Showing 12001 words to 15000 words out of 92754 words

Chapter 5 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf

10 Jul 2025

2464



Cikin murmishin yak'e yace "ni fah kada ku damu mumy and brother bana jin dad'in jiki nane amman ba
wani abun ba ne "

Sam basu yarda da abin da yace ba amman tun da har yak'i sanar musu to abin babba ne, hka dai suka
bashi shawara akan ya dage da addu'a sosai akan abin da yake damun shi godiya yayi musu sannan ya
tashi ya tafi d'akin shi ya rufe kofa tare da jingina a jikin kofar xuciyar shi cike da tunanin mufidah.

Acan palo kuwa da kallo suka bishi cikin tsananin tausayin shi, kafin kuma Yah sadeeq yayi wa mumy
sallama yana sanar da ita gidan su mufidah xai je, nan tayi mishi addu'ar dawowa lafia tare da bashi
sak'on ya gaida mata da mufidah.


Musaddiq kuwa dakyar ya iya jan kafar shi xuwa bakin bed d'in shi ya janyo drower din jikin bed side ya
janyo wani d'an k'aramin littafi wanda kallo d'aya nayi mishi na tabbatar da diary din shi ne Wanda yake
rubuta mahimman abun da ya shafi sirrin shi a ciki, biro ya d'auko ya buge tsakiyar page ya fara rubutu
kamar hka.......

*NAYI SAKE!*

_Tun ranar da na fara d'ora kwayar idanuna akan ta nake jin wani abu a tattare da xuciya ta da jiki na,
ban tabbatar da son da nake mata sai ranar da ta xuba min juice a jikina na kaita gida na ta wanke min a
cikin daren da na taimake ta daga hannun wasu 6ata gari har jiki na ya had'u da jikin ta a ranar na
tabbatar da sonta a cikin xuciya ta ina niyyar neman soyayyar ta............_


_sai dai kash d'an uwana yaya na da nake dashi shi kad'ai ya furta yana son ta yayana mai kauna ta da
son bani farinciki a ko da yaushe, na hak'ura da ita har abada saboda nasan nayin saken da nasan baxan
ta6a samun ta ba a rayuwa ta_


_son ki ne xai xama ajali na don nasan har na mutu baxan ta6a dai na k'aunar ki ba, i luv yhu so much
*M*, i really luv yhu_.

Yana gama fad'in hka ya rufe littafin tare da ajiye wa ya fad'a kogin tunani sosai ga son mufidah yana
k'ara nukurkusar xuciyar shi lokaci d'aya wani mugun ciwon kai ya kama shi cikin en mintuna wani
xaxxafan xaxxa6i ya rufe shi sai karkarwa sanyi yake sosai jikin shi ya d'auki wani mugun xafi lokaci d'aya
kuma ya fara wani jan numfashi wanda dak'yar ya ke fita.


Yah sadeeq bayan yaje gidan su mufidah anan farfajiyar gidan ya had'u da Yah Omar yana kok'arin tafiya
gidan su nabila nan suka rungume junan su sannan suka yi musabiha cikin murmishi Yah Omar yace
"Hmmm wannan gayun dai nasan xuwa wurin mutuniyar kayi ba xuwa na ne ba "

Cikin dariya sadeeq yace "yes nawan ashe ka gano hkan "
Tafawa suka sannan suka juya xuwa cikin gidan bayan sun gaisa da umman su mufidah sannan Yah Omar
ya kai shi palon saukar bak'i daga hka yace
"toh ni Naga ma aiki na xan tafi wajen tawa matar to be Insha Allah"
"Yayi kyau friend ngde sai ka dawo "

"ba Godiya tsakanin mu sadeeq mun riga da mun xama en uwan juna sai mun yi waya bye "

