Showing 18001 words to 21000 words out of 64084 words
Chapter 7 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt
gari Sunday suka shirya zuwa zuwa ziyaran yan'uwa da abokan arziki har gidan hajia Maman NURA, malam babba,malama hadiza sai gidan nafisa.
Duk jummai ta rokesu gafara, kuma am yafe mata.
Haka rayuwa ke tafia yau dadi gobe sabanin haka,duk abinda baba ya samu a kasuwa haka zai kawo,umma tayi yan dubarunta,su jummai su dafa aka nan aci.
Idan nafisa tayi abun marmari takan aiko masu,haka su allawiya suma suna taimaka wa sosai.
Da aka kama azumi wuri uku jummai ke zuwa tafsir tare da member's nasu na area council,hada waya suka bata kirar Samsung galaxy j1 fara mai kyau.
Sabida sun yanke shawarar bude wata kungiya mai suna""ANA MUSLIM"" DA NASFAT.
WANDA akayi selecting members masu, da'awa, tafsir,amsa tambayoyi,da kuma wayar da kan al'umma akan addinin islama.
Ana samun su a shafukan;-face book,watsapp,Twitter, istagram da sauransu.
Shine dalilin ba jummai waya da akayi.
Har yanzu bata bar sana'arta ba,na karatun novel.
Domin ciki tana tsintar abubuwa da dama na qaruwa,wanda take gyarawa,tai mashi kwaskwarima bisa hujjuji da tsarin addini ta turawa dumbin jama'a masu matsaloli makaman cin irin wanda ta karanta.
Result na weac ya fito.
Alhamdulilah;7 credit da 3pass Aysha ta samu.
Su jummai ma nasu ya fito, sunyi passing.
Jummai tace federal government girls collage minna.
Allawiya kuma Maryam BABANGIDA girls science schl minna.
Sosai su baba sukai farin ciki,sai dai babban tashin hankalin shi bai da,babu abinda ya aje da zai kaisu makaranta.
Ko abinci sai anyi yan dubaru, inaga ance biyan kudin makaranta federal, ga Aysha nason zuwa gaba.
Kuma burinshi kenan yaransa su sami ingantacen ilimi.
Da safe zai wuce kasuwa,ya hadu da Baban allawiya zaune kofar gida.
Hace sallamu alaikum mal.aminuπ€π»
Yace amin Alaika sallam mal.salis,barka da asuba, ya kwanan iYali?
Yace alhmdulilah,ya naka iyalin?
Yace lfy lau, ashe jarabawar yara tayi kyau,barkan MU da arziki.
Yace barka dai, ai yanzu babban matsalar yadda zasu ci gaba da karatun.
Yace tau mal.salis,Allah ke rufa asiri,aci gaba da adu'a,Allah zai kama mana.
Yace haka ne,bara in leqa kasuwar.
Yace tau sai na iso.
Nafisa ta sauka lafia ta samu da namiji, garinsu aka mai data wanka.
Allawiya ta fara zuwa makaranta,shiri sosai babanta ya mata zuwa boarding schl.
Jummai kam har yanzu anyi buga buga amma ina ko rabin kudin makarantar basu hada ba.
Shawara ta yanke na hakura da makarantar, ta koma makarantar su na farko ta koyi handwork.
Dole su umma badan sun so ba suka amince mata da zaman banzar da zatayi a gida gara hakan.
Ranar Monday tun da wuri ta shirya zuwa schl masu.
Uniform nata na da,ta Saka, ta kwashi credentials nata zuwa schl.
Koda ta isa sun gama assembly, har bakin office na principal ta isa.
Tace baba masenja ina kwana?
Yace wa nake gani kamar maryama?
Tace nice baba.
Yace lfy dai?
Tace nazo inci gaba da karatu ne,ko PC ta iso?
Yace eh, amma sai kin jira tare da baqo take.
Tace tau.
Takai 30minut zaune tana jira,duk mallami ya gito wurin sai ya tambayi dalilin zuwanta,duk ta tsawala.
Can PC tayi kiran baba,ya shiga.
Tace file din nan zaka kai workshop.
