Showing 15001 words to 18000 words out of 92754 words
Chapter 6 - YAYI SAKE COMPLETE BY A'ISHA A MUHD-1.pdf
idanun shi wad'anda suke a lumshe.
"ga tea nan kasha ga magungunan ka nan Idan ka gama xamu yi magana "
Cewar Dr muh'd yana mik'a wa musaddiq cup d'in da ya had'a tea bai yi musu ba yasa hannu ya kar6a ya
fara sha bayan ya shanye Dr muh'd ya bashi magungunan yasha sannan ya jiyo ya fuskan ci musaddiq
yasha Kunu sosai don yana son sanin gaskiar abin da yake damun shi ya fara da cewa
"musaddiq ina son sanin me yake damun ka, me kasa a ranka har yana kok'arin haddasa maka
mummunan ciwo a jikin ka? "
Kallon shi musaddiq yayi sannan ya kawar da kanshi daga kallon shi yace " babu abin da yake damuna
muh'd just ciwo daga Allah ne"
"enough musaddiq baxan ta6a yarda da abin da kace min ni nasan kan ka tuna ba ma 6oye wa junan mu
matsalar mu, idan kuma ka k'i fad'a min wlh xan je na gayawa su daddy su tambaye ka ae su dole ka fad'a
musu abin da yake damun ka ?" Cewar Dr muh'd kenan.
"kaiii ka yarda fah da gaske nake babu abin da yake damuna"
"Okay shikenan Allah ya baka lafia"
Fad'in Dr muh'd sannan ya nufi fita daga office d'in ranshi a matuk'ar 6ace, caraf yaji musaddiq ya rik'e
mishi hannu tare da cewa
"I'm so sorry aboki ni kaina bansan abin da yake damu na ka taya ni da addu'a kawai "
"ka cika ni Idan baxa ka fad'a min gaskia ba na rabu da tambayar ka abin da yake damun ka su daddy xan
fad'a wa"
Musaddiq ya rasa ta inda xai kauce wa muh'd a wannan Karon don yak'i tsayawa ya yarda da abin da yake
ce mishi idanun shi sun yi ja sosai ga wani irin jiri da yake ji da axabbaben ciwon kai baisan lokacin da ya
bud'e baki yace
"ina son ta muh'd soyayyar tace tasa na shiga cikin wannan halin na rasa yanda xanyi na cire ta daga cikin
xuciya ta "
Koma wa yayi ya xauna da k'arfi kan kujera sannan ya cigaba da cewa "baxan iya fad'a maka adadin son
da nake mata ba amman nayi sake abokina na rasa ta har abada "
Sakin baki Dr muh'd yayi yana kallon musaddiq cikin mamaki don shi tun da yake dashi bai ta6a ganin
yayi mishi xancen mace ba a hankali ya k'araso inda musaddiq yake xaune hannun shi rik'e da kanshi da
yake masifar yi mishi ciwo kamar xai cire, dafa mishi kafad'ar shi yayi tare da cewa "ita wace musaddiq,
taya akayi kayi sake har ta kubce maka? "
Cikin tsananin ciwon kai yace " mufidah ce aboki mufidah wadda Yah sadeeq xai aura itace nake nayi
saken da ban sanar mata ba har Yah sadeeq ya ganta gashi yana masifar son ta har iyaye sun yi magana
nan da two month's xa'a yi bikin "
Hannun shi yasa ya rik'o kafad'un muh'd da k'arfi yace "ka ji abin da yake damu na kuma nayi wa Kai na
alk'awarin baxan ta6a bari Yah sadeeq yasan wannan xancen ba har abada saboda nasan idan ya sa ni
wlh xai hak'ura ya bar min ita, kai ma na rok'e ka kada ka fad'a wa kowa wannan maganar har kuwa
rashin lafiyar da yake damu na, na hak'ura da ita har abada baxan rusa farinciki d'an uwana ba"
Wani mugun tausayin musaddiq ne ya kama muh'd har wasu k'walla sai da suka xubo mishi na tausayin
musaddiq hannu yasa ya goge hawayen tare da cewa
"tabbas nima baxan baka goyan bayan Yah sadeeq yasan wannan xancen ba don ni shaida ne akan irin
yanda masifar son ka nasan komai xai iya yi maka ,amman ina rok'an ka don Allah musaddiq ka cire
mufidah da ga ranka please"
Wani murmishin yak'e musaddiq ya saki tare da cewa "aikin gama ya gama muh'd don son mufidah ya
riga da ya shiga cikin xuciya ta baxan iya cire shi ba ni nasan da sonta xan mutu "
Yana gama fad'in hka ya mik'e tsaye tare da d'aukan briefcase din shi da key di'n mota, yayin da Dr muh'd
ya bishi da kallon tausayi tabbas abokin nashi yayi xurfi a son mufidah wannan shi ake kira da *YAYI
SAKE*, shi ma Dr muh'd di'n mik'e wa tsaye yayi bi bayan shi.
