Showing 9001 words to 12000 words out of 64084 words
Chapter 4 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt
wanan ai cin amana ne.
Tace idan bakyi ma Allah da manzan sa(saw)sai ki bari.
Ta kuma gaba abinta, tace ai gara da wayan nan tay Kara ka amsa duk cikin plan dina ne.
Da yaje staff rum teachers mamaki suke yadda akay jummai ta samu waya, sukace ya kamata a hukunta ta.
Yace suyi hakuri a bincike ta a hankali, yarinya ce maybe wayar wani brother tane, kuma yasan zata zo bada hakuri ta amsa sai a hukunta ta.
Da break jummai ta tara yara tace ai M.raji saurayin ta ne tunda ta shigo schl din, shima ya bata wayan nan, sanan idan basu yadda ba su tambayi su jemimah.
Haka magana yayi ta rotating cikin schl har yakai kunne shi.
Tabi duk note book da text book NATA ta rubuta
*M.RAJI LOVE MARYAM SALIS*
DA manyan baqi.
Cikin bacin rai ya shigo class din nasu, yace
Maryam
Allawiya
Helen
Jemimah
Margret
Meet me in the staff rum now
Ya juya
Murmushin ketat tai""tace nasan za ayi haka""
Tace masu magret kada Ku mancee yadda nace maku, kema Alawiyyah.
Duk jikin su yayi sanyi, tace "common guys u have to be strong ""
Ku tayani fighting battle din nan,i want everything to be over today.
Sukace it OK
Suna shiga staff rum teachers sukay masu caa
Wani mal.Ahmad yace, kubi a hankali, duka ko punishment ba zai yi solving issue nan ba kunga duk yara ne.
Ke Maryam tsakanin ki da Allah zakyi fada, kinsan mutuwa zakyi,ke guda za asa cikin kabarin ki, daga ke sai halin ki, ki fada gaskian lamari.
Ya kalli su Alawiyyah kuma haka.
Yace Maryam
Waya bakyi waya?
Shin meke tsakanin ki da Mallam Muhammad Raji?
Ta CE
Mallam during weekend yazo ya kawo min waya, nace ban amsa, yaba allawiya ta kawo cikin gida wai idan ban amsa ba zai yi punishing dina a schl, shine na amsa.
Mutuwar tsaya m.raji yayi.
Mal.Ahmad yace fadi tsakanin ki da Allah allawiya haka ne.
Tace tabbas anyi haka mal.,hada cewa yayi sirri ne kada a bari kowa ya sani.
Yace haka ne mal.raji.
Ya rasa abin cewa dan imani ya cika shi.
Tace tun ranar dana fara zuwa makaranar nan ya matsa min yana sonna, ai su Margret ne shaida.
Ta fidda book dinta da sauran text buk tace kaga .a abunda yake rubutamin duk ya amshi buk dina""M.raji love Maryam salis"".
Mallamai nata passing suna gani, abun mamaki kuma handwriting nashi ne.
Aka tambayi su Helen, suka bada tabbacin jummai keda gaskia.
Akace ko yana da abin cewa?
Yayi shiru, dan yace Allah dai zai fidda shi, dan cikin gallery akwai pics nashi ga kuma number shi ciki.
Aka cema su jummai kuwa, tazo da babanta gobe akwai meeting da teachers.
Jummai suka fita,tace masu kada wadda tazo da ubanta gobe zata wanke su ko da magana ya tashi.
Suka amsa, sudai sun tausaya mashi dan yanzu tsoro jummai ke basu.
Tace nasan kan ku ya kille da lamari na,sai an gama case din zan warware maku komi.
M.raji kam fargaba yake dan yasan bai da mafita, either ace ya aje aiki Ko ayi masa transfer, daman hukuncin kenan.
Aysha CE tajawo junmai tace wane iron rashin imani kenan da rashin tsoron Allah, wanan qazafi har ina?
Tur da mugun hali irin nakyi, dan wanan ya wuce QURUCIYA,sai rashin imani da mugun zuciya ace mutum ya hukunta ka akan laifin da ka aikata ba daidai ba kace sai ka rama, mallamin ka for that matter? Allah ganar dake gaskia,amma bazan bari kiyi succeeding ba.
