Showing 24001 words to 27000 words out of 64084 words

Chapter 9 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt

uwarta.

Da safe bayan Sun gama karyawa Baba yace zai tafi wurin amsar gaisuwa daga nan zai wuce kasuwa,umma ma ta shirya ta shiga gidansu Allawiya ta fada ma mamar su allawiyay ko zta samu daman zuwa suje tare gaisuwar anjima.

Jummai tace sister ya kamata mu shirya muje wurin ansar gaisuwa.

aysha tace kin mance shawarar dana baki jiya ne akan ki nisanta kanki da nura duk hanyar da kika san zaku hadu ki gujeta, kada ki sake mashi text ko kiranshi ta haka rai fara damuwa dake kuma yasan muhimanci nki.

Tace anya kuwa sis zan iya?

Tace insha Allah zaki iya,yanzu sai ranar adu'ar uku zamu koma.

Tace tau.

Bayan kwana uku suka shirya zuwa gidan hajia,hijab har kasa aysha tace jummai ta saka da nikab,sanan ba tare zasu shiga ba yadda idan yaga aysha ita guda Zai tunanen abinda ya faru ranar ya hana ki zuwa.
Tace yr wish is my command sis,suka tafa.


Jummai na gaba Aisha baya har suka isa kan jummai na qasa ta shige gidan,aysha kuwa hadda dukawa tai ma mazan waje gaisuwa,raji ko kallonta bai ba,duk da ranta ya baci haka ta daure ta shiga ciki.

Bayan gaishe gaishe suka nemi wuri suka zauna har su UMMA suka shigo lokacin aysha tace bari su koma gida tunda umma ta shigo,zasu fita ne shi kuma yana sauri ya shigo su gaisa da su umma yayi Karo da jummai tsaki yayi yace wane irin rayuwa Jeanne mutane kuna tafia baku kallon gabanku, ga wani tsumma da kika rufe fuska dashi tun kina yarinyarki useless ya shige gida.

Jummai hawaye ta fara yi suna tafia ta ce sister kin gani ko da gaske nefa Man din nan yayi hating dina cikin ma bai ga fuskata ba yake wanan bala'i inaga ya gane nice?

Aysha tace take it easy sister with time komi zai dai daita.


Haka jummai taci gaba da daurewa,duk wani kissa Da kisisina da mace Zatai ta mallaki zuciyar namiji jummai taji har ta gaji ba sa'a,raji sai wulakanta jummai yake duk ta kirashi zagi da cin mutunci,idan a hanya suka hadu the same thing,yanzu ko zai zo gaida su umma sai ya daidaici jummai bata gida,ita kuma UMMA bata taba nuna mashi tasan abunda kenan ba.

Admission din su aysha ya fito alhamdulilah taci weeding exams,takai duk wani kudi da ake bukata cikin ikon Allah Sun vata uniform da department''medical laboratory technician""diploma ne for 3years,kullum taje a taxi ta dawo a qasa,wata rana ma qasa take zuwa.

Tunda ta fara schl Samari sukai mata caa,students,leacturee da masu tare ta a hanya amma taki sauraren kowa sabida karatun ta tasa a gaba....


Da yake su jummai na hutu,idan aysha ta wuce schl sai duk taji gidan babu dadi yau dai shiryawa tai zuwa gidan allawiya, domin tunda aka kaita jummai vata sake zuwa ba.

Kwana Kin baya allawiyar ta kawo ma su ziyara wanda mijinta ya kawo ta sai yatsine yatsine take yi,ta kara fresh Hutu ya zauna.

Jummai tace allawiya wai ya maganar komawar ki makaranta ko secondary schl ki samu ki kamala.
Budan bakinta tace ai ana karatu ne Dan a samu abin digaro da akai,ita bata bukatan komi duk wani abu da diya Mace ke bukata mijinta na mata ita bata da matsalar komi..
Shine fa ya so zama masu fada da jummai sabidaw tana fada mata fascia, allawiya tace bakin ciki take mata taga ta samu inda zata huta ita ko mashinshiniu bata da,daga ita har yayarta....

Yanzu ta gama shiryawa kenan taji tsayuwar mota a kufar gidansu,tana dubawa taga Amina ce.

Da gudu ta rungume ta, tace Best friend shine ko ki kirani kice zaki zo?

