Showing 54001 words to 57000 words out of 64084 words
Chapter 19 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt
zaki sha mamaki(yana sa laushi,tsantsi da shekin fata ke harda wani kamshi na musamman za kiji yana fita a jikin ki)
Sanan gana ganyen magarya da sabulun salo dake su nayi suka hade wuri guda shima na wanka ne.
Wanan hadin lalle da garin ridi ne,ga kuma man zaitun da garin ridi duk shafe jiki za kiyi dasu bayan awa guda ayu wanka da wa'yan can sabbulai.
Don Allah jummai ki kula da amfani dasu kada kisa lalaci da wasa,domin har kullum ina k'ara fada masu sun fi sabulan turawa inganci da gyaran fata.
Duk da nasan suman ki na samun kulawa sosai amma ki guji amfani dana turawa sabida chemicals nasu,ga natural one's nan
hadin mayukan gyaran gashi,gasu nan na hada maki..man zogale,man kwakwa,man zaitun na hade wuri guda ana shafawa ana kitso dasu.
Gana gyaran k'afa....man shanu,man kwakwa,man rid'i da man allayyadi na had'a nan da dare zaki shafa a k'afa in zaki kwanta sai ki daure da leda,da safe ki wanke da ruwan d'umi ki shafa man zaitun da man r'idi.
Gasu nan ki tafi dasu ki juri amfani dasu ko a gidan ki,kina hadawa akai akai....insha Allahu zan kiyaye nan suka ta hira har lokacin sallah suka yi sallah...amina ta kirata akan ta iso...ok kiba umma kayakin ina gidan nafisa.
Amina ta shigo amarya kin sha kamshi..ke besty bana so fa,yasu mami lafiya lau suke suka ci gaba da hira sai karfe biyar na yamma mata uku suka kawo lefe,da dubu talatin sama na kayan lale kasan cewa basu samu daman saya ba...lefe yayi kyau kowa ya gani sai ya yaba,da zasu wuce aka basu kajin su da kayan drinks suna ta godiya...aysha sai santin kaya take yi koda suka k'irga gaba daya da atamfofi,less,shadda da material sun kama arba'in.,ga gudan make up kit babba,kai komi yaji sai san barka.....haka mitane ket shigowa ganin kaya sai santin kaya ake yi,allawiya ma mijinta ya kawo ta can gidan nafisa ta same su....jummai tace ki nga yadda kika zama big madam kuwa? Komi ya k'ara bunk'asa..atau kwanciyar hankali yafi komi dad'i banda matsalar komi yanzu sai d'an abunda ba a rasa ba...haka muke so Allah k'ara rufa asiri amin...sai da kafa ya d'auke suka koma gida sabida mijin nafisa 6pm yake dawo wa daga kasuwa.
Umma tace amina ga kayan ku nan da dubu talatin na kayan lalle....jawo akwatu nan tayi allawiya ta bude suka shiga duba kaya,nafisa sai santin kaya,amina na fadin kudin kaya,duk wanda aka d'aga sai ta fad'i kudin shi,jummai sai murmushi take yi tare da yaba ma mijinta akan namijin k'okarin da yayi wurin hada kayan nan....text mai dad'i ta rangwada mashi,ya kirata naga text na gode da adu'ar ki...kaya sun yi uncle Allah k'ara budi...amin akwai program din da za kiyi ne?dama walima ce kawai ranar yini za myi, sai d'un kuna da zan kai....hakan yayi kyau,kamar nawa kuke da bukata??...ko nawa yayi uncle tace cikin natsuwa...ki turo account number naki na turo maki dubu hamsin yayi ko?...Allah sanya masu albarka..ok ina jiran accnt No_din...ok.
Yana kashe wa ta tura mashi...nan da nan taji alert da yake mobile transfer yayi mata...tayi text na godiya.
Zare jiki umma tayi ta kai ma maman allawiya dubu ashirin cikon kudin dailu dilaliya ....sai dare driver ya zo amina ta wuce gida,alhaji saddat yazo daukan allawiya jummai tayi mata rakiya,bayan sun gaisa ya bata dubu goma gudun mawar shi,sabida yana mugun ganin mutuncin ta yadda ta kula da matar shi har komi ya dai dai ta tsakanin su...godiya tayi mashi suka wuce.