Yace amma ajiya akwai yarinya a wace tana jiranki,kuma ta dade.
Tace OK ta shigo mana ai mun kare.
Yana fita, yace ta shiga.
Da sallama ta shiga, tare da gaidata.
Tace ah Maryam lfy da safen nan,baki fara zuwa schl bane?
M.raji dake can ciki yana ta rubuce rubucen shi, ya dago kai suka hada ido.
Tayi saurin sauke idanunta,tare da cewa mrng sir
Yace mrng, yaci gaba da ayukan shi, amma hankalin shina wurin su,rabon shi da ita tun haduwan su gidan hajia kusan shekara biu kenan.
Tayima principal bayanin abinda ya kawo ta.
Tace Maryam salis kina daya daga cikin daliban da suka ma schl din nan hidima,kuma ni nayi tsaye a ministry akan a zaba maki makarantar kwarai,ai babu student namu da aka taba turawa can, Dan haka bai kamata ki yanke wanan shawara ba.
Sabida nan daga ss1 zuwa 3 duk aikin hannu ake koya masu kamar;-carpenter, tailoring,mechanic,hand knitting etc,shiyasa bama barunku nan ai, ko su daga kauyuka suke zuwa.
Tace tau babu yadda na iya ne bamu da halin biyan wanan schl din.
Tace tau Maryam gaskia Banso haka ba, kawo file naki ki shiga class.
Tace thank u very much Ma.
Ta juya zata fita zuwa class.
M.raji yace keeee!kada ki kuskura ki qara koda taku guda ne daga wurinnnnnnnnπ‘
*L££MA*......π
Idan an
[12/02, 17:13] βͺ+234 816 432 1306β¬: *B W A*π
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
π·π·π·π·π·π·
*QURUCIYAR JUMMAI*
π·π·π·π·π·π·
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*π·
*BRILLIANT WRITER'S ASSO*.....ππ
*gare ki sury marubuciyar ARNE,hakika kin fadakar,nishadantar,ilimantar tare da tunatarwa,gaskia ARNE ya kayatar da dumbin jama'a,sai fatan alheri""jazakallah""*
*yabon gwani ya zama dole,adade anayi sai gaskia,jameela musa(meelat)INA tayaki farin ciki murna da annashu wa na kamala littafin ki mai suna RASHIN RABO,Allah kara lfy da basira,ya kara daukaka ya bamu ikon amfana da darusan dake ciki amin*
*37-38*
Tsayawa tayi cak,gabantaa na tsananta faduwa.
Yace Dan baki da hankali ace maki abu bai dace dake ba kice sai kinyi.
PC tace amma tana da gaskia fa,da zaman da zatai a gida ba banan lokaci gara nan din.
Yace kyaleni da ita PC,taukin kai ke gareta da girman kai tun tana karama,dama mai hali bai fasa halinsa.
Ai suna da organization a fomwan na taimaka na marayu da masu karamin karfi,mai zai hana tayi compain,zasu taimaka ai.
PC tace ai yarinya ce bata yi wanan tunane ba.
Yanzu akwai wani taimako ne da zaka iya mata?
Yace niyyata kenan, amma dana ga baku sakani ciki ba na kyale ku.
Tace Maryam kinga raji yanzu tare da Matar governor yake, ta bude wani organization na EXTENDED HAND(FULL EFFORT)suna taimaka ma mata masu ciki da kananan yara ta fanin lfy,marasa galihu ta fanin karatu,manoma,bada talafi da sauransu,kuma file din nan da kika ganshi dasu list ne na students namu da suka koyi handwork zai kai wurin Matar governor, idan sun qare karatu a raba masu kayan aiki.
Tace tau mummy nasan da wanan talafi, amma banyi tunane hada MU member's zamu amfana da ita ba tunda marasa galihu ake ba.
Yace yanzu ban file naki duk abunda kenan zan zo gidanku.
Ta bashi tare da mashi godia.
A hanyanta na komawa gida tana ta zancen zuci.
Tace lalai raji mutumin kwarai ne duk da abunda ta aikata akanshi zai taimaka mata.