Jummai tace dallah mallama dakata, bata fin karfina kikay ba,kuma ba tsoron ki nike jiba,anyi mashi sharrin ahi waye, nida ya Kama ya dirka kamar jakar gidan ubansa ba haihuwata akayi ba,cikin bainar jama'a ya kunyata ni,ya cimin mutunci hadda fadin dan ubana sai na bar makaranta,shi tunda ba ubansa keda makarantar ba ai yanzu dole ya bar ta.
Kazafi kuma walahi wayan nan ta ceceshi,nai mashi mai sauki dan va abunda na yi niyyar laka mashi kenan ba,sai gashi ya amshi waya abun yazo min a sawake.
Walahi idan bakyi cire bakin ki cikin maganan ba,zan manta mun hada jini dake MU samu matsala. Dan kunne yaji jiki ya tsira.
Shi kuma NURA sai ya fadamin hadin shi da M.Rajiiiiiiiiii
*LยฃยฃMA*๐โ๐ป
[17/01, 02:14] โช+234 812 140 7930โฌ: ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
๐ท๐ท๐ท๐ท๐ท๐ท
*QURUCIYAR JUMMAI*
๐ท๐ท๐ท๐ท๐ท๐ท
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LยฃยฃMA*๐
*@AMยฃยฃNCI WRITER'S ASSOCIATION*๐โ๐ป
*domin samun kayatatun littafan mu a shafukan fcbk tuntube:-AMยฃยฃNCI WRITERS NOVEL'S GROUP*
*GODIA GARE KU MARA ADADI MASOYA LITTAFIN QURUCIYAR JUMMAI WA YAN DA NA SANI,DA WA YAN DA BAN SANI BA.ALLAH BAR KAUNA DA AMINCI*
*21-22*
Da suka dawo gida ,Aysha taso fada masu umma abinda jummai ta aikata, sai tayi tunanen ai tunda ance su zo da iyayen su idan baba ya je zai ji.
Jummai gidan hajia taje,hajia tace ya makaranta.
Tace lfy lau.
Tace hajia ina nura?
Tace ya tafi kauye kuta rasuwa akai mana, sai gobe zai dawo.
Tace ba matsala,zani gida.
Tace gashi yau ban dafa komi ba.
Tace nagode hajia.
Ki gaida su umman ki.
Tau tace ta wuce.
Da yamma sun je islamiyya,taje biya karatu wurin mallama hadiza.
Tace Mara kunya, kin min tsaye saman kai,, bara ki duqa yadda sauran yan uwan ki sukai ba.
Tace kai na ke ciwo, bari har biyawa yakai kaina zan duka.
Tace tatatar Mara kunya ai sai in ba keba, sai kin bada amsa,idan bakyi dukawa ki tafi bazan biya ba.
Jummai ta juya shike nan ai.
Finciko hijabin ta mallama hadiza tayi, tace dawo nan bara mutunci, maimaita abinda kika fadi.
Tace ban fadi tunda ba zagin ki nay ba.
Tace Iliya miqo min bulalar nan.
Jummai tace duk kika bugeni zan rama, na fada makyi banda lfy, sanan ba zagin ki nayi ba.
Caula mata bulalar tayi.
Ta rike da Sauri,kada ki sake.
Ta hizge zata sake bugunta, jummai ta ware ta wanke mata fuska da mari mai lafia.
Ta dafe kuncyi LA LA laaa kika mare ni,
Anas, kabiru, Iliya Ku kamo min ita..
Haba kafa mai naci ban baka ba sai gidan Hajia da yake yafi kusa da Islamiyyar.
Ganin mutum Hajia tayi cikin daki sai haqi take yi.
Tace lafia,waya biyo ki.
Taba hajia lbr.
Hajia tace haba jummai, kina girma kina kara shiriricewa,mallamar kice fa, duk abunda tai maki bai kamata ki rama ba,ke kenan babu mai makyi shaidar kwarai?
A haka kike son nura ya aure ki,yanzu fa ko mutuwa kikai ba mai makyi shaidar kwarai.
