Showing 105001 words to 108000 words out of 126557 words

Chapter 36 - MIJIN MALAMA Book 2 Complete by Nimcey Sarauta .txt

ta ce "I love you, I love you Man, na ji tsoro!" Ya riƙo fuskarta yana kashe mata ido ɗaya, yana jin zuciyarta na bugawa, sun jima a haka kafin ya kama hannunta suka nufi reception, Alhassan na ganinsu ya tafi da gudu ya nufi wajen Khalil yana faɗin "Aby" Khalil bai saki Majeederh ba ya ɗauki Alhassan ya ƙarasa inda su Innati suke da su Abbu, Innati ta riƙe haɓa hannunta riƙe da bottle water mai ɗan iskan sanyi sai turiri yake ta ranƙwashi Alhassan ta ce "Algungumi to kai dai ba abokin arziƙi bane a gaskiya, wani abu ne kuma Aby?" Majeederh ta yi murmushi Mami ta ce "Har kun fito?" Ta ce "Eh Mami" Innati tayi ƙasa da murya ta ce "To ya naji ban ji wani ihu yana tashi ba?" Abbu ya kalleta da mamaki a hankali ya ce
"Ihun me kuma?" Innati ta ce "Na mutuwar Soja mana?" Abbu ya sake kallon Innati da mamaki sosai ya ce "Wani ne ya ce ya mutu?" Innati ta ce "To jira nake a fito da gawa fa? Ashe bai mutu ba? Zaman me yake ba gwara ya margaya uban kowa ya huta da rashin tawakkalinsa ba? Wai da gaske yana raye?" Ba wanda ya ce mata komai ta fashe da kuka sosai tana zare gefen zaninta ta ce "Bafa ƴar iska bace ni da zanna magana ana mini kallon wata arniyar legas, kawai a kira dreba ya kai ni gida duk sanda ya mutu na dawo" Khalil ya ɗauke idanunsa wallahi kamar an masa dole dole wajan furta "Zamu tafi" Mami ta ce "Tafiya kuma? Yau ɗin nan Khalil ko can gidanmu ba kuje ba" Jee ta ce "A'a zamu" Ta ce "To shikenan" Majeederh ta amshi Al'hussain ta rungume, Khalil ya kama hannun Baby Khalil su biyar abinsu sukai waje, Khalil ya kalli Majeederh sai ya ɗan kwaɓe fuska ta haɗe rai itama ya miƙa mata key ya ce "Plx" karɓa kawai tayi ta nufi wajen driver, bayan ta ajjiye Al'hussain a baya, baby khalil ma na baya, Alhassan na cinyar Khalil tayi Bismillah tare da yiwa motar key tai reverse a hankali ta harba motar zuwa bakin gate ganin zata nufi hanyar gidan Uncle Bello a taƙaice ya ce "Hubb Lodge Road" Ta kalle shi waya yake dannawa ta ɗauke kanta4d, a jikinta take jin duk motsinta akan idanunsa, tayi murmushi kawai tana mai ci-gaba da driving.


