Showing 21001 words to 24000 words out of 64084 words

Chapter 8 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt

sada su da wata kofa ta nan suka shiga babban palour ke ka'sa,a gefe dinning area,daga sama kuma đakuna ne.

Tace zauna best friend bara inma mami magana.

Tace tau

Saman tahau tare da bude kofar wani tangamemen master bedroom,tace sallamu alaikum ya mami.
Tace wa'alaiki sallamu ya nurul qalbi,ya schl din?

Tace alhamdulilah mami,best friend na palour.

Tace so serious, muje tau.
Tana gaba mami na bayanta,takunsu taji tabar kale kale tare da saita kanta.

Sallama mami tai,jummai ta amsa tare da zamewa kasa"ina wini mami?

Ta đagota tare da rungumeta lfy lau my doughter, ya schl?

Tace lfy lau mami
ya parents naki da aysha?

Tace duk suna gaida ki.

Tace barakallah masha Allah yau gani ga doughter,feel at home kinji mun zama daya.
tace thank u ma.
Tace gashi abban ku na office ku karasa ciki kuci abinci.

sama suka haura room na amina,room ne babba ya gaji da tsaruwa sai sanyin AC ke tashi,chest of drower ta bude fa ciro wayarta kirar samsung galaxy S4 ta kuna,tace bara na watsa ruwa muci abinci ko?
Jummai tace take yr time.

Toilet ta fada ta sakar ma kanta ruwa data fito ta saka duguwar riga armless yellow tare da fesa turare tai hanyar kitchen,tray babbata shako cike da kayan abinci ta dire saman center carpet,tace bismillah bestiy.

Saukowa jummai tyi amina tayi serving nasu fried rice with pepper chicken sai cabbage roll da coco nut juice.

Suna ci jummai na santi har suka kare amina ta tatara kayan ta mayar kitchen.

Gallary wayarta ta bude suna kallon picture suna hira.

Jummai tace bestiy amma abincin nan yayi sweet fa?

Tace ai mami ba daga nan ba wurin cooking

Jummai tace u mean ita ke cooking?
tace sosai ma ai mu bama da yanu aiki mu keyi.

Tace a gaida mami gaskia tai kokari.

4:0pm bayan sunyi sallah jummai tai musu sallama,amina taace bara ki kwana ba?

Tace haba bestiy ban fa cema umma kwana zanyi ba.

Tace ai bara tai fada ba idan ma kwanan kikayi.

sallama tai ma mami,sha tara ta arziki mami tai mata tare dasa driver ya mai data gida.

Aysha tayi interview a sa'a har sun bata admission medical laboratory technician suka bata da kyat aka samu kudin registeration ta fara karatu gadan gadan,wata rana ma a ka'sa take zuwa before ta isa tayi late,wani lokaci ta dawo ka'sa haka rayuwa ke tafia.

Su jummai ma anyi hutu sai shirye shiryen auren allawiya suke,lefe akwati set guda aka kawo kaya sun hadu matuka.

Jummai tace yanzu allawiya da gaskia kin bar karatu dan kiyi aurr?

Tace sosai ma ai ban iya bari gayen nan ya kufce min.

An fara hidimar buki kawayen allawiya yan duniya duk sun halara inda su farry suka kama hydro hotel da amarya nan zasu zauna har a gama buki,party kala uku suka hada banda wanda ango ya hada.

Jummai kam jaye jiki tai har suka gama gudun wulakanci da rainin arziki,kai amarya kawai taje,kamar yadda amarya tasha kyau haka gidanta babu abinda ba'i saka mata ba daga ita sai akwatunanta tazo.

Aysha sun rubuta weeding exams yanzu hutu suke yi,suna zaune around 4pm suna hira da jummai umma tace kwana biu dan nan shiru bai wai wayemu ba ko lafia?

Aysha tace walahi kuwa umma kwana biu ma bamu ziyarci hajia ba sis shirya muje.
tace tau,umma tace ai kuwa kun kyauta..

Shiryawa sukayi suka kama hanya,suna isa mutane suka gani makil kofar gidan.
aysha tace subhanallah meke faruwa?
Jummai tace sai mun kara sa.

Suna isa sukai gaisuwa,m.raji jummai ta hanga zaune tsakiyar mutane duk ya susuce idanun nan sunyi jawur.

Suna shiga cikin gida hajia ce zaune cikin mutane da cazbaha a hannunta.
gaisheta sukai,aysha tace rasuwa akai ne hajia?

Ta fashe da kuka tace mun rasa nura,ubangiji ya dauki abinshi.

Jummai garin yaya?

Aysha innalilahi wainna ilaihi raji'un.....


