Showing 30001 words to 33000 words out of 64084 words

Chapter 11 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt

ya yanke shawarar ya fada ma hajia gaskia jummai ce matar da ya zaba a
matsayin abokiyar rayuwar shi........












*LEEMA*✍🏻

*BRILLIANT WRITERS ASSO*....πŸ–Š



🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*QURUCIYAR JUMMAI*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍🏻

*Dedicated to*;-
*Rukkaya Hassan othman*

*Gaisuwar ban girma gare ku brilliant writers asso.Allah kara basira da daukaka amin*


*Godia mara adadi gare ku masoya buk din "Quruciyar jummai"ina ganin sakwanin ku na fatan alheri da gaisuwa Allah bar mu tare ya bar zumunci*




*53-54*



Nifa kai nake sauraro ka tasani a gaba kayi shiru idan baka da abin cewa zan shiga daga ciki dare ya raba""cewar hajia""


Yace amh,ahm ahm,dama akan maganar yarinyar da zan aura ne.

Eyhim ina jinka dan albarka yar ina ce?

Shiru ya biyo baya na nan mintuna,can ya runtse idanu tare da karfin halin furta ""JUMMAI""ce hajia.

Ta ran gwuda ayururiiiiiii!
Alhamdulilah masha Allahu dama nai maka sha'awarta yarinya mai natsuwa da sanin ya kamata,tunda nura ya rasu take matukar bani tausayi nake adu'ar Allah bata miji da zai rike'ta da gaskiya,ashe Allah ya amshi adu'ata..

Tace ina fatan kun fahimci juna da ita?

Ya tsinci kansa da cewa eh hajia.
Tace Allah maka albarka gobe zani kuta wurin alhaji babba duk yadda mu kai zaka ji.

Yace tau sai da safe.

Tace Allah bamu alheri.

Yana shiga daki ya fada saman matrass nashi tare da ce wa oh ni muhammadu what have i gotten myself into,yarinyar da na tsana the most wai yanzu baki na ke furta ita zan aura,ita zata zama abokiyar rayuwata.

Wait shin ko tana sona har yanzu oho,ko ta samu wani saurayin?

Allah kama mini,haka ya kwanta da tunane tunane iri iri.


Da safe hajia tai kauyen kuta wurin yan uwansu domin maganar auren Raji.

Sosai sukai maraba da maganar tare da alkawarin zuwa friday zasu shigo nema mashi aurenta.

Cike da farin ciki hajia ta dawo gida.

Da dare take fada ma raji yadda tai da yan uwansu akan ya fada ma baba ranar friday za su zo neman auren jummai.

Tace insha Allah hajia zan fada mashi.

Safe kasuwa ya iske baba ya fada mashi.

Sosai baba yayi farin ciki.
Haka sukai sallama baba nata mamaki dai dai da rana daya bai taba sanin soyaya ke tsakanin jummai da raji ba,amma da ya tuna da irin hidimar da yayi tayi ma jummai kafin ta samu makaranta sai yaga ba abin mamaki bane.

Fatan alheri ya bisu dashi domin duk wanda ya samu raji a matsayin suruku tabas yayi babban dace.

Da ya dawo ne yake fadama umma yadda sukai da raji,tare da tambayan ta dama tasan da soyayar dake tsakanin raji da jummai ne?

Tai saurin amsawa eh

Yace maddala.

Haka umma ta yita tunanen yaushe har jummai suka dai dai ta da raji bata sani har yakai ga maganar aure.

Tace shin aysha dama raji sun dai daita da jummai ne?

Tace gaskia umma banda wanan labari.

Umma tace kinji kinji abinda raji ya fada ma babanku.

Tace amma abun da mamaki gaskia ace jummai sun fahinci juna amma bata fada ma kowa ba tabbas akwai wata a ka'sa,amma jummai sai tafi kowa farin ciki idan taji wanan labari.

Umma tace Allah dawo da ita lafia.
Amin aysha ta amsa.


A kaduna kuwa jummai an zama yar gayu,an ka'ra waye wa,yanzu shirye shiryen dawowa gida suke yi sabida tun last week hutu ya ka're.


Ranar friday baba ya gayaci abokan arziki su taya shi tar ban wakilan raji.

Tabarma babba aka shimfida a zauren gidan zuwa 10:30am suka iso su hudu cikin 406.

Tarba na musamman suka samu wurin su baba.
Bayan sun gabatar da bukatan su,baba ya amince.
Dubu goma suka bayar na gaisuwa da kwandon goro,chew gum da kwalin sweet.

