Showing 39001 words to 42000 words out of 64084 words

Chapter 14 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt

daga ni sai shi gidan bai da dirty,ban iya wani abinci ba bayan shinkafa da miya,tuwo,taliya sai indomie da tea,ban san abubuwan da mijina yafi so ba ta fanin abinci,abin sha,sutura,colour da sauransu,ban san yadda zan tarbi miji ba idan ya dawo daga wurin aiki,ban iya magana mai dad'i ba kullum cikin fada da tashin hankali nida miji,ga kayan abinci iri iri amma ban san yadda zan sarafa su ba kullum daga charting da tsofin samari na sai waya da friends dina,su farry kuwa sai k'ara ingizani suke akan nayita shuka masa rashin mutunci kada ya raina ni,amma maganar gaskiya ina son mijina sosai.

Ajiyar zuciya jummai tayi, ina nan ina zagin bawan Allah ashe kece mai laifi allawiya walahi yayi mugun maki adalci da bai sake ki ba,watan lokacin nan kyale ki yayi ko zakiyi realizinig mistakes naki amma inna kanki na hayak'i shiyasa ya koroki gida kuma dole ya amshe wayanki yace ciki ba nashi ba tunda ba cikin hayacin sa ya yi kwanciyar aure dake ba ga kuma zahiri yana gani kina charting da samarin ki kamar ba mai ilimin addinin ba,gaske dai ya mashe wayar duk hanUKnka mai sanda yake maki amma kika rumtse idanunki,mace babu gyara taya zai samu gamsuwa da natsuwa dake?dole yake neman matan banza,kullum ya nufoki sai warin mayukan bleaching ke tashi a jikin ki instead of turare,babu tsafta kullum cikin kazanta dole ya raba d'aki dake,abinci kala guda kike girka masa kullum dole nefa ya bar cin abincin ki.
Yanzu yaushe yace zaki koma?
Eh tau idan munyi kwana arba'in.
Zanyi ma nafisa magana kinsan yar gaya ce shiyoyin nijar,can garinsu sana'an da akeyi kenan gidansu gyaran jiki na amare,zawarawa da matan aure duk ta iya sosai yanzu ma ita umma tai ma magana zata fara min,yanzu dai zan daga maku kafa a fara dake tunda kwata kwata 3weeks ya rage ku koma.
Nako gode jummai Allah barku tare da mijinki.amin

Nace shawara kayayakin nan dana samu na buki ya zanyi dasu?
Gaskiya kudadenki tunda suna da dama a saya maku fegi(land)kinga idan Allah ya hore ku gida abunku su baba su koma ku huta biyan haya.
zanuwa da sabulai ki raba gida uku,guda na mama,guda naki,guda ki ba mijinki kice kason yan uwanshi ne kiji mai zai ce kota haka zaki samu shiga wurin dangin shi koda bai kaiki inda suke ba, kayan baby kuma ki aje mata abunta idan ma buki ya kama baki da abun bayar wa kina iya dauka ki bayar.

Am so impress wai yaushe kika yi hankali haka jummai?zama cikin masu hankali mana,lokacin da nake cikin ku in banda k'ara izani da kuke yi ina aikata rashin hankali babu abunda na k'aru dashi sai zallar QURUCIYA.

Na tuna bani adu'oin na fara daga gobe sabida bamu da enough time.

samu biro da takarda,shinfid'e baby tayi cikin gadonta ta dauko sabon memo mai hotun baby da biro ina jinki mallama maryam muhammad raji.

Bara mu fara da wurudi(lazumi kenan)

1-ki yawaita salati ga annabi(SAW) a k'alla koda sau d'ari ne a rana Allah zai biya maki kowace irin bukata da kike dashi,saba'in a lahira,talatin a nan duniya.kinga ko muna da bukatu da dama.

neman gafara domin kin tafka kura kurai da dama kafin kuyi aure koshi na iya hanaku samun kwanciyar hankali.
ki laminci karanta
Subhanal lahi sau talatin da uku(33)

alhamdulilahi sau talatin da uku(33)

Allahu akbar sau talatin da uku(33)
Sanan ki cike na d'arin da
"la'ilaha illal lahu,wahdahu la sharika lahu,lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai'in kadir"
Idan kika rik'e wanan Allah zai shafe maki zunuban ki koda sun kai yawan ruwan teku ne.
kuma kina iya hadawa da
"subhanal lahi wabi hamdihi" sau d'ari(100)
ko
"astagfirul lahal lazi la ilaha illa huwal hayyul kayyumu wa atubu ilaihi"
Sau uku a duk lokacin da kikayi sallah.

