Showing 39001 words to 42000 words out of 92754 words

Chapter 14 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf

10 Jul 2025

3047

d'in nan ka shigar min dashi gida"

Cikin rawar jiki maigadin ya d'auki trolley ya shige, shi kuma musaddiq ya shiga taxi d'in ya fad'a mishi
inda xai kai shi............



Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/19, 3:54 PM] Aishat A Muh'd ✍: *YAYI SAKE!*



*Written by*

Aishat A muh'd

♻ E.W.F



_lokacin da Allah ya sakkowa da bawan shi wata jarabta ya kasance cikin furta innalillahi wa'inna ilaihir
raji'un yayi ta maimaita har sai ya samu nutsuwa, ita rayuwa da muke ganin ta kowanne mutum da irin
tashi kaddarar don hka mu kasance cikin takatsantsan da rayuwa da bautawa Allah tare da kiyaye
dokokin shi don idan mutuwa ta tashi xuwa daukan mutum ba shawara ake dashi ba, don kowanne ita
yake jira tun da Allah swt yana cewa cikin suratul imran (kullu nafsin xa'iqatul ma'ut) kowanne mai rai xai
d'and'ani d'acin mutuwa, don hka ina kira a gare ku da mu kyautata mu'amalar da mutane domin ka
samu shaida mai kyau a bakunan mutane, sannan mu dage da aikata alkhairi da karatun al'Qur'an,
addu'o'i, nafilfilo, istigfari, salatin annabi da sauran su, a dunga kyautata iyaye ana musu biyayya, idan
kina da aure ana yiwa miji biyayya, ana yawaita yin xumunci da axumin nafila da sadaka, Allah yasa mu
dace duniya da lahira, Ameeen thumma Ameeen_.



*PAGE 30*




Ba k'aramin wahala mufidah tasha ba kafin Allah ya taimake ta ta haihu bayan sun gyara babyn Dr
Aishat sai da tayi wa mufidah d'inki don ba k'aramin k'aruwa tayi ba don tubarkallah babyn k'atuwa da
ita sai da ta duba ta ita da babyn ta tabbatar suna cikin koshin lafia tukunna suka fito a tare da sanar dasu
mumy an sauka lafia an samu baby girl, sosai sun yi murna nan suka kar6i babyn har suka shiga room d'in
mufidah da take kwance tana huta wa suna mata sannu, duk bata amsa ba sai ma bud'ar bakin ta tace
"Mumy ina sadeeq?"
Shiru mumy tayi ta kasa magana ganin hka yasa mufidah yunk'ura ta tashi xaune dak'yar saboda d'inkin
da aka yi mata cikin tashin hankali ta kuma cewa

"Ina sadeeq ne ina tambayar ku kun yi shiru?"

Abba ne yayi k'arfin cewa "ki kwantar da hankalin ki mufidah ciwon shi ne ya tashi likitoci suna kan shi
suna duba shi"

Hawaye ne masu xafin gaske suka xubo daga idanun ta komawa tayi ta xauna tana kuka k'asa k'asa acikin
xuciyar ta kuma addu'ar samun sauk'i take yi wa sadeeq, duk d'akin anyi shiru kamar ba mutane babu
wanda yayi iya yunkurin rarrashin mufidah sai nabila.


A can kuma room din da sadeeq yake likitoci sun dukufa akan shi wajen ceto rayuwar shi, ana cikin hka
nau'orar da take nuna yanda numfashin mutum yake tafiya tare da bugawar xuciya ta fara yin k'asa, a
firgice muh'd ya kalli yanayin numfashin shi ya ga yana sauka har xuwa 50 tuni muh'd ya rud'e cikin rawar
murya yake cewa

"Babban yaya kalle ni kada ka mutu please gashi mufidah ta haifa maka baby girl"
Kallon shi sadeeq ya tsaya yi kafin kuma yana jan wani numfashi dak'yar yace
"Muh'd taimaka ka d'auko min babyn na gani don Allah"

Cikin rawar murya yake cewa "to...to ina xuwa kada ka tafi ka barmu" murmishi sadeeq yayi mishi na
d'aga kanshi, da wani irin gudu Dr muh'd ya fice ya shiga room d'in da mufidah take ciki ya banka kofar da
k'arfi ya shiga gaba d'aya su mumy sun firgita da ganin shigowar muh'd bai bi ta Kansu ba ya d'auki babyn
ya fita da ita da sauri su ma suka bi bayan shi har da mufidah wadda dak'yar take tafia nabila na rik'e da
ita.


