Showing 27001 words to 30000 words out of 64084 words
Chapter 10 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt
muka fara zina ya maidani kamar matar sa a lokacin duk yana da bukata yazo schl ya daukeni zuwa hotel har na samu ciki ya kaini hospital aka cire,nace masa gaskia na gaji da aikata sabon Allah sai dai ya fito mui aure,yace idan na amince na hakura da karatuna,da naki yace tau na biyashi duk abinda ya kashe bin,domin yasan bamu da halin biya da haka har na gabatar dashi wurin su baba da yake masu son abun duniya ne babu wanj dogon bincike suka amince dashi.
Dama ban san yan uwanshi ba yacesuna kano da haka har mukai aure tun dana shigo gidan nan hakuri nike yi,ya raba daki dani baya kusan tana,gadai kayan abinci ya aje da kudi amma babu kwanciyar hankali,idan nayi magana yace ai duk abunda yake bukata gareni ya riga ya samu kwanciyar me zai dani yanzu,idan ya fita sai tsakiyar dare yake dawo wa,yavar cin abinci na, baya kulani,ya amshe wayata daya saya min,zinari daya saka min cikin lefe ya amshe abinsa,sai kawo matan banza cikin gida,ranar ya dawo cikin maye dana fara masa wa'azi ya zane ni ya mani kaca kaca kuma ya kwanta dani a wulakance ashe tun daga lokacin ciki ya shiga,daga ce banda lfy ya bani 5k naje hospital aka ce shigar ciki ne yanzu haka yace va cikin sa bane tunda bai kwanciya da ni,kinji halin kuncin da nake ciki.....
Tace allawiya sai dana baki shawara akan kibi komi a sannu gagawa ba naki bane amma ina kika ki amincewa,gashi aure tun ba a je ko ina ba an fara samun matsala.
Yanzu kam ciki nashi ne dole ya amsa kuma sai kinyi hakuri sosai,kinsan ita aure ibada ce,idan kika daure kuma kika dauketa a matsayin ibada sai kiga Allah ya baki ikon cin wanan jarabawa,ki rike sirrin ki da mijinki kada ki sake fadda ma kowa halin da kuke ciki kosu mama ne,sanan duk wani kyautatawa da kika san kina masa ki linka akan na baya,duk yadda zai kai ga wulakanta ki kada ki gaji da kyautata masa
Ki kire wayan nan abhbhwa da zan zayano maki insha Allah za a samu canji;
Ibada
Tsafta
Ladabi
Biyaya
Kyautatawa
Gyaran jiki
kalolin abinci masu dadi,koda baya ci kada ki gaji da dafawa kina aje masa.
Duk dare kada ki bari ya fara neman ki kibi duk wata hanya da zaki ja raayinsa a kanyi har ya kwanta dake.
Duk da baki san danginsa ba,duk wani aboki da kikasan yana hulda dasu ki kyautata masu kada ki sake su san halin da kuke ciki.
Maganan karatu daya hanaki,kiyi hakuri haka Allah ya tsara maki,haka waya idan ya hanaki rikewa kada ki kuskura ki masa gadama,idan ma gida yace kada kije the same thing ki bishi da yadda yake so indai bai sabawa addini ba.
Yanzu tashi ki shiga wanka,na tayaki gyara gidan muyi girki.
Tace nagode nagode sosai jummai hakika bani da yar uwa da aminiya ta gaskia sama dake.
Tace haba allawiya ko kin mance QURUCIYAR mu?
Tayi daria ban mance ba jummai jummai jummalaaaa
tace haaaa alawiya mai jagalin ido ba karfi sai tonan fada,suka tafa.
Wanka allawiya ta shiga,jummai ta gyara gidan sosai ya dau kamshi,ta girka masu vegetable macaroni,suka ci da akayi sallah ta kama hanyan gida.
Allawiya kamar tayi kuka haka suka rabu...
A kwana a tashi babu wuya yanzu su jummai 3rd term exams suke zanawa na shiga ss2.
aysha kuma sun gama semester exams anyi hutu,ta samu wani private asibiti kusa dasu tana zuwa koyon aiki,nan ta hadu da wani abdulrahim ya kawo kakarshi mace test na sugar,ita incharge nasu yaba tayi text din.
Kaka tace ke yarinya yanzo dan tsabar rashin imani wanan alurar zaki caka min a yatsata?
Tace kaka kiyi hakuri lafiyar ki muke bukata tafiye mana komi muhimmanci.
Tace ai sai da na fada ma abdo lfy ta lau yace alambaran sai ya kawoni.
