Showing 27001 words to 30000 words out of 92754 words
Chapter 10 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf
na kan hannun sadeeq da ya yake rik'e da hannun mufidah
daurewa kawai yake amman ji yake kamar ya d'ora hannu amai yana xunduma ihu ko yaji sassaucin abin
da yake cikin xuciyar shi.
A hankali sadeeq ya cika hannun mufidah tare da rungume d'an uwan shi a jikin cikin wata irin soyayyar
en uwantaka ta jini, lokaci d'aya idanun su ya ciko da hawaye, amman musaddiq ya had'iye kukan nashi
shi kuwa sadeeq sai da hawayen shi suka xubo sakin shi musaddiq yayi tare da rik'e kafad'un shi yana
girgixa kai alamar kada Yayi kuka cikin rawar murya yace
" ka barni nayi musaddiq bana son rabu wa da kai ko na second ne balle tsawon kwanaki xamu d'auka
batare da ganin juna ba sai dai jin murya a waya"
Hannun shi musaddiq yasa a fuskar sadeeq yana goge mishi hawayen da suke xuba da 'yantsun shi, cikin
rawar murya musaddiq ya bud'e baki yace
"Calm down Yah sadeeq kukan ka yana k'ara karyar min da gwiwar tafia, idan kana son ganina xaka iya
xuwa inda nake nima idan na samu hutu xan na xuwa insha Allah ka taya ni da addu'a"
K'ara rungume junan su suka yi gaba d'aya sun bawa daddy, mumy, Dr muh'd da mufidah tausayi sosai,
har sai da mufidah ta yi hawayen tausayin su musaddiq yana kula da yanda take fitar da hawayen sam
baya son ganin hawaye a fuskar ta hkan ba k'aramin rikita shi yake ba, bai san lokacin da ya sanya hannu
a aljihun black jeans d'in shi ya d'auko wani kyakkyawan hankacif ya mik'a mata ba tare da ya kalle ta ba
ko yayi mata magana.
Babu wanda ya kula da hkan sai Dr muh'd, ita ma mufidah bata san lokacin da ta mik'a hannu ta kar6a ba
don hankacif d'in ya birge ta pink colour ne da adon white flower's a jiki sai tashin k'amshin turaren shi
yake mai matuk'ar dad'i.
A fuskar ta tasa tare da shak'ar k'amshin saboda dad'in shi sai da ta lumshe idanun ta kafin ta goge
hawayen fuskar ta ta, wani tunani ta fara yi kafin kuma ta tuna ita matar aure ce a yanxu da gaggawa ta
kauda tunanin tare da yin astagafrullah a cikin xuciyar ta.
Ganin mutane sun fara shiga jirgin ne yasa daddy yace " musaddiq lokaci fa yayi a hak'ura hka da
sallamar"
Cikin sanyin jiki ya cika sadeeq tare da juyawa don su yi sallama da muh'd aikuwa sadeeq ya k'ara sa
hannu ya rik'e shi gam, kallon shi daddy yayi tare da cewa
"Kae sadeeq cika shi mana kada ka 6ata mishi lokaci"
Dak'yar sadeeq ya cika musaddiq ya rungume muh'd sannan suka k'ara yin sallama da iyayen shi har yayi
taku na biyu xai yi na uku yaji sanyayyiyar muryar mufidah tana cewa
"Allah ya kiyaye hanya malam"
Ko juyo wa bai yi ba yayi gaba don yanda yake xuciyar shi tayi rauni da yawa, suna kallon shi har ya fara
tattaka matattakalar jirgin dai dai yaxo xai shige cikin jirgin ya jiyo ya kalli iyayen shi da d'an uwan shi tare
da abokin shi aminin shi bai kalli wajen mufidah ba ya d'aga musu hannu tare da shige wa cikin jirgin da
sauri kada xuciyar shi ta karaya Yayi kuka.
