Showing 84001 words to 87000 words out of 126557 words

Chapter 29 - MIJIN MALAMA Book 2 Complete by Nimcey Sarauta .txt

Khalil dake tsaye kamar an dasa shi, ya kama hannun khalil ya haɗa dana Majeederh ya ce "Gata nan halak makal" Uncle Bello ya ce "Ka kula karta mace don soyayyar mijin Malama" Khalil a hankali ya damƙe hannu Majeederh, bashi da wata kalma da zai iya yi mata bayani ko ban haƙuri, he just need a hug ko zai samu nutsuwa, ji yake kamar ya jata ya rungume amma ko mutuwa na Kunyar Idanun mahaifi balle soyayya, a hankali Mami ta ce "Ibrahim kuje" Ya yi jim kansa a ƙasa sai ya ce "Ƙasar zamu bari" Sai a lokacin Gimbiya ya buɗe dara-daran kyawawa idanunta ta kalli Khalil tana jin kamar sbd ita ne zai bar ƙasar, Maman Alpha ta ce "Wacce ƙasa zaku to Khalil? Majeederh ba zata jure zirga-zirgan jirgi ba, sbd cikin jikinta" Shi dai ya yi shiru ba alamar zai yi magana, da sauri kuma ya damƙe hannu Majeederh tare da yin waje gabaɗaya suka bisu da kallo tare da addu'ar kiyayewar Ubangiji.. Tunda suka ɗauki hanya ba wanda ya ce komai, kowa da tunanin zuciyarsa, suna bayan mota driver na jansu, har suka isa lafiya Road lokacin ajjiyar zuciya kawai Majeederh ke saukewa a hankali, driver na yin parking ita ta fara fita Khalil ya bita da idanu, ko ba tayi magana ba yasan fushi tayi, a hankali ya bi bayanta suka samu Debeka zaune a parlour tana waya, tana ganin su tayi saurin kashe wayar kanta a ƙasa sai kuma ta kalli Khalil da sauri ta miƙe ta ce "Wclm sweetheart" Tayi kamar zata rungume shi, Khalil ya ɗan kalli Majeederh data ɗan saci kallonsa sai ya yi peaking kumatun Debeka ba tare da ya ce komai ba ya shige part ɗinsa, kansa ne kawai yake sarawa yana buƙatar tunani, sanin son waye asalin mahaifinsa Mr President ya ɗarso a zuciyarsa, da yadda zai yaje ya dawo da biyuninsa zuwa gare shi, a fili ya furta "Who is she? Ni ban san kamarta bama" Ya furzar da iska daga cikin bakinsa yana ƙara narkewa a jikin haɗaɗɗan bed ɗin nasa, cikin nutsuwa ya sake mirginawa a lokaci na babu adadi, yasan ko da wasa Dad ba zai ajjiye masa biyuni a Germany na, ƙasar kuma da yafi zuwa suna da yawa, taya zai iya suggestion wacce ƙasar ya kaita? Ya miƙe tsaye tare da nufar bathroom ya sakarwa kansa shower ruwan ya jima yana dukansa kafin ya kashe ya ɗauki tooth brush da Colgate ya wanke bakinsa ya fesa Rose Petal marmalade mint a bakinsa, time ya duba yaga lokacin sallah da saura, har ya zauna sai ya miƙe zuwa Library ɗin shi ya zauna saman chair yana ɗan jujjuyawa. System ce gabansa ya shiga searching sunan President Denial David, nan da nan aka watso masa bayanai akan mahaifin nasa, ya dinga dubawa amma babu abinda ya gani na ba daidai ba, information ɗin abubuwan da suke similar da abinda yake nema aka sake zubu masa, gently yake dubawa one by one har yazo kan wani suna DDMASTER BOM. Duka bayanan akan Fataucin mutane, Human trafficking; the unlawful act of transporting or coercing people in order to benefit fof forced labour or sexual exploitation. Daga nan kuma haramtattun miyagun ƙwayoyi, wanda suke taka rawa wajan lalata ƴan mata da matan auren da suke gidan su, hankalinsa ya tashi domin hadda ɗaya daga cikin wanda aka bawa Majeederh, hankalin Khalil ya tashi haka kawai yake son kawo ƙarshen zaluncin mutumin, domin ɓarnar yake sosai musamman ga al'ummar Nigeria da kulli Shaye-shaye yake ƙara yawa ba mata ba maza, ga violence everywhere. Ya yi jim ganin an rubuta a ƙasan sunan mutumin _A dangerous person_ Khalil ya yi shiru tunani fal ran shi, idan har zai kawo ƙarshen wannan dole sai ya zama jami'ai gashi he's not interesting, ku magana zai yi da Hukumar da ke yaƙi da fataucin mutane ta Najeriya, NAPTIP?. Miƙewa ya yi ya nufi waje yana fita yaga still Debaka na nan kuma a upstairs take ya juya da sauri ya tuna yau a ɗakin ta yake, sai kuma ya shafa kansa ya ce "Allah ka yafe, na tuba" Ya murza ƙofar dake jikin part ɗinsa wacce kuma kai tsaye ta tafi har bedroom ɗin Majeederh.