Tace haba hajia, kenan ko kai keda gaskia sai a tauye ka.
Tace ta ya zaa bakyi gaskia bayan ba ai makyi shaidar kwarai ba.
Idan kina so MU shirya, kuma kina son auren NURA ki koma ki bada hakuri.
Tace walahi bazan bada hakuri ba, kuma nabar islamiyyar nan har abada, NURA kuma ai dama ba sonshi nike yi ba.
Sai Anjima.
Ta wuce fuuuuuu.
Hajia tace Allah shirye ki, dama ai kallan nuran nakye, ina zai kai Mara kunya irin wanan yarinya.
Washe gari, da wuce taje makaranta, tace masu marget ko an tambayi iyayensu suce basu gari duk sunyi tafia,alawiyya tace riqonta ake ba iyayenta bane, ita kuma zata ce babanta yace bai zuwa.
Haka kuwa akai, bayan dogon bincike a cikin wayan da kuma shaidun karya irin su alawiyya, da kuma yadda M.raji yayi shiru, shi bai karyata zancen ba, kuma bai gasgata ba""dan a ganinsa ko teachers yan uwansa sun isa bada shaidan kwarai a kansa,amma suka rufe idanu, suka gasgata zancen yara kamar su jummai.
Management ta rubuta letter aka aika ministry duk abunda ta yanke dai dai ne, sanan an dakatar dashi tukum till fortheer notice.
Principal, mallamai da dalibai sunyi bakin cikin rashin mallami mai kwazo da hazaka kamar M.Raji
Hatta su Margret sai da suka tausaya mashi, tare dayin dana sani.
Ita kam uwar gayya ko a jikinta.
Ranar MSS hadda waazi akai akan M.raji wai yana Neman bata tarbiyar dalibai...
Aysha tayi takaicin hada jini da jummai, yanzu ace kamar jummai Yar shekara goma sha biu tasan ta hada makirci,tuggu da qazafi har a dakatar da mutum a kan aikin sa.
Da umma taji lbr ranta ya baci matuka haka baba, amma ba yadda suka Iya da jummai sai adu'a.
*PLS KUYI HAKURI DA WANAN BAN JIN DADIN JIKI NA NE*
[22/01, 00:56] โช+234 812 140 7930โฌ: ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
๐ท๐ท๐ท๐ท๐ท๐ท
*QURUCIYAR JUMMAI*
๐ท๐ท๐ท๐ท๐ท๐ท
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LยฃยฃMA*๐
*@AMยฃยฃNCI WRITER'S ASSOCIATION*๐ค
*domin samun qayatattun littafan mu a shafukan fcbk a tuntube mu @AMยฃยฃNCI WRITER'S NOVEL GROUP*๐โ๐ป
*23-24*
Ranar friday a assembly principal ta sanar dasu anyi M.raji transfer, sanan tayi Kira ga masu hali irin nasa su gyara..
Aka watse assembly kowa na alhinin rashin jarumi,gwarzon mallami irin Muhammad raji.
Haka sukaci gaba da karatu cikin fahimta da natsuwa.
Jummai bata da aiki yanzu sai karatun littafan Hausa na soyaya, kawayen allawiya ke dauko mata da yake tana da saurin karatu tana iya kare 1 & 2 kafin a tashi schl,taje da saura gida tana kai har 2::00am na dare tana karatun novel, amma duk da haka bai hanata mai da hankali kan karatun taba, duk test da assignment da ake basu yana kokari sosai, yanzu shirye shiryen exams suke saboda azumi ya gabato.
Aysha ma baa barta a baya ba,dumin tana da hazaka itama,yanzu shirin Junior leaving suke yi.
A islamiyyah kuwa ta dade da sauke al-Qur'ani mai girma, yanzu karatun littafan addini take yi sai hadda da ta maida hankali akai sosai, yanzu bata fita gashin masara sabida shirye shiryen azumi.
Jummai ne zaune da allawiya bisan beanchi a kofar gidan su.
Tace allawiya mai zai hana MU shiga sabon makarantar islamiyyar nan na bayan layin mu.
Tace ai guda biu ne sabbi wane cikin?
Tace ke ""nurul Islam""din
Allawiya tace lalai jummai an fara hankali.