Da dare bayan ta gama shafe shafen ta na gyaran fata ta k'ara bude kayan suna kallo da aysha...umma tace aysha ku kwaso ma baban ku kaya ya gani...bude masa kayan suka yi sosai ya yaba da kayan ..umma tai mashi bayanin dubu talatin na kayan lale,yace ki aje hanunki.
Jummai taba umma 10k da alhaji saddat ya bata.
daga organization nasu ""da'awa commitee" suka had'a ma jummai dubu hamsin amiran su ta kawo mata,gudun nawar su,sosai umma ta k'ara gode ma Allah....da mami ta kai ma dadyn su amina kukan ya taimaka ma jummai basu da,cewa yayi me mami taga za a yi masu wanda zasu yi farin ciki,umma tace gado ko kujeru amma zata tambayi amina me jumman tafi buk'ata....ta samu amina kwance saman bed nata tana charting...sannu mami,yauwa daughter dama maganar jummai ne menene kike ganin sun fi buk'ata a yanzu??
Gaskiya mami gado ko kujeru amma zan tuntube ta naji....ok sai naji daga gare ku zuwa gobe zai bada kudin..mun gode mami.
Waya tayi ma jummai tare da mata bayani tace gaskiya nafi son gado besty sabida ya riga da ya gyara palour...ok gobe ki zo muje kasuwa da mami...ah basai nazo ba besty ki zab'a min colour mai kyau kuma kimin godiya..tau sai da safe.
Su umma ta fada ma baba yace Allahu akbar bani da abin cewa sai fatan Allah ya masu sakaya da gidan aljanah,umma kam kokan dad'i ta fashe dashi.
Da safe daga company da suka sayo gadon gida suka wuto ma jummai dashi,daga nan mami tagga kayan lefe.godiya kam da fatan alheri su mami sun sha shi,umma tace har gida zasu zo godiya ita da baba wurin dady...mami tace haba umman su mun zama d'aya ai haka suka tafi akan sai amina ta zo.
Gaba daya gaba daya suka hada kudin da aka samu,hadda wanda rajinya turo mata dubu d'ari da talatin,da yake anty balki ta dauki nauyin had'a masu walima a kofar gidan su jummai""mami tace lallai tunda balki ta kyauta tawa jummai nasu tazo d'aya""amina tace ai mugun shiri auke yi da jummai.anty khadija ta aiko ma jummai da turaruka na ruwa dana itace...na jiki,na d'aki,dana tsuguno..na ruwa kuma su rum freshner dasu humra...sai tsumin b'aure cike da galan,nonon rak'umi galan guda,tsumin dabinoda zuman mata kafin ta iso...
Bayan jummai ta zab'i kayan da za akai mata dunki
Su aysha da amina suka kai dunku nan material kala uku,less uku,atamfa uku da shadda uku express suke buk'ata da kyar ya amshi dubu ashirin sabida ma telan su amina ne shiya sa ya raga masu...sauran dubu d'ari akayi sayayan kayan kitchen da sauran abubuwan da ba a saya ba...suka dawo da kaya nik'i nik'i,umma tace gaskiya kudin sunyi afki...haka suka yita samun gudun mawa daga ban gare da dama har aka sayi katifa da sauran abubuwan da ba a saya ba...satin buki ya zagayo yan kauye suka fara tururuwan zuwa gidan umma ba masaka tsinke wani muciya,kwarya,kwanun sha,samira,tsintsiya, da sauran tarkace da ake samu moatly a kauye...ga buhun masara da na shinkafa shanshara buhu biyu...su aka kyara ana ci...kayan Gara kuwa gidan su allawiya umma taba maman su allawiya kudi a sayi flour nayin dib'ilan,cincin,alkaki,nakiya da dak'uwa.
Ango ya samu iso wa can gidan shi ya sauka da abokanshi, sabida gidan hajiya ya ciki da mutane...yaso ganinta a ranar amma ina mutane sun yi yawa gidan su jummai kuma umma ta hanata fita wai suyi hakuri haka nan har ta tare......washe gari ma haka yaso ganin matarshi umma na tsare da ita shawara suka yanke da ta saci hanya su hadu gidan shi da dare...sai da ta bare kowa ya kwanta ta susud'a ta fita can k'asan layin su ta hangi motar shi..kwankwa sawa tayi ya bude mata,ta shiga ya ja suka wuce........
