Showing 51001 words to 54000 words out of 64084 words

Chapter 18 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt

tun bata saki jiki ba har ta sake ana hiran da ita...can hajia tace dare yayi fa ka maidata gida mana ko nan zata kwana?hajia kada kisa umma ta aiko mun da samaci cewar jummai,ai mijinki ne babu abunda zata yi maki...mik'ewa yayi muje ko..tau sai da safe hajia mun gode ...a hanya yace baby ya kamata kiyi min list na abubuwan da kike da bukata asa a lefe...uncle ni banda mattsala duk abunda kasa inaso...a'a baby duk da nasan choice naki amma kema hakk'in ki ne kuma under wears ai ban san size naki ba...tau zan rubuta...u have to make it snappy fa dashi zan wuce...akwai matar aboki na dake lagos zan bata kudi a sayi wasu kaya ki can saura kuma xan tura kudi kano ne...tau uncle..ki gaida su umma sai na shigo da safe..ok sweet dreams.


Baba kam har yayi bacci,umma na zaune tana jiran dawo wan auta jummai...ke sai yanzu kika ga daman dawo wa yar dad'i mijin?shiru tayi wuce mazza ki kwanta ba ana maki hanunka mai sanda kin kasa gane wa ba,walahi namiji ne dai wayau zai maki ya d'irka maki ciki...dariya ya kwace ma jummai amma ta kunshe baki,kai umma hakan ma bazai faru ba insha Allahu..yayi kyau sai da safe,tau umma...haka ta kwana cike da kewar mijinta.

Tunda asuba bayan ta idar da sallah ta gyara gidan ta dama kunun koko ta zuba ma su umma nasu ita da baba,aysha tasha nata ta kama hanyar zuwa wurin exams..Baba yace jummai zuwa gobe zanje can mahuta wurin yan uwana ko akwai wani abu da zasu iya mun game da maganan kayan dazamu saya na d'aki da kuma na gara,idan ma ban samo ba zan sayar da gonata na gado azo a fara sayaya lokaci na tafiya... baba basai kun matsa ma kanku ba duk abunda Allah ya hure maka ayi min Allah sa albarka.amin maryam...haka suka ta hira har raji ya shigo cikin shigar k'ana nan kaya yayi kyau barakallah,cikin girmama wa ya gaisa dasu umma..yana palour zaune ta shigo da jug na koko,plate na k'osai sai cup da spoon....har k'asa ta duk'a ina kwana uncle?ya shafi kanta lafiya lau baby kin tashi lafiya?....lafiya lau....kamar kin san banyi break fast ba kuwa..kokon ta tsiyaya mashi a cup,ta zuba sugar da powder milk ta mik'a mashi...jazakallahu fil jannah my lovely wife..amin my lovely husband.

Yana sha suna hira har ya gama yayi hamdallah,gaskiya baby kina shagwaba ni fa da kayan dadi!kai uncle is my duty na kula da kai so ba shagwaba ka nake yi ba aiki na ne..Allah maki albarka amin amin.

Amh dama maganar kayan daki na riga na gyara palour an sa kujeru da kayan kallo so d'aku na kawai za a gyara maki sabida nan zaki fara zama har muga abun da Allah zai yi sai ki koma abuja ko?..tau uncle zan ma su umma magana...gobe da safe zan wuce,yaushe zaku fara neco?..next week wednesday,ok nama muktar magana ranar Monday zai kai ki bank ku bude accnt a first bank,savings accnt zaki bud'e fa,ko akwai abunda kike da buk'ata,?a'a...ok zani kuta anjima tare da hajia anyi rasuwa sai da dare dai zan shigo...uncle zanje tace cikin shagwaba..No baki tare ba fa baby bana son yawan yawo..shike nan Allah jikan shi da rahama..amin baby,har waje ta rakashi da yake da bike yazo,motar na gida.

Umma tayi ma bayanin abunda raji yace game da kayan d'aki..d'an albarka,Allah mashibsakaya da gidan aljana amin.

Da dare suka zauna da aysha suka yi list din irin kayan da take so a saka a cikin lefe...kai sister sunyi yawa fa..ai haka ake yi kinga idan ma sunyi yawa can wa yanda zai aika zasu rage kayan ne...tau shike nan.