haka idan lamari ya dagule maki,kin shiga mumunan kunci da rasa mafita,to tashi kiyi alwala,ki fuskanci alk'ibla karanta fatiha,ayatul kursiyyu da suratul-tinni sai inna anzalnahu,sanan ki daga hannunki sama rok'i Allah bukatan ki,Allah zai amsa.

insha Allahu zan dage dayi..
Adu'oi kuma akan mijin nan naki kinsan burtsatsen namiji ne.

ki kyautata alwala kiyi sallah raka'a biyu sai ki karanta aya ta goma a cikin suratul khafi kafa dari uku da goma sha uku(313).

Idan kuma kishi ya ko dangin miji ne suka taso ki gaba ki tashi cikin dare yi alwala kiyi sallah raka'a biyu sai ki karanta
astagfirulah sau dari(100)
lailaha ilallahu sau dari(100)
Allahuma sali ala sayidina muhammadun wasalim sau dari(100).

na sanki da saurin fushi allawiya ga afu'ar yaye fushi;-lailaha illahuwal azimul halimul la'ilaha illahuwal rabbul arshil azim,la'ilaha illahuwa rabbus samawati wa rabbul ardi wa rabbul arshil kareem.

Amma wani lokuta ya kamata nayi wanan adu'oin?
Ko wane lokaci kina iya yi musaman ma idan kina cikin tsarki.
amma lokuta da wuraren da ake karbar adu'a sune;

Daren lailatulk'adir
Yankin dare na karshe(daga karfe ukun dare zuwa asalatu).
Gurbin sallolin farilla(lokacin sallar farillah).
Tsakanin kiran sallah da ik'ama.
Lokacin saukar ruwan sama.da dai sauran su

wayan allawiya yayi ringing,tace kinga babanta ne ya kira maybe yazo ne,nima kin tuna min wayata a kashe take nasan uncle ya neme ni.insha Allah idan na zauna zamu ci gaba hadda nafiloli zan baki.

Tare suka fito,gaisawa jummai tayi da alhaji sadat
godia sosai ya mata akan hidimar da tayi musu,sai da safe tama allawiya ta shige gida tare da rufe kofar sabida kowa ya shigo.
bata samu daman yin wanka ba sabida dare ya raba alwala tayi ta sauya kaya zuwa na bacci ta haye gado tare da kunna wayanta text kawai ta gani na uncle yana mata ban gaji tayi reply har bacci ya kwasheta bai kira ba.
*asuba ta gari mallama maryam salis (mrs raji)*








*LEEMA*✍🏻

*⚜BRILLIANT WRITER'S ASS*..πŸ–Š


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*QURUCIYAR JUMMAI*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍🏻


*Ramlat ar manga(real me dambu)ina taya ki murnar kamala littafin ki mai suna"KISHIYATA JAHADINA" gaskiya ya k'ayatar tare da nuna dumbin darusa jazakallah,inda kika yi kuskure Allah yafe mana baki da amin*

*inna lilahi wa inna ilaihi raji'un ina mika ta'aziyata gareku ""habeeba idrees da hawwa m.u(smasher)"a bisa rashi da muka yi na baba,Allah ubangiji ya jik'anshi da rahama yasa aljana fir'dausi tazam makoma agareshi,yasa can ta fiye masa nan.Allah baku hakurin rashi amin thumma amin*πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»

*61-62*



Yau sun makara sallar asuba sabida gajiyan aikin buki haka suka tashi tare da yin sallah aka gyara gidan as usual.

Suna karya wa ne umma tace yanzu zan gagauta zuwa kasuwan gwari nasan sun fito yanzu a samu ko yan sabulai ne da zaki rik'a masu tsaraba,ah umma ai ba tafiyar safe bace tunda ba nisa yace sai zuwa karfe goma sha biu zamu wuce.
Duk daya ai gara a saya a aje in case koda ya canza shawara cewar aysha.

Baba yace shawar wari ake tsakanin uwa da d'iya ba a saka ni ciki?
Umma ttace baban su maganar tsaraba muke yi,ai hakan ma yayi kyau ni zan fita kasuwa jummai idan kun isa kya gaishe mun da su alhaji.
Tau baba a dawo lafiya.