Tace kaka ai ba ace kina da ciwon ba gwaji kawai za ai dan kara tabbatar da lafiyar ki.
Tace au kaji yar albarka amma shi ba haka yace min ba.
Abdulrahim yace siste don't mind her pls do yr work.
Tace is part of my work to re-assure and make her comfortable.
Kaka tace shin wai shawarar me kuke ne,kada fa ku canza magana da turanci,idan inada ciwon ne kawai a fada min gaskia
Tayi murmushi kaka bayani nake mashi ai,domin yanzu nema zanyi maki gwajin.
Haka sukai ta drama da kaka har akayi aka gama,abdulrahim sai dariya yake masu.
Koda aka duba sugar ta is normal,ta nuna ma incharge nasu yace tai masu bayani mana.
Nan tayi masu bayana tare da masu shawar warin abubunda da zasu kiyaye idan basa so sugar ta hau.
Godia sosai abdul yayi,canza har she yayi kada kaka ta ganoshi yace pls sister may i have yr phone number?
Tace i dont have phone.
Yace wonderful as big as u are.
Tayi murmushi
Yace what of yr home address.
Nan ta fada mashi sukayi sallama,domin gaskia gayen ya kwanta mata a rai.
su jummai sun kare exams lfy anyi hutu.
Mami da kanta tazo har gida ta roki da umma subar jummai tabi amina kaduna hutu wurin anty balki,ya suka iya dole baba ya amince tare da mata nasiha mai ratsa zuciya.
Haka ta shirya cike da kewar yar uwarta suka lula kaduna garin gwamna............
*LEEMA*βπ»
*BRILLIANT WRITERS ASSO*....π
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
π·π·π·π·π·π·
*QURUCIYAR JUMMAI*
π·π·π·π·π·π·
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*βπ»
*51-52*
A gajiye suka isa kaduna GRA nan gidan anty khadija yake,babban gida ne wanda ya gaji da tsaruwa.
Da sallama suka shiga,ta ce lale maraba da mutan naija.
Amina tace anty hoo,ya gida ina izzidine?
Tace basu dade da fita ba tare da uncle bash inaga family house nasu suka tafi.
Jummai ta duka har kasa ina wuni,mun same ku lafia?
Cikin fara'a anty khadija tace lafia lau jummai barakallah masha Allah yau dai gani ga jumman amina ko?
Duk sai daria,tace ya mutanen gida su umma da mami?
Amina tace lafia lau suna gai daku.
Tace muna amsawa.
Anty tace kande,kande.
Naam anty gani
Dauki bag nasu ki kai the other room din.
Tace yes ma
Ta kali su jummai sannunku da zuwa anzo lafia tare da rusuna wa.
Suka amsa lafia lau.
Amina tace anty wata mai aikin kika canza ne?
Tace eh walahi ai kwatakwali ce yar binin republic kin san sun fi iya aiki.
Tace haka ne anty,aikin ma naki guda nawa daga wanke wanke sai share share ko?
Tace sai idan abban izzidine na gari wurinta yake kwana.
Tace ku karasa ciki mana ku wasa ruwa,idan kunyi sallah maci abinci.
Suka amsa tau tare da mikewa.
Daki ne babba dauke da family bed,dressing mirror,wordrop sai toilet.
Jummai tace amma gidan nan fa ya tsaru.
Amina tace ai mijin anty politician ne akwai ya'yan banki.
Wanka suka yi tare da yin sallah,suka shirya kayansu a wordrop.
Shiryawa sukai cikin riga da wando na pakistan wanda mami ta saya masu lokacin da taje dubai.
Koda suka fito anty na zaune inda suka barta tana kallon zeeworld.
Tace yan matan mami har kun shirya?
suka ce eh anty,tace muje table muci abinci,vegetable macaroni ne sai yam porrage.
Haka suka cika cikinsu cikin nishadi,suka dawo palour aka ci gaba da hira tana tambayansu labarin gida.
Tace wai amina ya su aliyu da matar shi?
Tace uhmmm anty suna nan dai yadda kika sani babu wani canji anty balki ai ba dama wurin keta duk ta mallake mana dan'uwa sai yadda tace yake yi.
Anty tace kada kiga laifinshi ai yan zuru haka suke da zaran kayi sake dan'ka,dan uwanka ko mijinka ya aure su sunan ka sorry sai yadda suka juya shi idan anyi magana suce ba boka ba mallam baiwa ce.
Jummai dai bata sa masu baki ba sabida family issue ne bai shafe ta ba.
