Showing 63001 words to 64084 words out of 64084 words

Chapter 22 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt

jummai na zaune saman bed tayi tagumi,raji ma haka,bayan gaishe gaishe aysha ta hada masu tea cup biyu,umma tace daure ka amsa ko k'adan ne kasha ''haka ya amsa yana sepping kamar mai shan magani..haka aka matsa ma jummai tasha kadan,umma tace ya kamata raji ya koma wurin amsan gaisuwa tunda sun iso,badan yaso ba ya wuce gidan hajia...zuwa 10am doctor ya iso''nurses ya umurta dasu shirya jummai su shigo da ita theater room ....Bayan minti talatin aka ce su umma su bada kaya''aysha ta bayar''yara biyu aka fito dasu(baby girl da baby boy)yan bakwai ni(7month)yaran kyawawa,amma k'ana na ne sosai...sai da aka k'ara awa guda, aka fito da ita tana sharar baccin ta...nan aysha tayi ta kiran yan uwa tana fada masu labari mai dad'i before u know hospital ya cika da yan uwa,kowa sai fad'i yake nura da hajia sun tafi kuma sun dawo....haka anty balki ta kwashe su zuwa wqni gidan friend nata kusa da hospital,tai masu wanka fes ta shirya su..sai da yamma jummai ta farka''hadda kukan ta wai ciwo ya dame ta,ga yunwa da k'ishin ruwa''umma tace don ma baki d'an d'a na azabar da mata keji ba wurin nak'uda da haihuwa..suna cikin haka ne Raji ya shigo da abokan shi,haka suka ta daukan babies domin sunyi kama da baban su sak banban cin yaran launin fata"macen fara,namijin b'aki"

Raji na zub da hawaye yayi masu huduba macen aisha'sunan hajia'namijin nura..yace daga yau yarana sunci sunan aysha da nura,ban yadda a 6oye sunansu ba..kabara akayi gaba da'ya,abokanshi suka mashi sallama,nan ya zauna har dare yana rarasin matar shi'umma da taga haka ta wuce gida.

Bayan sati guda aka sallami jummai,gidan umma ta koma''gidan hajia kuma anyi ad'uar kwana bakwai'' mutune sun watse'saura na gida,koda aka tambayi raji menene yake so cikin kayan hajia?.ya nuna babu abunda yake bukata'haka yan uwa suka rabe kayan hajia..gidan da take ciki dama gadon nura ne kuma ya rasu bai bar kowa ba..shawara aka yanke da asa gidan a kasuwa a gina masu masallaci ladan yakai kabarin su.

Har yanzu raji bai koma dai dai ba,ya zama shiru shiru,kullum cikin tunane...an kai kayan barka gidan su jummai da manyan raguna biyu'su anty balki ne yan bakin gado'uwar dakin mai jego'..amina ma nan take yini kafin ta fara schl..Anty khadija ma tazo da baby'n ta ahmad..jummai taji karfin jikinta sosai sabida tana samun kulawa na musamman 'sati biu da haihuwa aka yanka ma yara ragon su,ba wani taro akayi ba sabida jimamin mutuwar hajia,amma sun samu kyaututuka.


Raji ya koma bakin aikin sa tare da cuku cukun nema masu gida a abuja'a ''cewar sa bazai iya zama a minna ba hajia '.

Amina ma ta xuce schl,soyaya sai abunda yayi gaba tsakaninta da farhan,hadda alkawarin aure dadyn farhan yayi masu idan ta maida hankali a karatu.

Bayan wata biyu twins sunyi kwari,raji yazo ya wuce dasu abuja da mai rainon su'jummai ansha gyara sosai'..
Aysha
ma na fama da laulayin ciki,ga aikinsu babu hutu,abdul yaso ta aje aiki ''ta nuna rashin amincewarta domin adashe take yi da zumar biya ma iyayenta kudin kujeran makka su sauke farali.




*BAYAN SHEKARU UKU*

abubuwa da dama sun faru ciki hadda auren amina da farhan bayan ta gama schl''suna zaune lagos.
Aysha ta haifi baby girl taci sunan umma.

aysha ta biya ma umma da baba kudin kujeran makka,abdul ya biya mata itama tare suka tafi suka sauke farali.

koda suka dawo raji yasa an gyara ma su baba gidan ya koma ''2bedroom flat''da toilet ciki.

