Showing 60001 words to 63000 words out of 64084 words

Chapter 21 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt

zama lafiya mai daurewa amin''hira suka ci gaba dayi take ba jummai labari ai kud'aden da abdul kan bata 10k duk karshen wata na trasport da kuna wayanda yake bata na kashe wa ta shiga adashe dasu yanzu ta kwashi dubu dari kuma ya bata dubu hamsin ta k'ara idan akwai abunda take son saya har sun je kasuwa da friend nata faiza sun yi sayayan kayan kitchen da wasu tar kace'''tace gaskiya kinyi dubara sister an fara biyan kune?...tau kinsan anyi posting namu ne kafin result ya fito idan yayi kyau za a dauke ka aiki parmanent,amma su na bamu wani abu duk karshen wata.Allah taimaka.

Har suka wuce hajiya bata farfado ba,su jummai na nan dai sallah ke tadasu ita da raji domin mutane sun rage sosai,allawiya ma tazo har da abinci ta kawo''sai da yamma ta farfado,doctor ya kira ya duduba ta,yace taji dama sosai ana iya bata abinci ko wane iri taci,nan jummai ta zuba mata abincin da allawiya ta kawo,kuma alhamdulilah taci sosai''haka suka yita hira da ita sai da dare ya raba tace su wuce gida domin akwai mai kwana da ita''''a hanya ya tsaya ya masu take away''domin ya lura da jummai taki cin komi a hospital sai coke data sha''suna iya gida tare suka yi wanka''ta zuba mashi abincin da yayo take away''ke bara kici bane??no coke kawai zansha bana jin yunwa''na you sabi''ya cika cikin shi,ta kwace kayan basu tsaya dogon hira ba suka shige domin a gajiye suke''jummai kam ta murzu hanun mijinta cikin daren nan,ta jigata sosai amma yaki sarara mata gashi maranta sai mugun ciwo yake mata''haka ta hakura har ya samu natsuwa.
Da safe a dadafe ta gyara gidan ta hada break fast mai yawa hada na hospital''babu yadda bai yi da ita ba taci abinci'' tace ai taci kafin ya tashi daga bacci,haka ya hakura ya cika cikin sa da abincin matar sa mai dad'i
wayanta ta kuna ta kira anty balki ta fada mata hajiya na hospital'''ta kira amina ma ta fada mata''tace insha Allah zan shigo yau sabida jiya mukayi sendforth party namu'''jummai tace iye yan mata su graduate manya,ina ruwan amindago an gama secondary schl''dariya abun yaba amina sosai,mami tace keda wa?jummai ce ke tsokana ta ''''mami ta amshi wayan suka gaisa da jummai,tayi mata ya mai jiki?.tace taji dama sosai''nan tace sai sun zo''haka suka shirya zuwa hospital''hajia taji sauki garau sai d'an abunda ba'a rasa ba''yan dubi ya sai zuwa suke yi ciki hadda baban su jummai''anty balki hadda abinci ta kawo''su mami ma kayan fruits suka kawo.
yanzu kullum a hospital suke yini sai dare yayi su koma gida''Raji na lak'e da jummai baya raga mata kullum sai ya amshi hakk'in sa na aure''tun tana hakuri har abun ya fara damunta,domin ta gane shi mutum ne mabuk'aci sosai,gashi yanzu bata cin abincu kwata kwata ta tsani abinci sai coke take yini sha''ga ciwon mara dake matsa mata kullum idan suna kwanciyar aure''haka dai ta barshi akan period din ta ke son zuwa,amma kuma abun yak'i zuwa har lokaci ya wuce sai ciwon mara ta barshi akan maybe canji yanayi ne..

Ranar kawo lefe jummai ta kira amina gidan ta suka soya kaji goma da katon na drinks biyar suka wuto gida dasu'' allawiya ta zo itama da fried rice kula guda sabida daga kontagora za a wuto da lefen''baby rahma tayi wayau sosai''gida ya cika da yan uwa da abokan arziki''jummai ta cire kaji biyar da katon na fanta taba umma nasu ne.
Sai zuwa karfe uku suka iso cikin sharon''mata uku,maza biyu'''sallah suka fara yi aka gabatar masu da fried rice na allawiya''sun ci sosai tare da yabawa da karamci irin na iyayen aysha''set guda na akwatuna da kayan lalle''maza kuma suka gana da su baba aka bada sadaki naira dubu hamsin.
Barakallah kaya sun dama na jummai a kyau da tsada sun shanye""sabida bank manager ne"ga family nasu akwai y'ayan bank'''''sai da suka yi sallar la'asar suka juya da kajin su da drinks sai 10k da jummai ta basu.