Tace ke cikin littafin nan da na karanta naga mijin yafi son amaryan sabida tana da ilimin addini kuma ga ibada.
Ita uwar gidan kullum office, ko karatun sallah bata iya ba.
Allawiya tace haka ne kinsan mutane vasu gane ba,gani suke littafan hausa bata tarbiya yake, kuma ai ba duka aka taru aka zama daya ba.
Wake daya ke bata iri, sai kaga mace ta zauna ta rubuta zallar batsa a littafi mutane ayita wawason karantawa, wasu yaran hadda cewa suke idan ba littafin wan ce ba, bana karatun na wan ce domin babu show a ciki.
Shi yasa mallamai kan ce rubutun da karatun littafan Hausa duk haramun ne.
Sabida masu rubuta batsan,sun bata tarbiyar yara da dama,dan yanzu har yar primary zaka ga tana karatun littafai, TAMA fi wata babban mace zaqe wa.
Masu rubutu akan kyawawan yan mata da samari,manyan masu kudi,yadda ake mugun tarairayar mace a gidan mijinta,many an motoci, yadda samari ke kashe ma mata million yin kudi da dai sauran su.
Sun bata tarbiyar yan mata da dama, sun kashe ma mata aure da dama.
Sai kaga budurwa tace, ita tafi son saurayi kyakyawa,mai mugun kudi, manyan motoci,babban gida sanan uban shi wani ne a gwamnati,Wanda kuwa cikin maza dari hardly ne ki samu Biyar masu irin abubuwan nan da kike so, daga nan ayita zaman jira har ki tsufe a gidan Ku, wasu kuma su shiga karuwanci dan su samu irin abinda wance keda acikin littafi.
Yanzu an var aduba Qualities da addini ya tanadar mana wurin Neman aure irin
Addini
Assali
Ilimi
Tarbiyar da makamantar su
Wurin mace kuma
.
Addini
Asalli
Illimi
Kyau
Dukiyaa da makamantar su
Sai jiran tsamani, ina kira ga yan mata da samari da MU kyara, MU mika lamuran MU ga ubangiji, sai yayi mana zavi mafi alkhairy.
Masu rubutan da basu fayace batsa ciki sai kuga baa damu da littafan su ba.amma inda za a natsu a karanta sai kuga an amfana da abubuwa da dama.
Wani mistake guda kuma da writers ke yawan yi
Sai kaga littafin Hausa ne fa, amma sai turanci yafi hausar yawa a ciki.
Bamu bin ka'idodin rubutu,idan Hausa zaki rubuta, ya zamana zallar hausar ce.
Idan turanci zaki rubuta, ki rubuta zallar turancin ki.
Domin wasu karatun hausan kawai suka iya, basu Iya na turanci ba.
Wash sun iya karatun turancin amma basu San ma'anar sa ba,wani lokaci marubuciya sai tayi amfani da manyan kalmomi ko jimloli na turanci.
*DON ALLAH MU GYARA*
*ina kira ga writer's din MU da MU gyara,MU rinka rubutu akan abinda ke tafia da addinin MU,al'adun mu zamani,lokaci da kuma abinda ke yiwuwa*
Sun rubuta exams din cikin nasara, bayan sun gama ne aka basu Hutu sai bayan sallah da sati guda zasuyi resuming, kowa ya tafi gida cike da kewar juna.
Form suka amso, bayan sun ciki suka mayar.
An fara azumi cikin kwanciyar hankali, su jummai kuma sun fara zuwa islamiyya
Bayan sallar asuba;- hadda sai 7 am ake tashi.
10am aje islamiyya,zuwa 2pm bayan sunyi sallah a can, a fara tafsirin al-Qur'ani mai girma zuwa 4pm ake tashi, sai hadda na dare 8:0pm to 10:0pm.
Yanzu ta fara natsuwa tana gaida mutane,sabanin da,tana kama ma ummma aikin gida, idan kaga tayi fada janta akayi.
Wani mai kudi a unguwar su""alhaji na wudil""yayi sabuwar amarya nafisa.
Buzuwa ce bata iya komi ba, ko sanwa, dama jininta ya hadu da Aysha.
