Showing 57001 words to 60000 words out of 92754 words

Chapter 20 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf

10 Jul 2025

3040

ne yaxo mishi wanda xamowar mufidah matar shi a yau shi yasa shi jin garau
dashi,hawayen farincikin nan har yanxu dai fita suke daga idanun shi fuskar shi dauke da murmishi.


Turo kofar akayi da sauri musaddiq ya juya don ganin wane, had'a ido suka yi da Dr John wanda ya saki
baki da hanci yana kallon musaddiq, murmishi ya sakarwa Dr John kafin yayi mishi alama da hannu ta
wannan kallon hka fah?.

Gane hkan da Dr John yayi yasa shi cewa
" I don't believe wai musaddiq ne a gaba na ya samu lafia "

Er dariya musaddiq yayi tare da rungume Dr John cikin tsananin farinciki yace
"Friend ka taya ni murna na samu mufidah"

Kallon rashin fahimta Dr John yayi mishi hkan da ya gani ne yasa shi bashi labarin abin da yake faruwa
dashi, kallon shi Dr John yake cike da tsantsar mamaki tare da jinjina mishi sosai daman en nigeria suna
yiwa matan su irin wannan so hka har mutum ya kamu da ciwo, nan ya taya musaddiq murna kafin kuma
ya sake duba shi xai kuma rik'e shi sai xuwa nan da gobe xai sallame shi,aikuwa musaddiq ya tubure shi
ya warke fah gida xai tafi.

Ganin ya dage baxai kuma kwanan hospital ba yasa Dr John sallamar shi yana ta tsokanar shi murmishi
kawai musaddiq yake yi ,kawai idan ya tuna yanxu mufidah ta xama tashi wani farinciki ne yake ratsa
cikin xuciyar shi wanda bai ta6a jin hakan ba.


Yana k'arasa wa gidan shi wanka yayi tare da shirya wa cikin white 3quater and t-shirt white mara hannu
bayan ya fesa perfume's a jikin shi ya dawo parlour ya kwanta jikin kujera.


Hannun shi dauke da phone d'in shi yana sake karanta message's d'in daddy,mumy and muh'd yana
murmishin farinciki shi kad'ai ko yunwa baya ji a cikin shi don farincikin yau ya kosar dashi,idan ya lumshe
idanun shi cute face d'in mufidah yake hango wa tare da beautiful pink lips d'in ta har da wani lashe Lip's
d'in shi, Lokaci d'aya kuma wani abu ya fad'o mishi a ran shi nan take fuskar shi ta nuna tsantsar damuwa
duk farincikin da yake cikin xuciyar shi ya kau a Lokaci d'aya saboda tuno d'an uwan shi yayan shi sadeeq.


Ya tuna sadeeq fah ya auri mufidah har sun haifi afnan shine har yake murna da auren ta, anya kuwa xai
iya xaman aure da mufidah matar da d'an uwan shi yayi xaman aure da ita na tsawon wasu en shekaru,
anya yayi wa kanshi adalci da auren ta, nan wani abu ya tokare me mak'ogaro ya rasa abin da yake mishi
dad'i, xai xauna da ita ko don tayi mishi renon afnan saboda yarda da yayi da tarbiyyar ta yasan afnan
xata samu tarbiyya mai kyau idan yaso sai ya xa6i wata baby girl d'in ya aura don biyan buk'atar kanshi
don baxa ta samu so daga wurin shi ba wannan son ya rufe shi tun daga kan mufidah, nan take yayi
na'am da wannan shawarar tashi sai lokacin yaji sukuni a cikin xuciyar shi abin da ya tsaya mishi a
mak'ogaron ya tafi...