Sai da mutane suka rage suka k'ara duba kaya,nan jummai ke tambatan ta kontagora zata zauna ko nan?..tace kontagora yayi gida,amma ya kama masu gidan haya a nan two bedroom flat''tunda nan yake aiki''sosai jummai taji ma yar uawarta dad'i sai dare raji yazo d'auka rta daga hospital'''bayan sun gaisa dasu baba tayi masu sallama suka wuce gida''''hada fargaba take dare yai yace zai amshi hakk'in sa'''yau kuka ta saka masa akan ita ya saurara mata haka wanan ta gaji kullum bata jin dad'in komi sai ciwon mara da take k'are wa dashi amma ya matsa mata da abu guda''''yace ai shi yana jin dadi kuma idan lafiya ne bata da shi ai sai tayi magana suje hospital ba '''ta aza masa kuka ba''idan kuma ta gaji dashi ne yak'ara aure'''dama ya fada mata k'arin auren shi na hanunta''haka dai ya lala6ata har ya samu natsuwa ya barta da ciwon mara.

yau suna hospital wurin hajia tana zaune suna hira,wata nurse t shigo dama sun saba da jummai,suna mutunci sosai'''ta canza harshe da turanci tana tambayan nurse din meke kawo ma mace yawan ciwon mara idan mijinta na saduwa da ita?tambayan farko da nurse tay mata shine ko tana da shigan ciki ne?'''tace gaskiya bata sani ba,amma bata yi period nata ba last month gashi har wani wata ya k'are,kuma bata cin abinci''''tace ta biyo ta lab suka tafi ta amshi fitsarin jummai tayi pregnancy test''positive ya nuna''tace ma jummai ai k'aramin ciki ke gareta'''murna sosai tayi ta dawo daki''''abunda bata sani ba hajia najin turanci sabida mijinta tsohon soja ne har lagos sun zauna'''sai da raji yazo daukar jummai hajia ta juya harshe da gwaranci take fada ma raji ya binciki matar shi kaman tana da shigan ciki''yace tau''da suka dawo gida ranar bai sex da ita ba dad'i sosai taji,kuma yayi noticing nata''da safe daya matsa mata taci abinci hadda kuka ta saka masa''ita lalai coke zata sha''ya hanata sha yaga iya gudun ruwanta amma stil tak'i cin komi.
Da suka zo hospital ne doctor ya kira shi akan ya gama binciken da zai yi''a india ake aikin kuma million goma ne kudin aiki sanan doctor'n dake aikin duk april yake yi''Raji yace zamu shirya ayi mana booking before then'' sallama ya rubuta ta koma gida taci gaba da shan mgungunan ta tunda yanzu febury muke before april ta sake dawo wa check up kafin su wuce...nan ya mashi complain akan jummai...daria doctor yayi tare da cewa ya shigo d ita ayi scarning''koda tazo akayi cikinta wata biyu sai dai ba a cikin mahaifa yake ba shi yasa take fada da ciwon mara lokacin da yake saduwa da ita''sabida haka dole ya daga mata kafa har cikin yakai wata biyar,kuma duk wani aiki gida for now ta bar yi,idan ba haka ba ana iya rasa baby'n'' an rubuta mata magunguna da zasu taimaka mata sai shawarwari daya basu''godia suka mashi''sosai raji yayi farin cikin samun cikin jummai''ita nata farin cikin da biyu ne zata huta da azabar da take sha idan yana saduwa da ita.
Da ya fada ma hajia murna sosai tayi hadda hawaye wai nura ya mutu,ga sabon nura an sama mata''haka suka tatara kaya zuwa gida yaso kwarai hajia ta koma gidan su da zama,tak'i amincewa'sabida k'anwarta na nan wadda mijinta ya mutu''ta dawo wurin hajia ita ke jin yarta''haka ya hakura ya kaita gida''cikin di'yan kau'nar hajia aka dauko ma jummai guda wada zasu zauna tare tana ta yata aikace aikacen gida''raji kam duk bukatan shi ya tashi haka zai rarashi jummai har ta amince ya biya bukatan shi''sabida gaskiya yanzu alhamdulilah ba kamar da ba ta br jin ciwon maran''amma kam babu abunda ya canza game da rashin cin abincin ta har yanzu coke take sha sosai....