Umma ma shirtyawa tayi ta wuce kasuwa,aysha tace yanzu kamata yayi mu amso kajin nan ayi miya dashi ko farar shinkafa ne a dafa ki wuce ma hajiya dashi zata ji dad'i,exactly sister kin kawo shawara.
Jeki amso bara na daura per boiling na shinkafa.
Da sallama ta shiga gidan nafisa,amarya ya kwanan su umma?
Lfy lau suka tashi dama kajin nan da na kawo ajiya nake bukata za muyi amfani dashi.

Tau bak'i za kuyi ne?a'a hajia zan ma abinci(white rice da stew)
Hakan yayi dai dai ga nik'a k'en tomatoe nan ki tafi dashi ku hada,mun gode fa da hidima.
Dama ina son magana dake akan batun allawiya ko zaki samu daman taimaka mata da gyaran jiki kafin ta koma?

Wanan ba matsala bane idan zata iya sayan kayayakin da zan buk'ata.
Mun gode zanyi magana da ita sai anjima,tau.

Aysha tace ke kuwa daga dauko kaji kin samu wuri kin yi zaman ki,kai sister magana na tsaya mukayi .
Hope ba sirrin mijinki kika kwashe kika fada mata ba?no maganar allawiya ne gama tomatoe ta bayar ayi miya,ok yanzu hasa wuta a murhun gawayi(chacol)ki wanke kazar ki sake soyata sai ki soya tomatoe din tunda alredy tafasashe ne.

Zuwan karfe goma har sun gama ta shiga wanka,lokacin umma ta dawo da sabulai na wanka yakai sunk'i shida,na wanki dozun uku,omo zip roal shida,sai maggi da gishiri mr chief.

Duduba kayan aysha tayi gaskiya sunyi kyau umma dai dai tsarabar yan kauye kenan,jummai ma data fito daga wanka taga kyau'n kayan.


Text ya mata cewa gashi nan zuwa sabida yau da yamma zai koma abuja,tace umma kinji ko gashi nan zuwa ma,ai anyi dai dai maza shirya da sauri kada ki tsaya nawa,aysha tace ga abinci nan ma mun dafa namu na gida na cikin kula har dare,ga na hajia dashi zata tafi.
Umma tace kunsan baban ko bai cikin shinkafa da dare sai dai na samo nashi tuwo wurin au allawiya.

super wax blue mai zanin yellow,red and white ta saka d'inkin riga da skirt,sai tar kacen yan kune,sarka,yan hanu da zobe,yadda amina ta mata make up ranar suna haka ta sake yin light make up ta shefe jikinta da turaruka ta fitar da babban mayafinta kashka yellow da takarmi half cover yellow.

Aysha da daura mata dankwali ne suka ji sallamar shi,rusunawa yayi ina kwana umma?lafiya lau ya mutanen gida,sannu da hidima fa Allah saka da aljana.
Amin thumma amin,ke fito haka nan ko wuce kada ki bata mashi lokaci.
Fitowa tayi dauke da basket inda kulolin abinci ke ciki sai babban leda na kayan tsaraba,mayafinta rik'e a hannu da purse nata

Aysha tace ina kwana uncle?lafiya lau ya amsa.

Umma mun tafi,haka da mayafi a hannu?ta aje basket din ta yafa saman kafad'a.
Kofar baya ta bude ta aje kayan,ta dawo gaba ta zauna gud morning uncle?morning yace a takaice yana mamakin hali irin na jummai.

A kofar gidan su yayi parking ta fito dauke da basket mayafi na fad'owa tana faman gyarawa suka yadda zango a paloun hajia.

Ina kwana hajia?lafiya lau ya mutanen gidan ku?
Lafiya lau suke ga abinci nan nace bara na kawo miki tace cikin jin kunya.
Ai ko kin gyauta don mijin naki yau a makare ya tashi kuma da b'akin hali ko karyawa bai tsaya yiba yace zai tafi dauko ki,dauko plate a kitchen ki zuba mashi.

Plate spoon da serving spoon ta dauko,shi dai sai dane danen waya yake yi,ta zuba mashi shinkafar kad'an sai nama kawai,dan ta lura dashi bai cikin abinci sosai sai kwalama.
Hajia yace dauki kaci,yace tau bai yi niyar ci ba amma da yaji dadin abincin bai san sanda ya cinye duka ba,ta kwashe kayan ta dauraye,hajia tace da kin barsu ai na wanke ku hanzarta rana nayi gashi ana neman ka a wurin aiki.

Tace tau sai mun dawo,ku gaishe su.