Dukannin su jiki a sanyaye har sai da jirgin tashi suka daina ganin shi sannan suka shiga mota sai gida, har
suka k'arasa gida babu mai magana a cikin su saboda kewar musaddiq duk ta dame su.
Tun a hanya Dr muh'd ya wuce gida don baxai iya k'arasa wa ba tun da babu aminin shi, daddy da mumy
ma part d'in su suka shige, hka mufidah ta kama hannun sadeeq suka wuce part d'in su don bata son su
takura wa su mumy tun da weekend ne.
Suna shiga part d'in su sadeeq ya xame hannun shi daga na mufidah ya shige bedroom d'in shi da kallon
mamaki mufidah ta bishi da kallo, ta6e bakin ta tayi tare da xama a kan kujera shiru tayi na en mintuna
tana tunani kafin kuma ta tashi ta shige bedroom d'in ta mayafin da tayi rolling d'in kanta dashi ta cire ta
ajiye tare da hankacif d'in da musaddiq ya bata, cire gown d'in jikin ta tayi tare da d'aura towel ta shige
toilet.
Cikin en mintuna tayi wanka ta fito ta shirya cikin wata er riga iyakar ta gwiwar purple colour mai
k'aramin hannu, light make up tayi tare da gyara gashin kanta batasa ribbon ba ta sake shi hka a bayan ta
sai tashin k'amshi mai dad'i gashin yake, different perfumes and body spray's xuwa humra tayi amfani
dasu a jikin ta sannan ta xura flate shoe bak'i ta nufi bedroom d'in sadeeq da sallama a bakin ta ta shiga
d'akin.
Cikin nutsuwa ya d'ago kanshi ya kalle ta k'okarin amsa sallamar yake amman ya kasa saboda ganin
mufidah da yayi da wannan shigar tun da suke bata ta6a yi mishi irin wannan shigar ba, kafin ya ankara
yaji ta xauna akan kafafun shi ta sanya hannun ta a kafad'ar shi ta rik'e d'ayan hannun kuma ta rufe mishi
baki ganin yanda ya bud'e yana bin ta da kallo.
"Wannan bud'e bakin fa?"
Dariya suka sa lokaci kafin ya k'ara rungume ta ajikin shi cikin kunnen ta ya fad'a mata cewa
"Bud'e bakin kallon ki ne my wife kinyi kyau sosai"
Murmishi tayi tana mai sunkuyar da kanta a hankali ya fara gwada mata salon soyayyar shi mai sanyi, ita
ma mufida ta biye shi don tana so ta mantar dashi damuwar da yake ciki, bayan komai ya kammala ne
bacci mai dad'i ya d'auke su rungume da junan.............
Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ *E.W.F*
_ina kuke Ummiey Xeey dear and Aishan umma dear wannan shafin na ku ne kyauta, ina matuk'ar
alfahari da ku Allah ya bar xumunci a tsakanin mu_❤
*PAGE 21*
Sam musaddiq bai kula da mufidah ba har ya xauna a kusa da kujerar daddy, tea d'in da mumy ta
had'a musu ta ajiye yasa hannu ya d'auka a hankali ya fara shan tea d'in, cikin wata siririyar murya
mufidah ta bud'e baki tace
"Ina k'wana musaddiq?"
A matuk'ar rikice ya d'ago kanshi ya kalli inda take, had'a ido suka yi yayin da kuma lokaci d'aya ya furzar
da tea d'in da yake bakin shi ya kware sosai amman still idanun shi na kanta, da sauri daddy, mumy,
sadeeq tare da muh'd suke yi mishi sannu yayin da mufidah ta d'auki glass cup ta cika shi da ruwa mara
sanyi ta mik'a mishi tana cewa
"Sannu fah"
Da sauri mumy tasa hannu ta kar6i cup d'in hannun mufida ta sa wa musaddiq a baki, kad'an ya iya sha
ya cire cup d'in a baki tare da tashi da sauri ya bar wajen, muh'd ma ya juya ya kalli su daddy yace
"Daddy xamu je mu fara shirya shiryen tafiar musaddiq don nan da k'wana biyu xai tafi"
Cikin matuk'ar mamaki sadeeq yace "ina musaddiq d'in xai je?"
