Showing 36001 words to 39000 words out of 64084 words

Chapter 13 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt

ko mallama jummai).
Yana iso wa ya bude motar tare da bata wuta,ta fashe mai da kuka haba uncle wani irin zalunci kenan walahi dana san haka kake da ban yadda da wanan k'adararen auren ba,idan ma wani laifi na maka ai bai kamata ka hukunta ni ta wanan hanya ba ni mace ce mai rauni kuma mutum kamar ka.

Driving yake yi hankali kwance"cikin ranshi yace ya salam yarinyar nan bata da hakuri ita bata ga laifin data mashi ba ya bata umurni ta k'etare sanan yanzu tana masa vomiting rubbish a nan.

Bakin yahuza suya spot yayi parking,rik'e rigarshi tayi gaskia ni bara ka fita ka barni cikin zafin nan ba haka kawai in banda zalunci.
Buge bakinta yayi da bayan hanunshi stupid girl dama rashin kunyar naki na nan bai je ko ina ba ko?zan fita ba tare da nayi locking car din ba idan kin isa ko kofar motar nan ki taba kiga yadda zanyi k'asa k'asa dake a wurin nan idiot.

Wani sabon kuka ta fashe dashi walahi tunda ba ubana bane kai da zaka sa doka ban k'etare ba sai na fita tana yi tana bugun glass,yana kallon duk abinda take yi a nan inda ya ke zaune daga wurin ya dana lock na motar ta rufe,order yayi na rabin kaza sai sinasir da exotic hankali kwance ya zauna ya ci abin shi cikin natsuwa sanan ya tashi ya nufi mota, koda ya isa tayi bacci yace silly girl, ban da niyar cutar dake ko zaluntar ki "this is the only way da zanyi punishing naki" har kiyi realizing mistake naki amma nafi kowa sonki da tausayinki my baby.

Hajia ya kira take shaida mashi ai ta jima da dawo wa har tajlyi girki,yace gashi nan k"'arasuwa gida,tunanin yadda zai yi da jummai ya shiga yi babu halin ya mai data gida a haka duk ta yamutse.

Yana isa kofar gida ya fara shiga ya bude dakin su na samartakaa dama a soro dakin yake da dukan allama hajia bata jima da gama gyaran dakin ba,ya dawo ya sungumeta zuwa cikin dakin ya kwantar da ita saman katifa ya kuna mata fan yayi locking kofar ta waje sanan ya shiga cikin gida.

Bayan sun gaisa da hajia tace ai kana fita baka dad'e ba na dawo sunday ke fada min kazo shine na gyara maka dakin na dafa maka wani abun.

Yace ai nayita kiran wayarki baki dauka ba shine na lek'a can wurin su jummai daga nan na wuce masallaci.
Tau suna lafia ko?lafiya zau suke.

Ya wurin aikin naku babu wata matsala injin,babu matsalar komi hajia muje kofar gida kiga mota.

mayafi ta dauka suka fita tace masha Allahu mota tayi Allah sa a mure,amin ya amsa
Bubude mata cikin motar yayi ta gani sanan suka koma gida,tace abincin a nan zaka ci ko cikin daki?
A'a hajia daki zani da nayi wanka inci abincin.

Tace dauki ka tafi dashi,saman tray babban kula ne da jug na ruwa,cup,plate serving spoon da spoon.

koda ya shiga stil bacci take hankalinta kwance,ya tube kayanshi ya shiga toilet wanka yayi sosai ya fito daga shi sai boxer shafe jikin shi yayi da vesine intensive care body lotion,yayi cumbing kanshi sanan ya fesa body spray .
Three qurter black yasa da red armless mara nauyi koda ya duba agogo lokacin sallar la'asar yayi dadage wa yayi iya karfin shi ya d'ad'a ma jummai dundu a baya,zabura tayi ta mik'e zaune tana kale kale
Yace kasa sarkin bacci, uwar mai jego,k'irjin buki,unguwan zoma kasuwa a kai maki dole shin Allah ya baki ikon yin ko da sallar azuhur ne uwar yawon kasuwa ga la'asar ta riske ki?
Tura baki tayi,would u get up kina turamin baki ga toilet nan ki shiga kiyi alwala ya fita zuwa masallaci,wanke fuska tayi sanan tayi alwala data fito ta shafa lotion dinshi ta dauki turare fuuuu fuuu fuuu ta fesa sanan ta kabarta sallah haka ta hada azuhur da la'asar,koda ya dawo ta idar tana zaune da tasbaha a hanunta.