Jingina ya yi a jikin door yana zubawa gadon bayanta idanu, wanda yake da glowing gwanin sha'awa musamman da ta shafi kwalacca, ga Ƙamshin MORESQUE Midnight dake ratsa hancinsa, Khalil ji ya yi kamar bai taɓa jin ƙamshi mai masifar daɗi irin na yanzu ba, duk da yana masifar son turaren shi, yana jinsa daban amma da alama dai yanzu ɗan kwali yaja hula, he can't stay any longer domin ji yake kamar ana fusgar shi ne, Majeederh na tsaye tana ƙoƙarin shafa kwalacca ɗin a wuyanta zuwa ƙasan hammatarta, a hankali ta ji an rungumeta ta baya a ɓoye ta sauke ajjiyar zuciya, bata kula shi ba tana ji yana shasshafata can ya amshe kwalbar kwalacca ɗin ya sun shine da sauri ya kalli Majeederh ya kalli kwalbar sai kuma ya rausayar da kansa kamar yaro clamly a hankali can ciki ya ce "Duk wacce ta baki wannan je bata imani" Ta kalle shi ta ce "A sbd ta kashe wani?" Ya kwaɓe mata fuska ya girgiza kai ya ce "Eh" Ta harare shi ta ce "Wa?" Ya ce "Mijin Maluma" Tayi masa shiru tana ji yana tura kansa gabaɗaya wuyanta inda ya manta ne kawai bai shan-shana ba a jikinta, ya yi ya kwanta lamo ta fahimci da gaske ba shi ɗin ta kashe ta shirya tsaf ta ce "Malam fita" Ya mirgina ya ce "Zunubin naki ya yi yawa" Ya ware idanun sai kuma ya sanya ƙafa kamar zai ɗaga rigarta ya fizgota ta faɗo kansa saman ƙirjinsa ta ce "Fita matarka na jira" Ya lumshe idanunsa yana sauke numfashi a hankali ya ce "Naje ina?" Tana kunce gaban rigarsa ta ce "Ban son takura" Ya mirginata zuwa ƙasa ya yi mata rumfa sosai daidai kunnenta yana mata raɗa ya ce "Ya muke da Ayyu" Ta yi wani irin murmushi ta ce "Ohho" Ya yi squeezing bakinta ya ce "Kina son rabauta? Kuka a cikin jama'a?" Ta rufe Idanu ya ce "Ba gwara ki sani gaba ki cinye ba tas da wannan kukan? Ai kin san na miki yawa ma" Ya yi ya rungumeta sosai sune jima a haka ta ɗauka bacci yake can ta ji ya ce "I won't do it again, sorry" Ta yi shiru ya marairaice sosai ya ce "Ban sakewa" a hankali ta ce "It's ok" Ta juya shi itama zuwa ƙasa ta kwanta saman shi a nutse ta ce "Khalil" Ya ware idanunsa a kanta alamar dai yana jinta ta ce "Listen to your mother please" a ɗan zafafe ya ce "Waye mother ɗin?" Ta ce "Ummi" Ya ɓata fuska ya ce "Ni ban san wata Ummi ba, na ɗauka mother ɗin sunan wata ne" Ta daki ƙirjinsa sosai ya ce "Auchhhii" Ta ce "Ka gane me nake nufi, ka saurari mahaifiyarka don Allah" Ya lumshe idanunsa ya ce "I don't have a mother" Idanunta ya cika da hawaye ta ce "Don Allah" Cikin faɗa ya ce "Wai ke da zaki damu da ita ni damuwa ta yi dani ne? Idan sun yi faɗa da mijinta ni mene laifina da zata barni eh? Me na yi mata ta barni a gantale she left me bata san ya nake ba all this year's bata san waya bani tarbiyya ba, ilimi karatu, ko ɗan iska ɗan daba na zama ko kidnapper duk ita Ubangiji zai hukunta ta wofintar dani, she left me.....," Saukar bakin Majeederh cikin nasa ya tsayar da shi daga masifar da yake zubawa ya yi shiru yana sauke numfashi sbd yadda yake jin tana....
[12/09, 11:29 pm] Sdy Auwal Gstc: *MIJIN MALAMA*