Suka nuna bukatan su na son ayi auren cikin shekarar nan.

Baba ya nuna masu ai ss2 take ko yar'ta bata yi aure ba bare ita,suyi hakuri har wani shekara ta kare secondary schl.

Suka ce a basu lokaci su yi shawara da raji idan zai iya jira.

Ana taro ya watse cikin mutunci da girmamawa.


Da baba ya shigo gida ya fada ma umma yadda sukai.

Tace gaskia yadda suka ci buri akan sai jummai ta samu wadatacen ilimi kafin su aurar da ita.

Baba yace haka ne kana naka Allah na nashi duk da haka suna iya ba raji auren jummai domin sun san zai tsaya mata tayi ko wane irin karatu take so ko bayan sun yi aure.


umma tace haka ne baban su.

Da aysha ta dawo hospital(da yake yanzu attachment su ke yi)
Umma ta fada mata yadda aka yi.

Tace tau umma duk abinda kuka yanke dai dai ne.



Yanzu allawiya cikinta ya shiga wata na bakwai alhaji saddat ya dawo da ita gida kan sai ya neme ta ya gaji da ganinta da cikin shege a gidan shi,taji kukan bakin ciki sosai ranar mussaman yadda iyayenta suka nuna halin ko in kula a kanta kota kanta basa bi.


*A KADUNA*bayan driver ya gama loda kayan su a booth din mota suka ma anty da uncle bash sallama,izzidine sai kuka yake yu.

Uncle bash yace matafia Allah tsare ya kiyaye hanya sai kun zo aure na ko?

Jummai tace insha Allah.
Amina tace ai sai mun rigaka aure.

Yayi daria.
Anty tace jummai ki gaida gida na gode sosai da ziyara Allah bar zumunci,amina sai munyi waya.
Haka driver ya ja mota kamar su zub da hawaye.

Sai after 2pm suka isa minna,gidan mami suka sauka.

Sai da suka ci abinci sallah sanan mami tasa driver yakai jummai gidda tare da tsaraba niki niki.

Umma tayi farin cikin ganin yar nata cikin kwanciyar hankali haka aysha.

labari ta basu yadda kaduna ya ke irin zaman da sukai gidan anty da wuraren da suka je yawo.


Cikin tsarabar data dawo dashi akwai cabbage,arish potatoe,carrot,apple sai chocolate da sweet kala kala.

Umma ta cike na gidan su allawiya da sauran makwabtansu.

Aysha tace umma an cire na hajia kuwa?

Tace haka gara da kika tuna min bara a cire gobe sai jummai ta kai mata.

Umma tace shiga ma ki gaida Allawiya sabida tayi rashin lafia har ta kwanta asibiti wai hawan jini ke gare ta kuma ga tsohon ciki.

Tace subhanallah ashha abu bai yi kyau ba.

Haka ta kwashi tsaraban gidan su allawiya ta shiga.

Sallama tai mama tace ah mutanen kaduna an dawo lfy?

Tace lafia lau mama ashe allawiya bata ji dadi
ba?

Tace ai taji dama cikin halin ko in kula,shiga daga ciki mana tana daki.

Allawiya makure karshen gado duk tayi zufa

Jummai tace ashha allawiya sannu ashe abu yakai haka?

Ta kwashe komi ta fada ma jummai.

Jummai tace ai yanzu kan sai dai muci gaba da adu'a lamarin alhaji saddat ya girmama.

Tace kin san Allah tunda ya dawo dani gidan nan kusan sati biu kenan har yau ko leke bai zo ba.

Tayi ta kwantar mata da hankali tare da bata shawar wari.
Aysha ta shigo jummai baba na kiran ki,tace tau muje.
Sai da safe tama allawiya da mama.

Baba na zaune saman tabar ma a kofar dakin su shida umma.

Yayi gyaran murya;

Dama kina soyaya ne da raji?

Haka taji maganar banbarakwai,ta kalli unna da mamaki.

Umma tai mata allama data ce eh.

Tace eh baba

Yace masha Allahu iyayenshi sun zo neman auren ki kuma na basu yanzu su muke jira aji abinda suka yanke game da lokacin aure.

Cikin matsanai ciyar farin ciki tace tau baba.

Yace Allah maku albarka.
Suka amsa amin baba,jan aysha tayi daki,tace sister yaushe raji ya dawo har ya fara sona tare da gabatar da iyayenshi?