Da dare da ya shigo zobo kawai ta bashi don yace bai jin yunwa,haka suka sha hiran su na soyaya,ta bashi list din..kai baby ai sunyi k'adan kayan..ah uncle ina cewa ma sunyi yawa...No baby ai right naki ne insha Allah zanyi kokari..Allah k'ara bud'i na alheri.amin sai munyi waya kennan dan bazan shigo ba da safe,ranar monday ki shirya fa da wuri,..hugging nashi tayi Allah tsare ya kare ka a duk inda kake...amin baby light kiss ya bata a lips nata sabida baya son jawo ma kanshi aiki da daren nan haka suka rabo cikin shauk'in juna.



Haka ta kwana cikie da kewar mijinta,ranar sunday tunda safe baba ya wuce mahuta kwana biu yayi suka had'o shi da buhun masara,buhun gero,buhun dawa,buhun shinkafa biu shashara...shawara ya yanke akan ya sayar ya kunsa kudin shi ya dawo gida ya sayi wasu tunda bai iya dauko su daga can,daya sayar kwata kwata dubu ashirin ya tashi dasu,dole ya had'da ba babban gonan shi na gado da aka saya dubu talatin,duk kudin sun kama dubu hamsin,haka baba ya dawo gida cike da takaici.........







*LEEMA*✍🏻

*⚜BRILLIANT WRITER'S ASSO..*πŸ–Š

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*QURUCIYAR JUMMAI*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍🏻




*Wanan shafin naku ne member's na"HAUSA NOVEL'S ONLY"Group*

*Kuna a birnin heart d'ina masoyya na hak'ik'a*;-

*maimunat S kole*

*Hauea Ado Ahmed*

*Ummiabdallah*

Da ma sauran member's na 'HAUSA NOVELS ONLY"group kuna rai na soyayar ku a gare ni bata fad'uwa sai fatan Allah ya bar mu tare ya k'ara soyaya da aminci,amin.🀝🏻



*Daga taskarrrrr marubutan muuuu;-*

*kada kubari a baku labari brilliant writer's sun sake dawo maku da wasu zaffafan littafai wanda shahararun marubutan nan kamar haka suka kawo maku*;_
*Rubutacciyar Al'amari by jamila musa(meelat)*
*&*
*Ummu affan*✍🏻

*Dace da juna by Saleehat*✍🏻

*Kishiyata by maryam hassan muhammad(little)*✍🏻
*musha karatu lafiya*πŸ“š

*Nida ya Moha by Ramlat ar manga"real mai dambu zuciyar meelat musa*

*69-70*



Haka baba ya dawo rai ba dad'i,shawara umma ta bashi da a aje kud'in cikin account na jummai zuwa nan gaba idan an samu k'ari,idan ma ba a samu ba su tatalashi haka nan ko yar katifa so saya mata....haka kuwa a kayi jummai takai kudin bank.


Su jummai an fara neco sosai kai ya dau zafi,kullum ckin karatu take,bata samun kiran mijin ta akai akai kamar lokacin baya,sai shi in aiki ya masa sauk'i ya kirata,lokaci sai tafi yake yi ta bangare biyu'n shirye shirye ya kankama na bukin auren jummai.

Aysha kam ta gama exams tana ci gaba da zuwa koyon aiki a wani private lab"" ganisol laboratory "" dake k'asan layin su,soyaya tsakaninta da abdul sai abunda yayi gama..ta b'an garen yan uwanshi kuwa kowa yasan labarin aysha sun matsu bata shigo cikin su ba sabida natsuwan ta.

Allawiya ansha gyarana jiki har an gaji,sabida anty balki taba jummai shawara da kada a fara mata yanzu ta bari har ta gama exams,ta samu natsuwa hankalinta ya kwanta,babu inda take zuwa sai a fara gyaran fata da sauransu,amma taci gaba da amfani da had'e had'en da aka mata na k'arin ni'ima....Allawiya taso kwarai alhaji sid ya bari a gama auren jummai sai ta koma gida,ya nuna rashin amince wa sabida yayi missing nata sosai,musamman yadda yaga ta k'ara kyau,tayi fresh komi ya k'ara cika,ya matsu basu koma gidan su ba.