Ya kai hannun shi kan handle di'n kofar xai bud'e kenan aka turo kofar tare da shigo wa lokaci d'aya gaban
musaddiq da Dr muh'd yayi mummunan fad'uwa saboda had'a idon da suka yi da Yah sadeeq yana shigo
wa fuskar shi d'auke da tarin damuwa sosai da gani hankalin a matuk'ar tashe yake wajen musaddiq ya
nufa kai tsaye..................
Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*written by*
Aishat A muh'd
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
*PAGE 12*
Wajen musaddiq ya nufa kai tsaye sai da yaxo gab da shi tare da kamo hannun shi yace
" why musaddiq da xaka yi switch off d'in phone's din ka duk ka d'aga mana hankali ina office mumy ta
kirawo ni naxo na duba ka, gashi har time d'in dawowar ka ya wuce baka dawo ba?"
D'an murmishin yak'e musaddiq yayi tare da cewa " sorry bro ina lafia wani aiki ne ya rik'e ni shi yasa nayi
switch off d'in wayar "
"Okay amman kana sa wayar naka a silent ka daina kashe wa, don ka hankalina ya tashi sosai "
"Haba Yah sadeeq ni fah ba yaro ba ne "
Musaddiq ya fad'i yana dan Murmishi, hararar wasa Yah sadeeq yayi mishi tare da cewa "a wurin Mumy,
daddy da kuma ni duk kallon yaro muke ma so dole mu tattara dukanin kulawar mu kan ka "
Yah sadeeq ya k'arasa fad'i yana kallon fuskar musaddiq a yau sai yaga musaddiq din ya k'ara haske fiye
da koyaushe gashi ya rame amman da yake Yah sadeeq bai fiye irin wannan binciken ba sai kawai ya juya
da kallon shi kan muh'd yace
"likita bokan turai ya fama da patients ?"
Cikin murmishi Dr muh'd yace "lafia qlau Yah sadeeq ya aiki? "
"aiki Alhmdllh gashi nan muna ta fama yanxu ma daga office d'in nayo nan "
"Masha Allah, Allah ya taimaka "
"Ameen muh'd "
Daga hka suka fita daga office d'in gaba d'aya Dr muh'd ya shiga motar shi bayan sun yi sallama ya tafi,
yayin da Yah sadeeq yaki yarda musaddiq yayi driving dole sai motar Yah sadeeq din musaddiq ya shiga
yaja su gida kai tsaye suka nufa.
Hka lokaci ya cigaba da tafiya al'amura sunyi nisa don biki ya matso sosai kowanne 6angare suna shirye
shiryen bikin ango Yah sadeeq da ango Yah Omar kuwa kamar su matso da ranar bikin suke tsabar
xumud'i.