Shiru muh'd yayi ganin hka yasa daddy yace"muh'd je ka xan yiwa sadeeq bayanin komai"
"Toh daddy"
Yana gama fad'in hka ya fice daga palon yabi bayan musaddiq, daddy kuwa nan yayi wa sadeeq bayanin
karatu musaddiq xai je ya k'aro, nan fah sadeeq ya tubure lallai sai musaddiq ya hak'ura da tafia yayi
anan nigeria ko kuma ya tattara ya bishi can ko kuma ya hak'ura gaba d'aya da karatun don sam baya son
yin nesa da d'an uwan shi.
Nan fa daddy da mumy suka fara rarrashin shi, mufida kuwa ido ta xuba musu kawai tana kallon su don
bata da abin cewa, dak'yar suka shawo kan sadeeq ya amince da tafiyar musaddiq ba don ranshi ya so ba
don gaba d'aya baya k'aunar yin nesa da d'an uwan shi, yana mishi wani irin so da baxai kwatantu ba.
Mumy ce ta kalli mufidah wadda ta kula gaba d'aya a takura take dasu tace " 'yata tashi kije ki huta kin ji"
Sunkuyar da kai tayi cikin kunya tace " toh mumy"
Kallon sadeeq mumy tayi tare da cewa " ka bita ku tafi tare, idan kuna buk'atar wani abin ka kirawo ni a
waya ka sanar da ni"
" okay mumy"
Daga hka suka mik'e tare da tafiya part d'in su, da kallo mumy ta bisu kafin sai da suka 6acewa ganin ta
tukunna ta sauke idanun ta tare da sauke ajiyar xuciya, kallon ta daddy yayi tare da cewa
" Ya akayi mumyn sadeeq?"
Girgixa kai tayi tare da cewa " ba komai "
" ina son ki cire sa damuwa a cikin ranki game da tafiyar musaddiq, insha Allah babu abin da xai faru
dashi addu'a xaki nayi mishi"
" toh daddy xan yi yanda kace"
Ta fad'a tana Murmishi, shima daddyn cikin murmishi yace "yawwa tawan hka nake son ji"
Daga hka suka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali, amman mumy xuciyar ta tana tunanin yanxu
Wanne hali musaddiq yake ciki gaba d'aya ta matsu da ya tafi ko xuciyar ta ta samu sukuni don bata son
suna had'u wa da mufidah.
Bayan sun k'arasa part d'in su mufidah bedroom ta shige don ta samu bacci, idanun ta har wani xafi yake
saboda baccin da take ji, kwanciya tayi tare da k'ara k'arfin ac dake d'akin, shima sadeeq ganin hka yasa
ya bita bedroom d'in kwanciya yayi tare da janyo ta jikin shi ya rungume ta ba dad'e wa bacci yayi awon
gaba dasu gaba d'aya.
Musaddiq kuwa tun lokacin da ya fice daga palon da sauri wajen parking space ya k'arasa motar Dr
muh'd ya shige ya xauna tare da had'a kai da gwiwa hannun shi dukka biyun kuma suna saman kanshi
yana yamutsa gashin kanshi, idanun shi sunyi ja sosae, a lokacin idan ka ga musaddiq sai kayi mishi kukan
tausayi gaskia so masifa ne idan baka yi dace ba da yasan hka son mufidah xai mayar dashi da bai yi
saken da xai rasa ta ba a rayuwar shi.
