Showing 81001 words to 84000 words out of 126557 words

Chapter 28 - MIJIN MALAMA Book 2 Complete by Nimcey Sarauta .txt

suka buɗe, ta fahimci kuma zancan nashi a cikin kallon ta ce "May be yunwa kake ji, bari na fara kawo maka black tea" Bai ce mata komai ba ta yunƙura zata tashi ya cafko ta tare da dannewa ta yi ƙara ta ce "Our unborn, Khalil" Ya cire ƙafarsa daman he just wanted to hear her shout, dan bai taɓa jin tayi ihu ba, ya danneta underneath his breathe yana murza hancinsa akan nata ya ce "What food?" Ta zare Idanu jin da ƙarfinsa yazo this time ta riƙe shi ta ce "Bari ka fara cin abinci" Daidai kunnenta wanda ba lallai ta ji me ya ce ba, ya furta "I love food, but u're sweeter than food, I'll eat and eat and eat..... And won't be tired" Yana faɗin hakan ya kashe switch ɗin bedroom ɗin... Khalil na zaune a parlon part ɗinsa akai knocking door, yadda akai bugun a hankali yasan ko wacece, yana daga zaune ya sanya remote ya ɗan danna kafin a gajarce ya yi gyaran murya "Uhm" Ta fito a sirrince. Handle ɗin Ƙofar aka buɗe tare da shigowa ɗauke da sallama da muryarta mai cike da kamala, waje ta nema ta zauna a ɗan nesa da shi jin tayi shiru ya ɗago daga operating system ɗin da yake ya zuba mata narkakkun idanunsa wanda suke a lumshe, sai Kuma ya ware yana murza yatsunsa, ta fahimci me yake nufi calmly ta ce "Kazo down stairs" Ya sake zuba mata Idanu sai ya ɗauke kai yana danna system ɗin bayan ya kammala tura saƙon da zai tura kafin ya kashe ya ce "For?" Jee ta ce "Idonka zai gane maka" Vidcall ne ya shigo cikin system ɗin ta Khalil ya ɗaga da ɗan sauri fuskar wata ƙyakƙyawar matashiyar yarinya ta bayyana wacce zata iya 15 ko 16 ta ciki ta ce "Hi Spider" Fuskarsa ta faɗaɗa wanda ya sanya dimples ɗinsa bayyana a fili speaking calmly Khalil ya ce "Faɗimatu how far?" Tayi murmushi ta ce "Not good without u" Ya yi dai murmushi, ta ce "I missed you so much, na amshi ipad ɗin Uncle na kira ka" Khalil ya ce "Is he there?" Ta ce "Sure, yaushe zaka zo mun yi missing naka sosai" Khalil ya kalli Faɗimatu sosai ya ce "I'll come dear" Majeederh tayi saurin miƙewa ƙirjinta na ɗagawa har wani duhu take gani cikin idanunta ya miƙa hannu zai riƙota tayi saurin ficewa, Khalil ya shafa kai ya ce "Kin kori Matana Fattuma" Ta dinga dariya cike da ƙuruciya kana ta ce "Bye" Ya kashe tare da miƙewa tsaye, three quarter ne jikinsa mai kyau sai Gymashark sports t.shirt a jikinsa ya ɗora bandana exlty yadda Aberdeen Abduljabar Abbas ke shigarsa, ƙafarsa cikin Mon mule slippers ya nufi downstairs, da ɗan sauri yake harhaɗa steps ɗin benen wajan sakkowa, Majeederh kawai ya gani tsaye gaban deep freezer ta sanya hijab har ƙasa hannunta riƙe da boner tana haɗa turaren wuta, a hankali ya nufi inda take without making any sounds da zai nuna mata gashi nan, yana zuwa ya yi saurin ɗaga hijab ɗin tare da shigewa ciki ai kuwa ruff ya shige kasancewar babba ne hijab ɗin, da sauri Majeederh ta saki ƴar ƙara tana ƙoƙarin sakin boner ɗin jin mutum zuruf cikin hijab, a tsorace tana riƙe kanta tare da sauke numfashi da sauri da sauri kamar wacce ranta zai fita saboda jin abin da Khalil ke mata, daman yau taga take taken shi tunda ya ce babu inda za shi, ya tashi da wani masifar shan ƙamshi kuma sai a yanzu ne ta fahimci yadda ya samu gadon miskilanci jinin sarauta na zagaye a jinin jikinsa ga uwa uba halin Ummi dana Dad daya kwasa abu ya haɗe masa goma da ashirin, jikinta ya ɗauki rawa da ɓari jin a hankali ya sutale ƴar rigar dake jikinta zuwa ƙasa , tayi saurin ajiye boner ɗin tana riƙe rigar ganin ta hanata faɗuwa.


