Showing 117001 words to 120000 words out of 126557 words
Chapter 40 - MIJIN MALAMA Book 2 Complete by Nimcey Sarauta .txt
duniyar tunani ya ji an rungume shi ta gaba data baya ya buɗe idanu, Mai martaba Ajlaal Sultaan ya gani tsaye a gabansa ya rungume shi idanunsa na rinewa, Rohaan ya sake rungumesa ta baya, Zaytoon kasa magana tayi sai kuka data fashe da shi, Majeederh da Ƙhulud Arzaan suka rungume juna, farin cikin ganin Khalil da Ahalinsa ya wanke zuƙatan Granny da sauran, nan da nan aka fara shirya kayan buɗe baki na musamman ga baki na musamman wanda ba'a zaci zuwan nasu ba, musamman Dr Ibrahimul-khalil.
Har dare lokacin kiran Magriba a ƙasar Saudiyya Khalil bai sanya matarsa a idanunsa ba, sai yaran kawai yake gani hakan ya dame shi yana son ya ji wanne hali take ciki, gefe guda kuma ganin Ummie a parlour ya hana shi tambayar Majeederh, haka kurum Ubangiji ya sanya masa jin nauyi da shakkar Ummie ɗin hadda kunyarta. A hankali ta ajiye azkar ɗin hannunta ta kalle shi yana zaune saman dadduma ya ɗan kishingiɗe idanunsa rufe hannunsa ɗaya akan haɗaɗɗan kushin a lokacin sai ta gan shi bashi da maraba da Ajlal ta jima tana kallonsa kafin ta ɗan yi gyaran murya, Khalil ya buɗe gajiyayyun idanunsa tare da kallon Ummie a taƙaice ta ce "Idan kayi buɗe baki, sai ka zauna zaman jin mulki"
Ya zare idanu sosai ya ce "Mulki?" Ta haɗe rai ta ce "Eh, naga sarautar kake ji da ita yau" Ya ɗan kwaɓe mata fuska domin shi baya son wata sarauta bashi da wani zaɓi wanda ya shige hutawa, tunda ba gun aiki za shi ba, kuma ba zai iya zaman surutu da kowa ba da Jee na nan shi ne za su yi hira mai daɗi irin ta mata da miji. Ta kalle shi da kyau ta ce "Ibrahim" Ya kasa amsawa idanunsa dai na zube a kanta ta ce "Bakai kake da ikon zaɓar sarauta ba, sarauta ke zaɓar mutum kuma ta riga data shiga jikinka ta zame maka jinin jiki, either you like it or not, kai ɗin jinin sarauta ne kuma kana son ta" Ya girgiza kai kawai yana miƙewa tsaye tare da dawowa kusa da Ummie tareda juyawa gabaɗaya a taushashe kamar zai mata raɗa ya ce "Goodness, takura ce" bata ce masa komai ba,ya miƙe zuwa sashin da aka basu har ya shige ya dawo yana shafa kai, Ummie ta miƙe tana gyara zaman lafayar jikinta ta dube shi a tsanake ta ce "Lafiya?" Ya ce "Ummie irin takalmin Uncle Ajlaal" Ta ce "Ya yi me?" Ya kasa cewa komai ta ce "Kai kuma da baka son sarauta mene haɗinka da takalmin sarauta?" Ya juya da sauri yabar wajen, a tare Mai martaba Ajlaal Sultaan shi da Prince Rohaan suka fito suna tsaye hannunsu riƙe da Dabinon ajwa Khalil ya fito cikin wata kyakkyawar jallabiya mai zare shuɗi irin zanen jikin sarauta ne da ita, yadda yake a tsaye saman ƙafafuwansa zaka kula da yadda ya kerewa Mai martaba Ajlaal Sultaan a tsayi girma da faɗin jiki, Rohaan ya ce "Mijin Malama an fito?" Khalil bai ce komai ba, addu'ar daya koya wajen Majeederh yake nanatawa a ƙasan zuciyarsa a haka yana tsaye Alhassan da Al'hussain suka fito da Yaa K gabaɗaya jallabiya ce a jikinsu irin ta mahaifin su Khalil, Ajlaal da kansa ya ɗauki Alhassan Rohaan ya ɗauki Al'hussain Khalil ya kama hannun Babban ɗansa kuma takwaransa Ibrahim Khalil.