Data dawo gida tama su umma bayani yadda sukayi.
Aysha tace haka Allah ke lamarin shi,kabi mutum da sharri ya saka maka da alheri.
Umma tace ai ya zama darasi a gare ki,nan gaba ki kiyaye,hakuri nada Dadi.
Baba yayi buga buga har kauyensu yaje kozai samu wani abu ina, sai ma ci masa mutunci da sukayi,wai gara shi har ya samu abinda yasa yara makaranta har sun kare gaba da primary,babba yake son suje, su ga basu yara bayan makarantar allo,maza sai noma,mata kuwa an masu aure.
Haka ya dawo rai bace.
Allawiya nacan ana shan wuya a boarding schl,sai taurin kai ga rashin son aiki sai lalaci.
Tayi kuka tar ta gaji kan bata son boarding schl sabida seniority.
M.raji shiru shiru, tun jummai na kidayan kwana ki har ta kuma na sati yanzu har wata shiru babu lbrn karatun ta.
Aysha ke tausan ta akan suci gaba da hakuri,haka Allah ya tsara masu rayuwar su.
Itama ayshan yanzu koyarwa take a islamiyar su,duk wata 2500 ake biyanta.
Ban garen M.raji kuwa,yayi Iya kokarin shi ya samu ganin Matar governor musamman akan issue na jummai amma abin yaci tura,bata qasar tai tafia.
Idan ya amsa mata foarm a agency nasu dole government schl zata zaba taci gaba da zuwa shikuma bai son hakan sai wanan schl din,bcus it's the best.
Shiyasa taji shi shiru.
Taci gaba daa lamuran ta na ziyarce ziyarce wurin da'awa yanzu har qauyuka suke shiga suna bada talafi iri iri.
Sai da aka share wata guda cikin na biu ya samu ganin her excellency.
Bayan ya mata baya ni.
Tace mal.raji bawai naqi batunka bane amma abun da kamar wuce,sabida talafin nan da aljihuna nake yinta,bawai gwamnati ta dauki nauyin abbin ba,sanan govermnt schl muke tura wa kaima ka sani,yanzu kazo da maganan private schl kamar federal wanda duk tearm a kallan ana kashe almost 100+.
Yace Ma. A taimaka, a duba lamarin nan,she's very intelligent, pls kada muyi ruining feature nata.
Tace ai matsalar shine kona kashe kudin wurin tallafa mata tana iya karatun federal?
Wadda tai government schl tun daga primary, wane grantee kake dashi na zata iya karatu can?
Yace zata Iya insha Allah.
Tace yanzu kazo min da ita muyi mata interview tukun.
Yace insha Allah.
Da dare ranar Friday ya sallama gidansu jummai,tana shirin zuwa islamiyyar dare.
Umma tace jummai duba wake sallama.
Tace tau umma.
Tana fita taganshi,ihu ta saki tare da daka tsale,tace Mallam?
Yace Kedai bara ki taba girma ba, yimin sallama da Baba.
Tace tau tare da koma ciki.
Ta fadama baba, yace ai mai iso.
Jummai tai Mai jagoraa har cikin palourn su.
Bayan gaishe gaishe.
Yama baba da umma bayani yadda sukai da her excellency.
Baba yace tau yaro sannu da kokari fa,Allah Saka da alheri ya tabatar mana.
Suka amsa da amin.
Umma tace amma kana gani abin nan zai yiwo?
Yace insha Allah mama,adu'ar Ku Mike nema.
Aysha kema kici gaba da adu'a muga yadda Allah zai yi.
Tace tau Mallam
Ya masu sallama,su jummai suka mashi rakiya.
Yace Maryam kiyi karatu fa dai bamu San irin interview da zasuyi ba,zuwa Monday sai MU tafi.
Tace tau.
Monday tun da safe ta shirya zuwa 7:30am ya fito,tayi sallama da umma suka wuce saman bike nashi.
Sun isa ministry of women's affair and social development.
Babu wanda ya iso,wuri suka samu suka zauna.
sanye take da doguwar riga na material dark green da hijab white madaidaici da bakar safa.
