Showing 57001 words to 60000 words out of 64084 words
Chapter 20 - QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt
material mai laushi milk colour aka fitar mata dashi riga da skirt ,idan tayi sallar isha'i shi zata saka..su amina anata faman hada kaya sabida daga gidan amarya gida zata wuce.
Bayan sun yi sallar isha'i,aka had'a mata turare na garwashei,na jiki ta rufa da bargo ta turara jikinta,sai na tsuguno ya shiga jikinta da kyau,aka cika mata cup da nonon rak'umi ta shanye duka,ai tsumin 6aure shima tasha....anty balki ta shafe duk wani lungu da sak'o na jikin jummai da humra..oya sa kaya ki ganni lokaci na tafiya,sai jikinta yayi sanyi duk wani matsuwa da tayi na ganin ta koma gidan mijinta taji bata ma son barin gidansu,kuka ta fashe dashi..nafisa tace ba ke bace,ina matsuwa kikayi baki tafi ba?aysha ta fara hawaye ku bari mana,sister shirya baba na jiranki...haka ta saka kaya jiki ba kwari,amina yan son make up har ta jawo kayan zata fara shafa ma jummai...anty balki tace No ai babu make up yanzu haka zata tafi anty make up artiste..akayi dariya duka.
Dakin baba aka kaita,dama umma na ciki da sauran kawun nan jummai na kauye...nasiha sosai akayi mata mai ratsa zuciya sai kuka take hadda sheshek'a..umma ma sai da tayi kwala.
Baba yace ku hanzarta suna jiranku,Allah sa aje a sa'a.amin cewar anty balki.
Motoci ne na kece raini kar guda biyar na daukar mutane zuwa gidan amarya...anty tace su wuce ita zata dauki amarya a motar ta zuwa gidan hajia ta damk'a amanar jummai,sanan ta wuce da ita gidan ta...haka akayi jummai dqi kunshe cikin lafaya sai kuka take sha da kyar aka banbare ta jikin umma,ta koma ta rungume aysha suna kuka da kyar aka rabasu,dan aysha tace bata iya binsu sai dai taje gobe..jummai da amina na bayan motar anty balki,allawiya na gaba,nafisa mijinta bai bata izinin zuwa ba..haka take ta rusar kuka har aka isa kofar gidan hajia.
Da sallama suka shiga,hajia ta mik'e tare da kamo hanun jummai ta zaunar da ita a kusa da inda gwagwanin Raji ke zaune..hajia tace bari kuka d'iyata haf'in Allah ne banq mutum ba fatan mu Allah ya sa maku albarka a zaman ku,ya azurta ku da zuri'a d'ayiba aka amsa da amin..anty balki tace ga amana nan mun kawo maku na d'iyar,yarinya ce don Allah idan tayi ba dai dai ba a tsawata matq.
Suka amsa mun amsa hanu biu biu Allah taya mu rik'o,haka akayi tama amarya nasiha daga nan aka wuce da ita gidan ta..duk abunda ake yi Raji na dakin su na samar taka ya kulle kansa sai rusan kuka yake yi,ya tuna da dan uwanshi"Nura"yana ganin bai kyauta ma nura ba da ya auri jummansa,babynshi.
Koda suka isa gidan jummai mutane sun rage..da kafar dama ta shiga aka aje ta tsakiyar gado tana ta sheshekar kuka..haka suka zare jiki allawiya mijinta ya fara zuwa suka wuce,anty balki ma ta zare jiki ta matsu bata koma wurin mijinta ba daga ita sai amina sukayi saura.
Abokan ango sun yita kiran wayanshi a kashe,hajia akq kira tace baya gida sosai hankalinta ya tashi...ga dare nayi ba a ga ango ba..hajia tace suzo gida tana son ganin su...nan ta tambaye su ina da ina suka san yana zuwa??..kowa yace babu wqni dogon yawo da suka san yana yi...muktar yace a duba dakin shi mana..haka kuwa akayi yaci kuka har yayi bacci.koda aka ta6a jikin shi zafi rau...hajia tace da dukan allamu bai jin dad'i ku bashi yaci gaba da baccin shi,ku kira min jumman a waya.
Amina kam har ta gaji da zama,ba ango ba dalilin shi gashi tana son zuwa gida..can suka ji wayanta na ringing,amina tace Allah sa lafiya hajia ce mai kiran...jummai ta dauka da sallama muryar ta ya dashe...kina jina mijinki bai ji dad'in jiki ba yana kwance yar yayi bacci kina iya kwana ke d'aya ko zaki dawo nan ki kwana dashi???A'a hajia amina na nan zamu kwana tare Allah bashi lfy,ta kashe wayar tare da fashe wa da sabon kuka.