Da la'asar tace me zl zaku yi dinner dashi kande ta dafa maku ko kuna iya shiga kitchen?
jummai tace anty indomie ya ishemu ma sai after isha'i zamu dafa.
Tace ya maku kyau bara kuyi aure ai komin son jikin ku sai kun dafa heavy foid ba takamar ku cin light food ba.
Amina tace ai kema shaida ce anty babu bani receipy da bamu iya dafa wa ba kawai ra'ayi ne cin indomie fa.
Tace nima ai dietying nake yi cu's nayi adding weight da yawa ina son ragewa ne.
Jummai tace amma anty yadda kike siririya haka kice kinyi nauyi da yawa.
Tace tab ai badaga nan take ba sai kiga mai kiba amma baida weight sai mara kiba,kamar ni yadda kike ganina haka ina weighing 70kg fa.
Amina tace lalai kam ba daga nan ba,yanzu ya kike dieting din?
Tace kala kala ne depending on kona month nawa kike son yi,kina iya na 1month,2,3,4,5 har zuwa 6month,kinga ni yanzu na 3month zanyi.
Yadda na tsara;
9:am zanyi break fast da tea babu milo ko bounvita,sabida milo na hura mutum sosai.
Sai kuma 2:pm inyi lounch da vegetable,ko cream salad kawai.
Dinner 8:30pm fruit salad ko coffe.
Amina tace tab har 3month ban ci abinci mai nauyi ba har da nama fa anty?
Tace kina iya cin fish mana,nama kuma once in a while amma banda red meat(naman shanu) yafi komi hatsari,kawai zakiyi avoiding carbohydrate ne sosai irrin su rice,millet,yam,maize da sauransu.
Jummai tace ai kuwa mu yan arewa munfi kowa zake ma irin abincin nan musamman shinkafa da tuwo.
Anty tace ai rashin sani yafi dare duhu sabida abubuwan nan sunfi komi kawo mana matsala,sai kiga mace da safe anyi breakfast da kokon dawa,gero kona masara,ko aci masa.
Ayi lounch da shinkafa da miya
Ayi dinner da tuwo kona masara,dawa,shinkafa da sauransu kinga kuwa duk carbohydrate aka yini ana ci babu mixed diet ko wani canji yadda za'ayi balancing diet din.
amina tace amma anty ai karfi ba daya ba,idan wani nada hali wani bai dashi,sanan duk abinda ake samu a birni ba lale bane a samu a kauye.
Anty tace inji wa?
ai yan kauyen ke noma,suke shigo da amfanin gonar birni,ki fada min tsakanin kauyen da birni ina ne babu ganyen alayahu,zogala,tafasa,rama,dinkin da sauran ganyayakin.
Haka kazali ka tsakanin kauyen da birni ina ne ba'a kiwon kaji,awaki,zabbi,tantabara,zoma da sauran dabobi da ake ci.
Ina ne babu babu kwai,madarar shanu,wake ya'yan itatuwa(fruits)
Ke duk kauye sun fimu wayan nan abubuwa,sabida grednsee nasu basa ci bayan sun fimu bukatar abubuwar nan sai kaga sun kwaso an kawo birini ana sayar wa cikin farashi mai sauki,hadda tayin wulakanci ake masu..
Jummai tace haka ne anty walahi sai kin gansu a minna kasuwar kwara idan sun shigo cin kasuwa da su tomato,tatasai,tarugu,water melon,pineapple,mango,gurva haka zasu ta fama cikin rana babu sai masu tayin arziki sai na banza.
Anty tace haka ne fa,yanzu shawarwarin da muke basu idan sun zo ANC(awon ciki)
breakfast;idan koko ne ko wane iri a zuba madara kona naira goma ne,ko a sayi kosai a hada dashi.
Lunch;idan shinkafa ne a hada da wake,ko ganyen alayahu,zogale,cabbage ko latas,idan da hali a sa kifi ko danya ko busasa.
Dinner;idan tuwo ne ayi miyar ganye da manja,idan kuka ne asa wake ciki 'before u know kayi balancing diet naka.
Amina tace amma anty ai wasu basu da halin canjin abincin sai kiga daga shinkafa,dawa,masara,gero,wake sai sai doya idan da hali,su ya zasui tunda abinda mazajen su keda halin saka kenan.
Tace haba amina kamar ba mace ba,kina iya sarafa wayan nan kayan abincu ta hanyoyi da dama misali;-
Shinkafa;-
A dafata da miya,jellof ko da mai da yaji.