Yana ta latse latsen wayar shi, nan ta qare masa kallo tsaf;-fari ne ba can ba,dogo mai matsakaicin jiki,kyakyawa dashi,ga side box a fuskarshi mai dauke da duguwar hancii,madaidaicin baki,idanun shi cat eye.
Tayi nanauyar ajiyar zuciya, sai daya kaleta da mamaki,yace lafia dai?
Duk ta daburce tace lfy lau.
Cikin zuciyarta ta tace inama zai soni, gaskia dana mure. (Tau jummai daukar wa kai dala ba gammu).
Sai zuwa 10:30am tawagar Matar governor ta iso.
Yace wait for me here,cikin gagawa ya isa bakin motar, security na tatare shi.
Tace ah mal.raji yaune appointment namu ko?
Yace yes ma.
Tace OK Ku shugo kafin mu fara meeting.
Yace ma jummai ta natu idan sun shiga kada tace komi har sai an tambayeta.
Tace OK.
Palour ne babba yasha gyare gyare da kayan allatu na mure rayuwa.
Manya mata ne akalla sun kai goma ciki babu wadda bata sani ba.
Matar governor tace ah doughter kece ashe.
Hajia aysha ahmad lemu tace what brought her here?
M.raji yayi bayanin abunda ya sani.
Ameeran su na area council tace yanzu sister Maryam kina da damuwa ki kasa sanar da MU,bayan talafin nan a hanun MU yake, meye amfanin zaman tare?
Hajia Aysha Ahmad lemu tace, amma nasha fada maki idan kina da damuwa u come straight to me,baki dauki ni uwa ba kenan ilimin nan fa idan kika sameta duk CI gaban mune, domin addini kekewa hidima.
Her excellency tace bama sai kinyi interview ba, kuje gida duk abinda ke ciki mal.raji zai maki Magana.
Taimasu godia.
Da zasu wuce ta hau bike din,da gangan ta matse shi, ya kara gusa wa, da suka fara tafi ta qara matse shi har suka isa gida.
Tai mashi godia.
Taba su umma lbr, sosai su kai farin ciki da fatan alheri.
An share sati guda m.raji shiru, jummai kullum da tunanen shi take kwana dashi take tashi, wani irin mugun sonshi ke fuzgarta.
Gashi nura bai nan, yana Zaria wurin degree program nashi a ABU,faculty of law.bare ta tambaye shi M.raji.
Shiryawa tai taje gidan hajia.
Da sallam ta shiga, hajia tace lale maraba da jummai,yau kece a gidan namu?
Tace eh hajia, ya kwana biu.
Tace sai alheri,ya mutanen gidan Ku?
Tace duk lfy.
Hajia tace bismillah zauna.
Tace ko tare da surukin nawa kike?
Tace hajia ai ban isa aure ba,sai sister Aysha tayi tace .
Tace tau Allah maku zabi na alheri.
Tace amin,duk sukayi shiru,kowa da abinda yake tunane.
Can waya tayi ringing, hajia tace duba min wake Waya?
Tace raji ne.
Tace kama kama nim,Dan qeta handsfree tasa, dama abinda ya kawo ta kenan.
Yace sallamu alaikum hajia.
Tace amin alaika salam muhammadu,ya aiki,ya abujan?
Yace lfy lau hajia,dama in fada maki ne bazan dawo gobe ba sai friday.
Tace Allah kaimu,gama jummai nan tazo gaishe ni.
Yace wace jummai?
Tace dalibar ka.
Yace ban gane ba.
Tace ga ta kuyi Magana.
Yayi saurin kashe wayar.
Amsar wayan tayi ta qare ma number kallo, ta haddace shi cikin kanta.
Tace hajia ya kashe,zani gida ma.
Tace eyah ko ruwa baki sha ba.
Tace babu komi ai sai wani lokaci.
Tace wata seminar sukaje abuja.
Tace eyah.
Tace na gode fa,ki gaida su umma.
Tace zasu ji.
Tana zuwa gida ta bude wayanta tayi saving number m.raji.
Tace mataki na farko da zan dauka;-text tai mashi na fatan alheri.