Suna zuwa daidai ƙofar gidan Barrister Aliyu Sufyan Khalil ya ce "Stop the car" Ta juya da sauri ta kalle shi bai kalleta ba har zuwa lokacin gashinsa a zube yake a baya da gefen fuska ya fito, tana ƙoƙarin fitowa ya sakawa motar key ya nufi gate ɗin gidan Barrister Aliyu, ya ɗan tsaya, daidai nan kuma manyan motoci na ƴan sanda wanda Khalil yama IGP Latif Mahdi waya yana buƙata, kasancewar IGP yasan khalil ya kuma san ba zai iya cutar da kowa ba dole akwai dalilinsa na yin haka, ya sanya ya buga waya kai tsaye aka turo, Majeederh na cikin mota tana kallon ikon Allah tana addu'ar Allah ya sa ba wani abu Barrister yama Khalil ɗin ba, Khalil ya shiga gidan tare da knocking ba jimawa aka buɗe Aaliyyah ta yi wani fresh saboda cikin jikinta, ta zare idanunta ganin Khalil ta ce "Kspider, Yaya Khalil?" Ya ɗan fuske dole shi Yaya ne ta ce "Come in,ka shigo" Ya ɗan yi jim sai kuma ya shiga, banda wani irin ƙamshi babu abinda parlon yake komai gwanin sha'awa, ya nemi saman sabuwar kujerar dake parlon ya zauna, ta miƙe ta ce "Bari na kawo maka drinks" Ya ɗan murza yatsun yana ƙarewa parlon kallo ya taɓe baki speaking calmly ya ce "Ina...," Sai ya yi shiru ta ce "Yaa Aliyu?" Ya zuba mata idanu bai magana ba ta ce "Latifa?" Ya lumshe idanu ya buɗe ta ce "Tana bedroom ɗinta ta kulle, ai police ne suka zo kamata Yaa Aliyu ya hana tun daga nan ta shige bedroom ta kulle" Khalil ya miƙe yana zura hannu a aljihu ya zaro wani master key ya buɗe bedroom ɗin dake ta dawo down strairs da zama, yana buɗewa ya ce "come in" ba a ɗauki lokaci ba polices ɗin suka shigo, wasu manya guda uku amma mata. Latifa na ƙuryar gado taga an faɗo ciki hantar cikinta ya kaɗa ganin police ta fashe da kuka ta ce "Don darajar Allah da Annabi kuyi haƙuri ku yafe mini kuji tausayina don Allah..,” ɗaya daga ciki ta daki bakinta da ƙasan bindiga nan da nan jini ya fara zuba, suka damƙeta zuwa waje, Barrister Aliyu dake sakkowa ƙasa ya bi Khalil da kallo domin da farko bai gane shi ba, sai ya yi masa kama da actor's ɗin Nollywood, domin ko fuskarsa ba a gani sosai sai jajayen laɓɓansa. Latifa ta kalli Barrister Aliyu ta ce "Sweetheart don Allah don Annabi karka bari su tafi dani na shiga uku na lalace dame zan ji? Daman nasan hak'ƙin Majeederh ba zai barni ba, Khalil Oga sir kayi haƙuri saboda Allah Majeederh ta yafe mini itama" Khalil ya saka hannu ya tura sumar shi baya yana kallon Latifa ya ce "To bata yafe ba, idan ma haka ne ni mijin malama ban yafe ba" Ta dinga kuka tana turjewa tana kallon Zaki yaƙi kallonta ta juya ta kalli Aaliyyah ta ce "Aaliyyah ki taimaka mini idan na je gidan maza ni kaɗai kashe ni za su yi"
"Sanda kike zuwa wajen boka kina k'ulla sharri saboda kawai ki cutar da ɗan adam, ɗan adam ɗin ma wanda ya yarda dake kin nemi taimako ne?" Aaliyyah tayi dariyar rainin hankali ta ce "Kinci uban ɗan iska a rainin hankali, ai uban kuturu ya yi kaɗan balle na makaho, ita rayuwa daman juyin wainar tanda ce, kuma rawar ƴan mata na gaba ya koma baya, duk wanda ya ce tukunyar wani ba zata tafasa ba, billahi tashi ko ɗumi ba zatayi ba, ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta, maza gidan ɗan kande na jira ko zaman can zai wanke miki zunubanki"