Ranar asabar da yamma bayan jummai ta dawo daga schl wurin rubuta exams aka shirye Allawiya sosai tasha lale(zanen flower)na bak'i da jan lale,ga guiguyayen kan nan yasha mayukan gargajiya na tadda suma ya k'ara bak'i,tsayi da shek'i aka yarfa mata kitsun ta kanana gwanin sha'awa...amina ta mata light make up tayi kyau sosai domin yanzu jummai ta hana ta shafe shafen nan na mayukan bleaching..mai na musamman anty balki ta had'a masu na gyaran fata dashi take amfani yanzu.
Mota biyu alhaji saddat ya aiki dashi guda na kwasan kayan gara,guda na daukar mutane dama daga umma,jummai,amina sai allawiya..already ya sa an share gidan an gyara..da suka isa umma ta kara mata nafisa sosai mai ratsa jiki tayi masu sallama...jummai da amina suka k'ara gyara gidan yayi tsaf dashi kamar na wata sabuwar amarya shawar wari suka bata suka suka kama gaban su...da dare wanka ta k'ra yi ta sa wasu fitinanun kayan bacci,bayan ta k'ra turare gidan tayi ma baby rahma wanka ta aje ta cikin bed nata sai bacci....da sallama ya shigo ta tarbeshi da fara'a(abunda bata taba yiba kenan da can)kaji biu ya sayo da hollandia yuoghut,suka ci suka sha sai hamdallah...ruwan wanka ta had'a mashi yayi wanka ta fitar mashi da jalabiya milk colour..bayan ya shirya kamar maye ya fara laluban ta haka sula faranta ma juna rai cikin natsuwa basu runtsa ba cikin daren nan..sai da akayi kiran sallah sukayi wanka,lokacin baby rahma ta tashi sai tsala kuka take yi,da sauri ta fito daga toilet ta amshe ta,pampers ta fara cire mata tayi mata tsarki da ruwa masu dumi ta zauna cikin natsuwa tana shayar da ita...haka ya fito daga wamka ya same su gwanin sha'awa...murmushi yayi Allah maki albarka allawiya ban taba samun natsuwa dake ba irin jiya,fatana Allah sa farin ciki ya d'aure a cikin gidana,ya bani ikon kula daku...amin mijin ina mai nan afuwar ka akan abubuwan da suka faru a baya laifina ne,nice ban baka kulawa yadda ya kamata ba amma insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba...haba my life nima da laifin nawa tunda ke yarinya ce kina ta aikata abubuwa cikin rashin sani amma ban lurashe ki ba na saka maki idanu muna ta kwasan zunubai nima ki yafe min matata...babu komi ya wuce Allah bar mu tare amin,na tafi masallaci..data gama shayar da ita ta aje ta itama ta kabarta sallah....haka rayuwa mai dad'i ya kasance a gidan allawiya da mijinta tana kokari sosai qurin faranta masa,kuma tana kulla da yar ta iya gwarwado,shima yana kokarin sauke duk wani hakk'i nata da Allah ya d'aura mai.


Ta ban garen raji kuwa duk wani abu da ake buk'ata na kayan lefe da kayan lale duk ya h'ada..matan abokin shi dake lagos ya tura ma kudi aka sayi lesuka yan uban su kala goma,material kala biyar sai takalma da jakuna kala goma da akwati purple mai ratsin fari(best colour nashi fara jummai kuma purple)aka aiko mashi da kayan abuja...na kano kuma tare suka je da antyn shi dake kuta dama busineas dinta kenan idan za ayi aure a bata contract na had'o kayan lefe,tado suje tare da jummai ta zab'i abunda take so da kanta, ba da raji ba..amma jummai na exams.


Tamfofi daga manya zuwa k'anana kala goma,shadda biyar,hijabai kala goma,gyale kala shida..bai so a sayi gyale ba anty tace kada ya kuskura yama diyar mutane kulle sabida wani dalili nashi na banza wai kishi,ai ko manyan mallamai yanzu matan su na saka gyale zuwa programs,gidan buki ko cikin gida tana iya rolling gyale tai masa kwaliya.