Amina result na waec ya fito''alhamdulilah anyi nasara''yanzu shirye shiryen rubuta jamb take yi.

Shirye shiryen buki ya kankama gidan su jummai,da raji ya labarta masu tana da ciki sosai baba yayi murna,haka umma da ma duk yan uwa baki daya,anty balki sai tsokana rta take ''wai daga shiga sai daukar ciki''da anty khadija taji labari sosai ta taya jummai murna''ta basu hakuri akan bara ta samu zuwa auren aysha ba sabida cikin ta ya shiga watan haihuwa.
Sosai raji ya bude bakin aljihun shi a kan bukin aysha'''domin yana matuk'ar tausaya ma su baba halin rashi da suke ciki kusan rabin kayan d'aki shi yayi '''haka ya faranta ran jummai sosai''ta k'ara gode ma Allah da ya bata gurzon miji mai zuciyar yi,duk da rufin asirrin Allah ne kawai,amma raji akwai zuciyar yi.
Satin buki ya zagawo yanzu gida take yini sai dare yake zuwa daukan ta.
Ango ma ba a barshi a vaya ba sosai ya gyara gidan daya gina a kontagora da abubuwan more rayuwa''yace duk kayan da aka mata a saka a nan minna inda ya kama haya''kudi sosai ya sakar ma aysha domin fitar da iyayenta kunya sabida yasan halin yan wanshi akwai karyar arziki.
Haka kuwa akayi a bosso lowcot gidan yake madaidaici mai d'akuna biyu da palour,su nafisa,allawiya da jummai suka gyara gidan tsaf.

Amarya ansha gyara jiki har ta gaji''dama nafisa mutumiyar ta ne''su anty balki ma ba'a barsu a baya ba ''sun bata tasu gudun mawar'''yayin da k'awayen aysha watau faiza da sadiya suka tsaya tsayin daka domin ganin komi ya tafi yadda suka tsara''ranar alhamis aka yi kunshi da safe,da yamma kuma kamu duk a gidan nafisa.

Juma'a akayi walima na mata zalla a ''Lebo kutigi conference center''yan uwan ango sunyi ranmwar gani,yayin da jummai ta wadata wurin walima da kalolin girke girken ta mai dad'i da kayan shaye shaye,sai savonier's da sukayi rabo.

Ranar saturday da karfe goma sha biyu n rana dumbin jama'a suka shaida daurin auren
*Aysha salis*
&
*Abdulrahim mamman king*
Daurin auren da ya samu hallartan manyan yan kasuwa,manyan yan siyasa,manyan banker's da sauran mutane''bakin ango bai rufuwa sai fatan alheri ake mashi''sai da komi ya lafa ne aka bude masa dakin baba ya shiga da abokanshi,suka ci abinci''sanan amarya ta shigo da abokanta biyu aka gagaisa tare da fatan alheri''suka basu wuri su zanta.
Hugging nata yayi sosai yana zub da hawaye'''aysha nafi kowa farin ciki,nafi kowa sa'an mace ta gari,ina kara gode ma Allah daya bani ke a matsayin uwar ya'ya na''haba dear kada ka sani kuka nima nafika farin ciki da sa'a fatana Allah bar mu tare amin'''ki fada ma su faiza sai ku shirya idan ayi sallah zamu wuce kontagora''ta amsa sanan ya fita.
Haka amarya tayi wanka,ta shirya cikin atamfa super wax blue''abunka da farar mace ta haska sosai duk da kana hanko tashin hankali da jimamin rabuwa da iyaye akwayar idanunta haka take dauri ya''wurin baba aka kaita tasha nasiha sosai mai ratsa jiki''haka ma umma taja mata kunne sosai duk da sun san halin aysha bata da matsala kuma akwai hakuri da kau da kai'''da kyar aka rabata da jummai suna faman kuka''raji ya jaye matarshi zuwa gida sabida halin da take ciki kada ta ja ma baby'n su matsala.
Ba'a kwashi mutane da yawa ba,daga amarya da abokanta biyu,sai gwagwanin amarya uku suka kama hanyar kontagora.
Umma sosai taji kewar diyan nata gidan yayi mata fadi''ta rok'i kaunan baba data bar mata d'yarta rashida ta zauna wurin su'' gwamma ta amince sabida taga diyan umma duk masu hali suka aura''haka aka watse aka bar umma da rashida yar shekara goma sha biyu.