Yana cikin wannan halin ne muh'd ya k'araso wajen har ya shiga cikin motar ya xauna musaddiq baisan ya
shigo ba, girgixa kai yayi cike da tausayin musaddiq yasa hannun shi ya dafa kafad'ar shi d'ago jajayen
idanun shi yayi ya watsa su akan muh'd wanda yasa sai da gaban muh'd ya fad'i ganin yanda musaddiq ya
koma, cikin rarrashi muh'd yace
"Haba musaddiq kai fa kayi alkawarin cire son mufidah a cikin xuciyar ka, gashi idan kana irin hka daddy
da yah sadeeq xasu d'ago ka fa, don nasan mumy ta gama fahimtar komai magana ce kawai bata yi ba"
Shiru shi dai musaddiq Yayi amman yana sauraren abin da muh'd yake fad'a mishi, sai da suka 6ata lokaci
sosai muh'd yana rarrashin musaddiq har ya samu ya dawo dai dai tukunna suka tafi inda xasu je.
A cikin wad'annan kwanakin biyu musaddiq babu abin da yake sai shirye shiryen tafiar shi duk wani shiri
ya gama sai jiran ranar tafia kawai yake jira, sadeeq ya shiga damuwa sosai na tafiyar musaddiq amman
mufidah da mumy suna k'okari wajen lalla6a shi har dai ya d'an kwantar da hankalin shi.
Tun daga ranar musaddiq bai k'ara had'u wa da mufidah ba kuma shi kanshi yaji dad'in hka don baya son
ganin ta don ba k'aramin d'aga mishi hankali ganin ta yake ba.
A yau Saturday ne da yammacin ranar K'arfe 5 na yamman jirgin da xai je Australia xai tashi, don hka
musaddiq xuwa hud'u na yammacin ranar ya kammala komai, fito wa yayi daga bedroom d'in shi xuwa
palon mumy don su yi sallama yana shiga palon ya tarar da sadeeq da daddy a tsaye suna jiran shi don yi
mishi rakiya.
Rungume daddy yayi idanun shi sun cicciko da hawaye peck ya bawa daddy a kumatun shi tukunna ya
cika shi suka rungume junan su da sadeeq kowanne idanun shi cike da hawaye, d'ago kan da xai yi suka
sauka akan mufidah tana murmishin da yake k'ara mata kyau tayi kyau cikin wata Arabian gown blue
colour tayi rolling d'in kanta da red d'in veil ba k'aramin kyau tayi ba lips d'inta yasha red d'in jambaki,
wani irin abu ne ya tsayawa musaddiq a xuciyar shi da sauri ya kawar da kanshi daga kallon ta yana
k'okarin danne abin da yake ji.
Sakin sadeeq yayi tare da k'arasa wa wajen mumy wadda ta sakko daga up stairs da shirin ta na rakiyar
musaddiq airport, rungume ta ita ma yayi sosai mumy ta tsorata da yanda taji bugun xuciyar musaddiq,
hannun ta tasa ta shafa kanshi tare da rad'a mishi a kunnen shi
"Ka dage da addu'a musaddiq Allah ya yaye maka abin da yake damun ka, nima xan dunga you maka,
kada kana sa damuwa a cikin xuciyar ka don Allah kayi min wannan alkawarin"
D'aga kai yayi tare da cewa " xan yi abin da kika ce mumy nah"
Daga hka kuma suka d'unguma don tafiya airport rakiyar musaddiq ko inda mufidah take bai k'ara
marmarin kallo ba, sosai mufida abin da yake mata yana d'aure mata kai xai yi magana da kowa ban da
ita ko gaida shi tayi baya amsa wa, amman da ta tuna er tsamar da suke yi a skul maybe har yanxu bai
hak'ura ba ta6e baki tayi, hannun ta sadeeq ya kama suka fita daga palon da yake duk sun riga su yin
gaba.....................
Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 23*
Tun lokacin da musaddiq ya tafi xuciyar mumy ta kasa samun nutsuwa saboda batasan halin da d'anta
yake ciki ba, idan suka kirawo shi a waya muryar shi normal, but ae ba fah ta ganin shi batasan yanayin da
yake ciki ba, ta dage da taya shi addu'a sosai, hka a 6angaren daddy da shima addu'ar yake taya
musaddiq tare da Kiran shi a waya yana mishi nasiha cikin tausasawa da rarrashi, duk wata kulawa suna
yi mishi ta waya.