Yace koda kwana kikayi istigfari walahi Allah baya yafe zaifin da kama wani sai musamman ma mijinki dan haka ki sauke girman kai ki nemi gafara wurin mijinki,banza tayi dashi.wanene ya baki izinin zuwa kasuwa?
Hab'arta ya daga ke bada ke nake magana ba?

Cikin sanyin murya tace am sorry
For what?ai laifinki yawa ke dasu na farko kin fita bada izinin na ba zuwa kasuwa for that matter,nayita kiranki a waya baki d'aga ba,sanan jubi dressing d'in da matar aure tayi zuwa kasuwa fisabililah,sabida baki d'auke ni a bakin komi ba kuma ban isa dake ba ko?

Kin san da cewa ina abuja wani friend nawa ya kira ni wai yaga mata na a kasuwa ko mun zu weekend ne?all his thought dake naje abuja,haba maryam kina da ilimin addini fa,yanzu kinsa nayi loosing confidence a kan ki.

Bara na baki wani hint;-

*YARDA DA AMANA*;-walahi idan kika same su a wurin mijinki ki kwanta ki huta maryam,yarda shike sa mijinki ya amince maki,misali;kinga ke b'aka ce idan nace maryama fara ce tas koda baki daya mutanen duniyar nan zasu taru su ce maryam b'aka ce bazan taba yarda ba.
Menene ya janyo hakan?yarda da aminci dake tsakani na dake.
Idan kuwa babu yarda da amincin nan koda sun taru sunce ai maryama fara ce tas bazan taba amince wa da maganar su ba.Hope u understand?
Gyada kai tayi,kinga ni yanzu yarda dake nayi na baki amanar kula da kanki tare da kare mutunci na dana aurenki,amma kin manta kinyi facali dashi,kinga kuwa yanzu Allah kiyaye ko a hotel aka ce min an ganki bazan iya musawa ba duk da nasan halinki bara ki iya aikata haka ba.
I beg u in the name of Allah idan nace zauna nan maryam koda shekara zanyi ban dawo ba kada ki kuskure ki tashi daga inda na baki umurni ki zauna until i said so,did i make myself clear?
Daga kai tayi,uncle ka yafe min walahi hidima ce tayi mana yawa amma bada niyyar wani abu na aikata haka ba.
Babu komi maryam ai ba wani mugun abu kika yi ba is just that na tsani naga matar aure tana cud'anya da maza cikin kasuwa shine dalila,yanzu ci abinci na mai daki gida.

Dafafen doya ne da miyar stew,bata wani ci da yawa ba(idan kun tuna doya bata cikin tsarin abincin da jummai ke so).

Har kin gama?eh
Rufa mayafinki da kyau kinji?tau zan shiga in gaida hajia.
A'a ki bari ranar sunday tare zamu kuta ki gaishe su zan kai masu mota su gani.

Sun kama hanya yace gashi ban maki tsarabar komi ba ki shirya anjima muje shopping

Da ka barshi ai,bana son musu ke mata tace kuma ni nayi niyya ai ba ruk'o na kikayi ba.
Yana aje ta yace ki gaida su sai na dawo anjima.tau.

Yana juyawa ta shige gidan su allawiya(mai hali baya fasa halinsa)