Amarya sun isa kontagora lafiya''a mutunce yan uwan ango suka amshi su''bayan an damka amanarta wurin su, aka wuce da ita gidan ta dake federal lowcost''fadin tsaruwan gidan 6ata baki ne'''amarya sai kuka take,haka suka lala6ata ta tsagaita kukan''akayi sallah tare da cin abinci''ango ya bugu mata waya akan su shirya zuwa takwas na dare akwai dinner da antie's nashi suka shirya masu''haka akayi anko amarya da ango sukayi na gizna shadda milk colour sunsha kyau har sun gaji'''a safara hotel kontagora akayi dinner,an ci,an sha,an zuba kudi sosai ''sai lokacin ta k'ara tabbatar lalai abdul d'an dangi ne ''sai sha biyun dare aka watse.
Washe gari yan uwa ango nata zuwa ganin amarya kuma sun yaba da za6in abdul''sai da rana bayan sun ci abinci,sunyi sallah mota tazo daukan yan gidan amarya zuwa minna''da kuka ta rabu da friends nata''sister's na ango nata bata hakuri su suka zauna da ita har yamma''suka k'ara gyara gidan suka wuce.
Da dare ango ya shigo da abokanshi''bayn adu'oi da fatan alheri suka wuce''kaji ya shigo dasu da hollandia yughourt,bayan sun ci,sun sha,yayi wanka itama ya umurce ta da tayi wanka tare da dauro alwala'''nafila suka gabatar tare da dau'oi'n neman zama lafiya'''cikin natsuwa ango ya amshi budurcin matarsa,sai sam barka dasa Albarka.

Da safe zaza6i ya rufeta,sai daya taimaka mata tayi wanka,tana faman jin kunyan shi..yace ai gara kibar jin kunyata don mun zama hanta da jini,cikin tsadaden leshi ta shirya,bata yi make up ba amma tayi kyau..yan uwa nata zuwa sallamar amarya..haka rayuwa mai dumbin farin ciki ya kasance gidan aysha da abdul,kafin su dawo minna ta saba sosai da sister's na abdul m,sabida akwai ta da hakuri..wata guda a kontagora suka dawo minna,har gida ya kawota da dare suka gaishe dasu umma...murna sosai baba yayi daya gansu cikin kwanciyar hankali.

Haka ma jummai taje gidan aysha ta yini mata,domin yanzo tabar laulayi tana cin abinci sosai har cikin ya fara tasawa...nantake fada mata ai anty khadija ta k'ara haihuwar baby boy har anyi suna,raji ya hanata zuwa kaduna..sai yamma ta dawo gida

Result na national exams nasu aysha ya fito,kuma tayi passing,yanzu ta zama parmanent worke'r a general hospital minna.

Amina an rubuta jamb,kuma an samu score mai yau.. mami tace daddy'n ki yace ki shirya nxt month zaki wuce schl lagos(university na lagos)...amma mami ba hostel zan zauna ba ko?...eh tunda wan baban ki can yake sai ki zauna wurin su ma,haka daddy'n ku yace... Godia nike mami Allah k'ara girma...amin kada ki damu fatan mu ki samu ingantaciyar ilimi.

Rum nata ta shiga..tayi dialing wani number da naga an rubuta my destiny...hello baby love yadai..lafia lau my destiny ya aiki?..gamu nan muna fama..kasan me daddy yace zan na dawo lagos da karatu...wow gaskiya am very happy for both of us,akwai soyaya kenan...tana kashewa ta kira jummai guest what??..ina jinki..dady ya amince naje karatu lagos gidan su masoyina farhan...gaskiya na tayaki murna Allah taimaka.


Yanzu cikin jummai ya shiga wata bakwai''tuni ta fara zuwa awo''mijinta na bata kulawa na musamman suna zaman lafiya iya gwargwado..ta 6angaren hajia kuma tana samun kulawa na mussaman ga shirye shiryen fita da ita india ya kankama...wurin aiki Raji ya koma yayi report sabida tare dashi za'a india.

