Mumy, koh Sweet baby? "
"naji shikenan "
Cewar Mumy, nan ya fara ci suna d'an ta6a hira har ya gama, ya sanya hannu zai janyo tissue ya goge
bakin shi, da sauri Mufidah ta sanya hannu ta dauko mishi tissue paper d'in ta bashi, kar6a yayi tare da
cewa
"thank u habibty, Allah yayi miki albarka yasa ki haihu lafiya "
Cikin jin dad'in addu'ar da yayi mata tace
"Amin sweetheart ".
Tashi yayi tare da cewa
"Mumy yau na gaji, zan d'an je na huta kafin lokacin mangarib yayi "
Gid'a kai Mumy tayi tare da cewa
"Okay "
Kallon Mufidah yayi suka had'a ido yayi mata alamar da ido ta taso su tafi, langa6e kai tayi tana nuna
mishi Mumy na wurin, amman sai ya d'aga kafad'a alamar shi ina ruwan shi .
Mumy tana kallon shi sai kawai ta tashi tana cewa
"Mufidah ki tafi kema ki huta kin ji 'yata "
Tana gama fad'in haka ta wuce kitchen, gwalo Musaddiq yayi mata don yana kula da kunyar da ta
kamata, d'an hararar shi tayi irin ta wasan nan.
"ta so mu tafi habibty"
"zo ka d'auke ni idan kana son mu tafi "
"kai babyna agajiye nake, gashi kin k'ara nauyi sosai "
"toh shikenan tun da baza ka iya ba, naga kuma babyn ka ne ya samin nauyin tun da ba haka nake ba",ta
fad'a cikin shagwa6a .
'Yar dariya yayi kafin ya k'arasa inda take yana cewa
"Sorry 'yammata na, duk nauyin da kika yi Musaddiq d'in ki bazai kasa d'aukar ki ba "
Hannun shi ya sanya tare da taimaka mata ta tashi tsaye, sannan ya d'auke ta cak suka fita daga side d'in
Mumy zuwa nasu.
Yana shiga cikin parlourn wani k'amshin turare mai dad'i ya ziyarci hancin shi, ko'ina tsaf dashi cikin
zuciyar shi yana godiya ga Allah da ya azurta mishi Mufidah matsayin matar shi, duk da girman cikin da
yake jikin ta hakan bai hana ta tsaftace ko'ina ba, duk buk'atar da yazo mata da shi zata kar6e ta ko a
fuskar shi baza ta nuna mishi rashin jin dad'in hakan ba, ko da kuwa bata so, shi yasa kullum sonta yake
k'ara shiga cikin zuciyar shi.
Bai ajiye ta a ko'ina ba sai a bathroom, kallon ta yayi sai yaga tayi murmishi idan da sabo yaci ace ta saba
da hakan, tun da kullum ya dawo daga office idan zai yi wanka tare suke yi, ba ma iya na lokacin ba
kullum ma haka suke abin su.
Bayan sun gama wankan sun fito ne, kowanne d'aure da towel akan bed ya zaunar da Mufidah tare da
zama kusa da ita yace
"habibty yaushe zamu fara zuwa siyayyan kayan babyn mu? "
Kallon shi take cikin mamaki kafin tace
"Sweetheart ina ce last week ka tak'ura wa Mumy taje dubai ta siyo komai"
Murmishi yayi tare da cewa
"Duk da haka baby na, ina son mu je ki za6i ra'ayin ki "
Girgiza kai tayi tana jan kunnen shi d'aya da hannun ta tace
"Wannan kunnen baya jin abin da nace mishi yau da safe, ba haka nace mishi a bar maganar nan ba "
Yatsina fuska yayi tare da cewa
"Wash habibty it hurts fah, zan rama nima "
Dariya ya bata ganin yanda yake sosa wurin da ta rik'e, kafin tace
"sai dai ka rame d'an samari "
Zaro ido yayi kafin yace "tabd'ijam baby nine d'an samari? "
Cikin dariyar tsokana tace "Ehh mana "
Janyo ta yayi cikin jikin shi yana gyara mata gashin kanta tare da cewa
"lallai baby kin rainani da yawa, ni yanzu daddy ne ina da Afnan ga shi kin kusa haifa min new baby's "
Ya k'arasa fad'i yana shafa cikin ta tare da kissing d'in shi.
"baby's naji kace ba?"
Lumshe idanun shi yayi tare da bud'e su yace
"Yes of course insha Allah baby's zaki haifa min "
Kwa6e fuska tayi tace
"Wayyo Musaddiq ba kasan yanda ake shan wahalar haihu ba ne "
Dariya ta bashi ganin yanda tayi, cikin lalla6a ta yace
"Haba wacce wahala kuma baby, lafiya zaki haihu mybe ma kina bacci zan tashe ki nace kin haifa mana
baby "
Sosai maganar shi ta bata dariya, nan ta shiga yin dariyar shima ya taya ta, tsaya wa yayi da tashi dariya
ya zuba mata ido yana kallon ta cikin wata irin sha'awar ta,
"I luv u Mufidah "
Ya furta hakan cikin muryar shauk'in ta,
"I luv u too "
Mufidah ta mayar mishi da martanin maganar.