A 6angaren amarya mufidah da amarya nabila suma sai shirin su suke nabila sai rawar kai ake yi ita kuwa
mufidah gata nan dai ba wanda xai iya fahimtar halin da take ciki na farin ciki ko akasin hka.
Mufidah ce a xaune tana tunanin da ta rasa na mene gaba d'aya bata farin ciki da auren nan don ba wani
son Yah sadeeq take ba kawai kunyar shi take ji shi yasa ta kar6i soyayyar shi gashi yana mata kwarjini
sosai kuma Yah Omar da nabila su ne suka k'ara tunxura ta har ta yarda dashi dad'in dad'awa kuma yana
da halayya masu kyau iyayen ta da sauran en uwanta suna matuk'ar kaunar shi, ga biki ya matso don an
shiga satin da xa'a fara gabatar da bikin, k'arar Shigowar message ne a wayan ta yasa ta katse tunanin ta
tare da janyo wayar tana duba wa cikin mamaki don bakuwar number ce abin da aka rubuta ta fara
karanta
" _Nayi matuk'ar rashin furta miki abin da ya dad'e cikin xuciya ta, nayi nauyin baki wajen furta hakan sai
gashi wani yaxo ya riga ni har yana kok'arin mallakar ki matsayin matar shi._"
" _ki sani ni mai k'aunar ki ina son ki son da baki baxai iya furta wa nasan har na mutu ina k'aunar ki,
Allah ya baku xaman lafia ina miki fatan alkhairi daga mai k'aunar ki_ *M*"
Sosai abin ya d'aure wa mufidah kai abin ya bata mamaki ba Kad'an ba wannan wane shi me ya hana shi
fada mata sai yanxu, me yasa bai rubuta mata cikakken sunan shi ba sai M uhm dan ta6e baki tayi kawai
tare da furta cewa " koma wane to gaskia *YAYI SAKE!* sai yayi hak'uri ya sami wata kuma "
sai ta tsinci kanta da kasa goge mssg di'n a wayar ta ta xurfafa a tunanin wane wannan.
Lokacin da musaddiq ya tura wa mufidah messegen din yana kwance kan gado idanun shi cike da hawaye
ga xuciyar shi tana mishi wani rad'ad'i sosai kan shi kuwa kamar ya cire saboda a axabar ciwo goge mssg
di'n yayi sannan ya d'auko diary din shi ya rubuta abin da ya turawa mufidah sannan ya rufe diary din ya
ajiye shi.
Koma wa yayi ya kwanta yana wani jan numfashi dakyar da ana cire so Idan ya shiga cikin xuciya da tuni
ya cire son mufidah a cikin xuciyar shi ya huta d'aga idanun shi sama yayi tare da cewa
"Yah Allah ka kawo min agaji acikin wannan halin da nake ciki, Yah Allah ka cire min son mufidah daga
cikin xuciya ta"
Yana gama fad'in hka ya lumshe idon shi wasu hawaye ne masu xafin gaske suka xubo mishi daga idanun
shi.
"Ameeen thumma Ameeen "
Yaji an furta hakan da sauri ya bud'e idon shi ya kalli kofar shigowa wata ajiyar xuciya ya saki ganin Dr
muh'd ne a tsaye yana kallon shi irin kallon nan me cike da tausayin shi.
K'araso wa yayi cikin bedroom d'in ya xauna akan bed d'in tare da dafa hannun musaddiq yace "kayi
hak'uri musaddiq wannan itace kaddara Allah ya jarabce ka da son yarinyar da yayan ka xai aura, ina
rok'an ka ka cire son ta don Allah ina nan ina tayaka addu'a sosai Allah ya raba ka da wannan son don an
kai matakin da xuciyar ka ta ta6u da ciwo ina tsoron faruwar wani abu abokina "
Dr muh'd ya k'arasa fad'i yana mik'a wa musaddiq wata takarda, kar6a musaddiq yayi ya karanta yana
gama karanta wa yayi wani k'ayataccen murmishi wanda yasa Dr muh'd tsorata sosai ya bishi da kallon
mamaki Kafin ya ankara yaji musaddiq ya fara wani irin tari sosai tuni idanun shi suka fara xubar da
hawaye saboda axabar tarin da yake sai sannu Dr muh'd yake mishi kafin ya tashi ya bud'e frige ya d'auko
mishi faro mara sanyi ya nufo wajen shi dai dai lokacin musaddiq yayi wani tari da karfi sosai wanda sai
da jini ya fito ta bakin shi yana dafe da saitin xuciyar shi..............
