Showing 33001 words to 36000 words out of 64084 words

Chapter 12 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt

wanda abdulrahim ya dauki nauyi.
Abinci ne kala kala daga safara resturant aka kawo maza suka ci suka sha tare dayin hamdala,sai fatan alheri ake ma ango.
Shidai raji ya rasa meke damun shi,tabbas yana son jummai so na hakika,amma ya rasa gane farin ciki yake ciki ko bakib ciki,a lokacin ya tuna da dan uwan sa nura lokacin da yake son jummai duk suka yi waya sai yace ""uncle yaushe zaka dawo kaga baby,ina son baby uncle idan ban aureta ba bazan iya rayuwa ba,sai yanzu ya gane bai ma nura adalci ba da ya rabasu da jummai rana tsaka gashi yanzu shi ya aureta,inda nura nada rai da wane ido zai kaleshi tabbas Allah kadai yasan abinda ya shirya shi yasa ya dauki ran nura.


Cikin gida kuwa jummai taci kwaliya da atamfa hollandis cikin kala ukun da anty khadija ta aiko mata dashi tay amfani dasu ranar daurin aure.
Riga da skirt ne dinkin ya amshi jikinta sosai sai yan kune,sarka,zobe da yan hannu kirar indian designe ta yafa babban mayafi silver da takalmi silver colour,ba wani make up tayi ba.

Haka mutane keta shigowa suna masu Allah sanya alheri maza da mata,da aka rage ne abdulrahim ya shigo.


Cikin zolaya yace my run away bride.

Tayi shiru

Yace yau baki ya mutu an zama babban mace tau Allah sanya alheri ya bada hakuri yasa anyi a cikin nasara.
Amina ta amsa da amin

Bayan ya gaisa da umma ne ta kara mashi godiyar dawainiyar da yayi naabinci da drinks

Yace ai yiwa kai ne,yaso kebewa da aysha amma ina mutane sunyi yawa kamar yau ake taron buki kasan cewa umma mai son hulda da mutane ga sun zumunci.

haka ya hakura ya wuce.

Raji ma ya shigo da abokansa sun gaisa da mutane,umma tace amina ta wude dakin babansu su raji su shiga,yaso yace zasu wuce ne abokansa suka matsa suna sun sanin amarya dole suka shiga.

Jummai ta shigo tare da amina cikin sallama.

Duk suka amsa banfa goga raji.

Bayan gaishe gaishe,da yabawa da sukai da zabin raji aka rufe da adu'a.

Sai wani abokin raji yace ku fito mu basu wuri su zanta naga wani cika yake yana batsewa sabida bai samu kebewa da ita ba

Sauran suka ce ai kuba ware kanshi na rawa ya samu yar shila sweet 17,aka sa daria.

Daki ya rage daga jummai sai raji,kare bata kallo yayi sosai da sosai haka itama ta daga idanu ta kare masa kallo shadda ce a jikinsa light blue yasha aikin hannu babban riga da yar ciki sai hula itama light blue yayi kyau cikin kayan bako kadan ba.

Yace lafia na kallo na haka.

Tace uncle laifin me nai maka da kake fushi dani?

Ya kyaleta,tace haba uncle kamar ba musulmi,idan ma wani abun ne sai ka fadamin na nemi yafiyar ka,idan kuma akan abunda ya taba faruwa ne tun ina cikin ""QURUCYA""ta ya kama ta ya by now ka manta dashi sabida ko Allah nuna ma laifi mu nemi afuwa ya yafe mana bare mu yan adam?

Ko dama ba sona kake yiba ka aure ni?

Mikewa tsaye yayi cikin rafin nama sai wuce ta rungume shi ta baya ta fashe da matsanaiciyar kuka mai ratsa zuciya......




*LEEMA*✍🏻✍🏻

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO*...πŸ–Š


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*QURUCIYAR JUMMAI*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍🏻


*EDITING:- HASEENA OGANNIYAπŸ’ƒπŸΌ*


*wanan shafi naki ne ke daya kiyi yadda kike so dashi masoyiyata abin alfahari na,babu ya ke cikin birnin zuciyata a dad'e anayi sai gaskia murucin kan dutse sun buga dake sun barki,dakalin majina a hauki a zame ki hau mutum ki zauna dai dai, gaba dai gaba dai
*MY SADNAF*(nafisa ta sadiya haka taken yake)
*one love keep us together*πŸ‘©β€β€β€πŸ‘©


*57-58*


Cikin dasheshiyar murya yace "whats wrong with u?"