Ah jummai masu miji sai yanzu?eh tace a takaice.
Amina ta shigo da kayan duka ko,kin duba komi yayi?
Eh na duba Allah bar zumunci.amin
Gobe tunda safe kiyi ma yaya nafi'u magana yaje bakery ya amso sauran kayan,bazan samu zuwa ba.
babu komi ai kinyi k'ok'a ri,ina baby rahma?
Tana wurin mama ana mata wanya,tau anjima bazan samu shigowa ba zamu fita da uncle.
Babu matsala an kawo dunkuna fa ki duba mana,wani babban leda ta jawo kaya ne kala tara.
A'a ba kala bakwai aka kai dunki ba?
Tace eh daga baya cikin kudin daya ke yawan bani na aika aka sayo min irin material din nan nawa kuma aka dunka maku keda anty aysha muyi anko,su mama ma na cire masu turmi biu sunyi anko da umma.
Allah sarki allawiya rayuwa kenan bayan wuya sai dad'i Allah kara rufa asiri ya barmu tare.amin
Yiwa kai ne jummai kin taimake ni a lokacin da kowa ya juya min baya dan haka idan na mance alherin ki ai na zama butulu.
Yanzun ma bayan suna akwai wasu adu'oi da zan baki kinga yanzu Allah ya amshi adu'ar mu mutumin nan ya fara gane gaskia,be kamata muyi sakaci ba k'ara bada himma zamuyi wurin kai kukan mu ga mahalici har komi ya dai daita ki samu kiga yan uwanshi.

Tau sai an k'are harkar bukin sunan nan,tau sai gobe.

Tana shiga gida umma tace uwar mai jego sai yanzu?umma mun fita ne fa da uncle.
Ke zo nan fada min gaskia ina da ina kuka je,babu abinda ya shiga tsakanin ku ko?
Kai umma masallaci yaje,wurin cin abinci daga can ma bacci ya kwashe ni muka dawo gidan hajia(idan baku manta ba jummai bata da d'abi'ar k'arya tun tana karama)
Kiji tsoron Allah bai maki komi ba ko?
Bata san inda maganar umma ya dosa ba,daki ta shige.
Umma tace babu shaka ai tsaru zan fara baki kafin amin aika aika(ku tayani gani mutum da matarshi har wani aika aika ake tsoron ya faru)
Aysha tace har kun dawo inace ko sai gobe?haba sister ai sai umma ta cinye ni danya,ta bata labarin yadda suka yi dashi.
Tab ashe kin wahala kuma fa da gaskiyar shi don Allah ki kiyaye.

Taso kiran amina amma wayanta na hanunshi haka ta hakura da akayi sallar isha'i tayi wanka tare da mulke jikinta da turaruka humra wanda anty khadija ta aiko mata dasu daga kaduna,duguwar riga na material tasa daga sama an tsuke shi ka'asa kuma an bude sosai bata daura dankwalin ba ta fito cikin gida.
Aysha tace u look💋

thanks sister,umma tace sai ina kuma?
Fita zamu yi umma,sannu yar dad'i miji ina raba ki kina shige masa.
Haba umma mijinta nefa koma sayaya zasu ba wani wuri ba.
Ayyo ai sai kiyi bayani ko.
Suna cikin haka ya iso dukawa yayi a kofar gida suka gaisa da baba ya shigo ciki.
Ina yini umma,lafiya lau ya gajiyar hanya?
Babu gaji.
Ki tashi ku tafi kada ki bata masa lokaci tace tau mikewa tayi ta shiga daki.
Aysha tace sannu uncle,yauwa aysha ya makaranta?lfy lau.
Yace umma ga moto nan waje daga wurin aiki aka bani,tau Allah sanya albarka yasa a kashe lafia.amin suka amsa

Jummai ta fito sanye da kashka mayafi tayi rolling saman kanta,sai harara yake binta dashi.

Sai mun dawo umma,a dawo lafiya.
Suna shiga mota ya rik'e kunenta sai data saki k'ara,ke baki iya daukar simple instruction ne?wane irin dressing kenan wanan rariya da kika saka wai riga da wanan figaggiyar mayafi kina matar aure.

Kayi hakuri tau,hakuri guda ne idan mun isa ki tsaya cikin mota har in gama abinda zanyi,yaja mota.

A bakin "mustapha all store"yayi parking,tana kokarin fita yace ina zaki?go back my friend,zama ta gyara ya kuna mata AC ya rufe motar ruf ruf.
Man shafawa,sabulai,pad,turaruka,make up kit gaba daya ya saya nata kenan.

su umma sabulai,madara,milo,sugar cube,biscuit,chocolate da sauran tarkace ya kwaso masu aka mashi total ya biya.
Zuba kayan yayi a back sit yace me kike tunane?
Babu komi tace,jan motar yayi zuwa yahuza suya spot wuri ya samu can ciki yayi parking,wait for me yace.

Leda biu ya dawo dashi,yace ga naki wanan na hajia ne.