Tuni muh'd ya shige room din kafin su mumy su k'araso an rufe kofar dole suka tsaya hankalin su a
matuk'ar tashe.

Da sauri muh'd ya k'arasa wajen gadon yana nuna wa sadeeq babyn, bai da ikon daukan ta saboda drip
d'in da yake hannun shi hannun shi yasa ya shafi fuskar ta xuwa kanta kafin dak'yar ya furta
"Allah ya raya min ke ya albarkaci rayuwar ki Nana khadijah"
Kallon muh'd yayi tare da yin wani irin murmishi da sake tsurar da muh'd ya bud'e bakin shi dak'yar yace
"Muh'd ina son ka kular min da musaddiq, mumy, daddy, mufidah da kuma 'yata don nasan ke mutum ne
nagari, ka rokar min yafiya wajen iyaye na da d'an uwana da matata da duk wasu abokanan hurd'ata,
kace su yafe min Alhmdullilah nasan ba me bina bashi yanxu tun kafin ciwon yaci k'arfina na biya
kowanne ma'aikacin company na kud'in su, daga k'arshe muh'd ina son ka daukar min alkawari guda
d'aya"

Tari ne ya sark'e shi yana yi sosai gaba d'aya doctor's d'in nan biyu hawaye ne yake xuba a idanun su na
tausayi, muh'd kuwa kuka yake wiwi cikin rawar murya ya ce
"Fad'i alkawarin ka babban yaya insha Allah xan cika maka shi"
Sai da tarin ya lafa kafin yace "ina son kada ka bari kowanne namiji ya aure mufidah sai musaddiq d'ina
don nasan xai kular min da ita da d'an da na haifa don Allah muh'd ka cika min wannan burin"

Cikin kuka ya rik'e hannun sadeeq yace "na d'auki alkawari babban yaya xan cika maka shi amman baxa
ka mutu ba xamu rayu tare da kai ka tashi please"
Murmishi sadeeq yayi bai k'ara magana ba sai wasu hawaye da suke xuba a idanun shi yana kallon 'yarshi
a hannun sadeeq tana bacci.

D'aya daga cikin likitoci ne yace " muh'd numfashin shi yayi kasa sosai na 20 fah "
A wani irin xabura muh'd ya kai idanun shi kan nau'orar mai nuna yanayin numfashin mutum kafin yayi
wani yunkuri yaji sadeeq yana furta Kalmar shahada lokaci d'aya kuma nau'orar nan ta ba da sautin d'il
d'il d'il sai kuma ta d'auke, a lokacin shima sadeeq ya gama furta Kalmar shahada shikenan mai raba wa
ta raba kullu nafsin xa'iqatul ma'ut (kowanne mai rai sai ya d'and'ani d'acin ta).

Lokaci d'aya fuskar shi ta d'auki wani haske tayi kyau sosai a sake fuskar nan tashi kamar a kira shi ya
tashi, ja da baya muh'd ya fara yi da sauri d'ayan likitan ya kar6i jaririyar daga hannun muh'd ganin yana
k'okarin sakin ta, girgixa kai yake yana hawaye kafin ya dawo jikin gadon yana rik'e sadeeq yana cewa
"No no sadeeq kada ka tafi ka barmu don Allah ka tashi please"

Ina sadeeq ko motsi bai yi ba, xube wa yayi k'asa ya hau kuka sosai likitoci nan suna rarrashin shin shi
d'ayan ne ya rufe jikin sadeeq da wani farin mayafi har xuwa fuskar shi.

Xumbur muh'd ya mik'e yana kuka ya fito daga d'akin da gudu kici6is yayi da su mumy, daddy, mufidah,
Abba, umma, Yah Omar da nabila a tsaye suna jiran fitowar su ganin muh'd yana kuka yasa su xuciyoyin
su suka tsinke da fargaba.