"Everything is wrong wth me uncle".
"Yau inaso nasan matsayina a zuciyar ka idan sona ne baka yi gara a warware auren nan it will be better for both of us".

"Warware aure tsakani na dake ba abu bane mai yiwuwa dan haka zan tafi mutane na jira na a waje".

Kara shigewa jikin shi tai cikin shagwa6a tace "gaskiya ni babu inda zaka sai ka fad'a min gaskia".

Da yaga tana neman bata masa lokaci kada mutane su zargi wani abun yake mata cikin d'aki kawai yace "I love u baby"

Tace "say it again uncle"

I said "I love u is that all?"

"No"

"What next?"

Duk ta daburce farin ciki ya cikata tace "amma menene yasa baka kira na a waya?"

" I don't have yr number".... yace a tak'aice, hannu tasa cikin aljihun wandon shi ta zaro wayarshi kirar htc ta saka number ta tare da yin saving da ```baby love```, tace "wallahi uncle yanzu ba da bane duk baka kirani ba sai na fad'a ma hajia".

Dariya ta bashi yace "zan kira ai.
Promise?"

Yace "yes promise,sanan ta sake shi ya wuce".

Haka gidan keta cika da mutane, jummai kaya kala uku ta saka suna ta hutuna da wayan Amina har yamma tayi, lokacin mutane sun watse Amina ce ta rage.

Tace "amma jummai kinyi kokari fa abinda kika mashi dazu".

"Ah nidin ta wasa ce, cikin novel na gani shine na fara practicing".

Suka ta6a hira,bayan sallah isha'i driver yazo d'aukar amina suka yi sallama dasu umma, Jummai zata rakata umma tace "ina zuwa?"

"Rakiya zanyi umma", umma ce tayo kanta "da aure a kanki zaki raki ya? da izinin wa?,
Yanzu fa ba da bane."
"Kai umma nan da k'ofar gidan
Babu inda zaki,idan kina son hakan kirashi ki fada mashi idan ya yarda falilahil hamd".

Amina tace "umma ta fimu gaskia besty sai mun hadu a schl on monday".

"Tau ki gaida mami"

"Zata ji$.


Suna kwance a d'aki ita da aysha,tace "sister walahi jiki na kamar an bubugeni".

tace "gajiya ce sai kinyi bacci kin tashi zai watsaake.
Tau sister".

Abdulrahim ne ya kira aysha a dan wayarta kirar gioonie p2,suka sha soyayar su.
Jummai cikin ranta tace "oh inama ni uncle ya kira haka ai da nafi kowa farin ciki,anyway ko yanzu ai cikin farin cikin nike tunda burina ya cika na auren shi".

Da aysha ta gama wayar,tace "sister ko text ne ki tura ma uncle mana maybe gaji ce ta hanashi kiran ki".

haka ta tura mashi zunzurutun text na soyaya,har tayi bacci babh reply.

Raji kuwa koda text nata ya shigo yana kwance a d'akin shi yayi nisa cikin tunane a ganinshi kamar yaci amanar nura ne daya auri wacce yafi so a duniya,sanan yaji takaicin biye mata da yayi lokacin har ya furta mata kalmar so,sabida yayi alk'awari bazai ta6a furta mata yana sonta ba koda zai mutu da sonta a zuciyar shine.

Sai yaga tun ba aje ko ina ba ya kasa controlling kanshi wani irin mahaukacin sonta ke fizgarshi musamman ma idan suna tare shiyasa yake avoiding nata,yaji dadin text din sosai haka ya kwanta cikin nishad'i.



Da safe bayan sun gama gyare gyaren gida sun karya,tace "umma zan shiga duba allawiya".

Tace "kira mijinki a waya idan ya amince tau".

Haka ta koma daki ta zauna ciki da takaici.

Yinin ranar tana gida babu inda umma ta bari ta tafi.

Sai da dare yazo masu sallama akan gobe tunda safe sai wuce abuja yayi reporting.
Bayan sun gaisa da umma da baba,ya k'ara masu godia.

Umma tace "ya shiga palour mana",haka ya shiga ya zauna.
Can ta shigo da sallama dauke da jug da cup saman tray.

Doguwar riga ke jikinta na rubber pink sai stones a gaba da hanun rigar sai k'aramin mayafi bak'i ta yafa,ba laifi tayi kyau sabida rigar yabi jikinta.

Aje tray tayi a gabanshi ta zauna a hanun kujerar da yake zaune.
"Ina yini uncle" tace tare da kashe murya tana fari da idanu.