**********

Tana xaune a bedroom sai ga nabilah ta shigo fuskar ta dauke da tsantsar farinciki da annushuwa tana
cewa

"Kaga amarya a gidan Dr musaddiq nayi farinciki da wannan had'in Allah dai ya saka wa Dr muh'd da
alkhairi don yayi abin da ya dace"

Wata irin xabura mufidah tayi tare da mik'e tsaye har tana yin tuntu6e xata fad'i tsabar raxanar da tayi da
sauri nabilah ta rik'e ta tana cewa

"Hey Mr's musaddiq relax kada ki fad'i kiji ciwo a kasa cin amarci a 6ige da jinya"

Kallon ta mufidah take muryar ta na rawa tace
"Da gaske kike mufidah ko tsokana ta kike, don Allah kice min ba gaskiya ba ne?"

Ta k'arasa fad'a hawaye na xuba a kyakykyawar fuskar ta, wani mugun tausayin ta mufidah ne ya ratsa
nabilah cikin sanyin murya tace

"Wlh Allah da gaske nake mufidah an d'aura auren ki memakon da muh'd sai muka ji da musaddiq abin
ya bamu mamaki sosai don bamu san da hka ba"

D'an dakata wa tayi tare da jan numfashi ta dafa kafad'ar mufidah da hannun ta tare da cigaba da cewa

"Sai da mumy tayi kiran mu da umma tayi mana bayani, ashe lokacin da sadeeq yake daf da mutuwa ne
ya barwa muh'd wasiyya akan idan ya mutu don Allah kada ki auri kowa sai musaddiq don yasan idan ya
aure ki baxa ki da nasani ba kuma afnan xata tashi a hannun iyayen ta biyu wato ke da musaddiq, shine
muh'd ya rasa ta yanda xai fad'a muku wannan wasiyyar ke da musaddiq don yasan baxa ku ta6a amince
wa shine ya samu daddy,mumy,umma da Abba yake fad'a musu shine suka biyo ta wannan
hanyar,amman muh'd shima a yau aka d'aura auren shi tare da matar shi kuma er uwar shi nafisat "

Tuni mufidah ta 6arke da kukan bakinciki da takaici lallai muh'd ya raina mata hankali ashe manufar shi
kenan shi yasa duk lokacin da yaga wani ya tsaya da ita xai mata magana idan suna tare taga yayi kicin
kicin da fuska yana cika yana batsewa ashe da nashi dalilin, ae kuwa sam baxa ta ta6a yarda da wannan
had'in ba auren k'anin mijin ta.


Cikin fusata ta mik'e tsaye tare da juya bayan ta tace
"Nabilah wannan auren sunan shi matacce"

A firgice nabilah ta tashi tana cewa " me kike nufi mufidah? "

Juyo wa tayi tana kallon nabilah tare da cewa
"Ina nufin dole musaddiq ya sake ni baxan iya rayuwar aure dashi ba yana matsayin k'anin sadeeq sam
baxan iya ba, idan auren suke so nayi gwara na xa6i wani da kaina na aura ko mai mata uku ne yaje
matsayin ta hud'u na yarda da na xauna da musaddiq"

Kallon mamaki nabilah take mata kafin tace
"Kina nufin da ki xauna da musaddiq gwara ki aure mai mata uku?"
"Kwarai da gaske "
Mufidah ta fad'i hkan , "lallai na yarda har yanxu akwai sauran kuruciya a tattare da ke mufidah ki
godewa Allah, Allah ya baki miji tamkar da dubu wanda ko aure bai ta6a yi ba kice bakya so haba
mufidah"

Wata harara mufidah ta watsa mata tare da jan tsaki mtsww ta xauna a gefen bed tana fashewa da kuka
kuma lokaci d'aya don jin yanda wani abu ya tokare mata a mak'ogaron ta wanda ta rasa na mene, xama
nabilah tayi kusa da ita tare da cewa