*BOOK 2 PAGE 84*




*Arewabooks@Nimcyluv* 84


Khalil na driving a hankali idanunsa akan titi deep down na zuciyarsa tunanin yadda zai tunkari DDMASTER BOM yake, da yadda zai samu nasara akan shi. Ya sanya hannu yana ɗan hargitsa sumar kansa a nutse, shi fa duk duniya Allah daya halicce shi kawai yake jin tsoro, bashi da tsoro ko shakkar tun karar kowa, ya saba ɗaukan kasada tun kafin yanzu, balle wannan da yake ganin ko rayuwarsa ce ta salwalta, to ya yi sacrifice ne akan taimakon al'umma, daman bazai taɓa barin abinda yau zai ji ko mutuwa ya yi bashi tunani ko fargabar zuwa lahira. Ya sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya a hankali kuma ya danna bluetooth ɗin kunnen shi,yana yin roundabout a taushashe ya yi lallausan murmushi tare da lumshe idanunsa, still driving on the direction he was heading to.. zuciyarsa a bubbuɗe yake sauraran abinda take cewa da ɗan sauri kuma ya saki kan motar ta fara ƙara “ƙiiiiiiit" Ta cikin wayar Jee ta ce "Are you okay?" Ta ji shiru, har yanzu kuma motar tafiya take yaƙi riƙe kan nata, jin shiru ya sanya ta ruɗe sosai ta ce "Are you there ? Man, Man!" Duk ta ruɗe She wondered if there was an accident on his way, in a state of love and passion ya furta “I love you” He said that from the bottom of his heart full of weakness. Jee bata taɓa jin Khalil ya furta kalmar ba a gareta, sai ta ji sabon hargitsatsen yanayi, a hankali kuma nutsuwa ta fara saukar mata, ta yarda ta amince da dukkan abubuwan da zuciyarta ke gasgata mata, a hankali ta ce "You scared me" Ya dawo a hankali yana riƙe kan motar, kamar tana gaban shi ya sake furta "I love you, i love u Madam" A hankali ta ce "I know" Ya yi shiru sai numfashinsa dake sauka ya rage gudun motar a nutse a taushashe ya ce "How do u know?" Clamly ta ce "Your action, and emotions" Ya girgiza kai kawai yana shiga cikin Bristol Palace Hotel can ƙasa ya ce "Lallai yarinya" Jee ta ware idanunta tana jin kamar yana kusa da ita ne a hankali ta ce "I am older than u, am 35 u're just 20" Khalil ya dinga murmushi a kasalance ta ɗauka ma ba zai magana ba sai kuma ya ce "Kuma ƙwaninin yaron nan ya baki ciki in one time" Idanunsa ya sauka akan wani mai Guava ya ce "Madam" A hankali ta ce "Man" Ya furta "Guess what?" Tayi shiru sai ta ce "Ka shigo gida" Ya girgiza kai ya ce "Guava" Majeederh ta ce "Haba? Plz kazo mini da ita" Ya ce "Tab, ba zan tsaya ba" Ta ɗan yi tsakin shagwaɓa ta ce "Plz Man" Ya shafa gemunsa ya ce "With?" Ta ce "Apple, ice cream, pizza, with..." Ya dakatar da ita da "Hold on Madam, idan kika ci wannan How can you eat me?" Jee tayi saurin kashe wayar jin magana mai girma. Khalil na zaune saman kujera yana kallon mai martaba dake cewa "Sai yanzu?" Khalil ya ɗan kalli Mai martaba Ajlaal Sultaan yana harɗe ƙafarsa a kamalance da nutsuwar dake wanzuwa a jikinsa a kullum a ko yaushe tana ƙara fidda wata kwantacciyar Ilhama dake bayyana mazantakar shi da fitar dashi daga tubali na ƙuruciya zuwa na zalllar nagartacce, numfashi ya sauke a ɓoye yana shanye mamakin ganin Rohaan da Zaytoon a wajan ya jima yana kallon su, su ɗin ma shi suke kallo. Ya ɗauke ido
"Sorry, i took so long" Khalil Answered starring around them, a kuma taƙaice ya yi maganar
Roohan dake kula da Khalil ɗin ne ya ce "What's bothering you?" Roohan asked bitting into his finger. Khalil bai ce komai ba, bashi da niyyar cewa komai ɗin Zaytoon ta ce "Ibrahim kana tunanin uwa zata wofintar da ɗan data haifa? Kana jin a ranka da gangan ta barka?" A ɗan fusace Khalil yana saka ƙafa tare da buga table ɗin gabansa nan take ya tarwatse ya ce