Yana gama fad'in hka ya fice daga falon da sauri , bai fi mintuna 5 da tafiyar Yah Omar mufidah ta shigo
falon cikin sanyayyiyar muryar ta mai dad'in gaske tayi sallama cikin murmishi sadeeq ya amsa sallamar
cikin sauri ya mik'e tsaye ya kar6i babban plate di'n dake hannun ta ya ajiye kan table d'in tsakiyar palon
tukunna yayi mata nuni da ta xauna ae kuwa ta samu waje ta xauna tare da gaida shi nan ya amsa yana
kallon ta don tayi mishi kyau sosae gashi ta suturta jikin ta da hijab babba mai hannu hakan ba k'aramin
dad'i yaji ba xuciyar shi ta Kara k'aunar ta bayan sun gama gaisa wa ne ya fara janta da er hira ganin ta
kasa sakin jikin dashi daga K'arshe ya fara da yi mata bayanin abin da ya kawo shi

Tsugunna wa yayi a gaban ta amman bai ta6a mata jiki ba ya kwantar da murya a nutse ya fara cewa
"mufidah abin da ya kawo ni wajen ki ba komai bane sai neman soyayyar ki tun lokacin da na fara ganin
ki kuma auren ki xanyi ki bani dama na nuna miki son da nake miki "

shiru mufidah tayi tana tunani shi kuwa Yah sadeeq cigaba wa yayi da cewa "say something mufidah
please "

D'an ajiyar xuciya ta yi cikin jin kunyar shi tace "sai nayi tunani "
"Okay ba matsala Allah yasa naji kyakkyawan result "
murmish kawai yayi ya dan sha juice and snacks din da taka wo mishi suna er hira har xuwa gabannin
mangarib sannan yayi mata sallama ya tafi.


Mumy ce ta fito daga bedroom d'in ta xata shiga kitchen ta tuna tun da musaddiq ya shige bedroom d'in
shi bai fito ba hka kawai taji gaban ta ya fad'i da sauri ta nufi bedroom d'in tana shiga ta tarar da
musaddiq lullu6e da bargo kato ya kudundune a ciki yana rawar sanyi ga numfashin shi dak'yar ya ke jan
shi cikin tsananin tashin hankali ta nufi kan bed d'in tana cewa
"Musaddiq!"




Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*




*written by*

Aishat A muh'd

♻ *E.W.F*




*Page 10*




Da sauri mumy ta k'arasa kan bed d'in ta bud'e rufar da musaddiq yayi da bargo da sauri ta janye
hannun ta lokacin da ta ta6a jikin shi taji xafi xau dashi cikin kid'ime wa Mumy tace
"musaddiq me yake damun ka? "

Cikin rawar sanyi da murya yace "way... wayyo mumy xax..... xaxxa6i ne yake damunaaa"

Ya K'arasa fad'i yana jan wani irin numfashi da yasa gaban mumy muguwar fad'uwa cikin tashin hankali
tace "sannu bari na kirawo Dr muh'd ya duba ka sannu "

Cikin sauri mumy ta d'auki wayar musaddiq da take gefen bedside ta nemo number d'in Dr muh'd bayan
ya d'aga yana tsokanar musaddiq ya d'auka shi ne sai da yaji muryar mumy cikin girmama wa ya gaida
mumyn yana godewa Allah da bai yi wata maganar da xai ji kunya ba, mumy ce take sanar mishi Yayi
sauri ya xo ya duba musaddiq bashi da lafia tuni hankalin Dr muh'd ya tashi ya katse wayar da sauri ya
d'ebe kayan aiki ya shiga mota gidan su musaddiq ya nufa .

Dr muh'd abokin musaddiq ne sosai tare suka yi karatu har suka dawo nigeria suna xumunci sosae gashi a
gari d'aya suke sai xumuncin Ya k'ara k'arfi har iyayen su suma suka k'ulla xumunci sanadiyyar yaran su,
Dr muh'd yana bala'in son musaddiq sosai gashi halin su yaxo d'aya kosan ko yaushe yana gidan amman
musaddiq baya xuwa gidan su sosai sai ya kama.