Amina tace what again???..cewa tayi bacci da lafiya wai har yayi bacci,wai dqn wulak'anci nida mijina har hajia na tambaya ta idan zan zo na kwana dashine kl zan iya kwana ni d'aya a k'aton gidan nan,i hate him walahi...haba ki dawo cikin hankalin ki mana,nasan mijin ki yadda yake son ki bazai shirya komi on purpose ba....haka tay ta bata magana har tayi hakuri suka yi bacci.
Can gidan kuma basu runtsa ba kowa na tunanen halin da raji ke ciki"shiko hankali kwance yake baccin sa"...sai lokacin sallar asuba suka tashi wanka sukayi tare da gabatar da sallah,bayan ta idar suka zaga gida lokacin jummai taga yadda iyayenta quka yi namijin k'okari wurin gyara mata gida...suna zaune a palour ne aka yi sallama..faruk ne abokin raji ya shigo da flask da kula daga gidan hajia.
Bayan sun gaisa,amina ta tambqye shi jikin raji?yace yaji sauk'i damq strees ce kuma ya warware...Allah k'ara tsare wa..amin amarya bakya magana ko?murmushi tayi.
Haka suka yi breakfast mutane nata zuwa ganin gidan amarya..hadda dangi na nesa both fanin ango da na amarya...aysha ma tazo lokacin amina rayi masu sallama ta wuce gidan.
Sai da suka ke6e take fada ma aysha abunda ya faru jiya...hakuri ta k'ara bata tare da shawarwari.
A gidan hajiya kwa bayan yayi wanka ya karya,hajia tace ya tashi ya bar mata gida tunda abun ya zama lalaci,baya son zuwa gidan shi haka ya shirya ya koma gida da tawagar abokanshi... tana zaune suna hira da aysha ne quka ji tsayuwar motoci a harabar gidan,aysha ta lek'a,tqshi ki gyara mijinki ne da abokanshi...gyara fuska tayi ta canza shiga cikin hanzari tare da rufa babban gyale....da sallama suka shigo palour tare da zazaunawa aysha ta fito suka gaisa...raji yace tai ma jummai magana ga abokanshi sun zo mata sallama zasu koma abuja.....kamo hanun jummai tayi suka fito tare,ta nemi wuri suka zauna,bayan gaishe gaishe,akayi adu'a tare da fatan alheri,nan suka mata sallama aysha tace itama ta tashi tunda yamma tayi su aje ta gida..nan idanun jummai ya cika da hawaye,haka suka mata sallama.
Bayan ya rakasu bakin gate ya dawo ciki tan zaune inda ya barta...zama yayi a hanun kujeran ya rungumo ta ya isa haka menene akayi maki?..bakai bane jiya ka k'i zuwa..shh ya isa haka nan gashi na dawo bazan sake barin ki ba i promise...haka yaci gaba da rarashin ta har aka kira sallah ya wuce masallaci..gyara gidan ta k'ara yi ta shiga wanka tare da yin alwala, sallah ta gabatar..rigar baci ta saka mai laushi har guiwa ta daura hijab mai hannu har k'asa...daya fito daga masallaci ya biya k'asan layin su ya sayo gasasun kaji biyu da exotic,ita ya saya mata hollandia yoghurt...da sallama ya shigo tun daga palour kamshi,dakin da yaji karatun Qur'ani na tashi nan ya shiga,zaune take saman salaya rik'e da Qur'ani tana karatu....hamdala ya k'ara yi cikin zuciyar shi,sai da takai aya ta aje...sannu da shigo wa,yauwa baby na barka ke d'aya ko?ba komi ai.
Kamshin turaren nan na gida yamin dad'i sosai..murmushi tayi,dauko plate muci abinci ina palour...plate ta dauko da cups zuwa palour saman center table ta ajiye..yace yi serving namu mana.
Ta cire kazar saman plate tare da yanyankawa....ki cire hijab din mana..cikin jin konya ta cire,yana ta binta da kallo sai kamshi mai sanyi yare da saka nutsuwa ke fita daga jikinta,haka sukayi feeding na juna har suka k'oshi,ta kwashe kayan.