Sai da suka kama hanya sosai yace in tambaye ki mana?
Ina ji
Menene yasa bakya iya bin umurnin dana vaki?
Me nayi kuma uncle?
Wani tashen iya shege kw damun ki dazan hanaki yafa mayafi amma kin k'i hanuwa,ai da gani nayi da kike budurwa manyan hijabai kike sawa hada safa da nikaf yanzu ne da kika yi aure kike sha'awar tallar jikin ki?

Kayi hakuri naga ai babban mayafi ne kuma tare da kai zamu fita.
Oho mayafi ai mayafi ne komin girman shi,sanan idan tare zamu fita mutanen da zasu yita kallonki rufe masu idanu zanyi hadda wani make up ko?

Ya zama kai na farko kuma na k'arshe da zaki sake fita da mayafi koda vana nan ko make up,tau .

Cikin ranta tace na shiga uku wane irin mutum ne wanan mata na kwaliya mazajen su na apreciating,shi sai ruwan bala'i,yanzu yanzu zaka ga yana fara a anjima ya koma fada kamar mai aljannu.

Da ya gaji da zaman shiru ya kuna masu kira'a har suka isa kauyen kuta,a kofar wani babban gida suka yi parking,yace oya gyara mayafin nan ki aza shi saman kanki,ta gyara,sana wanan ledar fa tayi banza dashi.

Babban bishiyar mangoro ne a kofar gidan aka shimfida tabarma datijawa ke zaune suna shan iska sai yake suke faman yi,wuri ya samu ya zauna ya fara gaisawa dasu da yaren su na gwari suna amsawa cikin nisad'i,ya nuna ta tare da masu bayani da yare.
Ta shiga gaidasu,suna amsawa da fara'a duk suka mik'e zuwa qurin mota aka bude ana dudubawa da suka gama ya shiga cikin gida tana biye dashi akala part part dake cikin gidan yakai ashirin,sabida babban gida ne sosai(family house)
Haka akayita shiga da ita lungu lungu tana kai gaisuwa wasu ma ko hausa basa ji,duk inda ta shiga sai ta aje masu sunk'in sabulu na wanka guda,na wanki manya yanka uku da omo zip,haka tayi ta rabon tsaraba wasu ma kudi ta basu kasan cewar kayan basu iya va.
Anata zuwa kallon matan raji yar gayu kowa ya yaba da hankalin ta,abinci kuwa kala kala(duk wanda yasan gwara wa yasan su a noman doya)haba sakwara kwanu kwanu da miyan ganye da kaji,ko wane sai data tsakura "gata ba gwanar son doya ba"kada dai suce ta kyamace su.
An zaga da ita taga gari,shima fita yayi zuwa gidajen abokanshi na kauye sabida tun farkon rayuwar shi nan ya tashi da ya gama junior secondary schl zamanshi ya dawo hanun hajia kasan cewar kauyen babu senior secondary schl.
Sai zuwa la'asar suka ma yan kauye sallama,tsaraban doya,mango,cashuw,da kayan miya cike da buth na raji ga motar nashi karama(vibe ce)haka suka lalab'a sai da suka hau titi sosai yace nan gidan da muka fara zuwa nan ne gidan mu,inda aka haifeni kuma gidan mai unguwa da iyayen mu suka mutu ya rage k'anan iyayenmu,yanne da sauran diya da jikoki suke cikin gidan yanzu.

ina kika samu kudin yin tsaraba?umma ta sayo.
Shine baki min magana ba in baki kudi ki saya duk abinda kike b'ukata bayan nasha fada maki times without numbet idan kina da b'ukatan wani abu ki fada min,sorry kawai tace.
Abincin ki na dazu yahi dadi sosai kuma kinyi kyau yau fiye da kullum.
Cikin ranta tace sai an gama na mutum uban sababi a fara yabon shi,me kika ce?ba komi,gara ki fada kafmda ya kashe ki.

Haka suka iso gida a gajiya da tsaraba hajiya tace tun kafin ku iso sun bugu min waya suna ta yaba maki jummai a gaisheki gaskiya kinyi naminin kokari fa,yace ga tsaraba can ma cikin mota da suka bada,tace wanan ai nasu jummai na bana bukatan komi a ciki,haka sukata hira jefi jefi jummai kesa baki.

Yace karfe shida saura hajia abincin nan ya rage?eh yana kula ai
Ok ya mik'e tare da nuna jummai ki kai min d'aki zanyi wanka,idan na shirya gaba daya in ajiye ki agida daga nan zan wuce.