Aysha tace lover girl wayan nan tambayoyi duk ni daya.
Nan ta kwashe komi ta fada ma jummai.

Jummai tai kabbara tace tabbas ayar da amina ta bani yayi tasiri akan uncle,but sister amma me yasa bai kirani yaji daga gareni ba?

Tace and so what badai shiya kawo kansa ba,ai yayi mai wuyar sauran duk mai sauki ne.
Tafawa sukai,tace bara na shafa ma amina labari tana kokarin latsa wayar ta ringing guda amina ta dauka.

Jummai tace guest what raji ya turo magaba tan sa neman aure na.

Tayi wani ihu na farin ciki sai da jummai ta rufe kunuwanta.

Tace ai na fada maki ayar Allah ba wasa ba kadan ma kika gani sai raji ya zama kamar rakumi da akala........





*LEEMA*✍🏻


*BRILLIANT WRITERS ASSO*.....πŸ–Š


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*QURUCIYAR JUMMAI*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸



*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍

*EDITOR*
ASM££NA X££YANπŸ‘„


*Dedicated to*;
*Brilliant writers association*πŸ“šπŸ–Š


*55-56*





Sallamu alaikum,sallamu alaikum,sallamu alaikum.

Wa laiku musallam bismillah,ah raji dama kana jin sallama ka kyale?

Na amsa bata dai ji bane.

Jummai ta shigo gurfana wa tayi ina kwana hajia.

Lafia lau yar albarka ya mutanen gida?

Suna lafia sun ce a gaida ke.

Yaushe kika dawo.
Jiya .

Ina kwana uncle.

Ko Kalonta bai yiba yaci gaba da latse latsen wayar shi.

Hajia tace kana jifa ana gaisuwa.
Yace na amsa ai.

Tace oh yau kuma ba'kin halin naka ya tashi ko dan ka kai kudin aure ka fara wani tsare gida?

Shima bai amsa ba yaci gaba da aikin gaban sa yana yi yana satar kallon jummai tare da mamakin yadda ta ka'ra kyau da girma duk wani halita na jikinta ya kara fitowa da kyau,cikin zuciyar shi yace tsarki ya tabbata ga wanda ya hallici wanan kyakyawar sura.


Tace ga tsaraba nan umma tace a kawo maki.
Hajia tace madallah mun gode sosai''arish potatoe ne sai cabbage.


Haka ta kari zamanta suna dan taba hira da hajia,tace zan koma gida hajia.

Tace tun yanzu ?

Tace eh mun koma makaranta akwai shirye shiryen da zanyi ne.

tace kai tashi ka maidata gida rana yayi zafi.

Mike wa yayi ba tare da yace komi ba yayi hanyar waje.

Mike wa tayi jiki ba kwari ta fita,tsaye ta same shi jikin bike din.


Gajia tai da tsayuwar shiru ta kama hanya zata wuce yace keeee zo nan.

ta tsaya ba tare data kalleshi ba.
Dari biyar ya jiro ya jefa mata,ya hau bike nashi tare da watsa mata ku'ra.


Hawaye ne ya cika mata idanu kota kan kudin bata bi ba ta kama hanyar gida.

Cikin zuciyar ta ce na shiga uku wane irin mutum ne uncle da dukan allamu yana sona sabida naga sona cikin kwayar idanunshi,amma meke faruwa ne?

Haka ta isa gida cike da sake sake cikin ranta.


Washe gari a schl take fada ma amina abinda ke faruwa.
Tace best friend kina da aiki sabida na lura raji irin mutanen nan ne masu shegen zurfin ciki,girmai kai,miskilanci,ga riko infact ma yana da i don't care atitude,kinga kuwa kafin ka shawo kan irin wayan nan mutane sai kayi hakuri tare da yan dibaro.

amma definetly yana sonki baya so yayi admitting ne kawai.


Uhmm ai ni best friend na fara tsorata da lamarin uncle fa.


Tace tafi can tunda har ya iya turo iyayenshi gidan ku tabbas ba karamin so yake maki ba.

Tace Allah mana jagora amin.

Ban garen aysha kuwa an kawo kayan na gani ina so(engagement)daga gidansu abdulrahim.

Kwalin biscuit uku,chew gum uku,sweet uku,kwalin bobo uku sai 5k.

Mamansu allawiya be yan tarbar kaya dasu nafisa,5k din sama aka ba su tukuici.
Da kyat suka amsa ciki da girma mawa.