_kuyi hak'uri da wannan ban da chaji ne wlh_
Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*written by*
Aishat A muh'd
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
*PAGE 13*
Cikin wani irin sauri Dr muh'd ya k'arasa wajen musaddiq hankalin shi a matuk'ar tashe kamo shi yayi
ya ma rasa me xai yi mishi tsabar rikice wa, kallon musaddiq yake wanda bakin shi duk ya 6aci da jini
idanun shi sai wani lumshe wa suke yi gaba d'aya jikin shi ya saki ba k'arfi a tattare da shi.
Cikin dauriya musaddiq ya yago tissue ya goge jinin da ke gefen bakin shi tare da kallon muh'd yace
"kayi hak'uri aboki na nayi kok'ari wajen cire son mufidah a cikin xuciya ta hkan ya gagara, bansan ganin
ka cikin damuwa "
Tuni idanun muh'd sun fara xubar da hawayen tausayin musaddiq hannun shi yasa ya kamo na musaddiq
tukunna yace "kada ka damu aboki Insha Allah xaka samu lafia yanxu ka taso muje hospital na duba ka "
Girgixa kai musaddiq yayi tare da cewa "umh my friend na samu sauk'i fah "
Kura mishi ido muh'd yayi kamar me karantar wani abu a fuskar shi kafin yaja numfashi yace " na rok'e ka
ka taso mu tafi akwai abin da nake so na duba, kada kace min baxa ka ba please"
D'an murmishi musaddiq yayi kafin yace "Okay aboki ka wuce komai a waje na da ina da ikon cire abin da
yake damuna da na cire saboda bana son ganin ka cikin damuwa"
Shi ma Dr muh'd di'n Murmishi yayi tare da rungume musaddiq a jikin shi Kafin kuma yaje yayi wanka
bayan ya fito ne ya shirya cikin wani white jeans and T-shirt pink colour yayi matuk'ar yin kyau sai dai er
ramar da yayi yana gama fesa perfumes ya xura wani silifas na maxa white ne takalmin daga hka suka fita
daga d'akin xuwa farfajiyar gidan mota suka shiga asibitin da suke aiki suka nufa kai tsaye.
Bayan Dr muh'd yayi wa musaddiq gwaje gwajen da suka dace ya dad'a tausar shi tare da yi mishi nasiha
sosae akan ya rage sa tunani a cikin xuciyar ya dage da ibada yana kai kukan shi wajen Allah sosai nasihar
muh'd ta ratsa musaddiq kuma ya d'auki alk'awarin amfani da abin da yace.
Sun d'an dad'e a asibitin sannan suka dawo gida tare da magungunan da Dr muh'd ya bashi xai yi amfani
dasu, muh'd ya dad'e a gidan yana tausar musaddiq sai wajen 9 na dare ya bar gidan.
Tun daga ranar musaddiq ya dage da addu'a tare da kai kukan shi wajen mai dukka akan ya cire mishi son
mufidah a cikin xuciyar shi kuma Alhmdllh addu'a makamin mumini yana samun sassauci sosai a cikin
xuciyar shi.
Biki ya matso don an Kai lefen Yah sadeeq xuwa gidan su mufidah yayin da daga gidan su mufidah aka Kai
na Yah Omar sun shirya yin dinner, walima da sauran programs masu k'ayatar wa.