Latifa idanun na zubar da hawaye ta dubi Aaliyyah dasu ta ce "Aaliyyah ni kike faɗawa haka?" Aaliyyah ta saki dariya ta ce "Warr, ke awa karan kaɗa miya? Ina ruwana da girmanki? Ai Karen Bana Shi ke Maganin Zomon Bana, kin rufe idanunki kin cutar da rayuwar wacce take matsayin uwa mahaifiya , duniyata, kin raina wayonta saboda kina baƙin ciki da baiwar da Ubangiji ya yi mata, idanunki sun rufe kin manta Sara da sassaƙa ba sa hana gamji toho”. Lafita ta ce "Haba Aaliyyah sharrin shaiɗan ne na gane kuskurena ki bani dama na wanke laifukana, ni ban ɗauke ki kishiya ba, ki bawa Oga sir Yaya Khalil haƙuri muyi zaman amana ki yarda dani don Allah" Aaliyyah ta zare Idanu ta ce "Ina ganin Kura da Rana yaya zan yarda ta cije ni? Na shiga ban ɗauka ba, bata fidda ɓarawo, uhm wannan falsafar taki bata samu tunani mai kyau ba" Barrister Aliyu dai na tsaye, Khalil ya juya baya domin zai iya kaiwa Latifa duka shi kuma duk jikin da yake ɗauke da najasa da datti ba zai taɓa saka hannu akai ba, police ɗin suka ja Latifa har zuwa waje, Khalil ya juya zai fita Aaliyyah ta ce "Yaya Khalil Anti Jeederh fa? Ka zauna kaci abinci mana" Ya ɗan shafa kai clamly ya ce "No Thanks" Yana faɗin hakan ya juya saboda bashi da business da Aliyu, yana zuwa motar ƴan sandan na barin wajen kai tsaye kuma state C.i.d Khalil ya ce a shige da ita daga nan a shige da ita prison saboda yana da d'aurin gindi. Hankalin Majeederh ya tashi taso ko albarkacin baby khalil Latifa taci, ta dinga buga ƙofar Glass amma a rufe kafin a fitar da Latifa Khalil ya yi waya da gidan ƴan jarida na t.v dana redion Latifa tayi bayanin abubuwan data aikatawa Jee har yadda aka samu cikin da wanda ya yi shi, voice ɗin ya dinga zaga ko'ina dake live ne, abin ya yi trending cikin ƙank'anin lokaci, laifin Majeederh ya wanke a idanun jama'a da wanda suka aibatata da masu tsine mata, suka shiga neman yadda zasu ganta idanu rufe aka shiga tsinewa Latifa da mahaifinta Alhaji Bashir. Khalil na kallon yadda jee ke binsa da idanu bai kalleta ba taja motar bisa direction ɗin daya saita mata, babu inda kuma map ɗin ya tsayar dasu sai gaban wani haɗaɗɗan gidan mai masifar kyau da tsari ganin sunan Orphanage ta juya da sauri ta kalle shi, kafin tayi magana yara da yawa farare da baƙaƙe sun taho da gudu sun rungume Khalil, daga mai ɗane bayan shi sai mai riƙe hannunsa suna "We miss you Daddy" Majeederh taji idanunta ya cicciko da hawaye ashe ta wannan hanyar Ubangiji ke buɗawa Khalil ta rasa yadda a kullum arziƙin Khalil ƙara yawa yake ashe ga dalili, ta ɗan yi baya tana tuna sanda take kaisa orphanage ɗin shima when he was little, a hankali ta ce
"I love you gwarzona" Ya juya ya kalleta domin ya ji me ta ce hawayen daya gani a fuskarta ya sanya ya saki yaran, Alhassan tuni ya shige cikin yaran ya fara dambe dasu har an yaga masa riga, ya ƙarasa inda take a hankali ya buɗe bayan mota bata lura ba ta ji ta faɗa ya bi bayanta yana rufe ƙofar ya ɗan yi tafi driver yama motar key, Khalil ya yi ƙasa da glass suka haɗa idanu da Faɗimatu Majeederh ta dinga kallon yarinyar tana tuna sanda ta ganta a Vidcall ɗin Khalil, John ya ƙaraso yana yin ƙasa ya ce "Ranka ya daɗe" Khalil ya zubawa John Idanu ya ce "Nace maka me?" John ya jinjina kai ya ce "Kace yau tarihi zai maimaita kansa, zaka nunawa Malama Majeederh yadda kake sonta?" Khalil ya lumshe idanunsa speaking calmly ya ce "I love my wife John, kamar bata yadda ba amma zan tabbatar mata yau ɗinnan" Ya sake sauke numfashi yana buɗe zuciyarsa ya ƙara kallon John ya ce "Mun ɓata time, Sexy mama When will fasting begin?" Sexy Mama Majeederh ta maimaita a ranta tasan da ita yake, bata kalle shi ba ta ce "Today" Khalil ya ware idanunsa yana ɗan dukan kafaɗarta "Sexy mama!" Ta harare shi ya ɗage mata mata gira ya ce "But you didn't tell me" Tayi masa shiru ya saka hannu ya mintsineta a bombom da sauri ta ce "Ohh sorry!" Khalil ya juya ya kalli John ya ce "Kayi lists na komi ka turamin, ka bar su Alhassan wajen ka" Ya sauke glass yana riƙe numfashi da shafa ƙirji ya kalli Jee ya ce "Saboda na ɗan shafa ki?" Ta tura baki ta ce "Mintsinina kayi fa?" Ya damƙota yana ƙasa da murya ya ce "Bari mu ƙarasa yau za kiga asalin mijinki da yadda ake Mintsini"