Cikin en mintuna Dr muh'd ya k'arasa gidan kai tsaye d'akin musaddiq ya nufa a bakin kofa yayi kici'bis da
mumy tana ta safa da marwa ta kasa xama waje d'aya, d'akin ya shiga nan ya fara duba jikin musaddiq
cikin k'ware wa da iya aikin nashi.

Xaune na hango Dr muh'd ya xuba tagumi yana kallon musaddiq wanda yak'i yarda Yayi mishi allurar
bacci ko ya samu ya huta cikin damuwa d'auke a fuskar Dr muh'd yace
"my friend mene kasa a ranka hka me yake damun ka da xaka sa tunanin abu a ranka wanda xai janyo
mata wata matsalar, haba musaddiq kamar ba likita kake ba kene ma mai bawa wani shawara ma ya rage
tunani balle kai "

Kallon shi musaddiq kawai yake cigaba yayi da maganar shi yana cewa "ina son ka fad'a min matsalar ka
yanxu na gani ko Allah xai sa na baka wata shawarar ka daina barin abu a ranka kana tunani my friend "

D'an murmishin yak'e musaddiq yayi tare da cewa "me ka gano yake damuna aboki? "

Cikin tausayin musaddiq yace "naga jinin ka ya hau fah sannan yanayin bugun xuciyar ka ya k'aru fiye da
yanda mutum mai cikakken lafia take tell me what happened to you my friend? "

Musaddiq ya bud'e baki xai yi magana kenan Yah sadeeq ya turo kofar ya shigo d'akin hankalin shi a
matuk'ar tashe kama hannun musaddiq yayi yana cewa "brother me ya same ka ne yanxu mumy take
kirana a waya baka da lafia "

Jiyo wa yayi kan Dr muh'd yana cewa "Doctor sanar da ni abin da yake damuwa da d'an uwana kada kace
min wani babban ciwo ne please "

Yah sadeeq ya k'arasa fad'i idanun shi taf da hawaye cikin tausayin Yah sadeeq Dr muh'd ya bud'e baki xai
yi mishi bayanin abin da yake damun musaddiq sai suka had'a ido da musaddiq ya marairaice fuska tare
da yi mishi alama da hannu yana rok'an shi kada ya fad'a wa Yah sadeeq gaskiar abin da yake damun shi.

Cikin sanyin jiki Dr muh'd yace "Yah sadeeq xaxxa6in typhoid fever ne yake damun shi amman Insha Allah
xai samu lafia ka kwantar da hankalin ka "

Hannun Dr muh'd ya kamo yana cewa "Okay doctor thank u but ina son ka bashi kula wa sosai bana son
wani abu ya faru da k'anina "

"xanyi iyakar kok'ari na yah sadeeq kuma xai xamu lafia da sauri Insha Allah "

Rungume Dr muh'd yayi cikin jin dad'in abin da ya fad'i sannan ya dawo kan musaddiq tare da tatta6a
jikin shi jin xaxxa6in ya sauka yasa shi sakin wata ajiyar xuciya nan ya dunga yi mishi sannu duk motsin da
yayi hka ma mumy ta shigo suka had'u suna lalla6a shi Dr muh'd yana gefe xuciyar shi cike da tunanin me
musaddiq yasa a ranshi har xai kamu da hawan jini yana samun duk wata kulawa a wajen iyayen shi da
d'an uwan shi.

Har Dr muh'd ya tafi bai samu damar ke6ewa da musaddiq ba yaji abin da yasa a ranshi kuma me yasa
yak'i yarda Yah sadeeq yasan gaskiar abin da yake damun shi yasa shi yin k'arya da wannan tunanin ya
k'arasa gida.