Ruwa ta hada mashi yayi wanka,tare da zira jalabiya ya dawo palour,nan ya sameta zaune shiru...yadai ko kina kewar umma ne?kaman ka shiga zuciyata uncle..uhm sai dai kiyi hakuri haka aure yake,hira yake ta yanta dashi tana kwance a jikin shi har suka fara jin bacci ya kashe komi tare da rufe kofa....dakin shi suka shiga ya yaba kwarai da tsarin d'akin...alwala ya umurce ta da tayi suyi nafila,haka a kayi raka'a biu suka gabatar,ya kwararu adu'oi na neman tsari da zaman lafiya..bayan sun gama ta suka haye yago ya jawota jikin shi tare da kashe wuta,sai da ya bari ta saki jikinta ya fara wasani da ita cikin natsuwa,bayan wani lokaci yayi adu'ar saduwa da iyali..iya dauriya jummai ta yishi amma taji jiki sosai,bayan komi ya lafa yayi ta sa mata albarka tare da adu'ar Allah basu zuri'a d'ayiba....cikin natsuwa da kwanciyar hankali suke rayuwa jummai bata da matsalar komi sai dan abunda ba a rasa ba har mijinta ya koma bakin aikin shi da kuka suka rabo...
*BAYAN WATA UKU*
Result nasu jummai ya fito yayi kyau sosai,har gida taje ta kwada ma su umma da baba sunyi farin ciki...aysha ma sun fara rubuta final exams yan gidan su abdul sun zo maganar sa ranar aure..aka saka wata biyu bayan ta gama exams.
Jummai takai ziyara gidan hajia kus1n sau biyu,taje gidan anty balki da yake shiya guda suke(london street)sai ta zama uwar d'akin jummai...Ranar da ta kai ma mami ziyara murna sosai tayi domin jummai ta zamma babban mace,ta k'ara kyau da waye wa..tace ma amina ai nayi fushi tun da kika zo gidana sau uku baki sake zuwa ba...haba besty ku d'in ne baku da dama keda mijinki,soyaya kamar ku cinye junan ku,kuma mun fara waec shi yasa..haka ta yini sai yamma ta koma gida...
Matsala na farko da suka fara fuskanta raji yabar zuwa weekend yanzu idan tayi magana yace aiki ya masu yawa,tayi masa maganar komawarta schl da zaman banzan da take yi a gida yace bai abince ba,ko islamiya haka suka yi kaca kaca a waya ta kashe wayarta gaba daya.....
*LEEMA*βπ»
*βBRILLIANT WRITER'S ASSO...*π
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
π·π·π·π·π·π·
*QURUCIYAR JUMMAI*
π·π·π·π·π·π·
πΈπΈπΈπΈπΈπΈ
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*βπ»
*wanan shafi naku ne;QURUCIYAR JUMMAI FAN'S GROUP*
*kun nuna min k'auna,ina jin dad'in adu'oi'n ku a gare ni,Allah bar zumunci ya had'a fuskokin mu a aljannah fir'dausi amin*π€π»ππ»ππ»
*73-74*
ππππππππ
A bangaren raji kuma wani lokaci haka kawai yake jin ya tsani jummai musamman ya tuna da abunda ta yi mashi lokacin"QURUCIYAR TA"sai yaji baya ma ko son ganinta shine dalilin shi na rashin zuwa gida har aka share wata guda'''Idan ya kad'ai ta abun na mugun damun shi sabida yasan yana son matarshi,yana mugun kewar ta,sanan bata masa laifin komi ba,tana iya kacin k'ok'arinta wurin kyautata mashi'''idan hajia ta kira shi sai dai yace aiki ne ya masu yawa.
Jummai kuwa ta kashe wayarta gaba d'aya'''ta mik'a lamura nta wurin Allah''babu wanda yasan halin da take ciki'''adu'oi take yi sosai da nafilfili.(idan kika rasa gane kan mijin ki,kyautata alwala kiyi nafila raka'a biyu,idan an idar a karanta aya ta goma a cikin suratul khafi( sau 313)haka kuma
Imam Dairabi yana cewa duk wanda ya lazamci wanan nafila raka'a biyu bayan sallar magrib (ana yinsa ne akan ko wace irin buk'ata na alheri); ko wace raka'a ki karanta fatiha da kulhuwallahu kafa bakwai(7)idan anyi sallama a karanta "ya samadu"kafa(104)insha Allahu bukatar sa zata biya.