Debeka data sakko hannunta riƙe da handbag da waya kamar sauri take zata fita, harta gilma sai kuma ta tsaya sbd jin sukur sukur da take ga ƙamshin Khalil daya cika parlon, ta jima tsaye tana kallon Majeederh ganin yadda ta ƙara zama ƙatuwa, gently ta ƙarasa da nufin taɓa Majeederh ta ɗan bubbuga bayan Khalil da zaton na Jee ta ce "Hi" Cak! Majeederh tayi zuciyarta ta ɗan daina aiki na wasu daƙiƙu numfashinta ya fara ɗaukewa, da ƙyar ta saita kanta ta ce "Uhm" Debeka tayi tsaye ganin Majeederh bata juyo ba sai kuma ta ce "Na kira number sweetheart, baya ɗauka ki ce masa na ɗan fita....," Wani emotional sounds Jee ta saki tana yarfe hannu, sbd wani abu da Khalil yayi mata da bata taɓa tunanin akwai shi ba, tana jin yadda yake haɗa zufa ta cikin hijab kaɗai ta fahimci yanayinsa tayi ƙasa da murya ta ce What is this plx?" Can ciki ya ce "Zunubi nake rage miki" Debeka ta ce "Are you okay?" Majeederh couldn't speak, saboda bata nutsuwarta da ƙyar ta ce "Uhm" Debeka ta ce "Ok, bye" Tayi gaba Khalil ya manta inda yake ya ce "Bye dear" Debeka ta tsaya jin muryarsa, Jee tayi saurin rufe ido saboda kunya itama, Khalil ya kame fuska tare da ɗaga hijab ɗin ya fito kamar ya yi wanka da ruwan zafi sbd zufa, Debeka ta dinga kallonsa ya ɗaga shoulder clamly yana nufar gunta ya ce "Where? Ina?" Idanun Debeka ya cicciko da hawaye, ya kama hannunta suka fita waje Jee wani tashin hankali taji bazata taɓa jure ganin Khalil da wata ba, zuciyarta zafi take mata, ta sunkuya tare da mayar da rigarta ta gyara zaman pant din, daidai nan ƙyakƙyawan matar ta fito daga wani ɗan corridor hannunta riƙe da waya tana ɗan shafawa kamar bata so, wata lafiyayyiyar lafaya ce a jikinta white colour daka gani ba irin ta ƙasar nan bace, hannunta zube da zoben gold, farar ƙafarta akwai necklace mai kyau siririya, ta nemi waje ta zauna, da ɗan sauri Majeederh ta zube a gabanta kanta a ƙasa ta ce "He's coming, Ummi" Gimbiya ta ɗan kalli Majeederh, komai na majeederh irin na ƴar uwarta ne, babu abinda ya bambanta da ita sannu a hankali son Majeederh ke sauka a zuciyarta, na rabuwa tare kasuwa zuwa ko wacce ƙofa ta zuciyar tata, amma babu ko alamun hakan a saman fuskarta idan kaga yadda take kallon Majeederh zaka ɗauka babu so sai zallar tsana, bakinta ke motsawa tana son yin magana amma gabaɗaya laɓɓanta sun yi mata nauyi sosai, da ƙyar tana jan numfashi ta furta "Is he sleeping?" Kafin Majeederh tayi magana Khalil ya shigo a nutse cike da kamala yana wata kalar tafiya ɗaiɗai suna haɗa idanu da Jee ya yi mata harara, bai tsaya wahalar zagayowa ba, duk abinda zai bashi wahala baya so, ta bayan gujerar ya kama Jee na girgiza mai kai domin gabaɗaya bai kula da matar dake zaune ba, ya kama gujerar ya dirgo saman gujerar, still idanunsa akan Majeederh ya ce "I love you baby" wata waƙa ce ta Justin Bieber, ganin taƙi kula shi ya saka baki tare hura mata iska, tayi saurin ƙasa da kanta a ranta tana cewa "Ohhh my dear Khalil" Khalil ya lumshe idanunsa yana mai da numfashi, haka kurum ya ji nutsuwa na saukar masa a jikinsa, ya miƙar da ƙafarsa a hankali ya ji ya zunguru mutum ya buɗe fitinannun idanunsa wanda suka jirkice, idanunsa ya sauka akanta, itama ɗin shi take kallo ai da sauri ya hantsila har yana buge goshi, bai kuma sake yarda sun haɗa idanu ba ya miƙe ganin part ɗinsa ya masa nisa kawai ya shige ƙofar garden, Majeederh ta fahimci bawai gudun haka kurum ya kewa Ummi ba, akwai wani irin abu dake ɗawainiyya da shi, bai saba da uwa mahaifiya ba, shi yasa yake gujewa haɗuwar tasu. Majeederh ta miƙe zata bisa Gimbiya tayi mata gyaran muryar akan ta barshi. A hankali ta ce "Tell me something about him" Majeederh ta yi murmushi ta ce "He's stubborn" Calmly Gimbiya ta ce "I know" Jee ta ce "Khalil love's food"...