Cikin k'wanaki 2 musaddiq yana fama da wani xaxxa6i da ciwon kai duk yabi ya rame ya sake yin fari sosai
iyayen shi sosai suke kula dashi don duk a xaton su xaxxa6in typhoid ne basu san gaskiar xancen ba daga
Allah sai musaddiq din sai Dr muh'd sune suka san ainahin abin da yake damun shi kuma Har xuwa yanxu
Dr muh'd bai samu damar yin magana da musaddiq ba.

A 6angaren Yah sadeeq kuwa ba k'aramin tsorata yayi ba da jikin musaddiq amman ganin ya fara samun
sauk'in xaxxa6in yasa shi hankalin shi ya d'an kwanta, yah Omar da husna da nabila sun xo dubiyar shi a
ranar da yafi samun sauk'i su kaxo har ya samu damar fito wa palo yana xaune suka shigo palon Yah

sadeeq yana musu jagora da mufidah ya fara had'a ido ae kuwa take yaji gaban shi ya fad'i bugun xuciyar
shi na sake bugawa da sauri da sauri.

Bayan sun gaisa da Mumy suka yiwa musaddiq Sannu da jiki dak'yar ya iya bud'e bakin shi ya amsa nan
aka xauna ana er hira tashi musaddiq yayi ya shiga bedroom din shi mumy ma ta shige kitchen tana had'a
wa su mufidah abin motsa baki ganin hka yasa nabila ta bita tana taya ta ,yah sadeeq kuma yaja Yah
Omar xuwa part d'in da yake ginawa wanda yake fatan su rayu da mufidah a ciki har sadeeq yana
tsokanar mufidah ko xata je ta ga ni ae kuwa ta danna mishi harara dariya suka kyalkyale da ita shi da Yah
Omar da hka suka fita daga palon aka bar mufidah ita d'aya xaune.
Tsawon 5 mint tana xaune kamar ance d'ago kan ki sai ta hango musaddiq ya fito daga cikin d'akin shi
yana dafe da kanshi alamar ciwo yake mai sai ta ga kuma ya fara layi kamar xai fad'i k'asa ganin yana
kok'arin fad'uwa yasa mufidah tashi da sauri ta nufi wajen shi tana xuwa dai dai wajen da yake tsaye yayi
baya xai fad'i da sauri ta rik'o shi to da yake k'arfin namiji da mace ba d'aya ba kawai sai yayi jikin ta ita
kuma mufidah yafi k'arfin ta kawai sai tayi baya xata fad'i sai taji kuma an fisgo ta xuwa cikin jikin shi ta
fad'a kan faffad'en kirjin shi da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido yana mata wani irin kallo gaba d'aya
idanun shi sun canja Kala sun kai wajen second talatin suna kallon junan su don mufidah hka kawai taji ta
kasa d'auke idanun ta daga cikin idon shi.

Ji tayi ya raba ta da jikin shi ya juya ya koma cikin d'akin, ita ma mufidah ta koma kan kujera ta xauna
tana tunanin wannan wanne irin mutum ne a taimaka mishi babu godia dama nasani na barshi ya fad'i
Cewar mufidah a fili har da Murgud'a bakin ta kamar yana ganin ta.

Tana xaune a hka sai ga mumy da nabila sun fito daga kitchen kowannen su rike da babban plate a
hannun su da sauri mufidah taje ta kar6i abun hannun mumy ta ajiye akan table ana hka sai ga Yah
sadeeq da Yah Omar sun dawo sun d'an ta6a abun da Mumy ta kawo musu sannan suka yi mata sallama
suka tafi tare addu'ar Allah ya bawa musaddiq lafia.

Mufidah ta kar6i soyayyar sadeeq duk da ba wani son shi take sosai ba kunyar shi ce tasa ta amince da
soyayyar shi kuma ganin irin son da yake mata ya wuce misali gashi bashi da makusa nan fah iyaye suka
shiga xancen.