"Kada ki manta mufidah wannan wasiyyar sadeeq ce baya duniyar nan a matsayin ki na mijin ki wanda
kike matuk'ar so mutuwa ta raba tsakanin ku ya bar wasiyya baxa kiyi kok'arin cika mishi ita ba ko mai
wuyar ta kuwa,wannan auren da kuka yi da musaddiq shi xai tabbatar wa da mutane Cewar ke mai

kaunar sadeeq ce ta hak'ik'a tun da har kika iya cika mishi alkawarin shi kuma sadeeq xai matuk'ar
alfahari da ke, ni a matsayin na kawar ki aminiyar ki ina mai baki shawarar ki tsaya kiyi tunani sosai kafin
ki xartar da hukuncin da xuciyar ki take ingixa ki da kiyi"

Tana gama fad'in hka ta mik'e ta fice daga bedroom d'in wani 6angaren xuciyar ta cike da tausayin
mufidah wani 6angaren kuma haushin ta take ji na hukuncin da take kok'arin yankewa don tafi kowa
farinciki da jin wannan auren, "Yah Allah kada ka bawa shaitan xuga mufidah ta hanyar rabuwar ta da
musaddiq" ta furta hkan a cikin xuciyar ta.

Mufidah kuwa kuka ta rushe dashi sosai na tausayin kanta gashi nabilah tayi fushi da ita tun da har ta iya
tafiya ta barta cikin damuwa ba tare da ta tsaya ta rarrashe ta ba, ina xan sanya kaina naji dad'i dana sani
tun lokacin da umma ta fara yi min maganar aure na nutsu na xa6i wani cikin wadanda suke sona na
aura da tuni na huta da ganin wannan matsalar,ita ina xata iya xama da musaddiq mutumin da tun farkon
haduwar su basa shiri da junan su har yanxu ta ina xasu fara shirya kansu har suyi xama na fahimta
kowa yana ji da kanshi.

Yini tayi a d'aki ita d'aya mumy ce ma mai xuwa duba ta, nabilah kasa jure fushi da mufidah tayi don hkan
bata ta6a faruwa dasu d'in ba shi yasa ta kasa sakewa dole ta shigo d'akin tana rarrashin ta tare da yi
mata nasiha, sai lokacin mufidah taji damuwar ta ta d'an ragu taji sanyi ta wani 6angaren.


Har xuwa Lokacin tafia dinner yayi suka shirya suka tafi mufidah ba k'aramin kyau tayi ba baka ce ta ta6a
aure ba har 'ya ba, mumy baki yak'i rufuwa yau d'an ta ya samu abin da yake so xuciyar ta taf cikin
farinciki, haka sauran mutane masu xuwa taya su mumy murna da fatan alkhairi.


Sai yanxu mufidah taga matar muh'd nafeesat ba laifi tana da kyau gata da fara'a da hankali sai jan
mufidah take da hira ita kuwa mufidah ba bakin magana da uhm sai uhm uhm, tsananin ta da muh'd
kuwa mufidah harara kawai take aika mishi sai dai yayi murmishi yana girgixa kai don yasan shi mai laifi
ne wajen mufidah dole ya samu lokaci idan ta huce ya bata hak'uri, har aka tashi daga wurin dinner d'in
magana ta fatar baki bata had'a mufidah da muh'd na sai harara da take aika mishi, ko lokacin da ya fara
yi mata magana da sauri ta bar wajen don bata buk'atar jin komai daga wurin shi.

*******


Yana kwance kan bed tun da gari ya waye ya kasa tashi daga kan bed duk jikin shi a kasalance yake jin
shi,dauko wayar shi yayi yana duba wa ganin message's a what's app d'in shi yasa shi shiga domin duba
wa messages d'in muh'd ya fara shiga abin da ya gani ne yasa shi furta
"Ohhhh my Allah nagode maka da ka mallaka min wannan fine cute baby d'in"
Ya k'arasa fad'i yana dafa xuciyar shi don jin wani sabon sonta da yake shiga cikin xuciyar, pictures d'in ta
ne na wurin dinner da akayi ne muh'd ya turo mishi shine yake furta hkan da ya gani.