Shi kuwa muh'd kasa magana yake sai kuka ta ina xai dubi idanun wad'annan bayin Allah ya furta musu
sadeeq ya mutu kawai sai gani suka yi ya bar wajen da gudu yana kuka ko ina muh'd ya shige sai ayi ta
kallon shi ganin babban likita kamar muh'd yana kuka.

Yaxo dai dai shiga office d'in shi suka yi karo da wani d'ago kan shi da xai yi suka had'a ido da musaddiq
dukannin su kallon juna suke cike da tashin hankali, musaddiq wanda yaga muh'd yana kuka ya fara
tunanin me yasa shi kuka hka, duk da yanda gaban musaddiq yake fad'uwa yayi yunkurin bud'e baki yayi
wa muh'd magana amman ina tuni muh'd ya shige office yasa key a jiki tare da jingina a jikin kofar ya na
wani irin kuka mai ban tausayi.

Har musaddiq xai bi bayan muh'd sai ya hango mumyn shi don hka sai ya nufi wajen gaban shi na
matuk'ar fad'uwa.

Lokacin da likitocin suka ga muh'd ya fita sai d'aya ya turo gawar sadeeq d'ayan kuma yana rik'e da babyn
suka turo kofar suka fito fuskar su babu walwala ko kad'an idanun su sunyi ja sosai ganin an lullu6e
mutum da farin mayafi har kanshi lokaci d'aya mumy ta fashe da kuka tana cewa
"Shikenan sadeeq d'ina ya mutu innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"

Nan fah waje ya hargitse da kuka d'ayan likitan ne ya mik'a wa nabila babyn ta kar6a ita ma tana kuka
sosai.

Cikin dauriya Dr yace "I'm so sorry Allah ya kar6i ran yalla6ai sadeeq"
Jin abin da likitan yace yasa mufidah tayi baya ta xube a sume.

A lokacin musaddiq ya k'araso wajen ganin su mumy suna kuka babu wanda ya kula dashi a wajen,
jaririyar ya hango a hannun nabila kuma bai ga mufidah don tuni ta xube a sume wasu nurse's sun d'auke
ta don yi mata taimako gaggawa, sai kawai xuciyar shi ta bashi mufidah ce ta mutu wajen haihuwa take
gaban shi ya fad'i ya nufi wajen gawar sadeeq wadda take a lullu6e, sai lokacin su daddy suka ankara
dashi kafin su tsayar dashi ya sanya hannun shi yana k'okarin bud'e mayafin.............



_ina jiran comment's d'in ku fan's_


Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/20, 10:47 AM] Aishat A Muh'd ✍: *YAYI SAKE!*




*Written by*

Aishat A muh'd

♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM




*PAGE 31*

Sai lokacin su daddy suka ankara dashi kafin su yi wani yunkurin na tsayar dashi tuni ya k'arasa wajen
ya sanya hannun shi kan mayafin yana janye shi a hankali xuciyar shi na wani irin bugawa.


Yana gama janye mayafin fuskar sadeeq ta bayyana kamar an kirawo shi ya amsa, daskarewa musaddiq
yayi a tsayen ko kwakkwaran motsi ya kasa lokacin bugun xuciyar shi ya tsanan ta sosai fiye da d'axu
mintuna uku yayi a hkan kafin kuma ya bud'e bakin shi da k'arfi ya furta
" Yah sadeeq!"
Lokaci d'aya kuma idanun shi suka fara rufe wa kafin kuma yayi baya ya sulale a k'asa a sume.

Da gudu su daddy suka yi kanshi, mumy kuwa kuka take tana furta " shikenan musaddiq nasan shima
yabi d'an uwan nashi ya Allah ka bani hak'urin rashin su"

Kafin ta xube ita ma akan kujera tana shashshak'ar kuka cikin xuciyar ta tana karanta innalillahi wa'inna
ilaihir raji'un Allahumma arjurrni fil musubati wa'akbarni min khairul minha da sauran addu'ar da taxo
xuciyar ta gaba d'aya ta wani xabge ta rame lokaci d'aya saboda tsabar tashin hankali.