*LEEMA*βπ»
*βBRILLIANT WRITER'S ASSO..*π
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
π·π·π·π·π·π·
*QURUCIYAR JUMMAI*
π·π·π·π·π·π·
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*βπ»
*Dedicated to my sweet BEE*π¦
*71-72*
Basu tsaya ko ina ba sai london street,gidan su...fita yayi ya bude gate ya dawo tare da shigar da motar...tace uncle basu aliyu na ciki ba(friends nashi da suka zo daga abuja)..matsoraciya suna wurin yawon su.
Da sallama suka shiga,ya kuna light palour ya dau haske...hugging nata yayi baby kin ga palour'n ki???
Wow amazing uncle ka iya za6e fa,am very impress,Allah bar mu tare...amin baby zaunar da ita yayi saman three seater ya aza kanshi saman cinyar ta....baby kin k'ara kyau da haske ga wani k'amshi na musamman na fita daga jikin ki""da yake kayan bacci ke jikinta ta d'auro zani sama...sai shak'ar kamshin jikin ta yake yi,menene sirrin baby?....far tayi da idanu kwanciyar hankali my darling husband...uhm yayi kyau ni da hankali na ba a kwance yake ba gashi nan duk na rame,nayi bak'i har kin fini haske yanzu...lokaci ne.
Uncle ban san wace kalma zanyi amfani dashi ba wurin nuna godiya ta a gare ka akan hidimomi da kake ta faman yi,Allah k'ara rufa asirri...amin baby idan ban maki ba wa zan mawa?albashina fa na da yawa kusan #200,0000,kinga dole na kyautata maki,fata na ki za'ma kamilar mace,sawwama,k'awwama....insha Allah.
Suna hira yana k'ara shigewa jikinta,tana faman lumshe idanu"abunka da wadda ta tsumu""tana ta shafan suman kanshi a hankali,yana lumshe idanu.
Ya fara romancing nata sosai da sosai,gaskiya koda hakk'in sa zai nema bara ta iya hanashi ba sabida itama a buk'ace take....kasa ta6uka komi tayi sabida jikinta duk ya saki...haka yayi k'idansa yayi rawarsa har ya gaji dan kanshi ya kyale ta.
Bayan komi ya lafa ta duba agogon wayanshi karfe 1:30am...zaro idanu tayi,na shiga uku uncle me zan ce da umma idan na koma gida yanzu dare yayi sosai fa,koma a bud'e na baro masu gida....kada ki damu idan mun isa zan kira aysha ku shiga tare.
Suna isa kofar gidan su,yayi dialing number aysha,bugu biyu ta dauka..kun dawo ne?eh anty babba...ok ta shigo kawai umma na dakin baba ai...ya kali jummai ki shiga ba wata matsala matsora ciya kawai...da hanzari ta fita daga motar ta shige gida tare da turo kofa.
Aysha tace naga fitar ki ai,koda na kira wayar ki tana dak'i..shi yasa ban koma bacci ba nayi ta jiran dawo warki masu miji""ta k'are maganar cikin zolaya...nagode sister,kin san yunwa nake ji?walahi tun wainar da naci kwara biu da safe sai ruwa da nake ta sha...ya za ayi kiji yunwa ana d'ura maki had'e had'e na k'arin ni'ima,ga mijinki yazo kun ci soyayya kun k'oshi...kai sister am serious walahi yunwa nake ji...jona heater ki had'a tea,ga short cake nan ciki wanda mukayi order da abdul za a raba wurin friends day gobe....tea ta had'a mai kauri,tana sha suna hira har sta gama.
Aysha ta kalle ta yanzu sister banda gobe shike nan mun rabu??tunda aka haife ki tare muke kwana,bamu ta6a raba makwanci ba sai da na je sch,da lokacin da kika je kaduna...tausayin yar uwanta taji ya rufe ta,fashe wa da kuka tayi,aysha tace shhhhh ba kuka nace ki min ba ai hira muke yi ko?....haka ne sister sai na tuna da lokacin da nike fama da "QURUCIYA"abubuwan da nayi ta maki,ki yafe ni sister...common kema kin fad'i ai "QURUCIYA"ce,Allah yafe mana baki daya.amin..haka suka yita hira har aka kira sallar asuba,bayan sun iddar da sallah,yan k'auye suka gyara gida aka fara aikace aikace kasan cewa ranar za a je jere.