Majeederh na zaune a saman dining bayan ta gama zubawa kowa abinci dake daman ita tayi, Rohaan ya kalli plate ɗin Khalil lafiyayyen ƙosai ne wanda ya ji ƙwai da kayan ƙamshi, sai kuma kunun gyaɗa wanda ya ji madara sai nau'in kayan itatuwa ya ce "Ya mu duk kika zuba mana abinci shi kuma sai kayan ruwa?" A tare Ummie da Majeederh suka ce "Dare ne ai, sun masa nauyi" Roohan ya ce "Ya Allah ka aurar dani ka kawo wacce zata ce tana so na" A tare Zizi da Badi sukai dariya gabaɗaya sun yi zuru-zuru saboda basu taɓa zama da yunwa sai wannan shekarar ba. Ƙhulud na kallon yadda Khalil ke bin Majeederh da kallo yama kasa cin abincin ita kuma taƙi yarda ya sanya idanunsa a nata, Ƙhulud Arzaan ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce
"Na'am, Majeederh kike kira Granny?" Jee ta ɗago kanta ta kalli Ƙhulud Arzaan ta ce "Malama Majeederh Granny na kiranki fa, tun ɗazu maybe ba kiji bane" Majeederh ta miƙe daman ta gama abinda take Ƙhulud ta kalli Khalil tare da kashe masa ido ɗaya, ya shafa kai yana ɗaukan ragowar kunun gyaɗar da yake a cup ya miƙe tsaye hannunsa ɗaya zube cikin Aljihu Zizi ta ce "Baka gama cin abincin ba Kspider" Bai juya ba balle ya bata amsa, Ummie bata ce komai ba domin tasan me zai aikata,ta kalli Zoya da Zohal da twins ta ce "Kuzo muje, zaku harami?" Suka ɗaga mata kai da sauri ta kwashi yaran zuwa sashinta.
A hankali Majeederh ta shiga bedroom ɗin Zaytoon idanunta ya sauka akan Granny wacce take kwance saman bed ɗinta tana bacci dalilin maganin data sha, gyara mata kwanciya tayi tare da juyawa ta nufi waje a daidai wani corridor wanda aka kashe hasken wajen ta tsaya tana lalubar hanya, tana ƙoƙarin tafiya ta ji an rungumeta ta baya, ta sauke ajiyar zuciya gabanta na faɗuwa sosai ƙamshin turaren shi ya jima da bayyana mata waye, sun jima haka kafin ya juyo da ita gabansa bakinta na rawa ta ce "Ka sake ni?" Ya yi mata shiru sai sake matseta ya yi a ƙirjinsa yana sauke ajiyar zuciya a hankali, ta fara kokawar kwacewa ya san kuma hakan na nufin ta yi fushi ne, ya ɗan kurɓi kunun hannunsa tare da ajiye cup ɗin saman window ya damƙo kanta yana haɗe fuskokinsu waje guda laɓɓansa a saman nata, Majeederh ta buɗe baki da niyyar yin magana ya yi saurin juye mata kunun bakinsa hakan ya haddasa mata yin shiru bisa dole ba dan tayi niyya ɗin ba, ya sunkuya tare da ɗaukanta ya bi ta can ƙofar baya ya nufi sashinsu da ita, idanunta rufe tana sake kwantar da kanta a lafiyayyen ƙirjinsa tare da shaƙar ƙamshin turaren shi na Boadicea The Victorious mai kwantar mata da zuciya,a nutse a hankali kuma ta buɗe maƙoshinta tare da shanye kunun ɗaya juyewa mata, har daɗi da garɗin gyaɗar suka mamaye bakinta.
Khalil na zuwa ya kwantar da ita saman gado ganin tana ƙoƙarin tashi ya bi bayanta ya danneta da ƙirjinsa tayi saurin rufe Idanu tana damƙe damtsen hannunsa muryarta na rawa saboda hancinsa da yake goga mata a dugan wuyanta ta ce "Ma...man cikina, our baby" Ya sassauta nauyinsa yana zame abayar jikinta hannunsa ɗaya ya sauka a kan mararta data fara girma sosai daga nan kuma ya fara shafa dugwayen ƙafafuwanta idanunta rufe jikinta ya fara ɗaukan rawa ta ce "Let go of me?"