Haka aka raba kaya aka aika mahuta wurin dangi saura aka raba ma makwabta.

Allawiya har yanzu babu wani lavari alhaji saddat yaki waiwayenta ga ciki yayi nauyi yanzu 8month kenan,jummai ke shiga idan ta dawo schl tana debe mata kewa da yake yanzu harkan da'awan su sai jefi jefi suke tafiye tafiye..

Posting letter na raji ya fito daga federal government,inda aka yi posting nashi national lottery trust fund abuja.

zuwa monday zai yi reporting,duk hankalin hajia ya tashi sabida ta tsani wani nata yayi nesa da ita tun rasuwar nura.

Tace gaskia ya kamata akayi magana da iyayen yarinyar nan ayi auren nan kusa idan yaso taci gaba da karatu a gidanka.

Yace tau hajia zan je na same su.

Schl nasu ya fara zuwa ya nemi principal da asa sunan jummai cikin yan ss3 masu waec bana.

Tace ko menene dalilin sa na yin haka?

Ya nuna mata ai jummai nada babban jiki tayi girma a ss2 tunda tana da ko'kari ayi trying.

Tace babu matsala za a duba masu.

Yana fita ya wuce kasuwa wurin baba,bayan sun gaisa.
Yace dama daga makarantar su jummai nake mallaman su suka kirani akan suna neman dama abari jummai tayi jarabawa da yan aji shida sabida la'akari da sukai da hazakar ta.

Baba yave madalla hakan ma yayi kyau.
Ya ka'ra sunne kai,sanan baba inaso ayi daurin aure cikin satin nan idan ta gama zana jarabawar sai ta tare,sabida an maidani aiki abuja kuma hajia duk ta tashi hankalinta.

Baba yace ba matsala zan yi shawara da yan uwan nawa na can mahuta duk yadda suka ce zan neme ka.

Yace na gode baba Allah kara girma.


Da dare bayan sun gama cin abinci yace saratu ina yaran na?

Tace jummai na wurin allawiya,aysha tayi wurin hadda.

Yace kinji kinji yadda mokai da yaron nan raji me kika gani?

Tace mallam maganar gaskia kada mu tsaya bata lokaci a amince da bokatan yaron nan,kasan yan uwanka dai ba kulawa ke gare su ba amma a kira su a waya domin fidda hakin su.

Yace haka ne,shigowan jummai ya dakatar da su daga zantawar da suke yi.

Baba yace zo zauna,ta bidi wuri ta zauna.

Yace dama yaron nan ne raji yake son a daura auren ku cikin satin nan kafin ya tafi abuja wurin aiki me kika gani?

Tace baba amma maganar karatu na kuma fa?

Yace ina ce ai sai da kokayi magana dashi kafin ya same ni.

dole ta amsa eh baba,yace maganar karatu ya fada min daga can makarantar naku sun nemi izini da a barki kiyi jarabawa da yan aji shida,bayan jarabawar sai ki tare.

Cikin matsanan ciyar mamaki ta amsa tau baba duk shawarar da kuka yanki dai dai ne.

Yace saratu karfe nawa yanzu?

Umma ta leka cikin palour 8:30pm mallam.

Yace au ashe dare bai yi ba,auta akwai kudi cikin wayar ki kuwa?

Tace eh baba,yace kira min baban ku na can mahuta yanzu.

Ta binciko number tayi dialing ringing biu ya dauka sallamu alaikum.

Baba ya ce waalaiku musallam yaya bala ya kuka wuni?

Yace lafia lau muke salisu,ya iyalinka da yara duka?

Yace duk suna lafia dama kan maganar auren maryam ne.

Yace kodai aysha?

Yace a'a ita mai nemanta ya amince har ta kamala karatun ta,ita maryam din ce dai yaron ya matsa yana so a daura aure cikin satin nan sabida ya samu aiki abuja idan ta kamala jarabawan gamawa sai ayi buki?

Baba bala yace ai hakan ma yayi kyau yoo menene amfanin bokon diya mace ma,gara su ma sun samu mu nan yaranmu ai suna da shekara goma sha daya muke aurar dasu.

Baba yace ai itama maryamun sha bakwai ke gareta,aysha ce ma mai ashirin

yace subhanallah ka gani ko har shekara ashirin babu aure ai gara a hada su duka a daura ko?

Yace bari dai ayi da wanda ke bukata yanzu menene shawarar ku?