Haka zalika idan kana so Allah ya yaye maka wani bak'in ciki da kake ciki '''sai kayi sallar nafila raka'a biyu''bayan fatiha a ko wace raka'a sai a karanta wanan aya kafa(7)Rabbanakashif anna azaba anna mi'uminun''bayan anyi sallama sai ayi adu'i Allah zai yaye.
Sai wanan wanda ya zame ma jummai kamar farilla.
Idan ana son jawo hankalin mutum duk inda yake ya dawo gida(idan ma 6ata yayi,ko asiri,ko sammu aka masa)sai ayi sallah raka'a biyu ko wacce raka'a fatiha da innahu ala rajihila qadir sau(41)bayan ayi sallama sai a karanta innahu ala rajihi laqadir sau(313)idan an gama ayi adu'a abunda ya sawaka insha Allah za a ga abin mamaki'''haka ta ri'k'a kai kukan ta wurin Allah
Rana tsaka Allah maji ruk'un bawa ya amshi adu'ar ta,tana kwance saman three seater a palonta rik'e da chasbaha a hanunta tana lazumin"tuna wa tayi da abunda ya faru jiya tsakanin ta da aysha''' har gida aysha tazo ta fada mata hajia ba lafiya jiya suman ta uku a general hospital akayi admitting nata hada k'arin jini,abdulrahim ya bada jini,anyi ta kiran raji bai d'aga ba tazo tambayan jummai ko lafiya??...take ce mata lafiya lau,aiki ne ya masa yawa amma insha Allahu zai zo week d'in nan''ta nemi da jummai ta biyota suje hospital'''tace A'a sai ya iso zasu tare'''nan suka rabu baram baram wai jin dad'in aure ya sa jummai ta canza rayuwar ta kwata kwata,bata waya da kowa,bata zuwa gidan kowa yanzu,har yakai da tazo har gida ta fada mata rashin lafiyar surukar ta,tace bara ta ba sai mijinta ya dawo''''tayi ta ba aysha hak'uri,amma ina da fushi ta fita daga gidan jummai'''jummai ta shiga rera kuka na bak'in ciki'''ta ya zata fita bada izinin mijinta ba,menene amfanin wayarta tunda kota kira mijinta mai d'aga wa'''Allah take rok'o ya kawo mata karshen wanan jaraba wa da yayi mata.
Alamar tsayuwar moto taji a compound na gidan'''bata damu da ta duba ba tasan bai wuce amina ko allawiya suke yawan kawo mata ziyara,domin Alhaji saddat ya saya ma allawiya k'aramar mota sabida fita anguwa tunda ba zama yake yi ba'''nocking kofar palour taji anayi''da sauri ta share hawayen da ya zubo mata''shigo a b'ude yake''da sallama ya shigo cikin razana ta mik'e tsaye!!!
Sanye yake da suit ash colour,hanunsa dauke da brefcase''''daga ganinsa kasan hankkalinshi kwance sabida babu alamar damuwa a tatare dashi''''da gudu ta shek'o tayi hugging nashi cikin matsanaiciyar kuka'''tana dukan k'irjin shi da hanuwan ta duka biyu''why why uncle ka manta alkawarin daka dauka akan bara ka taba juya min baya ba,menene nayi maka da zafi haka da kamin irin wanan hukunci,na wahala sosai a dalilin rashinka 2months is not a joke uncle,kwata kwata fa wata na biyar kenan a gidan ka,shekara guda kuma da daurin auren mu,ashe haka aure yake,duk yadda kuke son juna kake kyautata ma mijinka sai shaid'an yasan ta inda zai shiga tsakanin ku yaga ya wargaza farin ciki da jin dad'in ku,yaga ya lalata aure,walahi ba zai tab'a yin gala6a akan mu ba'''tsaye yayi kaman gunki yana sauraren ta domin kam lalai sai shaidan'''a iya saninshi babu abunda tayi mashi na rashin kyautata wa'''ajiyar zuciya yayi yana mai zub da hawaye baby ki yafemin ban kyauta maki ba,nasha yi maki alkawari bana cika wa but insha Allah komi ya koma normal daga yau bazan sake barin ki ba tare zamu koma abuja ''''kinga na dauko annual leave na wata uku'''aaba uncle ni baka min laifin komi ba jarabta ce ta ubangiji kuma nayi tawakali a matsayina na musulma,ka dena kuka mana.