"I won't" Ya furta a taƙaice kafin ya mirgina gefe yana jawota ya ɗorata saman ƙirjinsa, hannayensa rungume da ƙugunta ta baya wanne ya haɗa da nasa ya manne waje guda, bakinsa a kunnenta yana fesa mata numfashi mai zafi ƙamshin kunun na fitowa saboda ko brush bai yi ba, bayanta yake shafawa a hankali har ya samu nasarar ɓalle rigar jikinta ta rage sai Inner wears, jikin Majeederh ya saki domin Khalil ya san duk abinda tafi ƙauna a nutse a taushashe kamar mai raɗa yana ƙasa da muryarsa ya ce "I'm sorry" Ta yi masa shiru ya sake cewa "please" Ta buɗe ido tana kallonsa kafin ta ce "Sorry for?"
"My mistake" Ya mirgina kai yana tallafo fuskarta ya ce "Na miki ihu gaban mutane, babban damuwata gaban yaranmu" Ta ɗan yi murmushi ta ce "It's ok" Ya shagwaɓe mata fuska yana kwaikwayon muryarta ya ce "Kiyi haƙuri i won't do it again, ina tsananin son ki kuma shi ne sanadi ALLAH YANA GANI, and ba laifi na bane"
"Laifi na ne kenan?"
Ta tambaye shi tana tsare shi da sexy eyes ɗinta wanda nan take suka sake sauyawa Khalil lissafi ya kasa furta komai sai lip's ɗinta daya fara zagayewa da hannunsa ta ce "You don't trust me, kana tunanin zan iya cin amanarka ne? Idan zan ci me ya sa lokacin da ake zaton ka mutum banci ba? Sai yanzu, da nake ganin ba zan iya rayuwa babu kai ba? Da nake ganin ka riga ka cike dukkan gurbin zuciyata da soyayyarka, da nake ganin ka zama silar yaye damuwata, sai yanzu da hankalinmu ya kwanta, babba abu kuma ina sonka amma shi ne zaka mini ihu a gaban mutane harda ma John?" Sai kawai ta fashe da kukan shagwaɓa tana buga ƙafa da yarfe hannu tare da girgiza jikinta, hakan yasa gabaɗaya na jikin nata motsawa Khalil ya ƙarasa susucewa ya rarumota ya rungumeta sosai yana sauke wani irin numfashi a kiɗime ya fara sauke mata wasu Single Lip Kiss, breathing ɗinsa na sauka a zafafe, so yake ya rarrasheta amma sam bai san ya zai yi ba, ita kanta Majeederh sai data tsorata, tun tana dauriya ta fara ture shi zufa ta wanke mata jiki a gigice a kuma wahale ta ce "Cikina, marata" Maimakon ya saketa tunda ya samu abinda yake so amma kamar ta ƙara masa ƙarfi ne ya sake mata Leave a Mark Kiss, yana ficewa daga hayyacinsa jikin Jee ya fara saki ta raina kanta yau asalin Dr Ibrahimul-khalil take gani, wasu irin hawayen so da ƙaunar mijinta suka dinga fita daga cikin idanunta, tasan baya hayyacinsa da tuni ya fahimci halin da take ciki kuma daman tarata ya yi ta wannan hanyar yake son rarrashinta can ƙasa ta ce "Ya Allah kada kasa Khalil ya yi sanadin fitar cikin nan" idanunta na rufe hannunta ya saki, gudun ruwan da Khalil ya ji a cinyoyinsa wanda suke fita da zafi ya dawo dashi cikin hayyacinsa, ya zame daga jikinta da ƙyar wani buɗe Idanu ya yi lokacin da idanunsa ya sauka akan bedsheet ɗin da cinyoyinta jini yake fita daga jikinta harda guda-guda a gigice cike da tsoro ya tallafota yana "I am sorry Sexy mama, na rasa tunanina" Da ƙyar ta ce "Ka kira Ummie karmu rasa babynmu khalil....," Wani gudan jini ne ya sake fitowa wanda ya sanya Majeederh ƙanƙame Khalil jikinta na rawa.