*L££MA*✍🏻

*BRILLIANT WRITERS ASSO*... ✍🏻


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*QURUCIYAR JUMMAI*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L€€MA*✍🏻


*EDITED BY:SURAYYAHM S*





*47-48*



HAJIA tace nura ya rasu aysha lokaci yayi sai adu'a

Sallati aysha keta maimaitawa, jummai ko jugum tai kamar Matata domin mutuwar yai mugun tabata.

Aysha tace dama yai rashin lfy ne?

Wata yar uwar hajia tace yadda abokanshi suka bada labari lafia lau suka yini cikin dare matsanai cigar ciwon ciki ya tadda shi daga bacci kafin su isa asibiti nura ya cika da kalmaar shahada tare da neman gafarar Kowa.

Hajia ta kara fashewa da kuka tace nura ya tafi ya barmu da kewar sa,ya bar dan uwansa cikin matsanaiciyar tashin hankali domin raji haihuwar nura ne kawai bai Yi ba amma duk wani abu da iyaye kan ma dansu raji ya na nura babu irin gata da kulawa da Bai bashi ba ashe kwana kinsa ragagu ne.

Talatu yar uwar hajia tace bari ai raji na cikin tashin hankali domin yayi babban rashin dan'uwa kuma amini.

Hajia cikin kuka tace ina kika san yana cikin tashin hankali ma Wanda tun jiya da aka dawo da gawar nura idan banda kuka babu abinda yake yaki ci,yaki sha yaki magana da kowa ko gaisuwa aka masa bai iya amsawa sai kuka har yanzu aikin kebab.

Aysha tai nanauyar ajiyar zuciya tace haka ne hajia idan lokaci yayi babu Wanda ya isa ya hanaka tafia,duk wani kuka, rashin cin abinci bashine zai kawo saukin radadin da muke ji a zukatan mu ba aduar mu kawai ita yake bukata, kuma itace gatan da zamu masa a matsayin muna masoyan shi.

Hajia tace haka ne Aisha, jummai dai jugum tai duk gabobinta sunyi sanyi nura take gani a idanunta, tare da tuna moments din da sukayi spending tare lokacin tana cikin QURUCIYAR ta.

Adu'a sosai aysha tai aka shafa,tace jummai muje gida magrib ta gabato,mikewa tai jiki ba kwari bata ce da kowa komi ba ta kama hanya.

Hajia tace jummai ai hakuri tabbas keda raji akai ma mutuwa amma sai kun daure Kinji?

Daga kai kawai tai,suka kama hanya.

A kofar gida maza har Sun fara always, raji suka gani daga can gefe misa dakali zaune da buta a gabanshi da dukan alamu alwala zai amma ya tsaya shiru sai hawaye ke tarara a kyakyawar fuskar nan nashi.

Jummai ta nufi wurin shi kamar tababa maza sai kallonta suke,aysha kuma bata ma Ankara da abinda jummai tai ba.
dukawa tai a gabanshi tare dayin tagumi hanu nabiyu, kura mai ido tai tare da zub da hawaye, tace uncle; nura ya tafi ya barmu adu'a zamu bishi da ita domin itace kawar gatar da zamui masa a matsayinmu na masoyan shi.

Kura mata idanu yayi kamar mai nazarin wani abu,hannuwanshi biu ta rike gam tana zub da hawaye kauda kai yai yana kallon wani gun,ta kara matse hanuwanshi cikin nata tare da cewa uncle pls say something I can't bear to see u in pain,uncle kai ne farin ciki na pls look into my eye and promise me that everything will be alright,uncle plsssss talk to me"cikin matsanaicin kuka.

Aysha tazo ta jayeta,tace manene haka sister ki dawo cikin hankalin ki,baki ganin mutane na kallon ku, ki barshi yaji da abunda ke damunshi mana.

Tace haba sister u won't understand,na fishi shiga damuwa ta dalilin Halin da yake ciki.


Aysha tace haka ne jummai amma ba lalai bane ki fishi damuwa tunda shi jininshi ya rasa,ke kuma masoyi kika rasa.

Tayi murmushin yake tare da cewa sister shiyasa nace u won't understand,bani da masoyi duk fadin duniyar nan sama da uncle, tunda na malaki hankalin kai na na tsinci kaina cikin soyayar shi dumu dumb, tun ban gasgata kai nava ina tunanin zuciyata yaudara ta kawai take Yi, ashe ba haka bane, kullun kwanar duniya da tunanenshi nake kwana nake tashi,nasan na aikata abubuwa da dama lokacin QURUCIYA ta amma yanzu na gane gaskia nayi nadama mai tarin yawa sister ki taimake ni kada son uncle ya halaka ni.