Vest da half vest kala goma,breziar kala goma sha biu,under wear skirt kala goma sha biyar,skin tight kala goma,slepping dress kala goma,jalabiya kala biyar,english wears kala biyar,darduma kala biyu,sai tarkacen kayan make up,su sark'a yan kunne,da yan hannu,da kayan man shafawa,sabulai, da sauran tarkace..haka suka dawo lefe ya kamalu a abuja suka tsaya ta shirye kayan cikin akwatuna dole hand bags da takalma cikin ghana most go aka zuwa akwatuna sun cika..ita ta wuto da kayan zuwa minna gidan hajia sabida bazai samu zuwa ba sai satin buki..

Waya yayi da abokin shi muktar sabida ya dauk'i su muhamamd da bello(abokan nura)aje a sauke kayan da yayi order a gyara palour..koda suka isa motar kaya na jiransu a kofar gida,gate suka bud'e aka shiga da kayan ,muktar na bada order yada za'a yi arranging kayan...royal chairs ne purple and white set guda aka jera a babban palour'n,sai center carpet the same colour da cen ter table nashi..babban plasma tv ne na company LG aka aza saman tv stand,sai decodar na DSTV da Manyan home theater,aka aza manyan frame guda uku na ayatul kur'siyu,falaqi da nas palour'n ya tsaru gaskiya..dama goga raji ya bada order kada a sa curtains sai ranar da zaa kawo amarya.

Su jummai an k'are exams sai fatan samun sakama ko mai kyau, haka ta rabu da friends nata wayanda akayi zaman mutunci tana mai cike da kewar su""da yake federal schl ne"most of the students ba yan gari bane daga other state suka zo karatu,d'a d'aiku ne yan gari kuma sun mata alkawarin zuwa wurin bukinta idan Allah ya yarda,sabida tun tana b'oye tana da aure har suka gane dalili kuwa bakin amina bai da linzami..jummai taso zuwa senfort walima da za a gabatar nasu a schl din mijinta ya nuna rashin amince warshi,haka ta hak'ura.

Buki saura sati biu hankalin baba ya tashi kwarai da gaske bai samu talafu wurin kowa ba ga lokaci na tafiya..umma ta bashi shawara da tunda d'akuna biu ke gidan jummai cikin dubu hamsin din nan a saya mata gado d'aya d'ayan dakin kuma a saka mata katifa.

Haka ko akayi jummai taje bank ta ciro kudin,maman allawiya tace ga shawara mai zai hana muje gidan dailu dilaliya ana samun kaya masu kyau wa'yanda basu sha jiki ba mu saya mata gado can?...umma tace tau muje mu duba.

Da yamma suka shirya sai gidan dailu dilaliya,koda suka isa an kawo mata wani set na italy'n bed wai mai shi aure da wata uku miji ya saketa yanzu kudi suke so ta koma makaranta...gadon sabo ne gaskiya da dressing mirror nashi,wordrop da site drower..umma tace nawa soka ce ,dailu tace gaskiya dubu d'ari suka ce..maman allawiya tace haba dailu an zama d'aya fa gaskiya dubh arba'in zamu biya...uhmm kun so kanku da yawa ai ko su dubu dari biyu da hamsin suka saya dan suna bukatan kudi ne tace a sayar haka....umma tace a taimaka mu bada dubu hamsin walahi shike nan ma a hanuna ko mi bamu saya bafa na kayan aure.

Tau maman aysha bazan k'ita taku ba amma bara na kira yarinyar kuji ta bakinta..ai ba wai mun karyata ki bane abunda muke dashi kenan.

Yanzu dai bara na kira taa waya idan ta amince banda matsala,akayi dialing number ta dauka,dailu tai mata bayani...gaskiya bai baru haka ba ina laifin dubu tamanin?maman allawiya ta amshi wayan baiwar Allah ki taimaka mana mu rufa ma junan mu asiri,kina sun kudi muna son kaya ko ba haka bane,gaskiya idan ya maku dubu saba'in ku biya domin idan kun duba kayan nan babu abunda sukayi fa kuma ko a saba'in din na fadi sosai....haka ne amma kiji tausayin mu ki kara ragewa walahi dubu hamsin nazo dashi"cewar umma"
Mama kun so kanku da yawa idan mai yi maku saba'in ba kawai mu bar shi,babu komi yarinya mun amince ama yanzu hamsin zamu bayar zuwa gobe a ciko saura...shike nan Allah sanya masu albarka don Allah ku cika alkawari mama...ai ba za ma a dauki kaya ba sai an cika kudi cewar umma.