Ya k'ara rungume ta '''tun a palour ya fara hot romance da ita''cikin duba ra ta jashi zuwa room nashi''sun kai awa guda ana abu d'aya''tabbas sunyi missing junan su'' sun samu natsuwa alhamdulilah'''wanka sukayi ta dafa masu indomie da kwai suka ci'''sai data tabbata ya samu natsuwa take fada mashi hajia na hospital''subhanallah tun yaushe??aysha tace tun jiya hadda k'arin jini aka mata'''tashi ki shirya muje'''nagode sosai da kika tsare min kanki a inda na aje ki,Allah maki albarka amin.
A hanzarce suka isa general hospital minna,aminity ward room 6,tun a waje suka fara haduwa da yan uwa maza na can kuta ana ta gagaisawa,dak'in cike da yan uwa maza da mata,bayan an gagaisa ne yake tambaya wane likita ke duba ta?nurse ta nuna mashi office na likitan''bayan sun gaisa,yace shine yaron mara lafiyar dake aminity word room 6,yau yazo daga wurin aiki'''file nata likita ya dauko tare da mik'a ma raji,ya gama dudubawa bai gane komi ba''''yace i need more clearification doctor'''blood cancer ke damun mahaifiyar ka,a bincikin da muka yi ne muka gano ya dad'e a jikinta sosai''what blood cancer hajia how,when???
Be a man'' kada ka tadda hankalin ka jiya brother baka abdulrahim ya bada jini anyi mata k'arin jin,sanan mun daurata kan magunguna lasu inganci insha Allahu zai lafa''yanzu doctor u mean bazai warke gaba dayq ba sai lafawa??wanene ni da zan yanke hukunci,Allah kadai yasan gaibu'''amma gaskiya mostly masu fama da irin ciwon basu cika warke wa ba sabida ya riga da ya lalata jini dake cikin cikin su,gradually zai lalata duk wani organ na jikinsu har akai ga rasa mutum'''mostly abunda ake masu suji saukin abun for some years shine a fita dasu k'asashen waje a kwashe jinin da ke jikin su a zuwa wani jinin''''amma yanzu doctor kana ganin ita idan aka mata zata warke??i ca'nt predict sai abunda Allah yayi''mutuwa da rayuwa duk tana hanun Allah..ina so ayi making arragement for her zamu fitar da ita waje''''doctor ya kali raji up and down zaka iya kashe wayan nan kud'ade kuwa?...me ka dauke ni talaka ko me?bara kaji koda duk abunda na malaka zai k'are sai na nema mata magani'''it ok since u said so,i will make an enquiry,what ever is their i will let u know...
Ko da ya fito ya samu abdulrahim zaune a saman wani beanch yana latse latsen waya''gaisawa suka yi,ya mashi godiya sosai akan taimakon da yayi masu''''haba an zama daya ai''nan raji ke fada mashi abunda doctor yace'''hakan ma yayi dai dai,idan ana bukatan wani taimako dai feel free to ask me''insha Allah zamu yi iya kacin kokarin bada duk wata gudun mawa muga an samu ci gaba ta fanin lafiyar ta''''nan suka zauna suka tattau nawa sabida tun da aka mata alluran bacci da safe har yanzu bata farfad'o ba..
Cikin d'aki kuma jummai ce raku6e a gefe ta rafka uban tagumi tare da zuba ma hajia idanu''sallaman aysha suka gani tana dauke da basket na abinci,umma da maman allawiya na bayanta''ko kallon jummai bata yiba a dole fushi take da jummai,bayan an gagaisa ne''''yan uwan raji keta ma umma godiya akan yadda suka tsaya tsayin daka suna bada gudun mawa yadda ya kamata''''tace babu komi ai an zama daya''sai da suka ke6e da jummai umma ke fada mata tunda kwana biyu taki zuwa gida,ga wayanta bai zuwa ana ta faman shirye shiryen auren aysha,karshen wata za a kawo lefe da sadaki''murna sosai tayi,tace insha Allah zata shigo kafin lokacin''ta kali aysha sister don Allah ki yi hakuri idan nayi maki ba dai dai ba,bani da wata yar uwa duk duniya sama bake,kefa kika ce nayi biyaya ga mijina,na zauna inda ya ajeni komin runtsi kuma na 6oye sirrin mijina?ya kamata ki fahimce duk abunda nake yi ya zama min dole ne ko dun kare mutuncin aure na''ta share ma jummai hawaye na fahimce ki,fatan komi ya dai dai ta tsakanin ki da mijin ki?gyada kai tayi''masha Allah,Allah kara rufa asirri ya baku