Aysha takan shiga ta koya mata abinci, gyaran gida, tana mata lalle da kiso,musamman ma da azumin nan da mijin kanyi shefanai mai yawa iri iri, gidan aysah kan yini ta na koya mata abubuwa tare da kama mata aiki.
Tunda umma ba wani abin azo a gani suke dafawa ba, iyaka kunu ne sai tuwo sai kwadon ganye.
Ranar da baba yasamu kasuwa kamar Friday,sai ayi ruwan tea ba bread, shinkafa,ko faten doya kona dankalin Hausa.
Nafisa na matukar tausaya masu, sabida haka duk abinda sukayi na bude baki tana dibar masu,taba Aysha hadda kwancen kayanta, dan kayan kwaliya,sabulai da sauran su..
Haka Allawiya idan sunyi abun marmari takan dibar wa jummai.
Hajia ta zayane ma nura duk rashin mutunci da rashin kunyar da jummai tai mata.
Ta umurce shi da ya fita hanyar jummai, dan ba maccen aure bace, duk da tasan yana matukar son jummai,bata hanashi gaisuwar mutunci da jummai da yan gidan su ba,amma maganar soyaya babu shi.
Yace insha Allah Hajia za nayi yadda kikace...
Yayai mayawa mayawa gidan su jummai, sai ace tana islamiyyah,Aysha kuma na gidan alhaji na wudil, haka ya hakura dan ko ya kira wayan daya ba jummai switch off,yana son jin inda takai wayan.
Sai da azumi ya kwana goma, jummai ta kwashi yara suje tashe gidan Hajia.
Sallama sukayi,suka fara wakar
Ke ina zaaki da kaya
Jummai da aka azama kunshin kaya tace.
Kishiya tak koro ni, ko gado ban dauko ba.
Da yake babu wutar NEPA, Hajia bata gane su ba, tace NURA ya dauki sauran kosai,da soyayyen dankalin Hausa,ga naira hamsin ya hada ya basu.
Yana mika masu, ya jaye jummai gefe, yace minti biyar.
Tace kada fa Ku canye kayan nan.
Yace nayi ta zuwa gida ban samun ki,ina wayar nan?
Tace kace wayarka ka biyo, dama ka bani ne dan kamin gori?
Yace bashi na tambaye ki ba.
Tace waya an amshe a makaranta.
Yace what! Dan me zaki schl da waya?
Tace abokai na naje nuna mawa.
Yace ki fadamin sunan mallamin daya amshe dan sai ya bani wayata
Kin San nawa wayar nan take kuwa?
Ko police ina Iya kai masu akan wayar nan,duk wani hoto da lamba mai muhimmanci na cikin wayar nan.
Ta hasala sai me,je ka kira police din mana,ka wani cika Mani kunne akan wata akwalar wayar ka.
Gashi nan cikin littafin Hausa hadda motor saurayi ke saya ma buduwarshi,kayan azumi ne, su kayan sallah da kudin kashewa.
Amma kai wata tsiyar ka taba tsinana min?
Yace ohh ta nan kika bullu kuma, waya sani ko sayar da wayar kikayi
Tace na sayar, nima a sayar dani,talakar banza.
Tace kuzo MU wuce dallah.
Yace ba shaka,daman dan talaka bai Iya samun wuri ba, kamar Shi jummai zata kira da dan talaka, bata dubi kanta ba, zai yi maganinta,ba dan ya dauko police abin ya shafe jummai dole a hada da ita,babu yadda ya iya,dole sai yayi hakuri da halin jummai..
Tana sauri zata Haddar dare, wani mutum yayi ta biyanta yana mallama sallamu alaikum.
Waalaiku musallam,lafia Mallam?
Yace ki bani dama na dade ina sonki, sunana alhaji KABIRU mai shadda, mata na uku.
Walahi duk abinda kika so ina zaka yi miki shiyya,ga babban gida gare ni, akwai motar hawa ta alfarma, umra,hajji dut dake za ana keji Yar diya.
Cikin zuciyarta tace, ga irin mijin novel, amma babu Khan fuska, babu tsari,gashi wani gaba,gara ga tsufa da dukan alamu ma jahili ne.