"Wai meke damunki?"
Ta turo baki "da kayi me kuma?"
"Sit proper mana kada wani ya shigo ya gan mu haka".

"Sai me ai kai mijina ne",ta tsiyaya ruwan a cup ta kai bakin shi.
Yace oh my God wace irin yarinya ce ke".

matar uncle raji ce ni,ya amshi cup d'in a hanunta yayi sipping ruwan kad'an ya aje cup d'in.

"Uhm gobe zan wuce abuja probably zan kai a month ban shigo ba sabida sai na gama sanin kan aikin zan fara zuwa weekend,idan kinje schl ki sami pc zata fada maki class din da zaki koma,idan kuma da matsa just text me a matsayina na mijinki ban baki izinin kira na ba".

"Amma saboda me uncle"?.

"Saboda haka nake so ayi,so don't ague with me".

"Kaga fa yanzu ko k'ofar gida zani sai umma tace lalai sai na nemi izininka yanzu ya zanyi?".

"Maganar fita ban hanaki indai within this area ne,gidan hajia,schl,islamiya ko wani aiki na da'awa indai cikin gari ne amma aikin da ya wuce cikin minna ban amince ba,wani zuwa kasuwa,buki da sauran su".

"Gidansu amina da family nasu fa?"

"Ai kinji abinda nace ziyara cikin minna ban hana ba".

"Zan tafi sabida ban shirya kayan tafiya ba,biyo ni ki amshi sako".

Kuka ta fashe dashi sosai.

"Kin fara ko?
Menene aka miki na kuka?".

"Inda ban zo ba kice ban maki adalci ba,pls ya isa haka".


ta fad'a jikin shi "yanzu idan ban yi kuka ba me zanyi,tafiya fa zaka yi babu ranar dawo wa".

Tausayinta ya kamashi,k'ara rungumeta yayi sosai a jikin shi,wani irin feeling yake ji game da ita,gashi tak'i barin kukan.

Cikin natsuwa ya had'e bakinshi da nata,yana kissing nata a hankali,sai ajiyar zuciya take sauke wa,sai da ya tabbatar ta natsu ya cika, baki shi cikin nata idanunshi sunyi ja kamar garwashin wuta.

Bai iya magana ba sabida halin daya tsinci kanshi ciki,hanyar waje kawai yayi koda ya fita umma har sun rufe k'ofar su yayi hamdallah cikin ranshi.

Binshi waje tayi jiki ba k'wari,ya d'auko babban leda ya mik'a mata,tak'i amsawa hawaye ne ke ambaliya a fuskarta.
Aje ledar yayi a k'asa yaba machine nashi wuta ya wuce sabida idan ya biye mata sai su kwana ana abu d'aya.

Tana ganin tafiyar shi ta sake fashewa da sabon kuka,aysha da duk abinda ya faru tsakanin su tana ji da yake su d'akin baccin su cikin palour yake kuma tana ciki.

Dafa kafad'arta tayi,sister kiyi hak'uri wata rana sai labari,ledar aysha ta d'auka tare da rufo gida
Tana ta ba jummai baki har tayi shiru.


Da safe koda suka duba ledar man shafawa ne,turaruka,sabulai na wanka dana wanki,man kitso,always pad shampoo da dai sauran tarkacen mata sai 10k da yar guntuwar takarda.

Aysha ta kwasa kayan takai d'akin baba.
Umma tace "Allah sarki irin albarka hadda d'awainiya".

Baba yace "Allah mashi albarka ya k'ara bud'i",suka amsa da "amin".

Baba yace "jummai ta rik'e kud'in a hannunta idan wani lalura ya tashi mata na kudi tayi amfani dashi".

Tace "A'a umma ta rik'e idan ana bukatan wani abu ayi amfani dashi".

Haka ta shirya jiki babu k'wari zuwa schl dole babban hijab ta sa har k'asa idan ta shiga schl ta cire,sauk'in ta guda makarantar su mata zallah ne.

Suna zaune a class ta fito da guntuwar takardar da ya saka cikin kedan kayan da ya kawo mata,rubutu yayi kamar haka;-
" *sallamu alaikum ga kaya nan da 10k kiyi hakuri babu yawa idan akwai wani abu da kike da bukata text me*"

Tsaki tayi kare da mutsitsike takardan.

Amina tace whats wrong?

"Nothing that remaind me during break ki rakani office na pc".
Tace "ok"

Lokacin break suka tafi office din,bayan sun gaisheta jummai tai mata bayanin abunda ya kawo ta.