Sake matse ta yayi cikin jikin shi yana lalubar bakin ta, kissing d'in ta ya fara yi, nan fah ya fara aika mata
da zafafan kalamai tare da sak'onnin shi zuwa gare ta, cikin en mintuna suka fara shiga wata duniyar ta
daban.
*** *** ***
Cikin Mufidah ya shiga watanni na 8 ya girma sosai, duk ta bi ta kumbura ga girman ciki, zama dakyar
tashi dakyar don wani lokacin sai an taimaka da tashi tsaye.
Ba k'aramin tausaya mata Musaddiq dasu Mumy suke ba, kullum cikin bata kula wa da addu'ar Allah ya
sauke ta lafiya duk wani masoyin ta yake, don cikin yafi na Afnan girma sosai kuma tafi shan wahala.
Gaba d'aya ta k'agu taga ta haihu ko ta huta da wannan wahalar da take faman sha, wani lokacin ita take
k'arfafa wa Musaddiq gwiwa ganin duk yanda ya karaya ganin yanda take shan wahala.
Sam hankalin shi yanzu ba'a kwance yake ba, hospital d'in ma yanzu bai fiye zuwa ba sosai, ko yaje ma
hankalin shi yana gida, haka zai dawo gidan ya sata a gaba yayi ta kallon ta yana tambayar ta ko akwai
inda yake mata ciwo, ko tana son wani abin.
A haka lokaci yana tafiya, rana ku na wuce wa har cikin Mufidah ya shiga wata na tara da sati uku, ta
kusan cinye wata na goma shiru babu alamar haihuwa, sai dai ciwon mara da baya da take yi, wannan
kuma daman idan ciki ya tsufa haka zaka yi ta fama har zuwa lokacin da za'a haihu lafiya.
Musaddiq gajiya yayi da ganin yanda take shan wahala duk ta rame sai kumburi da k'aton ciki da farin da
ta k'ara yi, ya fad'a wa Mumy kawai ayi mata cs a cire cikin, nan Mumy tak'i yarda sam saboda duk wani
gwaje gwaje da aka yi mata an tabbatar lafia qlau take da babyn, sai dai kawai lokacin haihuwar ne da bai
zo ba.
Sai da cikin Mufidah ya shiga wata 10 dai dai, a wata safiyar monday ta tashi da nak'uda, nan da nan
suka wuce hospital d'in Dr Musaddiq, kai tsaye labour room na daban aka wuce da ita.
Musaddiq kasa fita yayi daga room d'in yana rik'e da ita a jikin shi, ga Doctor Aishat nd nurse Billy ladan
suna kanta lol, duk wani taimakon da ya kamata su yi mata suna mata.
Mufidah wahala dai tasha a wannan lokacin, don sai ta ga haihuwar Afnan sauk'i gare ta fiye da wannan,
Musaddiq har da hawayen tausayin habibty d'in shi, tun safe ake fama har zuwa daf da mangarib sannan
Allah ya sauke ta lafiya, ta haihu beautiful baby's boy's d'in ta, masu kama da Musaddiq like father like
son.
Tuni Musaddiq mai hawaye ya koma yin dariyar farinciki, bayan angama gyara su tsaf ne an kaisu d'akin
hutu, tukunna su Mumy suka samu ganin su.
Kowanne ka kalle shi yana cikin farinciki da murna da wannan k'aruwar da aka samu ta yara biyu maza,
Musaddiq wanda baki yak'i rufuwa yana zaune kusa da Mufidah da take baccin wahalar da ta gama sha.
Dr Muh'd wanda ya ke d'auke da d'ayan babyn ya kalli Musaddiq yace
"lover boy sai a daina kukan tausayi a koma na farinciki "
Gaba d'aya aka kwashe da dariya, yayin da Musaddiq ya harari Muh'd, sai washe gari da safe aka sallame
su zuwa gida, kafin su k'araso tuni 'yan uwa da abokanan arzik'i sun zo don taya su murnar samun
kyautar Allah wanda kud'in ka ko mulkin ka bazai sa ka samu ba, sai dai idan Allah ya baka, Allah ya bamu
yara masu albarka ya kare mana su tare da basa ilimi mai amfani, ya tarbiyyantar mana dasu irin
tarbiyyar addinin islam, Amin.
Mumy dawo da Mufidah tayi side d'in ta domin bata kula sosai, tana kuma taya ta rainon 'yan biyu don
rainon su sai da taimako, hakan kuwa ba k'aramin tak'ura wa Musaddiq aka yi ba, shima sai ya tattara ya
dawo side d'in cikin d'akin shi na da, Afnan sai rawar kai ake an samu k'anne har biyu.
Daren ranar Musaddiq ya shiga d'akin Mufidah ya tarar da ita kwance kan bed, ga yaran kwance kusa da
ita suna baccin su hankali kwance, k'arasa wa yayi ya zauna kusa da k'afafun ta yana cewa
"Babyna kin yi bacci ne? "
Tashi tayi tana murmishi tare da koma wa kusa da shi ta kwanta a cikin jikin shi, k'ara gyara mata
kwanciyar yayi a jikin shi yanda zata fi jin dad'i sosai,
"ban yi bacci ba, ina jiran ka ne don nasan zaka shigo "
Mufidah ta bashi amsa, wani dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar shi, kullum Mufidah k'ara shiga zuciyar
shi