Tace bari kedai muna zaune da mami nce yau gidan ku zan yini shine fa tasa driver ya kawo ni.

Tace ai kin kyauta yasu mamin?
Tace lafiya lau.

Tace ina su umma da anty aysha?

Tace umma sunje gidan buki ita da maman su allawiya, sister kuma Sun fara lecture.

Amina tace na tayata murna Allah nuna mana lokaci muma.
Jummai tace amin,ai da baki sameni ba danshirin zuwa gidan allawiya nai.

Tace wanan mara kunyar kawar taki,wait naga duk kin rame menene matsalar ki Best friend.

Jummai tai shru

Tace kodai mutuwar nura ne ya razana ki haka?

tace kedai bari akan Uncle ne,ta kwashe komi ta fada ma Amina.

Amina ta hasala

Tace to hell with him,shidin me takalan banza Wanda tsiya tai mashi kaka gida,idan banda kaddara me zaki Yi dashi?

Tace haba bestiy walahi Allah ya daura min sonshi fa 'I can't do without him ne.

Tace u too funny bestiy kamar raji kike ikirari baki iya rayuwa ba dashi ba?
Tacee did u know the worse part of it?
Yanzu mafa avoiding dina yake Yi,ga sonshi kullun karu wa take cikin zuciya ta.
V
Amina tace sha kurumin ki Zane baki wani adu'a ayar al-qur'ani ce duk kika karanta shi sau bakwai, a duk karshen ayar ki ambaci sunan raji da iyayenshi walahi walahi walahi ko sarauta dunguru gum ke Samar kansa dan girman kai walahi sai ya soki,so na fascia mahaukacin so Wanda bai taba ma kowa irin sa ba shida Kansan zai kawo kansa wurin ki.........



*LEEMA*✍🏻

*BRILLIANT WRITERS ASSO*...πŸ–Š

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*QURUCIYAR JUMMAI*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*HALIMATU SADIYA MUHAMMED*
*LEEMA*✍🏻




*49-50*



Jummai tace da kuwa nafi kowa farin ciki idan har uncle da kansa zai furta kalmar so a gare ni.


Amma kuma ya sahihancin adu'ar?

Amina tace ace maki ayar al-qur'ani har wani sahihanci kike nema kuma?

Tace yi hakuri bestiy kinsan gara kayi bincike sabida shirka tafi ko wani laifi girma a duniya.


Tace haka ne best friend ga aduar kamar haka;-fala yahzunka qauluhum inna na'alamu ma yusiruna waMa yu'ulinun(sai sunan shi)
Haka zaki maimaita har sau bakwai.

Tace masha Allah kamar nasan ayar cikin suratul yaseen.
Tace eh cikin suratul yaseen yake aya ta saba'in da shida(76)

Tace godia nike Allahu yabar kauna da aminci besty.

Tace haba ai yiwa kai ne.
Suka ci gaba da hiransu na duniya har umma ta dawo suka gaisa da amina.
Tace amma jummai baki da kirki haka akeyi kin bar diyar mutane da yunwa sai hira kuke yi.


Amina tace umma ai ban jima da zuwa ba kuma sai zuwa anjima zamu dafa indomie.

Umma tace aikin kenan kullum indomie,idan kukai aure ya zaku qare da maza jenku?

Jummai tace kai umma ai zamui masu abinda suke so.

Tace Allah nuna mana lokaci.
Suka amsa amin umma.

Sai 30pm aysha ta dawo nan jummai ke bata labarin shawarar da amina ta bata.

Aysha tace insha Allah amina zatai kokari ta gwada Allah dai ya mana jagora amin.

Bayan sallar la'asar driver ya dawo amina tai masu sallama,tsara umma ta bata na danyar masara,danyar gyada da mango.
Sosai amina tai godia dan abubuwar da tafi so kenan.

Tace tau besty sai munyi charting ko?

Tace ina gaida mami dasu anty duk abinda ake ciki zan fada miki.
Haka amina ta wuce suna daga ma juna hannu.


*WACECE AMINA MUHAMMED*?