Tace "dama uncle naki ya nemi alfarma kiyi exams da ss3 students wanda nasan babu tamtama u can make it,yanzu zaki fara shiga cikinsu kuna revision tare sabida time table na waec ya kusa fito wa".

Tace "thank u"

Amina tace "ai na fad'a maki shi ya nemi alfarma gaskia am sorry to say yr husband is simple definately very hard to understand".


Har aka tashi schl hiran raji suke yi.

Koda ta dawo gida ta bud'e wayanta ya mata text biyu.
Na farko yana shaida mata ya kama hanya ta taya shi da adu'a.
Na biyu kuma ya isa lafiya yana gaida mutanen gida.


Ango raji ya isa abuja lafiya office ya fara tsaya wa inada aka nuna mashi office nashi a matsayinshi na director tare da yin introducing nashi ga sauran maaikatan.

Sai 4:30pm suka tashi aiki motor suka bashi kyauta da matsakaicin gida a wuse zone 2 1bedroom ne da palour sai toilet ciki,a office zai rink'a yin breakfast da lunch.

Komi akwai a gidan na more rayuwa haka ya wuni da tunanen jummai.


aysha sun gama attachment nasu yanzu ta shiga 200level karatu babu kama hannun yaro,fanin soyayarta da abdul sai abunda yayi gaba.


Jummai dai kullum cikin tura ma mijinta text take yi sabida ta d'au alk'awarin bara ta ta'ba tsallake umurninshi ba tunda yace kada ta kira shi barata kuwa kira ba koda sonshi zai zama ajalinta.

Oga raji yayi 3weeks kenan a abuja aiki suke sosai babu kama hanun yaro sai dare,yana ganin text na jummai kuma hakan na masa dad'i sosai amma bai ta'ba attempting yin reply ba,sabida duk yaji muryanta yakan tsunduma cikin halin sha'awarta gashi yana tsoron aikata sa'bon Allah.

A ko wane lokaci ya kasance shi d'aya tunaninta ke adabar shi musamman idan ya tuna da lokacin da yayi kissing nata sai duk hankalinshi ya tashi.


Da dare allawiya ta tashi da nak'uda ranga ranga aka kwasheta sai general hospital minna bayan doguwar nak'uda da asuba ta haifi d'iyarta mace kyakyawa sak babanta.

Allawiya anji jiki sai kwanan wahala ake yi sai k'arfe biyu na rana aka sallamo su daga hospital.
Jummai na dawo wa schl umma ta fad'a mata ai cikin murna ko tu'be uniform bata yi ba tai hanyar waje da gudu umma na kekeke,ina har ta fad'a gidansu allawiya

Tace "Allah mai iko d'iya sak mahaifinta,sannu allawiya ya k'arfin jiki".
Tace "naji sauk'i".

"babanta ya sani kuwa?"

"Eh yazo hospital d'in ma ina bacci yaga baby wai har ya mata hud'uba da sunan mahaifiyar shi ramatu,ga kaya can daya kawo akwatuna ne set guda shak'e da kayan baby dana mai jego sai set d'in kayan wanka".

Jummai tace "better ai tunda ya kula ya aiki da wani abu".

Yanzu alhaji sid kullum sai yazo ganin baby Allah ya d'aura mashi mugun sonta sai hidima yake masu.

Kaya suka ware kala bakwai aka ba tela ya d'unko ma mai jego,jiki na rawa ya bada kud'in d'unki.
Jummai tace "Allah ne ya amshi adu'ar mu".

Allawiya tace "haka ne jummai Allah kara shige mana gaba amin".

Ana gobe suna babban rago ya kawo da buhun shinkafa buhu guda na flour da sauran tarkace.

Dole jummai ta kira amina akan tazo da driver gidan su suje kasuwa sayan sevoniars.

Jummai abu ya kai garesu bata nan bata can
Jalabiya ta zura baki ta yane kanta da mayafinshi sai slipers dake k'afanta suka kama hanyar kasuwa.

Aysha na schl umma na gidan su allawiya anata faman aikin masa na gobe.

Da suka isa basu nan basu can sai sayaya suke yi ana rugawa cikin buth har 1:30pm
Tace ma driver ya biya dasu oasis bakery suyi bucking na donut da short cake k'wara d'ari d'ari na gobe da zasu sa a take away na 'yan walima.

Mallam abu driver yace "hajia ko hanzarta ko zamu samu sallah juma'a".

Jummai tace "ai na sha'afa yau juma'a".

amina "tace ina wayanki?"