Ana dambun shinkafa
birabiskon shinkafa
Faten shinkafa.
Garinta ana kunun shinkafa
Wainar shinkafa
Tuwon garin shinkafa da sauransu.
Masara;-
Tuwon masara
dambum masara
Fatan masara
Kina iya surfata a jika har sai tayi taushi a dafata haka fara kamar shinkafa aci da mai da yaji ko ayi jellof dinta da wake.
ana wainar ta
Ana kokon masara da sauransu.
Dawa;-
Ana tuwo
Danwaken garin dawa
Ana dafata da wake aci da mai da yaji
Kokon dawa da sauransu
Gero;-
Tuwon garin gero
Wainar gero
Gumban gero
furar jero
Wake;-
Ana faten wake
Miyar wake
Alalan wake
Dan waken garin wake
Ana dafawa da shinkafa,doya,dankali da sauransu.
doya;-
Sakwara
A dafa da miya,fate ko da mai da yaji
Ana soyawa da kwai,ko haka nan
Ana alalanta
Da sauransu.
Tace kinga ni mijini da yake yafi gane ma tuwo da dare,sai na tukashi ruwa ruwa yadda ko ya yacita bara ta cika masa ciki ba.
Jummai tace agaisheki anty lalai ilimi nada dadi mussaman ma fanin har kar lafia,idan kayi karatun sai ka tafiyar da gidanka da iyalinka bisa ka'ida.
Tace haka yake jummai shi yasa muke so kuma ku dage ku sabo ingantacen ilimi yadda al'umma zasu amfana.
Tace ku raba kanku da yawan cin indomie da kwai.
Amina tace sabida ne naga ai light food ne.
Tace light foid for where?
Ai indomie yafi komi hura mutum nan da nan aga kayi mugun nauyi ko kiba,sabida shi indomie flour ne,flour ko da cassava ake yin da wanda yana daya daga cikin carbohydrate,kwai kuma colestrul ne yafi komi kawo heart failure.
Jummai tace insha Allah zamu kiyaye anty,ko yanzu mun karu da abubuwa da dama.
Amina tace ai shiyasa nake son zuwa gidan anty.
sai bayan isha'i uncle bash ya dawo da izzidine dasu ice cream,chocolate,biscuit da sauran kayan kwalam.
Da sallama uncle bash ya shigo.
Duk suka amsa,yace ah mutanen minna ne kunzo lafia.
Amina tace uncle bashari lafia lau.
Yace kin fara ko?
Kin san bana son basharin nan fa,ya juya wurin jummai sanu da zuwa kawar mu ya hanya?
Tace lafia yau ya muka sameku
Yace lafia lau sister
Amina tace ka ma bar wani kashe murya babu abinda zakai da kai.
Yace Allah sarki amin dago mai laya tambayi anty ai na fitar da matan,idan ba don haka va da walahi baki isa ki hanani auren kawarmu ba.
Tace see you tsofai tsofai wace mace zata aure tsoho irin ka
yace talk true ko ke kin kyasa ai nace banyi dake,shike ake wani kushewa.
Anty tace bismillah kun fara kenan,dama duk amina tazo garin nan banda hutu idan uncle na nan.
jummai dai daki ta koma ta bar masu palourn domin sun isheta da surutu.
Bashar wanda aka fi sani da uncle bash yara da manya a family nasu ka'ni g mijin anty khadija,ya kare ABU zaria tunda yayi service nashi a kaduna ya dawo gidan anty khadija da zama,dama can tasu tazo daya suna mugun shiri da ita.
Fari ne kyayawa dogo,yana da fara'a sosai da son mutane musaman ma ka'nanan yara,yana ji da izzidine kamar shiya haife shi,shi yasa duk yana gida suna tare idan fita zai haka izzidine zai lake masa dole sai sun fita tare..
Izzidine yazo kyakyawa fari tas dan shekara 7 ya rugu da gudu oyoyo anty.
Amina ta rungume shi oyoyo boi,how u?
Yace fine anty.
Haka suka ta hira cikin raha da annashuwa har dare ya raba kowa yayi hanyar dakin shi.
Tana shina ta samu har jummai tayi bacci,tace kassar banza bata da wuyan bacci,ta bidi wuri ta kwanta(asuba ta gari yan matan anty khadija).
A minna kuwa soyaya mai tsafta ke gudana tsakanin aysha da abdukrahim.