Diyace a wurin ambassador muhammad kere da hajia sadiya muhammad kere.
Asalin su nufawan lapai ne a niger state,aiki ya kawo su cikin minna,diyansu hudu guda ya rasu.

anty khadija ce babba tayi aure tana kaduna nurse ce danta guda iziddine,sai bros aliyu yana zaune a cikin minna a federal high court yake aiki matar shi balki da diyansu biu safna da humaira,sai amina,sai yusuf daya rasu.



Jummai ta maida ayar da amina ta bata a matsayin abin fadin ta kullum cikin karantawa take tare da ambatar sunan raji hade dana mahaifinshi,amma shiru har an share sati babu shi babu labarin,sosai take kai ma hajia ziyara tana debe mata kewa,duk wani aikin gida ita ke mata amma bata ganin raji.
Har dai ta gaji ta tambayi hajia,tace mata ai ya tafi south africa course na 6month.
Haka jummai ta dawo gida jiki ba kwari.

Tace umma ashe uncle tafia yayi?

Umma tace eh yazo yai mana sallama ai kuna islammiya ranar.
Tace amma umna shine ko ki fada mana?
Tace kona fada maki maganin me zai maki,sai ma tashin hankali da damuwa da zaki sa ma kanki.
Tace babu komi Allah na nan.

Umma tausayin yar nata ne fil cikik ranta,ta rasa wanan irin bakar kaddara,ace kamar jummai wai namiji zai nuna ma kiyaya,tafi aysha kyau,dira da tsarin jiki hasken fata kawai aysha zata nuna mata.


Ban garen raji kuwa tafiyar a vazata tazo mashi unexpectecd aka kirashi akan yada daya daga cikin wayanda kwamnatin kasar ta zaba zuwa south africa course kuma 3days aka basu suyu duk shirin da zasui na tafia.

Da zai tafi hajia ta nuna rashin amincewarta a cewarta ta hanyar karo karatu a wata uwa duniya ta rasa tilon dan ta nura,yanzu vara ta bara guda gudan kaninta ya tafi har south africa karatu ba.
Da kyar ya rarasheta ta amince domin taso ace ya fitar da mata idan ya dawo ayi batun aure tunda shi daya take da dan'uwa da suka fito ciki daya gashi iyayensu sun dade da rasuwa.

haka ya lalabata ya samu ya tafi da alkawarin idan ya dawo zai kokari ya fida mata.


Yana kwance a hotel din da aka sauke su bayan ya dawo lecture duk kwana kin nan tunanen jummai yake yawan yi,ga wani feeling na mussaman da yake ji game da ita,duk ya runtse idanu ita yake gani duke gaban shi tana rokonshi yaso ta,babu kalmar dake yawo cikin kunuwan shi kullum kanar cewa da tayi;-
*uncle nura ya tafi ya barmu ad'a zamu bishi da ita domin itace kawai gatar da za muyi masa amatsayin munamasoyan shi*.........

Duk ya tuna da wanan kalamai nata sai yaji bugun zuciyar shi ya tsanaita ga yawan faduwar gaba da yake ji duk ya tuna da ita,sai yanzu ya fara regretting abinda ya mata lokacin domin yanzu mugun tausayin yarinyar yake ji duk ya tuna da ita.

Duk ya tuna yadda ya wuto ba tare da yayi sallama da ita ba sai yaji duk babu dadi(nikam nace muje zuwa mallam raji)


Yanzu su jummai sunyi resuming schl ta mai da hankali sosai akan karatun ta domin science class take,duk ta tatara maganan raji ta aje amma duk ta tunashi sai ta karanta ayar nan tare da ambato sunan shi sai taji wani sabon sonshi na kara shigarta.

Suna zaune cikin class during break fast,amina tace besty walahi wani abu ke damuna.

jummai tace tau faddi inji

Tace kinsan cousin brother na da suke lagos farhan wanda na baki labari yace yana sona ina masa wulakanci?

Tace sosai ma

Tace yanzu na fara sonshi har mun dai daita dashi,ammma kinsan daddy ya hananj kula samari sai na gama karatu har na samu aiki?

Tace nafa sani besty

Tace ranar mami ta kamani muna waya da farhan,ina faman fadin i miss u alot,i love u.

Umma ta amshe wayar ta kuma fada ma daddy duk abunda taji,fada sosai yayi kamar zai dake ni,yayi season wayar sanan ya kira abban farhan akan wai a ja masa kunne kada ya bata masa diya karatu zanyi.