Zuwa 10:0am amina ta iso da kayanta na kwana...bayan sun gaisa tace anjima idan anty khadija ta iso zasu shigo da mami...wow Allah kawo ta lafiya amin.
Gidan nafisa suka wuce dama can za su zauna kuma a harabar gidan za suyi friends day da karfe 4:30pm...amina taje wurin taila ta amso d'unkunan jummai....ba k'arya sunyi kyau sosai,bayan sun gama ganin kayan ne aka shirya a wani akwati...aysha tace amina shiga gida ki bud'e kayan lefe ki ciro duk abubuwan da za ta b'ukata sabida yau zasu wuce jere da kayan duka...tau akwati guda empty ta ware ta cire ma jummai under wears,mayafi da su sark'a wanda za tayi amfani dasu yau da gobe,daga nan suka wuce wurin saloon aka wanke masu kai aka gyara suka dawo gida...mai lale har gida tazo(zanen fulawa) ta zana ma jummai manyar indian designe da yaji jan lale,haka aka yita ma su lalen...kawayen su har sun fara zuwa...babbban daki guda mai toilet ciki nafisa ta bar masu,allawiya ma ta iso ana ta hira cikin raha.
Zuwa karfe biu lokacin anty khadija ta iso gidan su jummai ita da mami...cikin girmama wa aka tarbe su kayan ciye ciye aka cika masu gaba da shi...bayan sun gaisa da umma da sauran yan uwa aka k'ara yi masu godiya akan hidimar da suka yi...can sai ga anty balki ta iso da moton ta discussion continue ash colour cikin shiga ta alfarma nan kallo ya koma kanta,ko kamshin ta na daban ne...da sallama ta shigo,anty khadija sai hararar ta take yi...cikin girmamawa ta gaida mami ta amsa ba yabo ba falassa,ta gaida anty khadija itama haka...ta koma cikin gida suka gaisa dasu umma...ina amaren suke??suna gidan nafisa,yaro aka sa ya rakata gidan...cikin farin ciki jummai ta tarbe ta da allawiya,amina kam sai d'ari d'ari take da ita.....ita ta ware ma jummai kayan da zata saka yanzu wani hollandis hadad'e ash colour mai manyan furan ni grean da fari"kudin sa yakai 25k)dunkin riga da zani,sai wanda zata saka anjima na friends day swiss less ne lemon grean da orange,dunkin riga da skirt...gasu nan na fitar maki,zamu wurin jere maybe koda zamu dawo kun gama...tau anty naso kina nan fa?ke maryam ai sai yan mata....
Umma ta aika duk inda suke da ajiyar kaya an amso,kowa sai santin kaya yake yi...babban motar kwasan kaya biu raji ya aiko dashi..Nan anty balki tayi ma umma magana akan su uku zasu jere...ita,anty khadija da yar uwar baba na kontagora,basa son tarkacen mutane da yawa.
haka kuwa akayi bayan an gama loda kayan suka wuce london street inda gidan jummai yake...a cikin mota tana ta jan anty khadija da hira'da yake su motar da suka shiga'tace motar kaya yayi gaba zasu bisu baya... Da suka isa sai yaba kyau'n palour'n suke yi,tun anty khadija na share anty balki har ta sake maza suka shigo masu da kayan ...gadon da daddy ya saya ma jummai shi aka saka a dakin miji,sabida yafi kyau da tsada,wanda umma ta saya aka saka a dakin jumma,aka gyara kitchen komi yayi tsaf tsaf...bayan sun sa curtain anty balki tace kada a shimfid'a bed sheet sai gobe da yamma dai dai an kusa kawo amarya...haka akayi suka share gida suka kulle gidan..
Su jummai an sha kyau ciki indian material lemon grean da orange kamar ka sace ta...su aysha,allawiya,amina, nafisa da suran k'awayen suyi ankon cikin riga lemon grean polo an rubuta happy marriege life a gaban rigar,baya kuma an rubuta
princess maryam salis
&
Prince muhammad Raji
Wasu wando suka,wqsu tommy skirt abun ya k'ayatar.