Har dare bai kira ba,bai reply ba.
Ta sake mashi good night text.
Har kwana biu shiru babu reply, kuma bata fasa mashi text ba na well wishes.
Da dare tana chart da wayanta, bayan ta gama tura ma yan GRP nasu amsoshin tambayoyin su.
Ta tura NATA tambayar kamar haka-;
*sΓ llamu alaikum,wata baiwar Allah ce Allah ya azama son wani bawan Allah, amma shi baima San tanayi ba,Dan Allah Ku bata shawara*
Haba kamar jira suke message din ya shigo sai comments.
Wasu na fadin taci gaba da neman zabin Allah,idan alheri ne Allah zai tabatar.
Wasu na fadin taci gaba da kyautata mashi ta hanyar;-text messages, phone call,da kula da duk abubuwan da yake so,da wayan'da baya so.
Wasu kuma sukace ta fada mashi shine kawai kwanciyar hankalinta.
*ta tura masu godia da shawarwarin da suka bata*
Yanke shawara tayi ta fada mashi kawai, duk hukuncin daya yanke dai dai ne.........
*L££MA*π
*BRILLIANT WRITER'S ASSO*....π
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
π·π·π·π·π·π·
*QURUCIYAR JUMMAI*
π·π·π·π·π·π·
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*βπ»
*labarin ummerherny*!
*wata sabuwa inji yan caca'ku garzaya kasuwa ko nemi naku kada ku sake a baku lbr*
*shin leema kina nufin a kasuwa kawai zamu iya samun wanan ka'yatacen littafi da muka da'de muna jira*?π
*haba kawata ummu farhana'kyauta kina iya karanta littafin cikin kwanciyar hankali a duk inda kike*
*har kinsa nakai zaune aminiyata leema ko zaki warware min zare da abawa*
*sosai ma kuwa ummu farhana, shafukar sada zumunta zaki shi a wayar ki kamar;wattsap,face buk da sauransu*
*wow gaskia naji dadi aminiyata leema*
*habba ummu farhana ana tare*π€π»
*leema wata labari naji da duminta*
*tau oganiya bani nasha*
*da gaskia ne wanan shaharariyar marubuciyar mai suna 'jamila musa"( meelat)zata fara sabon littafi mai suna "SO MUGUN WASA"*
*tabbas haka yake miss oganniya yana nan tafee*
*gaskia nayi farin ciki sosai leema' domin na dade banga marubuta masu hadin kai, basira da kware wa wurin rubuta littafai masu ilimantar wa,fadakarwa,nishadantarwa,wa'azantarwa tare da kayatarwa irin"BRILLIANT WRITER'S ASSO..."*
*HAKA YAKE OGANNIYA GODIA MUKE*π€π»
*39-40*
da wanan tunane ta kwanta.
Da gari ya waye bayan ta gama aikace aikace na gida,tayi wanka ta shirya cikin shadda orange dunkin riga da skirt yasha adon surfani lemon green""cikin kayan da nafisa ta bata""
Hira suke da aysha akan batun karatun su.
Tace sis kinga m.raji shiru ko lfy gashi 1st tearm na batun qarewa.
jummai ta nisa'yayi tafia ne sis naje wurin hajia can na samu lbr.
Tace Allah mana jagora.amin
Umma ta shigo da kwanon sameera a hanunta.
Jummai ta mike ta amshi kwanon,tace umma har kin dawo?
tace eh,miya ne na samo ma baban ku ko zai samu ya karya ya fita kasuwa.
Tace tau umma tare da shiga dan madaidaicin kitchen nasu.
Gyara miyar tayi tare da tsamar tuwo yanka biu ta sama baba a plate ta daura bisa silver tray ta kai mashi daki.
Hada kayan wanki sukai na gidan baki da'ya zuwa rijiyar kwakwara.
Zuwa karfe 12:0am suka dawo niki niki da kayan wanki,bayan sun gama shanya ne a igiyar kofar gida,ta tatara bucket din suka shiga gida da sallama.
Umma ta amsa tace har kun dawo?
Aysha tace eh umma.
Jummai ta kwanta ssman carpet tace wash umma na gaji.