Jummai tace yanzu duk dangan takar dake tsakanin dady da abban farhan haka ya rufe idanu ya ci masa mutunci?

tace hmmm baki san halin dady ba game da boko ko uwarshi yana iya cima mutunci da balle yayanshi.

Tace Allah kyauta,yanzu gobe zan shigo da phone dina schl sai kiyi masa text na ban hakuri maybe ya kira kima sai ku shirya yadda zaku rinka magana.

amma ba hujja vace ace wai sai mace baliga ta gama kadatun neman duniya sanan tayi aure,duk wani banna da zai auko a lokacin fa iyaye nada babban share nasu na zunubi.

Yanzu ma akan abinda muke da'awa kenan kauye da birnin kwana kin nan zamu fara tafiye tafiye da ameera na area council.

Amina tace gaskia ya kamata idan so samu ne har gidanmu ki turo su suhi ma su daddy wa'azi,dan gaski aure nike so fisabililah.

Tace kici gaba da adu'a ain shi aure lokaci ne duk lokacin mutum yayi babu wanda ya isa ya hana abun faruwa,kuma matar mutum kabarin shi.

Tace nagode sosai da shawarwarunki bestiy Allah var zumunci.amin
Any way har yanzu babu wani labari a ban garen uncle raji?

Tace uhmm babu fa sai idan yayu waya da hajia tace mun ai ya kirata yana lfy amma bai tava tambayata ba.

Amina tace kyaleshi walahi karya yace yace bai fara jin wani abu gane dake ba all this while,Allah dai ya dawo dashi lfy.

Jummai tace amin thumma amin.



Raji ya rasa yadda zaiyi har ya cika wata guda kenan a south africa kullum abu sai gaba yake,bashi da aiki sai tunanen jummai,sai yabaf abun akan tausayinta da kuma rashin mutuncin da ya mata yasa yake yawan tunanenta.

Dama gida aka basu,da yaje lecture ya dawo,yayi wanka dama ana basu duk irin abincin da suke so,ya kwanta ya huta sai idan ya gaji da tunane yaje zaga gari...

Duk ya kira hajia yana son tambayar jummai amma girman kai ya hana.

Jummai na kwance tana bacci bayan sun dawo daga wani kauye kuta wurin yawon da'awar su,taji wayanta na ringing.
Tana dubawa taga new number ;sallamu alaikum
Allawiya tace jummai don Allah kizo yanzu

Tace lfy Allawiya?

Ta fashe da kuka va lfy ba dan Allah jummai duk abinda kike yi ki bari kizo gidana yanzu.

Tace subhanallahi meke faruwa?

Tace kedai kizo
Tace tau gani a hanya.

Shiryawa tai cikin Riga da skirt na material milk colour da farar hijab ta fito

Umma zanje gidan allawiya yanzu ta kirani da dukan allamu tana cikin damuwa.

Tace tau ki gaisheta Allah sa lafia sai kin dawo.

Tace tau,adaidaita ta tsare ta fada mashi tunga lowcost
Yace hajia kudin ki dari da hamsin
Tace muje mallam.

Haka ta matsu bata isa gidan ba.

Tana isa da sauri ta fito tare da bashi kudinshi,ta bude gate din gidan cikin sauri.
Nocking din part na allawiya tai,tace shigo a bude yake.

Shiga tai komi kaca kaca,ga allawiya daga ita sai daura gaba zaune dabasss saman tiels.

Tace yar uwata menene ke faru dake?

Tace na shiga uku ummai ashe alhaji saddat ba mutumin arziki bane,makaryaci,ma yaudari,mazinaci,azzalumi ta kara fashewa da kuka.

Jumma tace calm yrself,ki natsu ki warware min abinda ke faruwa.

Tace da farko da ya fara neman soyayata naki amincewa su farry suka zugani akan yana da arziki in amince naci arziki,haka muka fara tun bana jin sonshi cikin zuciyata daya fara mani hidima sosai na fara mugun sonshi,duk wani abu da nake so na mure rayuwa yana min,har ya fada nemana da fasikanci da farko ban amince ba ya nuna aurena zaiyi duk da haka naqi,su farry suka yita zugani har na vashi kaina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login