"I don't have a mother in this world, if you called me just to tell me that I have a mother, I'm sorry am not interested" Ya miƙe tsaye yana hargitsa sumar kansa sai huci yake ya sake kallon Zaytoon ya ce "Granny, ki faɗa mata ni ta bar mini gida, me ya sa ta barni, ya akai sukai aure matsalarta ce da mijinta, yadda na tashi ba kulawar iyaye ban wulaƙanta ba, yanzu ma babu abinda zai sameni, su ne su kashe kansu ma sbd girman kai da jinkimar su, i don't want her in my life anymore"
Yana faɗin hakan ya ɗauki wayarsa da rigarsa ta sama ya yi waje, suka bisa da kallo Roohan kallon ikon Allah kawai yake, idan ba kuskuren gani ya yi ba, bakinsa har wani tiririn masifa yake. Mai martaba Ajlaal Sultaan kawai yake girgizawa a hankali yake sakin lallausan murmushi daman ya ji a jikinsa hakance zata kasance. Zaytoon da abin duniya ya isheta ta ce "Ikon Allah, Ubangiji ka sassauta masa zafin zuciyar nan" Roohan ya ce "Amin, ku haɗa da ragowar ruwan sallar asr, matarsa na haƙuri"


"Kuma aka ce zai yi mata haka?" Mai martaba ya furta a hankali yana gyara zaman shi kamar baya so, cike da kamala kuma ya ce "Khalil loves his wife more than anything, he is afraid of losing nothing but his wife, ya sadaukar da komai saboda ita, ya sota fiye da kima yana kan sonta a yanzu, a gobe,jibi har gaban abada idan akwai, yanzu da ransa yake a ɓacan nan ba zai ƙarasa mata haka ba, sai ya samu nutsuwa" Roohan ya ce "Ɗan kwali ya ja hula kenan, kada dai labarin soyayyar ya zama na LAYLERH DA MAJNOON" Mai martaba ya ɗan kalli Roohan ya ce "Kasan labarin Layler da Majnoon? Roohan ka sani?" Roohan ya ɗaga shoulder ya ce "Na dai san an zuba soyayya, ina son labarin soyayya" Mai martaba ya girgiza kai kawai ba tare da ya ce komai ba, Ƙhulud dake tsaye ta ce "Ita Layler mutuwa take duk soyayyar da suka sha, shi kuma Majnoon haukacewa yake, ai asalin sunan shi Ƙais Majnoon ana nufin mahaukaci" Roohan ya yi kamar zai yi kuka sosai ya ce "But sun yi aure before Layler died?" Ta girgiza kai ta ce "Ko kaɗan, basu mallaki junan su ba" Ya sake cewa "To irin Soyayyar nan fa masifa ce, bata da wani amfani" Da sauri Zaytoon ta ce اصمت يا" روهان، لا أريد أن أحدث الكثير من الضجيج" Zaytoon ta ƙara cewa "Yin Allah, ƙaddara haɗuwa ko rabuwar masoya, baka da iko ko zarafin ja da hakan".... Latifa na zaune gaban Dr ta ce "I'm still wondering Dr" Ya ware Idanu ya ce "Reason?" Ta ce "Taya kasan ni ba ƴar Babanmu bace? Nasan Blood group baya ɗaya daga cikin abinda ke sawa a gane ɗan wane ko ba ɗan shi ba" Dr ya jinjina kai ya ce "Exaclty, u got it well, kafin rasuwar Malam Umaru ya shaida mini yana zargin Alhji Bashir akan shi ne mahaifinki ya taɓa ganinsa da wata yarinya mai tsananin kama dake, domin zargin shi ya tabbata ya ce ayi DNA test, shi da kansa ya bani gashin kanki" Latifa Omar ta goge zufa ta ce "Dr ya DNA test yake?"