Ranar ba bara su ta6a mantawa dashi ba a kundin rayuwar su,ranar da aka wayi gari babu hajia rai yayi halin sa..jummai suma tayi,nan da nan raji ya rud'e ya sungumeta sai hospital,cikin gagawa aka amshe ta sai emergency... kasa ta6uka komi yayi,ga gida ana jiranshi ayi jana'iza..aysha ya kira a waya tare da fata mata halin da ake ciki..cikin gagawa ta iso tare da abdul..shawara ta bayar kada a sanar dasu umma ,gudun tashin hankalin su,ita zata zauna da ita,su tafi wurin jana'iza...haka akayi kuwa suka kama hanyar gidan hajia....koda suka isa an shiryata nan raji ya gurfana a gaban gawan hajia domin yin adu'a..amma ko uffan bai iya furtawa ba,idanun shi sun bushe,ya kasa ta6uka komi ba haka aka sallaci gawan hajia aka kaita gidan ta na gaskia.(Allahu akbar ,dama rai ba a bakin komi yake ba,Allah sa mu cika da kyau da imani.amin)


su umma ke amsan gaisuwa a gidan hajia...aysha na hospital tare da jummai,sabida doctor yace a sanadiyar faduwar da tayi saman cikin lokacin da taji rasuwar hajia,dole a bata agaji na gagawa sabida abunda ke cikinta ya bugu..drip aka saka mata,kafin ta farfado ayi scarning a gani....can gidan rasuwa mutane nata tururuwan zuwa gaisuwar rasuwa ciki hadda su mami,nafisa,anty balki,allawiya,amina da sauran mutanen arziki,ga dangi na nesa dana kusa duk sun iso sabida da asuba ta rasu.....daga gidan gaisuwa hospital suke ta zuwa duba jummai amma har lokacin bata farka ba.

Raji na zaune cikin mutane a kofar gida tare da abdul,ga friends nashi duk sun hallara,amma idan ka ganshi bai cewa k'ala yayi zugum...sai ban baki ake masa,lalai kuka rahama ce ga bawa,raji kam ko kukan Allah bai bashi daman yiba,domin baida kamar hajia suk duniya,ta bashi ingantaciyar ilimi,ta rik'e shi kamar ita ta haife shi,kuma ya'shi ce,sai mutuwar nura ya dawo mashi sabo fil.

A hospital yan uwa sun cika d'aki cirko cirko,aysha na fad'a masu anyi scarning ance in har ba a cire abunda ke cikin jummai ba ana daf da rasa baby'n...anty balki tace yanzu kam halin da raji ke ciki idan ya rasa baby'n nan abun zai masa yawa,gara ayi aiki..aysha ta kira abdul ta fada mashi..kama hanun raji yayi ya saka shi front sit yayi locking,jan motar yayi sai harabar hospital..raji dai zugum yayi kamar ta6a6e har suka shiga office na likita...bayani ya k'ara masu,ya nemi da mijinta ya saka hannu doming ayi booking nata for C/S..bayani abdul yayi mashi raji ne miji amma ga matsalar da yake ciki,abdul yasa hannu...dakin suka shiga,raji na ganinta ya rungume ta tare fashe da kuka mai tsuma zuciya..abdul yace kada a rarashe shi gara yayi ko zai ji sauk'i a ranshi..fita sukayi suka basu wuri...haka yayi mai isar'shi..baby ki tashi,hajia ta tafi ta barmu,bani da kowa sai ke,kada ki barni baby,ki taimaka min..haka yayi ta sambatu har ya gaji dan kanshi,yace su aysha suje gida shi zai kwana da ita''babu yadda basu yi dashi ba akan ya koma wurin amsan gaisuwa'''yace a'a..haka suka wuce.

sai cikin dare ta farka,dama doctor yace kada a bata abinci ''ceiling take kallo,hawaye ya zuba a idanunta,rarashinta ya shiga yi da ban baki,tayi shiru amma bata ce komi ba,haka suka kwana rungume da juna.

da safe aysha tayi abinci kula biyu, sai da suka biya gidan jummai suka dauki duk abunda za a bukata a hospital.... kula guda gidan rasuwa ta aje,cikin hanzari suka biya gida ta gaya ma baba halin da jummai ke ciki..yace ta fada ma umman su Allah ba jummai lafiya shi zai wuce wurin amsan gaisuwa...tare da umma suka wuce hospital

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login