Dr muh'd kuwa bud'e kofar office d'in yayi kad'an yaga musaddiq baya nan don hka sai ya fito ya nufi
inda suke idanun shi na xubar hawaye, yana k'arasa wa ya hango musaddiq a k'asa a sume su daddy da
Abba suna k'okarin daukan shi, a rud'e ya k'arasa wajen da gudu ya cakumi jikin musaddiq yana kuka
yana cewa
"No musaddiq kada ka bishi kai ma nima xuciya ta xata buga na bi ku baxan jure rashin ka ba"

Maganganun da muh'd yake shi ya sake tsinka xuciyoyin su daddy yana rik'e da musaddiq yana kuka sosai
dak'yar Yah Omar ya rik'e muh'd aka shigar da musaddiq emergency room don ceto rayuwar shi.


A cikin ambulance aka sanya gawar sadeeq daddy da Abba suna xaune kusa da gawar, umma, mumy,
nabila da jaririyar kuma suka shiga motar Yah Omar suka nufo gida domin sada shi da gidan shi na gaskia,
mumy babu uhm babu uhm uhm hawaye ne kawai yake fita a idon ta xuciyar ta tana wani irin xugi da
rad'ad'i.


An samu nasarar farfad'owar mufidah Dr Aishat tana k'okarin yi mata allurar bacci don ta huta amman
mufidah tak'i yarda cikin kuka take cewa
"Doctor na rok'e ki da kada kiyi min allurar bacci ki bar ni naje na yiwa mijina kallon k'arshe don nasan
baxan k'ara ganin shi ba sai a photo"

Wani mugun tausayin ta ne ya kama Dr Aishat don hka ta dafa kafad'ar ta tana cewa
"Baxan miki ba mufidah amman ina son ki bar kukan nan addu'a yanxu sadeeq yafi bukata fiye da komai
a wajen ki kin ji"
Gid'a kai tayi nan ta kamo hannun ta suka fito daga room d'in.


Musaddiq ma an samu ya farfad'o yana bud'e idanun shi komai ya dawo mishi sabo don hka ya yunk'ura
ya tashi yana jin wani jiri da axababben ciwon kai ga xuciyar shi da take mishi xugi yana dafe da saitin
xuciyar ya layi ya nufi kofa xai fita a lokacin muh'd shima ya murd'a handle d'in kofar ya shigo suka tsaya
kallon kallon tsakanin su, ganin musaddiq yana yin baya xai fad'i cikin xafin nama muh'd ya rik'e shi cikin
wata irin murya yace

"Muh'd da gaske ne Yah sadeeq ya tafi ya barni, kace mishi ya dawo ina bukatar kasance wa dashi dama
nine na mutu ba Yah sadeeq ba baxan iya jurar rashin shi ba nima xan bishi muh'd ya Allah nima ka d'auki
rai na huta da......"

Cikin kuka muh'd ya toshe wa musaddiq bakin shi don yasan baya cikin hayyacin shi, " kadai na fad'in hka
musaddiq Allahn da ya bamu shi ya kar6i abin shi yanxu addu'ar mu kad'ai Yah sadeeq yake bukata ka
taso yanxu mu je gida"

Yana rik'e dashi suka fito har farfajiyar asibitin a lokacin kuma Dr Aishat ta sanya mufidah a motar ta xata
kai ta gida sai gasu sun fito don hka sai kawai muh'd ya sanya musaddiq a bayan motar shima ya shiga ya
xauna kusa dashi don baxai iya driven yanxu ba.

Nan Dr Aishat ta ja motar ta suka fita daga asibitin, karatun Qur'an ta kunna cikin motar don samun
nutsuwa ae kuwa duk shiru suka yi suna sauraren karatun Qur'an d'in da hka har suka k'arasa gida.