Sadeeq kuwa bayan en kwanaki da tafiyar musaddiq ya cire damuwar rashin d'an uwan nashi a kusa
dashi, don yana samun kulawa sosai a wajen matar shi mufidah, xaman su suke lafia cikin kwanciyar
hankali, duk da sadeeq yana da sanyin hali a komai nashi daga kallon yanayin shi kasan bashi da xafi
komai cikin sanyi yake shi yasa suke xaman su lafia ba mai jin Kansu.
Mumy ma tana k'aunar mufidah saboda hankalin ta da nutsuwar ta gashi tana matuk'ar kulawa da d'anta
shi yasa duk abin da ta samu xata nemi mufidah ta bata.
Saboda kwanciyar hankali mufidah tayi wata er k'iba kad'an ta k'ara haske da kyau abin ta, tana samun
kulawa sosai a wajen mijin ta da iyayen shi, bata da wata matsala a yanxu sai wadda ba'a rasa kowanne
d'an adam da ita ba.
Tsawon watannin su biyu da aure bata fita ko'ina ba amman a yau tayi niyyar tambayar shi tana son taje
gida daga can xata wuce gidan Yah Omar wajen nabila don ita nabila xuwan ta biyu gidan tana yi mata
yini, a xuwa na biyun ne tace baxa ta k'ara xuwa ba sai ta je, shi yasa ta yanke shawarar fita gobe.
Wajen K'arfe biyar da rabi ne ta shiga kitchen don yi musu girki dare, abinci mara nauyi tayi niyyar yi
musu don hka jeelop na taliya take son yi, nan ta fara aikin ta cikin kware wa ta yayyanka su vegetables
da yin blending d'in kayan miya.
Cikin tsawon mintuna ta kammala jeelop d'in ta xuba a food Flak's sannan tayi musu chicken pepper
soup, sai coconut juice wanda yasha coconut and pineapple aciki sosai tare da milk ta ruwa tana gama
wa ta sanya a frige bayan ta juye shi a jug.
Food Flak's d'in ta d'iba ta kai dinning area ta jera tukunna ta dawo ta kitchen ta d'auki plate's, spoon da
glass cup's ta kai su dinning bayan ta gama sannan ta gyara kitchen d'in tare da yin wanke wanke, bayan
ta gama da kitchen ne, ta gyara falo tare da sa mishi turaren wuta mai k'amshi tuni ko'ina a falon ya
d'auki k'amshi, sannan ta wuce bedroom's d'in su ta gyara, tana gama wa sai ta fad'a toilet tayi wanka
tare da d'aura alwala don mangarib tayi.
Bayan ta idar da sallahr mangarib ne ta xauna tana karatun Qur'an har xuwa lokacin sallahr isha'e, bayan
ta idar tayi shafa'i da wutiri ne tare da addu'o'in ta tukunna ta tashi ta cire abayat d'in da tasa tayi sallah.
Wajen dressing mirror ta k'arasa ta shafa wani cream tare da yin light make up, tukunna ta k'arasa
wardrobe ta bud'e 6angaren English wear's ta d'auko wani jeans white ne da t-shirt pink colour mara
hannu bayan ta gama wa kayan ne sai ta gyara gashin kanta ta gefe tayi parking d'in gashin nata tayi kyau
sosai kamar wata er baby, perfumes ta fesa tare da shafa humra mai tsananin k'amshi a jikin ta, falo ta
fito ta xauna tana kallon film d'in thor a mbc 2.
Ko mintuna bakwai bata yi da xama ba sadeeq yayi sallama tare da shigowa palourn, d'ago kai tayi ta
kalle shi tare da amsa mishi sallamar cikin muryar ta mai dad'i.
K'arasa wa yayi tare da xama kusa da ita yana kallon ta yace " my wife kin yi