Aisha tace u better wake up from yr fake dream,kin manta dangan takar dake tsakanin nura da uncle NE?
ko kin Manta soyayar da kikai da nura dacan baya?
ko kuma manta wa kikai da irin rashin mutuncin da kika shuka masa lokacin baya?

Tace dangantaka!
Ai ba aurena nura yai ba,kuma addini ya yarje ma uba da da su nemi mace guda aure duk mai rabo ya dauka,bare ko aure na nura yai muka rabo Uncle na iya aure na.

Maganar soyaya kuma niban tava son nura ba duk da ina cikin QURUCIYA ya nemi soyayata bai samu ba bare yanzu dana mallaki hankalin kai na.


Abunda ya faru tsakanina da Uncle kuma ai QURUCIYA yasa na aikata hakan, sanan kada ki Manta sister ko Allah muka ma laifi muka tuba zai gafarta mana Bale Dan Adam.

aysha tace so serious, nidan kinga tafiya ta tunda baki da hankali.

Finciko jummai yai ya tatare hijab nata ya hada da wuyanta ya matse;yace kina hauka NE, dan tsabar rainin wayau saw rashin hankali ki dubi tsabar idanu na wai ni kike so,dan baki da kunya a gavana kike fadin baki son dan uwana wanda ya bar duniya ina cikin bakin cikin rabuwa dashi?
Walahi jummai OR what ever u call yrself na tsane ki,na tsaneki bana son ganinki,bana kaunar kids, bazan taba sonki ba wawiya dakikiya kawai mara imani da tausayi...

Aisha tace
uncle pls kada ka biye mata yarinyace na roke Ka da girman Allah Ka kyaleta plz.

Yace Aisha i hate this girl walahi, I hate seeing her around me ever since that incident occur,daurewa kawai nake ina kyautata mata all this while sabida yar uwata ce musulma.

Magan ganunshi yai ma aysha ciwo kwarai daurewa tai taja hanun jummai domin Jana's sun fara fitowa masallaci kada a fuskanci abinda ke faruwa.

Jummai na turjewa, aysha na qara jan hannunta da zuciya ya dibeta wanke mata fuska tai da mari mai lafia tace kwakwalwar ki ya tabu ne?
Ko kin fara shan wani abu ne, namiji yace ya tsaneki bai son ganin ki dole ne ko shi daya ne namiji duk fadin duniya?
Kamar ki da kyan ki,assali da iliminki har namiji zai fito promp and clear yace yayi hating nake and u are stil wasting yr precious time on him, dallah mu tafi gida to hell with him.

jummai tace sister allow him to kill me, tunda bai son ganina amma walahi bazan bar sonshi ba kuma idan kaga bamui aure ba Allah ne bai nufa ba...

Haka aysha ta rinka janta har suka isa gida,umma tace lfy tun bayan LA'asar sai yanzu?

Aysha da zuciyay ya kai mata ko ina cikin bacin rai tai ma umma bayani tun daga kan mutuwar nura da suka isko har rashin hankalin da jummai tai wurin m. Raji.

Sallati UMMA tai tace Ashe nura lokaci yayi Allah bai nufa yaci muriyar karatun da yayi ba,Allah masa rahama yasa can ya fiye masa nan,yakai haske kabarin sa Amin.

Amma jummai banji dadin abinda kika aikata ba a bainar jama'a kamar ba mace mai hankali ba,haba ina iliminki,tarbiyar ki da natsuwar ki jummai?

ta fashe da kuka umma ya zanyi da rayuwata, na dade ina dakon soyayar shi UMMA, gara na fada mashi gaskia yafi min, dama option biu ne,either ya amince da soyayata ko kishiyar haka.

Tau jummai lalai kina cikin tsaka mai wuya Allah mana jagora kici gava da adu'a kinji auta ta.

Tace umma pls kada kuga laifina bani na daura ma kaina sonshi ba Allah ya daura min.

Aysha tace na fahimce ki sister zan tayaki da adu'a, suka rungume Juna,aysha tace see u ba kunya ni yayar ki naki ydda da soyayar kowa amma as little as u are kin san soyaya silly girl😍

Daria jummai tai,umma tace bana Son kowa yasan da maganar nan hata baban ku,mu barshi tsakanin mu kunji?
Suka amsa tace kuje kui sallah kuxo kuci abinci...

Suka Mike zuwa daki,jummai ta Dade cikin sujada tana kwararo adu'ar neman zabin Allah akan soyayar ta da uncle daga karshe tai ma NURA adu'ar neman rahamar ubangiji..


Shawar wari aysha ta bata akan yada Zata shawo kan uncle cikin ruwan shanyi.
Sosai jummai taji dadin shawarwarin yar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login