Yazo har gida ya gabatar da kanshi wurin baba,bayan dogon binciki ne baba ya amince masa da zuwa wurin aysha,haka suke gudanar da soyayar su cikin tsafta,har waya ya kawo mata kirar gioonie p2 da kyar ta amsa,yanzu shike kai ta schl da safe idan zai je wurin aiki wata rana idan yana da time ya dauko ta idan bai da ta hau bike.
*WANENE ABDULRAHIM*?
Abdulrahim king haifafen garin kontagora,niger state ne,mahaifinshi mamman king sanane ne a garin sabida babban dan siyasa ne kuma dan kasuwa ya rike muka'mai da dama na gwamnati kafin Allah ya amshi abinsa.
Yana da matar aure daya hajia ramatu wacce ake kira da hajia yaya,dayan ta takwas akwai general garba duba yana kaduna tare da iyalin sa,hajia iya tana aure cikin kontagora,hajia fati wace aka fi sani da anty ladin mustapha(kasan cewa sunan mijinta DR mustapha),ibrahim(iro)yana minna da matarshi,mustapha shima yana minna da matarshi sai ka'ramin su abdulrahim wanda bank manager ne a nan minna.
Allawiya kuma tana can sai faman wahala a gudan alhaji saddat,yadda ta aje break fast haka zata dauke shi ta aje lunch,shima haka zata dauka ta aje dinner ko kallon inda abincin yake bai yi,shawarwarin da jummai ta bata babu wanda bata jaraba ba all in vein,data matsa mashi ma cewa yayi bayan ya gama da ita a waje me zatayi ya burgeshi,duk wani abu na burgewa da mace zata ma namiji ta gama mashi a waje dan haka tabar wahalar da kanta,duk tayi baki man bleaching ya ka're,ta rame ga laulayin ciki ya tasata gaba.
Raji kuwa ya gama course nashi a dadafe kullum da tunanen jummai yake kwana dashi yake yini,tun yana aje abun a matsayin tausayawa har ya gane soyayar jummai ke neman halaka shi,babu bata lokacu ranar saturday ya hada inashi inashi ya gar zayo gida nigeria.
Hajia tayi farin ciki sosai domin ya dawo cikin koshin lafia,yayi kiba ya kara kyau ga fatar nan nashi sai sheke yake yi.
Tace masha Allah nayi matukar farin cikin dawo warka,Allah sa a amfana da abinda aka karanta.
Yace amin hajia,na same ku lafia?
Tace lafia lau raji,yanzu sai maganar aure ko?domin ginan ka daka bari ana yi sun kamala da yake ka bar masu isasun kudin aiki,yanzu wireing ya rage.
Yace eh hajia muna communicating dasu ai gobe ma insha Allah zanje inga yadda aikin ya kasance.
Tace ba wanan na tambaye ka ba,matar aure nace ka fada min yarinyar da kake so ai ma yan uwanka magana suje neman aure.
Yace haba hajia daga dawo wana ko hutawa banyi ba.
Tace kada fa ka manta kai kayi alkawari kana dawo wa zaka fitar da mata.
Yace ban manta ba hajia ki kwantar da hankalinki zaji ji labari mai dadi kwanan nan.
Tace Allah tabatar da alkhairi.amin.
Da safe ya shirya tsaf cikin riga da wando ash colur na yadi mai sulbi,kayan sun amshi jikinshi,yayi kyau sosai,sallama yama hajia akan zai ji side(can inda ake masa gini)
Tace a dawo lafia
Gidan su jummai ya fara zuwa,umma na zaune tana kyaran shinkafar tuwo.
Cikin fara'a ta tarbeshi,suka gaisa,tace saukar yaushe?
Yace jiya umma,ya su baba da sauran yara?
Tace lafia lau suke
Cikin ransa yace maybe su jummai na schl,amma fa da zumudin ganinta ya kwana gashi bai sameta a gida ba.
Sallama yama umma ya wuce side.
Babban fili ne an zagaye shi ciki aka gida 2bed rum flat da babban palour sai dining area,kitchen,store sai toilet cikin duk rum din.
Gaskia gidan yayi kyau sosai.
Su jummai ana can an zama yan kaduna,uncle bash shine idanunsu shike kai su ko ina cikin garin kaduna,family housd dinsu ma duk an saba da jummai,har zaria ya kai su cikin ABU ya nuna masu wurare.
Anty kuma ya zage sai koya masu abinci kala kala da wayar masu da kai yadda zasu zauna da mutane,idan kaga jummai yanzu zaka rantsr ba ita bace jumman umma da baba dan koli.
Raji yayi zuwa gaida umma har ya gaji bai ga jummai ba sanan girman kai ya hanashi tambayan ta.
Da haka