An gyara harabar gidan da canopy da kujeru sai table da aka aje abinci kala uku wanda suka girka da drinks kala kala,ga cool music na tashi...jummai na zaune a high table tare da amina sai gift ake aje masu,ana daukar pic kala kala,masu rawa nayi,masu cin abinci na ci,masu hira nayi hara masu daukar pic nayi...sai daf da magrib aka tashi....a hanzar ce ta shiga wanka,koda ta fita amina tace su anty sun koma gida,sun shigo kina wanka sai zuwa gobe idan sun dawo..tace kash nasu magana da anty balki kuwa,amma zan kirata..alwala tayi tare da gabatar da sallah...bayan sallar isha'i aka sa amarya a lalle sai faman kuka take kamar ranta zai fita...bayan komi ya lafa ta kira anty balki akan kada ta manta da dahuwara kaza da zata zo mata dashi gobe...yar dad'i miji ban manta ba..sanan sukayi sallama...pic na friends day ta tura ma mijinta ta wttsapp,suna ta charting har dare ya raba.
tun da asuba tayi wanka da had'in tattaciyar madarar shanu,ta mulke jikinta da turaruka masu kamshin gaske,ta shirrya cikin shadda dinkin half gown da zani...koda 10:am yayi an wuto da abincin walima daga gidan anty balki dama ita ta dauki nauyin walima...su amina na can suna faman saka kayan rabo cikin manyan jakuna na rabo kasan cewa 12:0pm zaa fara walima..kafin kace me dan mutum ya cika gidan su jummai,an gyara filin kofar gidan nan za a yi walima...zuwa 11:0am mutanen ta na area council suka iso mata da maza cike da bus,bayan sun shiga ciki sun gaisa da mutane suka koma waje inda za a yi walima suka zauna..wurin zaman mata dabam,na maza dabam..k'ira'a suka kunna yana tashi cikin suratul nisa'i haba nan da nan shiya ya dauka mutane nata tururuwar zuwa,bama da suka ji mal.alkali wada da mallama khadija mustapha zasu gabatar da wa'azi ba..ango ma ya iso da tawagar shi,cikin shiga ta alfarma kallo sai ya koma kan su ..table nasu dabam....a hanzar ce shirya cikin wata dakakiyar less mai laushi,wanda a k'alla kudin shi yakai 40k,simple dinki akayi na riga da skirt yasha stone work,sai alkebba da aka daura saman kayan...zo kaga kyau abunka da black beauty sai ta haska cikin kayan,sauran friends nasu black abaya kowa yasa yayi rolling red veil abun ya k'ayara..cikin natsuwa suka fito ana take ma jummai baya...mijinta sake baki yayi yana kallon matar shi,ga wani kishi daya taso mashi yadda abokanshi ke yaba kyau'n mattar shi.
Su anty balki,anty khadija,nafisa,allawiya da sauran mutane ma ba abarsu a baya ba suk sun hallara..yan gidan aogo ma haka su hajia da mutanen ta yan kuta....bayan bude taro da adu'a daga bakin amir na area council,sai karatun al-Qur'ani mai girma daga bakin PRO nasu...mal.alkali wada ya fara wa'azi akan hakki'in mace a kan mijinta,tare da shawar wari zuwa ga ango da maza baki d'aya,bayan ya gama akayi kabbara.
Sai mallama khadija mustapha tayi nata tunatar wa akan hakk'in mace akan mijinta tare da shawarwari zuwa ga amarya da mata duka,akayi kabbara..bayan anyi tambayoyi da adu'oi aka fara rabon abinci cikin take away mai marfi da manyan jakuna mai dauke da kayan buki..zuwa karfe 2:0pm aka tashi bayqn kowa ya ci,ya sha.
Gidan nafisa ta koma,
Wanka ta sake yi ta gabatar da sallah,ta shirya cikin shadda doguwar riga dark blue yasha stone work red ant white har k'asa...su amina ma an sake shiga cikin material less ta rako amarya gida ana ta gaisawa da mutane,suna yi mata fatan alheri har zuwa la'asar tana cikin gida..anty balki ta jata gefe ta bata had'in kaza da zata ci kafin a kai ta gidan miji....haka mutane keta tururuwan zuwa,umma na samun alheri..baba da abinci kala kala aka girka masa shida mutanenshi yan kasuwa...lokacin sallar magrib anty balki tace kiyi wanka gaba daya da hadin nan na sansamin lalle da turaruka sai ki dauraye jikin ki da ruwa mai kyau..bayan ta iddar da sallah ta zauna a natse ta cinye kazar nan tayi brush..wani simple