Yace tau kasan mu shawarar mu bata wuce eh,sabida kwandala bamu da na baka ayi jigilar buki haka bamu da na motar zuwa daurin aure ayi lafia Allah sanya alheri amin.dif ya kashe wayar

Umma tace nasan ayi haka sabida basu damu da kai ba bare abinda ka haifa.

Yace babu komi anyi mai wuyar ai.

Wayan nan da baba yayi ne jummai ta samu information akan raji da dalilinsa na son a daura aure cikin satin nan,amma abinda bata gane ba yaushe yan makarantar su suka ce aji mata jumping tayi waec da yan ss3?

bata da amsa dole sai taje schl gobe.

Misalin karfe goma na dare aysha ta dawo daga hadda,tace sis lafia baki zo hadda yau ba?

Tace har na shirya allawiya ta aiko kirana wai bata jin dadin jikinta haka dai na bata shawarwari,sai kuma ga baba da wani sabob magana wai za'a daura aure na da uncle ranar saturday.

Tace what garin yaya?
Nan jummai ta kwashe yafda akayi ta fada mata.


Tace yana iya yuwwu wa shiya je neman alfarman haka a schl naku fa
Tace komi mai yiwu wane sister,gashi bai taba zuwa hira wurina ba bare na fahimci likes and dislikes nashi.

Aysha tace mudai ci gaba da adu'a sister.



Dasu ka hadu da amina a schl ta fada mata abun dake faruwa.
Amina ta rankwada guda cikin class,duk attention na kowa ya dawo kansu.

Tace sa'idawar banza,yanzu duk yadda akayi shi yazo ya nemi alfarma wurin pc yanzu shekenan zaki koma ss3 da zama?

Tace ban sani ba sai naji daga pc

Tace amma wanan aure naku akwai drama miji bai taba wani hiran soyaya da mata ba komi yake so sai dai yabi ta hanun iyaye?walahi inda family namu ne da babu mai bashi aure,dan ya samu surukai masu sanyin hali ne kawai.

Tace ya zaayi ya labarin farhan?
Tace ya koma schl ai india dama holiday suka samu yazo kuna muna waya akai akai.

Jummai tace better.

Amina ta kurawa jummai idanu,tace lafia kike kalona haka?

Tace uhmm ina mamaki ne yanzu nan da 2days kin zama matar aure?

Tace ana mamaki da ikon Allah ne?

Tace a'a sai naji ma kamar nice dan na fiki bukatan aure,tace tab indai da uncle ne walahi baki fini bukata ba.

Haka suka ta hira har teacher ta shigo.

Raji ya dawo wurin baba dan jin hukuncin da suka yanke akan maganar sa,baba ya nuna amincewar shi dari bisa dari,godia sosai raji yayi,daga nan ya tafi kuta "da yake babu nisa da minna" ya fada masu yadda su kayi da baba.

Uncle nashi yace dama na dauki nauyin biya maka sadaki sauran yan uwanka zasu bada goro da minti nawa aka yanke sadakin?

yace ai sun ce duk abinda Allah ya hore.

Yace madallah haka ake so sai mun zo ranar saturday.

Haka yayi sallama dasu.


Duk wanda ya kamata ya san da daurin aure baba ya sanar dasu akan ranar saturday da karfe goma da rabi na safe.

Allawiya ta taya jummai farin ciki sosai domin duk wanda yasan raji yasan mutamin kirki ne,baida abokin fada,ga ilimi da natsuwa.

Da amina ta fada ma anty khadija murna sosai ta taya jummai domin darajar duk wata ya mace gidan mijinta,komin kankanta ko girmanki haka komin talauci ko dukiyar ki.

Dady da mami fada sosai suka ma jummai wai zata bata ma kanta career,tana karama a aurar da ita har kasuwa dady ya sami baba ya bashi shawara abar maganar auran nan har ta kare koda NCE ne.

Baba ya nuna ai yin Allah ne kuma lokacin ta ne yayi don haka duk abinda za ayi bazai hana auran faruwa ba.

Ta bangaren raji ya gayaci abokan sa da abokan aikin sa.
Haka mallaman islamiyyar su jummai da officials na area council maza hada sheik ahmad lemu duk sun sami halartar daurin auren;-

*MUHAMMAD RAJI*
&
*MARYAM SALIS*

Akan sadaki naira dubu hamsin.

Bayan gama daurin aure dama umma sun shiryama maza walima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login