Khalil na zaune a office ɗin NAPTIP sanye da wata Brown suit ya ɗan jujjuyawa akan gujerar da yake kai kafin ya ce "Ohh" Mutumin ya ce "Shi wannan DDMASTER BOM ɗin babu wanda zai taɓa ce maka koda wasa ya taɓa ganin fuskar shi, har yanzu kuma jami'anmu na sirri basu samu information ɗin komai akan shi ba, abu ɗaya suka samu nasara shi ne yana yawan shiga Pakistan da Singapore, akwai wani sansanin su dako tsuntsune ya shiga baya fitowa da rai balle mutum" Gently Khalil ya jinjina kai, kafin ya ce "I'll like to know, me DDMASTER BOM yake?" Musbah ya juya ya zaro wani record ya ce "Mutum ne mara imani da tausayi, yana Creating muggan makamai wa Pakistan, yana Fataucin mutane wasu a cire musu ƙoda a siyar wasu Idanu, ga safarar mata manya da yara, yana forcing nasu to sex ga manyan masu muƙamai na ƙasa ƙasa, ana masu kuɗi su suna mayar da matan jarinsu ne, ga siyar da miyagun ƙwayoyi" Khalil was speechless the same time shocked and confused ya ce "Taya suke samun matan?" Musbah ya ce "Taya ake ruɗar matan da zummar aikatau a ƙasashen waje? Kuma ko tsufa kikai basa barin mace dawowa gida harbeta sukeyi, ko kina jinin al'ada sai sun yi tarayya dake" Khalil ya miƙe tsaye yana zagaye office ɗin a fili ya ce “DDMASTER BOM” Da sauri ya ce "Ni zan kawo ƙarshen shi" Musbah yayi dariya sosai ya ce "Mr President zai iya baka kariya, amma kana ganin zaka iya kare iyalanka? A yau zaka iya ganin an shigo gidanka an yanka matarka akan Idanunka, duka haka aka dinga yi wa ma'aikatanmu, mu rayuwarmu cikin kasada take da hatsari mai tarin yawa, matanmu kullum cikin zullumi suke"
"Zan iya, zan kashe shi da hannu na, zan sauke girman kansa zan kawo ƙarshen zaluncin shi" Musbah ya danna abu ya ce "Ka shiga jerin ma'aikatan NAPTIP, hukumar dake yaƙi da fataucin mutane ta Najeriya" Khalil ya sauke numfashi Musbah ya ce "Akwai Card, wanne suna za a saka maka wanda ba za a gane kai bane, domin komai hukumar mu a sirrince take" Khalil ya dinga tunani a fili kuma ya ce "MIJIN MALAMA" Musba ya yi murmushi ya ce "Done, ur card is done already, ka fara shirye-shiryen tunkarar DDMASTER, ka kuma fara tunanin yadda zaka kula da ilayanka all the best" Khalil ya amshi Card ɗin sannan ya fice, yana fita Musbaj ya miƙe ya rufe ƙofar.