Tace an gode,plastic chair ya jawo masu guda biu suka zauna under umbrela tree.
Yadai kinyi shiru?babu komi,gara ki fadi kada ya kashe ki sabida am a stright forward man bana rike mutum a rai idan kamun ba dai dai ba zan fada maka gaskia,ba yabon kai ba ina da hakuri iya gwargwado,abubwan da kika ga inayi maki is for our own benefit,bawai bana sonki bane.
I love u the most maryam,ina so muyi building rayuwar mu based on soyaya,kauna,amana da gaskia,idan bamu gyara zaman mu yanzu ba sai yaushe?pls don't be offended u will get use to it kinji my wife.

Insha Allah zan gyara uncle,gud girl vanilla ice cream ya dauko babban rkba cikin kayan,ya bude ya fara bata tun tana kawar da kai har ta fara amsa,suna yi yana bata labarin wurin aikinsu yace ko zaki bini?
Done kai tayi,ya karatu kina gane wa sosai hope ba wani problem?
Eh time table ma ya fito on 12 of march zamu fara biology practical,ki maida hankali sosai Allah kuma ya bada sa'a.amin sai 10pm suka koma gida.


Ga wayanki,kuma kinyi kyau sosai yau irin dressing din da ake ma miji a cikin gida kenan bana zuwa unguwa bane take note.am a jelousy type.
Thanks for every thing uncle u make my day.
Di'nt worry,sleep well and always be a gud girls.
Kayan ta kwasa ta shige gida,idanun umma kyam bata yi bacci ba.

Umma baki yi bacci ba?ta ya hankali na zai kwanta kina waje,yanzu ya kwanta tunda na dawo ga kaya nan daya saya mana.
Ki aje gar gobe shidai baya gajiya da hidima.
Wanka tayi,ah sister baki yi bacci ba?eh yanzu muka gama waya da abdul,zata fara ba aysha labarin abubuwan da ya faru tace ke me yasa baki da sirri ne kullum bakin ki na yoyo ki bada labarin abinda ya faru tsakaninki da miji,ba haka ake yi ba boye sirrin ku zaki na yi ko umma bai kamata ta san abunda ke tsakanin ki da mijinki ba bare friends naki,naga bakinki bai da birki da abu ya faru ki kwace ki zazaga ma amina mutum sai Allah fa.
Tau sister zan kiyaye.
Kiranshi ya tada ita da asuba,tana dauka yace atashi ayi sallah ya kashe.
Sallah sukayi suka gyara gida kasan cewa yau suna,kayan ta fito dashi aka zazage umma tace masha Allah yayi kokari Allah sa albarka bara baban ku ya dawo daga wurin radin suna a nuna mashi kayan,akwai turmin zani da dubu biyar da abdulrahim ya kawo jiya bayan fitan ku aba mai haihuwa,ba za a bada kudi ba yanzu za acire sunk'in sabulu biu a hada da turmin zanin,kudin sai ki ma mutanen kuta tsaraba.

da baba ya dawo aka nuna mashi godia yayi,aysha tace kajin nan akai gidan nafisa ta aje mana a freazer tunda gasashe ne har mu tashi buk'aata.
Umma ta shiga da kayan taba maman allawiya sukayi godia taba allawiya ta ajiye.

Text jummai tai mashi akan zata kashe wayanta suna da aiki
Yayi reply uwar buki ayi aiki lafiya.
Su umma masar shinfa sukayi da safe,zuwa rana zasuyi jelof rice na taron buki.
Gidan su jummai kuwa alhaji sadat da kanshi ya damka mata komi za a masu tuwon semo,amala sai white rice shida abokanshi
Allawiya kuma tace dambun shinkafa take so sabida friends nata masu zuwa,jummai ta koma kamar mahaukaciya ita da aysha saukin su daya nafisa ta shigo tayasu aiki can sai ga amina ta iso.
Murhu uku aka hasa guda akayi miyar danyar kubewa plain,miyar ayoyo plain sai stew da yaji soyayen naman shanu.
Aka kwashe a kulali,sai white rice,kayi tuwon semo sai amala zuwa sha biu sun kamala,ai sai ga kaji kuma da za ayi pepper chicken da cream salad nacin shinkafa.
Saukin su guda an gyara kajin an yanyanka suka shiga tafada da kayan kamshi aka samu aka soya aka haka.
Su nafisa da amina ragwaye suka koma aikin zaune na yanke yanken cabbage,cucumber,carrot da su albasa aka hada zuwa karfe 1:30pm ya aiko daukan abincin amina da aysha suka kwasa zuwa mota.