Cikin kankanin lokaci aka tsayar da ranar auren sadeeq da mufidah, yah Omar da nabila to abune duk
ansan juna tun da dad'e wa ana xaune kusan tare sun xama kamar en uwan juna.

Shi kuwa musaddiq iyayen shi sun rasa gane kan shi yau lafia gobe cuta duk yabi ya rame ciwo kullum Cin
shi yake gashi yak'i gayawa Dr muh'd ko akwai wani taimako da xai yi mishi, kullum ya hau na jinin shi
maimakon ya sauka sai hawa yake har takai Dr muh'd ya duba shi a wata safiya bayan sun gama duba
patient din su hankalin Dr muh'd ba k'aramin tashi yayi ba ganin har xuciyar musaddiq ta fara ta6u wa
cikin tsananin tashin hankali Dr muh'd ya kalli musaddiq da yake kwance kan bed d'in asibitin yace
"yau baxan iya rabuwa da kai ba musaddiq sai ka fad'a min abin da yake damun ka, ko kuma na sanar
dasu daddy Don baxan xuba ido ka mutu a banxa ba "

Murmishin da musaddiq yayi sai da Dr muh'd ya tsorata bud'e baki yayi xai yi magana kenan wani tari ya
kama shi ya dunga yin tarin nan lokaci d'aya idanun shi da fuskar shi suka yi ja kanshi Dr muh'd yayi yana
mishi sannu gaba d'aya hankalin shi a tashe yake ya tsorata da jikin musaddiq sosai wani jan numfashi
musaddiq yayi yaraf kuma sai ya xube kan gadon kamar matacce cikin raxani da kad'uwa Dr muh'd ya fara
girgixa yana cewa
"na rok'e ka musaddiq ka tashi please "
Amman ina musaddiq bai ma san abin da yake yi ba.................





Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*




*written by*

Aishat A muh'd

♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*




*Page 11*




Amman ina musaddiq bai san ma yana yi ba, da gudu Dr muh'd ya fita daga room d'in yaje ya kirawo
wasu doctor's guda biyu nan suka had'u kan musaddiq suka fara kok'arin ceto rayuwar shi.

Sun dad'e sosai akan musaddiq Kafin Allah ya taimake su numfashin shi ya dawo dai dai nan suka sanya
mishi drip tare da yi mishi allurar bacci tukunna suka fita daga room d'in aka bar Dr muh'd yana xaune a
gefen shi ya xuba mishi ido yana kallon shi xuciyar shi cike da tsantsar tausayin shi.

Yini guda cur musaddiq yana bacci sai yamma sosai ya farka da Dr muh'd ya fara had'a ido lokacin da ya
farka cikin sauri Dr muh'd ya rik'e shi tare da cewa
"sannu musaddiq ya kake jin jikin na ka? "
Cikin kasala da sanyin murya yace "muh'd na samu lafia ngde sosae aboki "

Duba shi ya k'ara yi sannan ya taimaka mishi suka shige office d'in shi ruwan wanka mai d'umi Dr muh'd
ya had'a mishi bayan musaddiq yayi wanka tare da yin alwala ya fito ya gyara jikin shi sannan ya rama
sallolin da ake bin shi bayan ya idar ne ya kwanta kan doguwar kujerar da take cikin office d'in ya xurfafa
a tunanin mufidah kullum yana addu'ar Allah ya cire mishi son mufidah a cikin xuciyar shi amman kamar
k'ara mishi son nata ake ya rasa ya xai yi ya fitar da sonta daga cikin xuciyar shi.

Yana cikin wannan tunanin ne Dr muh'd ya shigo office d'in sau biyu yana sallama amman musaddiq bai ji
shi ba yayi xurfi a tunani sosai girgixa kai kawai yayi ya nufi inda yake kwance ya girgixa mishi kafad'a tare
da cewa
"Musaddiq!"
Firgigit ya dawo hayyacin shi yana kallon Dr muh'd da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login