A cikin wannan lokacin ne iyayen musaddiq suka fahimci bashi da lafia don ganin yanda yayi matuk'ar
rame wa sosai hankalin su yayi mugun tashi da ganin halin da d'an nasu yake ciki Hka shima Yah sadeeq
ba k'aramin tsorata yayi ba gashi sun yi tambayar duniyar nan ya fad'i abin da yake damun shi, amman
musaddiq fad'a musu Yayi ciwo ne kawai daga Allah, Sam basu yarda da abin da ya fad'a ba sun tambayi
Dr muh'd don sun san abokin shi ne xai sani amman musaddiq bai bashi umarnin fad'a ba nan fah mumy,
daddy da Yah sadeeq suka sama musaddiq ido aduk wani motsin shi don su karanci abin da yake damun
shi, yana sane dasu shi dai yayi alk'awarin baxai ta6a fad'a wa kowa ba bayan Dr muh'd.
Ranar Tuesday suka shirya yin kamu sosai sun tsara abin gwanin sha'awa, ranar friday kuma arabian night
suka yi asabar kuma umman mufidah da umman nabila suka shirya yin mother's day nan ma sun k'ayatar
sosai amare sun sha kyau ba irin mufidah ma an ci ansha an watse cikin farin ciki.
Rana sunday da safe wajen karfe 10:20 Yah sadeeq ya shigo palon cikin shigar wata tsadaddiyar shadda
fara sol da ita yayi matuk'ar yin kyau ya fito a ango sak nan en uwa suka fara tsokanar shi shi dai
murmishi kawai yake yi xuciyar da tsantsar farin ciki yau xai mallaki mufidah a matsayin matar shi ta
sunnah.
Adai dai lokacin musaddiq da Dr muh'd su ma suka shigo cikin falon sun sha ankon shaddar su cikin
shadda sky blue da bak'in takalmi har da hula ba k'aramin kyau suka yi ba musamman musaddiq da bai
saba sa manyan kaya ko wajen d'aurin auren bai yi niyyar xuwa ba sai da muh'd ya matsa mishi dakyar ya
iya shirya wa bai ma san da kayan ba sai da muh'd ya bashi, fuskar shi ba yabo ba fallasa mumy kuwa
kallon su ta dunga yi kamar ta mayar dasu ciki don tsabar son yaran nata.
Nan suka rungume ta cikin k'aunar mahaifiyar tasu d'an hawayen farinciki tasa hannu ta goge su tare da
dafa kan su tace "Allah ya raya min ku 'ya'ya nah, Allah ya albarkaci rayuwar ku Allah ya kare min ku "
"Ameeen thumma Ameeen muna godewa Allah da ya bamu ke a matsayin uwa mumy '
Kallon su take cikin so da k'aunar su tana murmishi, Dr muh'd kuwa shi ma kallon su yake cikin sha'awar
su wani 6ari na xuciyar shi yana cike da fargaba don baisan yanayin da musaddiq xai shi gaba idan yaji
sanarwar d'aurin auren yasan ya rabu da ita na har abada wani tausayin musaddiq ne ya k'ara kama shi
sosai, ana cikin hka daddy ya fito shi ma yayi shirin shi cikin manyan kaya na wata milk colour d'in shadda
nan suka rungume shi tare da bashi peck a kumatun shi kafin daga baya su dunguma xuwa wajen
farfajiyar gidan suka shiga mota d'aya Dr muh'd ne wajen driving musaddiq a gefen shi wanda ya tsurawa
waje ido lokaci xuwa lokaci xuciyar shi tana wani mugun fad'uwa, Yah sadeeq da daddy a baya sai sauran
en uwa da abokanan arxiki suka rufa musu baya xuwa wajen d'aurin aure............
Aishat A muh'd ✍
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: *YAYI SAKE!*
*written by*
Aishat A muh'd
♻ *E.W.F*
*PAGE 14*
Bayan sun isa wurin d'aurin auren mutane sosai sun taru manya