"maybe yana gida fa".

Haka kawai raji yaji gabanshi na mugun fad'uwa yayi ta kiran hajia bata d'auka ba,daga baya ya yanke shawarar kiran jummai yayi mata wajen 20miss calls bata d'auka ba yasan something is wrong,tun 12:am ya had'a kayanshi zuwa minna weekend da yake motar shine bana kasuwa ba 12:14pm a k'ofar gida tai mashi.
Koda ya duba k'ofar gida a rufe yake,ya tambayi mechanic na k'ofar gidansu yace mai hajia taje kuta tun jiya,ya sake trying number not rechable.
Tsaki yayi domin bai san ranar dawowanta ba yanke shawarar zuwa gidansu jummai yayi,yana gunguni yace "ita kuma wanan yarinya ko wane iskanci ne yahanata d'aukar waya oho".

Yana isa k'ofar gidan yayi parking mota gefe sallama yayi ta kwadawa shiru sai ga aysha ta dawo daga schl suka gaisa.
Tace "uncle saukan yaushe?".

Yace "ban jima ba,ya schl babban anty?"
Tace "lafia lau,baka shiga ba ka tsaya waje?"

"Nayita sallama ne shiru babu kowa", tace "eh maybe suna nan gidansu allawiya sabida ta haihu gobe suna aiki suke yi".

Yace "ai nayita kiran wayanta bata dauka ba".
Tace "shiga daga ciki bara na dubo maka ita"

Tare suka shiga a bashi ruwa a jug, ta aje littafan ta tana shiga gidansu allawiya ta fad'a ma umma raji yazo.
Tace "ai kuwa jummai na kasuwa tun safe ga wayanta nan na tsince shi ta yar saman gado ita uwar mai jego".

Tare da umma suka shigo gida, rusunawa yayi ya gaida umma cikin jin kunya.
Tace " sannu fa ya aiki ya hanya?"

yace "lafiya lau
gashi kuwa jummai suna kasuwa tun safe ita da amina ga wayar nata nan can na tsinto shi".

Amsar wayan yayi a hanun umma ranshi idan yayi dubu ya baci "wai yarinyar da yama gargad'i banda zuwa kasuwa shine yau tun safe take kasuwa har yanzu", sai yayi ya dubi agogon hanunshi yana tsaki.


2:0pm suka dawo gida suna k'ok'arin sauke kaya raji kuma ya fito zuwa masallaci.
'Kare mata kallo yayi da kyau, jalabiyar mai sul6i ne sosai yabi jikinta ga mayafin shi data yafa ya tatare ya koma kamar d'an kwali jelar sumanta kwance a gadon bayanta ya ya barbaje mugun takaicinta yaji.

Har gaban motan yaje ya damk'i hanunta ya wurgata back sit na motar shi ya bata wuta......








*LEEMA*✍🏻

*⚜BRILLIANT WRITER'S ASSO*....πŸ–Š

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*QURUCIYAR JUMMAI*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍🏻

*EDITED BY*;-
*LEEMA*


*masoyana abin alfahari na*;-
*Habeeba idrees(hubbeey)*
*Jamila mopol*
*Hawwa M.U(smasher)*
*Mienarh and her suruki hassan ATK*

*Hak'ika kun numa min k'auna da soyaya kuna a cikin birnin heart d'ina Alherin Allah ya isko ku a duk inda kuke a fad'in duniyar nan*πŸ€πŸ»πŸ‘πŸ»β€

*Hubbey Allah ya ba baban mu lafi mai amfani tare da albarka,yasa zakar jiki ne amin*πŸ‘πŸ»



*59-60*



A parking space na central mosque minna yayi parking motar yana k'okarin fita,tace uncle ina zaka?

Bai bita kanta ba ya fita tare dayin locking car din ya shige masallaci.

Haka ta zauna cikin zafi gashi duk wanda ya gifto sai ya kaleta dole ta kwanta saman sit.

Koda aka idar da sallah ya dauki kusan minti talatin(30minut)a cikin masallaci kafin ya fito wanda da gaya ya mata haka taji kwatan kwacin b'acin ran da ya shiga.

Data gaji da kwanciyar ta koma a zaune mutane da sun zo wuce wa sai sun kaleta gashi ya daidaicin inda keda rana sosai yayi parking kuma bakin hanya,tsaki tayi mutane dai akwai iya shege da auren ka ayita faman kallonka(nace wayanda suka kale ki a kasuwan kuma ba mutane bane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login