[11/2, 20:11] Ummu: *MIJIN MALAMA*


*BOOK 2 PAGE 101*




Wani tattausan murmushi ya yi mata yana ɗan ware idanunsa kaɗan, a hankali Majeederh ta mayar masa da martanin murmushin da ya yi mata ba tare da sani ko tsammanin hakan ba, ya zame idanunsa ya juya yana kallon wanda ke taɓa shi yana masa magana a hankali. Majeederh ta gyara nutsuwarta idanunta a ɗan lumshe bayan daidaita numfashinta da kuma sanin cewa camera ce a kanta ta numfasa tare da cewa“Ƙaddara! Idan na ce ƙaddara; ina nufin wani abu da Ubangiji ke jarabtar bawansa mumini da shi, ko da hakan ya kasance wani ne silar faruwar ƙaddarar ta mutum. Komai ya faru da mutum a rayuwa nufin Allah ne da kuma sahalewar shi, no matter what happens to you, you can't run from your destiny, ba ko wacce zuciya ce ke iya jure jarabawar Ubangiji dangane da rayuwa ba, mafi kyakkyawar zuciya da tsaftata ita ke yarda ba mutum ne ya ɗora mata abinda ya faru da ita ba, Ubangiji ne!. Gabaɗaya muna rayuwa da ƙaddarorinmu ne, inma muyi nasara akan su, inma suyi akanmu, cimma nasara a rayuwar waninka ta hanyar ganin bayansa wannan zato ne irin na masu ɓauɗaɗɗiyar zuciya, cimma nasara da yaƙini ga cigabanka na rayuwarka mai zuwa shi ne matakin farko na zama nagartacce da gina rayuwa ta gobe"
Majeederh tayi shiru saboda yadda zuciyarta ke rawa da gaske, bawai tsoran camera ɗin take ba, yadda duk ɗago fararen Idanunta da zata yi sai taga narkakkun idanunsa kwance a fuskarta, fuskarsa ɗauke da wani irin shu'umin murmushi mai kwantar da zafin zuciyar ko wacce ƴa mace, ta ja numfashi ta sauke tana mai janye idanunta daga gare shi, she wonder why he keep his eyes on her? Ta riƙe kanta da kyau tana buɗe hannayenta tare da ɗan jingina da chair ɗin da ke juyawa da ita ta ce “Destiny!"
Ta ɗora da “destiny, fate, and lot mean a future that someone or something will have. destiny and fate both suggest that the future has been decided or planned by God. destiny often suggests a future that includes something great and important, Destiny ita ke jan mutum zuwa ga victory ɗinka na abinda kake son Achieving a rayuwa!" Halima Ben Umar ta ce "Haka ne, victory nasara kenan shi ke kawo Achieving na goals long term and short terms, kuma shi ke jan ragamar rayuwa, amma Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Me ya sa aminiyarta ta kasance mutum na farko wajen wargaza rayuwarki? Menene ya ja hakan?" Kai tsaye Majeederh ta ce "Soyayya! Love is our true destiny. We do not find the meaning of life by ourselves alone, daban nuna mata so ba, da bata tsaya a gefena ba, da ban nuna mata so ba wata ƙila da abinda ya faru dani bai kasance hakan ba, da ban nuna mata so ba da ban kasance da mijina wanda ya zama silar wanke damuwa da raɗaɗin da zuciyata take ba, da ban nuna mata so ba wakila da Dr Ibrahim-Khalil bai zama mijin malama ba, da ban nuna mata so ba watakila da ban san wacece ita ɗin ba, da ban nuna mata so ba da wala'alla ban haɗu da dangin mahaifiyata ba, da ban nuna mata so ba babu shakka da ilimin da nake da shi a yanzu tarihi zai zama...," Hawayen daya fara taruwa a Idanunta ne ya sanya ta yi shiru tana haɗiye abinda take ji akan Latifa, bata son rauninta ya bayyana, amma Latifa ta riga data kassara rayuwarta, ta mata tabo, irin tabon da ba zai taɓa gogewa ba, tabon da aka zana shi da baƙin fenti maimakon baƙar tawada.