Suna shiga daki bayan ta gama serving nashi abincin, yace hada min ruwan wanka,ta shiga toilet ta hada mashi,yana gama ci ya shiga wanka,fitowa yayi daure da towel,ta done kanta k'asa har ya gama shiryawa ya dawo kusa da ita ya zauna tare da rungumo ta baby akwai abinda kike da b'ukata ne?

babu komi uncle,ya k'ura mata ido na baki amanar kanki ki kula min da kanki sosai kuma kiji tsoron Allah aduk inda kika kasance.
Insha Allahu zan kiyaye,ki mai da hankali wurin karatun ki,tau uncle.

Romancing nata ya fara yi cikin kware wa,tun tana d'ari d'ari har ta saki jiki tana mai da martani har ta fishi zak'ewa.

Sosai yaji d'adin yadda ta saki jiki dashi,sai daya gaji dan kanshi ya gyaleta.
Are u satisfy baby?ko aci gaba,ta gyaleshi idanunta na rumtse kamar mai bacci..open yr eyes and talk am your husban fell free..stil bata bashi amsa ba sabida jikinta yayi weak sosai,tashi mu tafi k'ara rungumeshi tayi tare da fashewa da matsanaiciyar kuka.
Haba baby na fada maki bana son kukan nan pls..ta share hawayenta tana faman sheshek'an kuka,wanke fuskar ki muje ko,ta mik'e zuwa toilet ta wanke sanan suka fita,sallama ya ma hajia tayi mashi fatan alheri suka kama hanyar gidansu jummai..a hanya hanunshi rik'e gam cikin nata yana ta kwantar mata da hankali har suka isa.
Agurguje yama umma sallama,tace gashi babansu na hnyar bai dawo ba har yanzu..a'a umma babu komi ina gaidashi sai na sake zuwa insha Allah wani sati..raka shi ta sake yi har cikin mota yace koma gida baby kada ki sani kuka yace""cikin zolaya""take care of yrself for me sai na kira ki..Uncke Allah kiyaye hanya,ya tsare min kai a duk inda kake..amin baby nagode da adu'a juyawa zayi zuwa gida yace wait baby who teach u all these thing?ignoring nashi tayi sabida kuka na k'okarin kwace mata...yan motar yayi ciki da tausayi tare da mamakin yadda yarinya k'arama kamar jummai ta iya tarairayar miji haka,gashi nan da nan ya sake da ita(kada kayi mamaki mal.raji ga hausa novel suna koyar da matan mu yadda zasu gyara zaman takewar su da mazajen su)

Har dare haka take sukuku,text ya mata ya isa lafiya kuma yayi kewar ta..reply tayi itama tayi kewarshi.

Bayan sallar ishai ita da allawiya suka shiga gidan nafisa da yake mijin nafisa yayi tafi'ya

bayan gaishe gaishe tace allawiya naji bayanin komi wurin jummai ,gyaranku akwai banbanci
Ke jummai naki daban ne kuma ba mai yawa ba tunda baki tab'a sanin namiji ba,babu ruwanki da wasu matsi,cushe cushen magunguna a gaban ki..sarki ne zaki fara da ruwan dumi sabida yana hana mace samun infection kuma yana hana budewar gaban mace onlike ruwan sanyi,sai had'de had'e na k'arin ni'ima,gyaran fata,breast duk da naga breast naki baya bukatan wani dogon gyara sai kuma ana gobe za a kai ki zamuyi hadin kaza da tantabara yar shila.

Allawiya zamu fara da matsi da gyaran breast daga hobe sabida bamu da enough time sai gyaran fata daga baya saura sati guda ki koma sai ayi hadin karin ni'ima.

Sanan zan koya masu wasu abubuwa da zaku hada da kan ku cikin sauki a gidajen mazajenku.
Jummai already kayakin ta na ajiya mub saya..allawiya ki bada 5k gobe mai kayana zai kawo min na zaba wayan da zamu fara amfani dfasu mu hada da kanmu a gida ku gani sabida gaba.

Sai gobe idan Allah ya kaimu a fara..mun gode Allah bar zumunci nafisa...


*LEEMA*✍🏻*⚜BRILLIANT WRITER'S ASS*..πŸ–Š


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*QURUCIYAR JUMMAI*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍🏻


*EDITOR*
ASMEENAT XEEYANπŸ‘„


*Ramlat ar manga(real me dambu)ina taya ki murnar kamala littafin ki mai suna"KISHIYATA JAHADINA" gaskiya ya k'ayatar tare da nuna dumbin darusa jazakallah,inda kika yi kuskure Allah yafe mana baki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login