Dak'yar suka samu damar shiga gidan saboda yanda mutane suka cika tun daga farkon layin ka shigo
motoci ne da mutane damk'am har xuwa cikin k'atuwar farfajiyar gidan, don cikin lokaci k'ank'ani
mutuwar SADEEQ ABUBAKAR ta kewaya ko'ina a fad'in sassan nigeria xuwa kasashen ketare don sadeeq
mutum ne managarci, hankali, tausayi, taimako babu ruwan shi kowa na shine gashi da sanyin hali ga
fara'a kai yabo dai sadeeq yasha shi daga bakunan mutane, shi yasa duk wanda yaji mutuwar ba k'aramin
girgixa shi take ba wasu har da kukan su.

A cikin palon daddy aka yi wa sadeeq wanka aka had'e shi kuma daddy da abban mufidah sai babban
aminin shi abokin shi Yah Omar suka had'e shi shi likkafani suna yi suna xubar hawaye mai k'una.


Bayan sun gama ne aka kirawo mumy don tayi mishi addu'a lokacin da mumy taga sadeeq a hka kusan
sumewa tayi numfashin ta ya fara yin sama har daddy xai fitar da ita daga palourn sai kuma ta fara yi
mishi addu'ar samun dace wa da rahmar ubangiji daga k'arshe kuma ta ce
"Sadeeq na yafe maka a matsayi na na mahaifiyar ka Allah yayi maka rahma yasa aljanna ce makomar ka"

Tana gama fad'in hka tayi shiru sai kuma ga mufidah da musaddiq nan tare da muh'd sun shigo palon
suma.

Musaddiq xama yayi a k'asa kusa dashi ya xuba mishi ido kawai yana kallon shi kamar wanda bai ta6a
ganin shi ba sai yau hawaye ma sun dai NA fita a idanun shi sai *K'UNAR XUCi* (littafin ummu safwan),
da yake yi.


Muh'd ne yayi k'okarin yi mishi addu'a shima hawaye na xuba a idon shi, mufidah kuwa kuka take sosai ta
kasa bud'e bakin ta tayi mishi, har xuwa lokacin da su daddy, Abba, Yah Omar da muh'd suka fara k'okarin
d'aga makarar da sadeeq yake ciki.

Sai lokacin mufidah ta rik'e makarar k'am tana cewa " bai fa mutu ba yayi min alkawarin xamu rayu da
juna ku dawo da shi"
Kuka take sosai tana sumbatu kamar mai ta6in hankali dak'yar mumy da umma suka janye ta aikuwa
suna sakin ta ta xura da gudu ta kuma rik'e makarar tana surutai sosai ta bawa mutanen wajen tausayi
don koma wa tayi kamar wata mahaukaciya sabon shiga.

Wannan karon mumy kasa rik'e ta tayi sai umma ce da Dr Aishat suka rik'e ta nabila kuwa jaririyar ce ta
tashi tana kuka shine take jijjiga ta a kafad'ar ta tana kallon mufidah tana kukan tausayin kawar ta ta.


Suna rik'e ta sai kuwa tayi baya ta xube a sume nan suka d'auke ta xuwa bedroom d'in mumy nan Dr
Aishat ta fara k'okarin ceto rayuwar ta bayan ta farfad'o tayi mata allurar bacci.


Shi kuwa musaddiq har aka fita da gawar sadeeq yana xaune a wurin ya kasa motsi duk kukan da
mufidah take da surutun da take bai san ana yi ba, xuwa can kuma ya mik'e xumbur ya fito lokacin har
sanya sadeeq cikin mota don da d'an nisa tsakanin su da mak'abartar cikin sauri ya shiga ya xauna kusa
da makarar muh'd yana kusa dashi.

Lokacin da aka sanya sadeeq cikin kabari daddy ne da musaddiq suka sanya shi a cikin an fara xuba k'asa
akan shi sai lokacin musaddiq ya dawo cikin hayyacin shi sai gani akayi kawai ya xube saman kabarin a
sume nan aka d'auke shi aka sanya shi a mota aka nufi gida dashi don bashi taimakon gaggawa.


Mutane sun fara tafia a mak'abartar amman daddy ya kasa tafiya kawai yayi xaman dirshe cikin k'asa
gaban kabarin sadeeq yana shafa saman kabarin dak'yar Abba da Yah Omar suka janye shi tare da sashi a
mota suka tafi gida..........



Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*


*Written by*

Aishat A muh'd

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login