Jummai ta k'ara haihuwar baby girl mai sunan ta maryam'raji yace a kirata da jummai'amma bai fata tayi irin QURUCIYAR momy'n ta.

Ya gina ma jummai makarantar islamiyya babba a cikin minna kusa da masallacin su hajia...Tare suka je saudiya aikin umra,ga mota daya siya ma jummai tana kai yara schl.

Allawiya ma ta k'ara haihuwa har yara biyu duka mata.


su jummai basu cika zuwa minna yanzu sai lokacin bukin sallah,ko wani abu ya taso ''a gidan su suke sauka..

Ranar sallar laya,umma na gani tayi shar cikin leshi red colour mai daukar ido tana faman fara'a,ga hauren makka ya zauna das a bakinta..palon su yasha tile da manyan ledar set,ga plasma manne a bango..rashida(diyar da umma ke rik'o)tana kwashe abinci a kuloli..sallama suka ji,yara ne kyawawa su hudu suka shigo da gudu'ka'ka oyoyo'ta rungume su,daga ina haka?su jummai da aysha suka shigo cikin shiga ta alfarma sai kamshi ke tashi,sunyi shar dasu kamar wasu matan governor's'ko wace na fara'a ga hauren makka na zinari na haskawa cikin bakin su.

umma tace daga ina haka yau sallah bara ku tsaya a gidajenku ba ku samu lada!!!kai umma jikokin ki suka tasamu a gaba sai an kawo su wurin ka'ka su amshi happy sallah cewar jummai...aysha tace ai mazajen mu suka ce a kawo su idan sun dawo masallaci mu wuce a bar maku su''rashida ta gaishe su suka ''da fara'a suka amsa''nan aka koma palour a na sabon gaisuwa,yara suka fara tsale saman kushin''umma tace kun gyara gidan ku kunzo ku 6ata nawa kafin mijina ya dawo ko?'''yara suka sheke da dariya'''jummai tace ji palour'n umma kamar na sabuwar amarya sabida tsaruwar shi ga kamshi''murmushi tayi''kuyi ma mazajen ku godia sanuwa suka saya mana na layya..sallama suka ji daga kofar palour.
baba,raji da abdul ne cikin ankon farin shadda da babban riga blue sunsha kyau da alama daga masallaci suka dawo.

Nan aka zauna tare da sabon gaisuwa,yara suka koma wurin baba'yan hamsin hamsin sabbi baba ya raba masu..rashida ta gabatar da abinci 'suka ci aka sha,bayan komi ya lafa suka masu umma sallama, kowa ya kama hanyar gidan shi'su umma aka bar ma yara'baba yace Allah mai iko yau ni mallam salis d'an koli ne da jikoki har hudu,ga surukai jarumai masu zuciyar yi,umma tace lalai Allah abun Godiya,bamu haifa da yawa ba amma gamu da jikoki ninkin abunda muka haifa,baba yayi murmushi irin nasu na manya dama haka yake'MAHAKUR CI MA WADACI'

a hanyar su jummai na komawa gida ta kalli raji cikin shaukin so'my master'happy sallah'..yayi murmushi ai sai mun isa gida zan amshi happy sallah na,da abunda yafi komi dad'i da muhimmanci a rayuwa ta,kinsan bana gajiya dake kullum sabuwa kike k'ara zama a wuri na'tell me what is the secret?..uhm my master u are the secret''godiya nike.. Allah shine abun godiy daya bani gwarzon miji kamar ka.

suna isa gida yayi horn,gate man ya wangale masu gate,yana parker motar shi ya sungumi matar shi sai bed room nasu......

suhanaka llahuma wa'bihamduka ash'hadu an la'ilaha illah amta astagfiruka wa atubu ilaihi
🔚🔚🔚



*KU SAURARI SABON LITAFINA MAI SUNA 'RIKICIN AURE NA'*



*LEEMA*✍🏻

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login