A hankali yake zagaye office ɗin, sai kuma ya zaro waya ya kira wata number ana ɗagawa ya ce "Ur son is here" Ya yi shiru sai kuma ya ce "Da alama ɗanka na cikinka ya shirya kawo ƙarshen ka, Family issues kenan" Ya ƙara yin shiru yana saurare sai kuma ya ce "Ok Sir, babu mamaki ɗan ka ya zama silar kawo ƙarshen girman kai da jinkimar ka, ya kuma kawo ƙarshen wutar gabar dake tsakaninka da mahaifiyar shi" Musbah ya ce "An yi masa I.d card da suna MIJIN MALAMA, kamar yadda na saba fidda sirrin hukumar NAPTIP a wannan karan ma na turo maka kuɗi kawai nake jira" Yana gama faɗin hakan ya kashe wayar. Musbah ya saki wata dariya sosai ya ce.
"Let's watch and see, waye zai winning waye zai zama loser, DDMASTER BOM KO MIJIN MALAMA, Mr President or Dr Ibrahim-Khalil? Waye za a kashe President Denial David or Abraham Denial David?
[12/09, 11:29 pm] Sdy Auwal Gstc: *MIJIN MALAMA*


*BOOK 2 PAGE 82*




~_*Arewabooks@Nimcyluv*_~ 82
Kafin Khalil ya ƙarasa Jee tayi saurin shiga tsakiya idanunta akan shi, wanda shi kuma yaƙi yarda ya haɗa nasa idanun nata, muryarta na rawa sosai ta ce "Me kake shirin yi?" Ya yi shiru da kuma sauri ya sanya hannunsa guda biyu ya ɗagata zuwa gefe cikin ɓacin rai ya nufi kan Dad, ita cikin sauri ta ƙara shigewa tsakiya idanunta akan shi ta ce "Idan ka taɓa shi zan zubar da cikin nan na jikina" Khalil ya juya a ɗan miskilance yana kallonta da yanayin dake nuna _“You are kidding”_ A karo na biyu ya ƙara saka hannu ya ɗauketa cak ya matse kafaɗarta idanunsa a warwaje ko magana ya kasa sbd masifar yadda yake jin zuciyarsa, sai kuma ya saketa ya matsa wajan Dad yana haɗe ƙirjin su waje guda kai baka ce mahaifinsa bane ya ce "Idan ita matar taka zaka kashe go ahead, i don't care daman ban santa ba" Ya wani cije baki Dad na jin yadda duk jikin Khalil ɗin ya ɗauki rawa kamar wanda wuta take ja, ya saka hannu ya damƙi wuyansa ya ce "Amma, da wasa ka ce zaka taɓa mini sister zaka san ku duka biyun na fiku zafin zuciya, I'll kill you" Majeederh dake tsaye ganin yadda Khalil ya shaƙe wuyan Dad ya sa da ƙarfi ta saka hannunta ta shiga dukan cikinta, Maman Alpha ta miƙe tana cewa "Majeederh wanne irin shirme ne haka? Kashe kan ki da baby zaki?" Maganar daya jawo hankalin Khalil kenan, ya saki wuyan Dad tare da juyawa ya zubawa Majeederh idanun ganin taƙi bari Maman Alpha ta riƙe ta, idanunta rufe take dukan cikinta ga wasu irin hawaye da suke bin idanunta masu zafi, a hanzarce Dad ya fice da cikin parlourn hannunsa riƙe da waya yana ɗagawa, Gimbiya na zaune ta harɗe ƙafafuwanta tun bayan maganar da Mr President ya yi na cewa Khalil has a sister, ta nemi waje ta zauna fuskarta haɗe ba wargi as always, ko tari ba tayi ba, duk wannan abun kuma ba zaka ce tana wajan ba, inda direction ɗin Majeederh yake bata ma kalla ba. Majeederh ta saki raunataccen kuka ta ce "Ki barni tunda baya jin magana, Khalil baya ji yanzu idan ya kashe Dad shi ma kashe shi za ayi ya yake so na yi da rayuwata? Da abinda zan haifa, ko farin cikin dana fara samu ne baya so....," Ta kasa ci-gaba da maganar, Maman Alpha ta ce "Haba Majeederh, taya tunaninki zai iya baki cewa Khalil zai kashe mahaifinsa? Shi fa ya haife shi, duk wutar gabar dake tsakani ba za a taɓa rasa soyayyar juna a zuƙantan su ba, tsakanin uba da ɗa sai Allah, muna fatan wannan abun ya zo ƙarshe" Majeederh ta girgiza