[11/2, 20:11] Ummu: Da sauri ya kalli Akeeth ya ce "Boss binsan zaka yi? zuwa can Saudiyya ɗin?" Akeeth ya dinga kallon yaron nasa mai suna Ziyad, ganin baiyi magana ba ya sanya Ziyad cewa "Idan babu damuwa kuma ba zan shiga rayuwarka ba, yau ɗaya ina son ka bani dama na baka shawara a matsayina na musulmi kuma ɗan uwanka, wanda yake ci a ƙasan ka" Akeeth ya ɗan yi gyaran murya hakan yasa driver ya ja suka nufi asibiti, Ziyad ya sake cewa "Ka bani dama please" "Ina jinka Ziyad, amma a cikin shawarar da zaka bani banda rabuwa da Malama Majeederh ok"
Da sauri Ziyad ya ce "Dole a kanta ne, ka saurare ni a karo na farko, ba zaka taɓa nadama a cikin shawarar da zan baka ba" A hankali Akeeth ya ce "Ina ji" Ziyad ya ce
"Kai babba ne, kuma mai hankali kasan menene ya dace da wanda bai dace ba Boss, yanzu menene ribarka idan ka auri wacce bata son ka?" Akeeth ya yi shiru, Ziyad ya ɗora da "Kai ne da matarka harda yara kuna rayuwa ta farin ciki, kwanciyar hankali da jin daɗi sai rana tsaka wani ya kawo kai da nufin rusa wannan farin cikin, da nufin rabaku rabuwa ta har abada bayan kuma duk duniya banda iyayenka ba wanda kake so sama da matarka don Allah ya zaka ji?" Akeeth ya rufe ido yana dafe kansa dake juya masa, a zaune yake amma jinsa yake kamar zai kifa, a hankali ya girgiza kansa ya ce "Ba zan barshi ba"
"Good, kuma tayaya kake tunanin Khalil zai barka ka raba su da Malama Majeederh? Idan da wanda zai fara bada shaidar soyayyar da sukewa junansu tun kafin su kasance miji da mata bai shige kai ba, zata kawo shi gidan marayunka, ya yi sati zuwa wata da ƙyar suke rabuwa, balle yanzu da yake ganin cewa ita ɗin matarsa ce? Kasan waye Khalil? Idan ransa ya ɓaci shi da mahaukaci bashi da banbanci, ina tunanin kamar ka shiga cikin hurumin Ubangiji ta hanyar nuna maitarka ta son matar aure, matar wani, kuma ba ƙiyayya tsakanin su balle ka ce" Akeeth kallon Ziyad kawai yake, sosai ya fahimta amma zuciyarsa ta kasa fahimta ko gane abubuwan da Ziyad ɗin ke faɗa masa a nutse ya ce "Amma na riga shi son ta, tun a lokacin da take kawo shi gidan marayun nake son ta, i don't know what comes over me dana kasa fuskantar ta da soyayya wallahi"
"Hakan yana nufin ita ɗin ba alheri bace gareka, ita ba kowa bace face ƙaddararka (Your destiny)" A hankali ya ce "Destiny? Fate? Ƙaddara kuma?" Ziyad ya jinjina kai ya ce "Ko shakka babu, Majeederh is your destiny ita ce ƙaddararka, duk abinda Ubangiji zai jarabci bawa da shi har yake wahalar da shi to tabbas abun nan shi ne ƙaddarar shi, kuma kar ka bari hakan ya yi tasiri a zuciyarka akwai mata da yawa a duniya masu ilimi, aji, kyau, da duk wasu Qualities da kake buƙata" A taƙaice Akeeth ya ce "Qualities ɗin Malama Majeederh da ban yake, she's different from others, daban take da sauran matan, kawai na yi sake ban taɓa zaton Abraham zai girma ya ce yana son Majeederh ba, ban taɓa zaton zata iya auren shi ba, na ɗauka za ta yi tunanin yarintar shi ta dubi ƙanƙantar shi" "Me zaka nuna masa a yanzu Boss? Dame zaka fi Khalil ɗin? Da shekaru ne dai kawai, su kuma shekaru are just a number" Akeeth ya kalli Ziyad kamar yana son gasgatawa, Ziyad ya girgiza kai ya ce "Kuma shi namiji a duk inda yake namiji baya ƙanƙanta, zanen sunan shi na namiji zai ta kasancewa cike da iko, kamar yadda Ubangiji ya faɗa a cikin Alkur'ani, suratul Nisa'i, maza gaba suke da mata zasu iya jagorantar su a komai, don Allah Boss karka raunata zuciyar Khalil yana tsananin so da ƙaunar matarsa, yadda ya shaƙu da matarsa ko da iyayensa bai shaƙu ba, ni nake bibiyar shi nake ganin komai, yana da ɓoyayyen sirri fitar shi kawai ake gani, amma yana da wani irin Qualities wanda ba ko wanne namiji ke dasu ba, yana yin abu don Allah shi ya sa bai damu daya faɗawa jama'a waye shi ba, yadda ba a haifeka mahaifa ɗaya da Majeederh ba, haka ba zaka taɓa mutuwa saboda baka sameta ba, believe me" Akeeth ya ce "Abraham bashi da hankali, yana da zuciya bai cancanta da zama Mijin Malama ba, ina tsoran watarana ya yi mata illa nafi kowa sanin waye shi wallahi, Ziyad kar kaga laifina ko ban auri Majeederh ba, kawai ta samu wanda zai dace da ita but Majeederh ba tayi deserving auren mutum kamar Abraham ba, duk wahalar nan data sha" Ziyad couldn't speak, ya kasa magana gabaɗaya sai kawai ya ja bakinshi ya yi shiru, hospital suka nufa aka bawa Ziyad gado saboda karayar hannunsa yana buƙatar resting bed.