Ya ɗan juya a hankali yana danna abu kafin ya juya mata system ɗinsa ya ce "A DNA test (genetic testing) is a medical test that can identify mutations in your genes, chromosomes or proteins, Dna ƙwayar halitta ne, mutum daga wanne dangi ya fito, ko yanki, idan akai sample na Dna yana tantance uba da ɗa, waye wanda ba ɗa da uba bane, har ƙabilar da kake ciki Dna test yana bayyanawa, musamman idan ana tantama akan ɗa, ana amfani da gashi wajan yin gwajin ko jini, idan har daga jikin mutane biyun ya fito, ko so kake ka gane kai ɗan wanne gari ne, gwajin Dna test yana nunawa" Latifa Omar ta share zufa" Dr ya ce "Genotype kuma ana yi kafin aure wajan tantance samuwar dacewar ƙwayar halitta, da gane wanne Iyali za a samar, misali idan AA da SS suka yi aure yaran da za'a haifa zasu kasance AS ne kariya, sannan ba normal Genotype bane, idan AS da AS suka yi aure idan sun samu yara huɗu biyu za su iya kasancewa sikila zallar jininsu ya zama SS, biyu kuma kariya AS" Latifa ta jinjina kai ta ce "Yanzu ina kake tunanin zan samu Alhji Bashir ɗin sunana ya yake?" Ya ce "Shi ɗin mai arziƙi ne sosai" Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Alhamdulillah" Sai kuma ya ce "Amma ya samu karayar arziƙi, don gidan da yake ma na haya ne, kinsan shi haihuwa da arziƙi na Allah ne daman" Ta kasa cewa komai ta sake shiga IG taga still Northern ɗin ba su yi mata reply ba, ita sam ba zata iya tarar Majeederh da wannan maganar ba, kuma tana buƙatar yafiyarta sosai..


Ddmaster bom na zaune saman wata mahaukaciyar kujera, ya rufe fuskar shi da ƙyalle wasu jibga jibgan mutane ne zagaye da shi, ko wanne ɗauke da manyan makamai da bindigogi na masifa, ya gyara zama sai kuma ya saki wata mahaukaciyar dariya yana sake duba I.d card ɗin ɗan nasa Khalil wanda ya shiga hukumar NAPTIP domin kawo ƙarshen shi, a fili ya ce "Baka san waye ubanka ba, lokacin da zaka sani kuma a ranar zaka mutu, kamar yadda na kawo ƙarshen Taj abokin ka, na sanya mota ta markaɗe shi" Wani babban yaron Ddmaster bom ya ce "Oga wai me ya sa kake son Gimbiya tazo nan?" Ya ce "Ina son kawo ƙarshen jinkimar ta, zuwanta gare ni shi ne zai zama silar kawo hakan, tun kafin na aureta na yi al'ƙawarin bawa wani Babba ita su kwanta saboda mugwayen kuɗin da zan samu, amma jinkimar matar ya rusa komai a lokacin kuma ta san waye ni tana ƙoƙarin tona asirina na saka a kasheta kisa na wulaƙanci amma sunci amanata ashe bata mutu ba" Ddmaster bom ya miƙe tsaye sai kuma ya sheƙe da wata dariya yana ƙyaƙyatawa ya ce "Akan kuɗi babu abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login