Tce raguwa haka kike babu auki sai son jiki.
aysha tace tayi kokari yau ai.
Umma tace kada na manta mallam raji yazo dazu,ga takada nan ya kawo ku duba.
Jummai tace amma meya sa bai jira mu va?
Umma tace kajita sauri take,yace ku duba a cika,inda ba'a gane ba ga lambar waya a kirashi gobe zai zo ya amsa.
Aysha ta bude tare da karantawa tace alhamdulilah am very happy for u my little sis admin letter ne.
Tace masha Allah.
Umma tace takadar makarantar ne?
suka ce eh
Tace masha Allahu,Allah abin godia,,oh yaro dan albarka yayi kokari,Allah dai ya biyashi ya bashi mata ta gari.
Aysha ta amsa amin umma.
bayan sun gama karanta wa tare da cikawa.
Suka adana har baba ya dawo.
Bayn sallar isha'i baba ya dawo masallaci,yaci abinci umma ta bashi takardan tare da mashi bayani.
Godia yayi ma Allah tare da shima m.raji albarka.
Kafin jummai ta kwanta sai da tai mashi gud 9te text,har tayi bacci babu reply.
Da safe as usual bayan sun gama gyaran gida sun karya,wanka na musamman jummai akai dan m.raji.
Zuwa 10:0am ya shigo da sallama.
Qare mai kallo jummai tai tsaf;geans trouser black yasa da t.shirt grean mai dogon hannu,gaskia ya hadu iya haduwa sai kamshin turaren coolbreaze ke tashi a jikinshi.
yace ke me kike tunani haka bako gaisuwa?
Tace uhm ba komi,an tashi lfy?
yace lfy lau.
Ya gaisa dasu umma,suka qara masa godia.
Yace makarantar bangare biu ne akwai na kwana,akwai masu jeka ka dawo.
amma na cika mata fanin jeka ka dawo,kuma matar gwamna ta biya duk kudin makarantar har ta qare.
Baba yace masha Allah yanzu yaushe zata fara?
Yqce sai an dawo hutu.
Suka qara masa godia.
Yaa masu sallama,jummai ta rakashi wirin bike
yace akwai magana ne.
Shuru tai,can tace sai yaushe zaka dawo?
Yce mezan maki?
Tace dama.....
*L££MA*βπ»
*BRILLIANT WRITER'S ASSO. ...*π
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
π·π·π·π·π·π·
*QURUCIYAR JUMMAI*
π·π·π·π·π·π·
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*βπ»
EDITING by ummerherny nerserllerh
*daga taskarrrr marubutan mu*
*brilliant writer's sun kasa kawo muku wasu labaran da dumi duminta ""FURUCI"" ""NAMIJI""suna nan tafe kada ku bari a baku labari*
*45-46*
Jummai najin daΔin schl nasu ba kamar wan cam ba,sabida wanan idan sun shiga 7:30am zuwa 8:am a fara lesson,10:30am aje break fast duk students din dianing zasu aci abinci,11am a dawo clasa zuwa 20pm aje masallaci ayi sallah daga nan sai gida,duk ranar Friday ake mss kuma yafi na schl nasu tsruwa.
Tana shiri da duk yan class din kasan cewarsu duka mata amma bata da aminiya kamar amina class rep.
Yau during break suna zauna a cafeteria suna hira.
Amina tace best friend mamin mu ta matsu ta ganki fa.
Jummai tace ai zata gani yau.
Sukaci gaba da hiran midtime test da zasu fara har akayi ranging bell suka koma class.
Da aka tashi bayan sun fito daga masallaci ne suka nufi bus stop suna jiran drivern gidan su amina,can sai gashi ya iso,duk suka gaidashi suka shiga gidan baya.
sai London street suka yi horn a bakin wani tafkeken gida,mai gadi ya wangale gate suka shiga a parking space ya aje motat inda akwai wasu motocin har uku.
Amina tace best friend here we come,let's get inside wankale baki jummai tai tana kalon gidan d mamaki wanda fadin tsaruwan shi banan baki ne.
Ta wani corridor sukabi ya