kai tana runtse Idanunta jikinta duka ɓari yake ta ce "Ki faɗa masa karya ƙara cewa zai yi kisa, wlh aka kashe Khalil mutuwa zan yi" laɓɓanta duka karkarwa suke, fuskarta ta rine tare da yin jajur musamman tsinin hancinta, yadda take kuka kaɗai zai sanya mutum hawaye, Maman Alpha ta ce "Ba zamu ga wannan ranar ba, In sha Allah Khalil ko sauro ba zai kashe ba balle mahaifinsa, har kuma a jawo a kashe shi" Majeederh ta riƙe hannun Maman Alpha sosai ta ce "Mama mutuwa zan yi idan Khalil baya raye, zan mutu zan bisa, ina son Khalil, ki faɗa masa ya daina maganar mutuwa haka ya yi mita a hospital, wlh zan kashe kaina idan Khalil baya duniya..!" Tsananin mamaki ta tausayi ya wanzuwa a zuciyar kowa, Maman Alpha ta saki Majeederh tare da kifa kanta a saman armchair ta saki wani irin kuka na matsanancin tausayin Majeederh da Khalil, sosai Maman Alpha ke kuka, wanne irin so ne wannan? Tunda Majeederh ta shafawa idanunta toka a gaban kowa take faɗin haka to lallai abun ya yi tsamari, a hankali Zaytoon ta yi ƙasa da kanta hawaye na zuba cikin idanunta, Mai martaba bai iya zama ba, ya miƙe yana jin jiri na ɗaukar shi a daddafe ya nufi waje yana mai kiran Rohaan daya fito da Zaytoon she's crying. Gimbiya yadda take a zaune haka ne a gareta har yanzu, domin ko yatsanta bata motsa ba, da kunne take jin komai bada Idanu ba, Abbu daya riƙe kansa da hannu bibbiyu yana tunani ya ɗago yana kallon yarinyar tashi, yanzu da ace da gaske ya hana auren nan ina hakƙin wannan son zai kai shi? Ko iya rabo ya isa ya kashe duk wanda ke ja da auren Khalil da Majeederh, tun ba a je ko'ina ba ga ciki ya bayyana, Abbu ya fahimci duk wannan ƙalubalan da kuma rashin auren da Majeederh ba tayi ba, da kuma yadda ya wahalar da Khalil, da fitowar Majeederh daga gidan Abuturab, da rashin auren Barrister Aliyu, da kuma rashin dawowar Alpha ba komai ne ya haddasa hakan ba sai RABO, rabon cikin dake jikinta, wanda kuma shi ne sanadin kawo jinkimar mutanen biyu wanda suke ƙoƙarin ruguza farin cikin MIJIN MALAMA da ita kanta malamar. Abbu ya miƙe jiki babu kuzari ya nufi inda Majeederh take durƙoshe, a hankali ya saka hannu ya miƙar da ita tsaye, a taushashe cikin nutsuwa da kamala ya riƙo hannunta tare da tallafo fuskarta a hankali ya ce "Hawwa'u" Ta kalle shi ta kasa cewa komai sai hawaye ya saka hannu ya goge mata hawayen ya ce "Meyasa sai kin nuna ke ƴar fari ce? Meyasa baki da wayo da dabara? Kin girma uwa zaki zama, kece wacce zaki taimakawa Ibrahim wajan ganin komai ya daidaita, kin raba shi da zafin zuciyar dake ɗawainiyya dashi, kin kawo silar daidaituwar shi da iyayensa, kin shirya su, kin zama silar sauke jinkimar su" Sharr hawaye ya sake sauka a Idanunta, Abbu ya fahimci rauninta akan mijinta Dr Ibrahimul-khalil Abraham, muryarta na rawa ta ce "Abbu, Khalil ba" Ya yi rufe mata baki ya ce "it's okay, ba bu abinda zai faru sai alheri just pray" Ta jinjina masa kai a hankali ya furta "Come closer" A hankali ya shige jikin Abbu ya rungumeta yana jin yadda take sauke ajjiyar zuciya, a yanzu kuma hadda kewar jikin Abbun nata ke damunta, sun jima haka kafin ya ce "I am sorry dear, ki yafe mini" Ta ce "Baka mini komai ba Abbu" Ya ce "Allah ya yi muku albarka ya baku zama lafiya, haƙuri da juriya da kau da kai" Ya kama hannunta har zuwa wajan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login