"Sorry Malama Majeederh Abdul'aziz Khan, idan kina kuka duka zaki samu hawayen muna son muyi learning daga cikin ƙaddarorinki" cewar Hafsat A.b Hamza. Majeederh ta yi murmushi kawai tana sauke numfashi juya idanunta ta yi ko zata hangi Khalil ta samu ƙarfin quiwa amma ko inuwar shi babu, ta yi ƙasa da kanta hannunta riƙe da tissue ta ce
"Tun bayan faruwar abun ban taɓa magana da kowa akan abinda Latifa tayi mini ba, even my husband Khalil, ban taɓa baƙin ciki a rayuwa irin baƙin cikin da na ji a sanda gaskiya tayi halinta ƙarya ta ƙare ba, fitila ta haska mini aminiyar dana yarda da ita,ita ce responsible na abinda ya faru dani, ta wargaza mini rayuwa, ban taɓa yarda ko gasgata Aminiya na baƙin ciki da samun aminiyarta ba sai yanzu, I have been ashamed! Ni da kaina ina jin kunya na buɗe baki nace wacce nayi trusting ɗinta ɗari bisa ɗari ita tayi mini haka, and do you know what?" Ta share hawayenta ta ce "Abu zai faru dani, kuma she's the first person da zan faɗawa ta bani shawara ashe duk kashe kaina nakeyi, sai yanzu nake tuna me ya sa ta ce na gudu na bar gidan mahaifina? Meyasa a lokacin baya ta saka na shafe fuskata da baƙi da sunan wai ko maza za suga kyauna? Amsa! Bata ƙaunar mu jera fuskata a buɗe gani take kamar ina disashe tauraronta ne, ta durƙusa akan ƙafafuwanta tana kuka, "wai na auri mijinta bata son ganina haka ashe she was just pretending! Babu hakan a zuciyarta, ban san adadin shekarun dana ɗauka tare da asirinta a jikina ba, ta sanya na zama mujiya a idanun maza, basa ganin kyauna basa ganin nagartata, ina zama wata kala a idanunsa, suna shakkar tunkarata da sunan soyayya, wanda hakan ya ja mini JINKIRIN AURE, nayi shekaru 35 a gaban iyayena cike da tashin hankali da damuwa, na sha suruta daga wajen ƴan uwana, mutanen unguwa da jama'ar gari, ana ce mini karuwa, ana cewa mai kuɗi nake so, ana cewa neman maza nake so shi yasa bana son aure...," Daidai nan ta fashe da wani irin raunataccen kuka tayi saurin rufe fuskarta da tafin hannunta, wani irin kuka take mai ban tausayi kai kace yanzu ne komai ke faruwa,People's bad comments about her in the past had an effect on her heart. Hafsat A.b Hamza da Fatima Jajere tuni suka fara kuka saboda akwai abin tausayi a labarin Majeederh, an kassara rayuwarta tako wanne ɓangaren wanda kuma ƘAWA ce silar komai. kuka tayi sosai wanda ya ja musu yanke recordings for some minutes domin samun nutsuwar zuciya.


A hankali ya miƙe cike da nutsuwa yana gyara zaman sunglasses ɗin fuskarsa, yadda fuskarsa tayi jajur zaka san kukan da Majeederh take ya taɓa zuciyarsa da gaske, ba zai iya jurewa ba domin yana gab da samun matsala a kamalance ya fice ta ƙofar baya daidai nan kuma ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious ya karaɗe wajen hakan ya sanya director da camera man ɗin da suke kusa ɗago kansu zuwa gare shi, if they are not mistaken wannan shi ne mijin Malama, the ex-president son, jikan masarautar Saudiyya hamshaƙin ɓoyayyiyar mai arziƙin nan na ban mamaki, mamallakin kamfanoni kala-kala, uban marayu wanda ba a san adadinsu ba, Dr Ibrahimul-khalil Abraham Kspider, Mijin Malama. Khalil ya haɗe fuska sosai domin baya ɗaukan raini, sai kame kansa yake kallo ɗaya kuma a tsanake zaka yi masa ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login