Dubu hamsin suka ba dailu akan ta adana masu kayan har su tashi dauka...tace nata kason fa..maman allawiya tace nayi maki alkawarin dubu biyu....a hanya umma tace shin wai ke ina zamu samu cikon dubu ashirin?kada ki damu maman aysha Allah na sane damu insha Allahu kafin gobe zai bude hanya na alheri...haka suka rabu......da suka dawo ne aysha tace umma hajia tazo tayi ta jiranki baki dawo ba tabar sak'o a fada maki gobe za a kawo lefe...Allah kai mu kawai tace domin hankalinta baya jikinta komi ya daburce mata sabida idan baba yaji labarin gado kawai ta saya da dubu hamsin ran sa sai yayi mugun baci ko katifa ba a saya ba....raji ya kira jummai cewa za a kawo lefe gobe thursday shi sai wani sati zai shigo....bayan sun gama waya take fada ma allawiya batun kawo lefe,tace sai ta shigo...ta kira amina kuma ta fad'a mata,yanzu mai ya kamata ayi na masu kawo kaya?

Jummai tace dama ana yin wani abune ba tukuici ake bayar wa ba?....ah besty yanzu ai an bar bada tukuici kaji ake soyaa masu kamar guda biyar haka da drinks ko katon biyu ne...tab ina zamu samu kudin sayan kaji har biyar?....haba kibar magana haka mana kamar ba musulma ba Allah zai kawo sai nazo goben...ok Allah tashe mu lafiya amin....mami tace keda wa awaya?....walahi jummai ce har ta bani tausayi lefenta za a kawo gobe kuma basu da abun ba masu kawo lefe,ina tunanen ma komi fa basu saya ba na auren nan?

Ayah poor them shine ai nake kokari nayi ma baban ku magana da khadija ko akwai abunda zasu iya yi akai...pls mami ki taimaka basu da ne suna cikin halin rashi...kada ki damu my daugter maganan kaji kuma gobe da safe ki tuna aje gidan gonar baban ku a yanko guda biyar d'in su gyara sai ki soya masu,drinks kuma ga 5k on your way ki saya masu nidai bazan samu zuwa ba muna da meeting a office,daga baya naje....mami u are the best Allah saka da alheri mun gode..haba baby yima kai ne,duk fa wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi.


Haka kuwa akayi tayi ma jummai waya akan zata zo da wa'yan nan abubuwa godiya sosai tayi ma ta...take fada ma su umma ai gashi yadda suka yi da amina hada kukan farin ciki umma tayi a cewarta mami ta fitar da ita kunyan surukan ta.

Jummai gidan nafisa ta shiga ta amso had'e had'en da zata fara amfani dasu
Na farko hadin gyaran fuska...man zaitun mai kyau,zuma da kwakwa aka guga ta aka tace ruwan sai ta hade su wuri guda..su zata rinka shafama fuskarta yayi 10minut a wanke.(ga masu pimples da black spot yana kashe su sosai)

Na gyaran fata kuma...kur kur,dilka,zuma,kwai da lemun tsami ta hade wuri gudakamar yadda ake kwaba lalle"amma yafi kwabin lale ruwa sai a shafe jiki da fuska bayan awa guda a shiga wanka.

Ta hade mata na sa laushin jiki...lalle,kwaiduwar kwai(egg yolk)guda uku,manja cokali uku sai kurkur...shima kwabawa tayi ,tace ki shafe jikin ki zuwa awa guda sai a wanke da ruwan dumi.

Had'in sabulun wanka...dettol,sabulun ghana,garin zogale,fararr albasa a hade wuri guda a k'irba su cikin turmi ana wanka dashi,ana wanke fuska(ga masu k'urajen fuska,yana kashe pimple da black spot)


Ga wani hadin na musamman dana hada maki...lemon tsami,tatacciyar madara,danyen kwai guda d'aya da ayaba...matse ayabar nayi da hanuna bayan na bare ta,na zuba tataciyar madarar shanu,na fasa kwai farin na zuba banda kwaiduwar ta(yolk) sai na matse lemun tsami ciki na gauraye ..ana shafe jiki yakai tsawon awa guda a wanke da ruwa dumi,kwana uku kawai za kiyi amfadi dashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login