Face d'in ta ya tsurawa ido yana kallo wani abu ne yaji yana ratsa shi tun daga kanshi har xuwa kafar shi,
yakai wajen mintuna 5 yana kallon ta sai kuma lokacin yaji wani uban kishi don yasan mutane da yawa
sun gane mishi mata, kallon picture's d'in kawai yake ji yake kamar yayi tsuntsu ya ganshi a gaban
mufidah, sai da ya kalli picture's d'in son ranshi kafin ya turawa da muh'd Cewar

" _Aboki nagode sosai amman ka tabbatar ka goge picture's d'in nan a wayar ka_"

Ya tura mishi ba jima wa muh'd ya turo mishi da reply na dariya kafin yace

" _Hhhh sarkin kishi ae tuni na goge tun lokacin da na turo maka ba sai ka fad'a min ba, ya kamata ka
dauki matar ka ko ka dawo nigeria gaba d'aya yaro don wlh aure da dad'i na baka labari yanxu hka gani
rungume da sweetheart dina_"

Ya turo mishi hkan tare da alamar gwalo, wani yarrr musaddiq yaji a cikin jikin shi gaba d'aya ya dauke
wuta ji yayi wani abu yana ratsa shi wata kasalar ce ta sake lullu6e shi wanda dakyar ya cewa muh'd

" _kai fa wani lokacin d'an air ne kai abin ya dama ni bai dame ni ba_"

Ganin muh'd yana yin typing alamar akwai abin da turo ya sashi kashe datar gaba d'aya don kada ya
hargitsa mishi tunani don shi kad'ai yasan abin da yake ji a yanxu dakyar ya iya tashi ya shiga toilet yana
cewa
"Muh'd yana neman hargitsa min tunani xuwa wani 6angare na daban wanda bai kamata ace na kasan ce
cikin yanayin yanxu ba"
Da hka ya sakarwa kanshi ruwa idanun shi a lumshe mufidah kawai yake hangowa.............



Aishat A Muh'd ✍
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*


*Written by*
Aishat A Muh'd

♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM

LIKE AND DROP UR COMMENTS FB PAGE

#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/


_Happy Birthday my billy ladan dear ina taya ki murnar k'arin shekara, Allah ya k'aro shekaru masu
albarka, na sadaukar da duk wannan page d'in don murnar wannan ranar, ina miki fatan alkhairi
tawan_

*PAGE 43*




Daren ranar mufidah bata samu cikakken bacci saboda tunanin auren ta da musaddiq da aka d'aura a
yau, ji take kamar a mafarki yau ita ce matar musaddiq mutumin da basa shiri da junan su, me yasa
sadeeq ka furta hkan baka san ba ma shiri da juna da k'anin ka ba, taya xamu iya had'a kanmu mu yi
xaman aure irin na mata da miji.


Da irin wad'annan tunane tunanen mufidah bacci yayi awon gaba da ita ba tare da ta shirya yin shi ba,
musaddiq kuwa ana shi 6angaren ya samu cikakken baccin wanda rabon da yayi irin shi tun lokacin da
sadeeq ya furta yana son mufidah, ranar baccin shi yayi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.


Washe gari en uwa suka tattafi gida ya rage daga mumy, daddy, mufidah da afnan sai en aiki, duk wani
motsin mufidah akan idon mumy don tana son karantar yanayin da take ciki, sai kuma aka ci sa'a mufidah
ta fito xuwa parlour fuskar ta wasai da ita sai dai kumburi da d'an ja da idanun suka yi mata, wasa take
wa afnan suna dariyar su sosae hkan ya faranta wa mumy rai tana mai fatan wannan auren ya dawwama
cikin amincen Allah da farin ciki.


Bayan sati d'aya da auren mufidah da musaddiq ne daddy yayi mata magana da ta cigaba da xuwa
hospital kafin musaddiq ya dawo, ae kuwa tayi farinciki sosae da hkan a ranar kuma da dare Dr muh'd
yaxo gidan tare da matar shi nafisat.