Tace alhaji KABIRU mai shadda yanzu hadda ZANi,kuma nayi latti,ka bani lokaci inyi shawara.
Yace konni Yar diya kamata aka shawara,walla hi diyata kada kiyi wa kanki tuwon tulo.
Ta kece da daria, lallai jummai zata wanki garra.
Tace sai kazo gida,ta wuce abinta.
Ya cije labba, Allah shi kai damu ga harawa.
Alhaji kabiru mai shadda ya aika da gero,sugar,madara da Milo aba Baban su jummai.
Ya sake aiko shadda na baba,atanfa umma sai leshi na jummai.
Umma tace shin Baban su kodai akwai abinda mutumin nan ke nema ne wurin mu?
Yace Saratu kenan, ya iskeni har rumfata ya min maganan jummai, nace yaje ya nemi yardanta idan ta amince Allah sanya wa abin albarka.
Umma tace ai itace dai dai dashi, badai jummai ba gajiya zai ya barta.
Yace haba Saratu kada kiyiwa diyarki baki mana.
Tace tau Allah zaba masu abinda yafi zama alkhairi.
Yace yauwa amin.
Da matsanaiciyar ciwo Mara jummai ta tashi,kamar zata mutu,Baba ya ce akaita clinic mana.
Koda akaje doctor ya dubata yace mensuration ta fara.
Antibiotics da pain relief ya bata, sai shawarwari yada zata kula da kanta lokacin period da bayan period.
Suka dawo gida, sati guda tayi ta gama.
Sallah saura kwana biu, alhaji KABIRU mai shadda ya kawo ma baba karamin buhun shinkafa da dubu biu na cefanai.
Ranar sallah bayan sun dawo masallaci da baba,umma ta zuba masu shinkafa da stew sai hadin salad da Aysha ta dawo masu dashi daga gidan nafisa.
Kwaliya jummai tai cikin leshin da alhaji KABIRU ya kawo, tayi kyau sosai.
Tace umma zani yawon sallah.
tace a daw lafia.
Ita da Alawiyyah,sai da suka zaga manyan gidajen layinsu.
Sai gidan hajia da fara'a ta tare su, ta zuba masu abinci da zobo.
Tace kunga nura kuwa?
Sukace aa.
Tace su duba dakin shi.
Dari biu ta basu, suka yi godia.
Da sallama suka siga dakin, shida BELLO ne.
Yace hajia jummai ya sallah.
Tace lafia lau mal.BELLO.
Nura yace tunda ni bata gaishe niba, ya mutanen gida.
Lafia ta amsa a takaice.
Fanta ya saya masu kwalba biu,ya kunna TV suna kallan legend of the seeker.
Haba ruwan sama aka fara kamar da bakin kwarya.
Yace Ku dakata har ruwan ya tsagaita.
Can sukaji ana bugun kofa.
Nura yatashi,yana budewa yace ah mutun sai yau, kwana da yawa.
Yace kai ban hanya ko sai ruwan ya kare a kai na?
Hanya ya bashi.
Yana shiga,yace ah Mallam bello kai ne?
Yace M.Raji manya Ashe ana ganin Ku?
Sai da gaban su jummai ya gadi.
Yace yan mata sannun Ku,suna hada idanu yace what! Maryam salis,allawiya๐๐ป
*LยฃยฃMA*๐โ๐ป
[21/01, 21:35] โช+234 812 140 7930โฌ: ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
๐ท๐ท๐ท๐ท๐ท๐ท
*QURUCIYAR JUMMAI*
๐ท๐ท๐ท๐ท๐ท๐ท
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LยฃยฃMA*๐
*@AMยฃยฃNCI WRITER'S ASSOCIATION*๐โ๐ป
*domin samun kayatatun littafan mu a shafukan fcbk Ku tuntube mu a:-AMยฃยฃNCI WRITERS NOVEL GROUP*๐ค
*25-26*
Ba jummai ba,ba Alawiyyah ba duk sai da hanjin cikin su ya kada.
Tattako wa yake zuwa inda jummai take tsaye,tana ja da baya, yana