Can cikin gida kuma vmasaka tsinke mata sun cika mai jego sai shiga ake ana sake kaya ita da baby rahma sunsha kyau.
Sai da sukayi sallah suna hutawa aminna tace amarya ya kukayi da angonki baki kirani ba nasha labari(da yaje amina irin mutanen nan ne masu shegen son jin gulma)

Aysha tayi saurin taron numfashin jummai tace nafisa na neman alfarma ki koma gidanta maganan gyaran jiki da tayi ma umma zaku fara yanzu,tace gaskia sister yayi sauri fa.
Nafisa tace ke kwata kwata waec da neko wata hudu akeyi fa kuma ya ishemu muyi duk abunda zamuyi cikin natsuwa ya bi jikin ki sosai kafin ki tare.
Tau naji bara mu aza tukunyar dambu kafin mai jego ta fara mana aike.
Haka suka ta hidima,anata serving mutane friends nasu duk sun zo hada yan karya su fedy da farry, basu suka gama ba sai lokacin sallar la'asar.

Nafita ta wuce gida sabida tayi bak'i,wanka suka shiga aka shirya lokacin jummai ke nuna ma amina kayan da raji ya sayo mata,amina tace Allah bamu damshen ku kin samu miji mai zuciyar yi,nan aka bude make up kit amina ta tsatsara masu kwaliya suak shiga gidan mai jego ai kallo ya koma sama kyawo na dukan kyawo su farry sai yatsine yatsine akeyi,fedy tace wow kin hango wasu big girls kuwa?
Farry tace dallah can mallama cooker's dinmu ne fa su jummai,taba amma sun fantama ai ko material din da ke jikinsu abun kallo ne sabida tsadar shi ga make up ya zauna a fuskar su daram masha Allah.
Mai jego ta saka nata material din irin nasu akayita hotuna hadda amina, sai yamma lis amina tai masu sallama ta kwashe tarkacen sevoniers ta wuce gida.

Bayan kowa ya watse ne an gyara gida allawiya tace ban san da wani irin baki zan maki godiya ba jummai kin fidda ni kunya wurin miji na,kin fidda shi kunya wurin abokanshi,badan kin tsara abubuwan nan haka ba kuma ya tafi according to plan da ai babu magana,tunda wayan nan yan iska su farry dana dauka abokan gaskia babu uwar da suka tab'uka min sai cika wuri da k'ananan maganganu da yatsine yatsine.
Haba allawiya nasha fada maki babu godiya a tsakanin mu,nima dana je kaduna hutu ne na koyi duk irin abubuwan nan wurin anty khadija kinsan mijinta babban dan siyasa ne idan zai yi b'aki haka muke yini a kitchen ana girke girke.
Tau gaskiya kafin na koma zaki koya min wasu abubuwa,baby rahama ce ta fara kuka jummai ta dauke ta sorry my baby wanene?mumy ce da friends nata suka hana ki hutawa yau ko.

ansheta ki bata tasha ga jikin yayi zafi ma sai kin bata paracetamol syrup,tana bata nono suna ci gaba da tataunawa kinga yanzu ya rokeni gafara akan duk abubuwan daya aikata min a baya sharrin shaidan ne kuma na yafe masa domin gaskiya da laifina ciki kinga kafin inyi aure yayi disvirgin dina,lokacin aure na babu abunda mama ta bani na k'arin ni'ima da gyaran jiki sai ma wasu uban capsule da su farry keta dura min na tighting gaban mace da gyara breast wai a cewarsu abunda ya kamata na gyara kenan kawai,koda nayi aure breast dina kamar silifas,gabana ya bude sosai,jikina in banda gel,cream da tubes na bleaching babu abinda nake shafawa ko turare ban damu dasu ba haka kai na yasha relaxer ya guiguye ina wata banyi cumbing nashi ba bate yaga kitso.

Gidana babu gyara ina sati guda banyi shara da mopping ba gani nake yi tunda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login