Mufidah bata wani kula shi ba sai nafisat d'in suke yin hira tsakanin su har mumy ta tashi ta shiga kitchen
ta barsu bayan sun gama gaisa wa.

Alama muh'd yayi wa nafisat da hannu kan ta bi mumy kitchen, d'an murmishi tayi tare da Kama hannun
afnan suka shige kitchen.

Cikin sanyin muryar shi yace
"mufidah kiyi hak'uri nasan ni mai laifi ne a wajen"

D'an ta6e baki tayi kafin tace "uhm muh'd me yasa lokacin da sadeeq yake bar maka wasiyyar na auri
musaddiq baka kirawo ni ba, wlh ba don sadeeq ne ya nemi da ka had'a auren mu da musaddiq ba, da
tun ranar da aka d'aura auren xaka sanya a warware shi"

Kallon ta muh'd yake cikin zuciyar shi yana cewa da kinsan son da musaddiq yake miki da baxa ki furta
wad'annan maganganun ba, kinsan adalilin ki ya kamu da cutar da bata warke wa ina addu'a da fatan
Allah ya kaimu lokacin da musaddiq xai furta miki abin da yake cikin xuciyar shi.

A fili kuwa cewa yayi "nima mufidah alk'awarin da na d'aukar sadeeq shi yasa na cika shi, tun daga
lokacin da aka d'aura auren naji kamar an cire min wani abu a jiki na da kaina lokacin naji hankali na ya
kwanta sosae mufidah "

D'an ajiyar numfashi yayi kafin ya cigaba da cewa
" ina sake baki hak'uri ni dai a adaina fushi dani, sannan kuma naji daddy yayi min maganar komawar ki
office ranar monday koh ? "

Cikin sanyi tace "ehhh nima d'axu ya sanar da ni"
"hakan yayi kyau Allah ya taimaka, tun da mun shirya a sakar min fuskar mana irin wannan d'aure fuskar
ae sai ki sa na dunga rawar jiki saboda tsoro ki sa matata da mijin ki su raina ni "

Dole tasa ta d'an saki fuskar da murmishi wanda har sai da dimples d'in ta suka lotsa kafin kuma ta
harare shi jin ya k'arasa maganar da mijin ta musaddiq.

Er dariya muh'd yayi yana fad'in ko ke fah "

Nan kuma suka cigaba da Er hira har xuwa lokacin da su mumy suka fito a kitchen, sun d'an jima a gidan
don sai wurin 9:30 na dare suka tafi bayan sun yi dinner har farfajiyar gidan mufidah ta rako shi suka yi
sallama suka tafi ita kuma ta dawo gida.


Acikin hka mufidah ta Fara xuwa hospital tana cigaba da aikin ta cikin kwanciyar hankali kuma hkan ba
k'aramin d'ebe mata kewa yake ba don ta d'an rage tunani sosai.


Kamar yau ranar weekend ce mufidah babu aiki tana kwance kan bed bata jin dad'in jikin ta tun safe ga
wata muguwar fad'uwar gaba da take damun ta tun safe, afnan ma da ta dame ta da surutu korar ta
wurin mumy tayi.

Shigowa mumy tayi cikin bedroom d'in hannun ta rik'e da mayafi alamar fita xata yi, Kallon mufidah tayi
fuskar ta dauke da murmishi tace

"mufidah na gama shirya wa xamu tafi, na rasa dalilin da ya hana ki bin mu gashi har afnan xamu tafi "

D'an murmishi mufidah tayi tare da tashi daga kwancen da take tace
"kiyi hak'uri mumy kin ga ranar monday ina da aiki na safe kuma xamu yi muhimmin meeting ranar shi
yasa "

Da yake london su mumy da daddy xasu je wajen dubiyar wani babban abokin daddy da aka kwantar
dashi acan, sun nemi da mufidah ta shirya su je ta k'i yarda kuma kwanaki uku kawai xasu yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login