Idanunsa rufe ya shigo cikin haɗaɗɗen parlourn gidan nasu, ya yi tsaye, magidanciyar matar dake zaune saman kujera da counter a hannunta ta kalli Akeeth a hankali ta ce "Baka sameta ba?" Ta faɗa a taushashe Akeeth ya yi saurin cillar da wayar hannunsa ya ƙarasa gaban Nenne ya zauna yana ɗora kansa a cinyarta ta shiga shafa kansa tana jin yana sauke ajiyar zuciya "Zaka haƙura yanzu dai ko? Ka tabbatar ba rabo tsakaninku?" Akeeth ya ɗago kai ya kalli mahaifiyarsa ya ce "Tayaya zan iya haƙura da ita Nene? Nida ita kamar ɓarin gyaɗa ne how can you imagine zan rayu without her eh?"
"Me kake so yanzu Akeeth?" A hankali ya ce "Your help, your support, and your prayer" Ta riƙe hannunsa ta ce "Addu'ata kullum tana zagaye da kai, ina yi ba ranar fashi"
Da sauri ya ce "Call Majeederh and ask her to love me, please Nene" Nene ta ce "Karka zama mai tsananin son kanka a cikin al'amarin rayuwa Akeeth, babu rabo tsakaninku tunda har bata kasance matarka ba, ka yarda cewa ba kai ne MIJIN MALAMA ba, Idan Rabo ya rantse ko babu ciwo dole a tafi, haka Idan Rabo ya rantse duk wahala duk ƙiyayya dole ta kasance matarka ka nutsu ka kwantar da hankalinka". A hankali idanunsa na cika da wasu hawaye masu zafi sosai ya ce "Nene!"
"Ka yi haƙuri" Ya damƙe hannunta sosai yana kifa kansa a cinyarta ya ce "Nene, zuciyata ba daɗi na yi kuskure" A hankali itama idanunta na cika da hawaye ta ce
"Babban kuskuren shi ne amfani da sunan Mr no name, da Akeeth ka sanya maybe da tasan da zamanka, kayiwa kanka uzuri kayiwa Majeederh uzuri idan da wacce ta cutar da rayuwarku bai huce Latifa Omar ba, ka yi addu'a ka manta" Ya yi shiru kawai, Nene ta shiga damuwa Akeeth kawai ta mallaka a duniya shi ɗin maraya ne ubansa ya mutu ya barshi da arziƙi kamar ba zasu ƙare ba, bashi da aiki sai na bata labarin Majeederh, ranar da aka ce Majeederh tayi cikin shege a sume suka nufi asibiti da shi, kuma shi ne wanda ya yi rubutu a media domin kare hak'ƙinta, tana ganin al'amarin shi kamar zaucewa irin na masu fama da shigar sabuwar Soyayya. Ta ce "Akeeth ga ƴar uwarka? Ga Rusul?" Ya girgiza kai kawai ya ce "ALLAH YANA GANI Idan har ban auri Majeederh ba to na haƙura da aure" Ta zare ido ta ce "Idan baka yi aure ba sai me? Ka rufa mini asiri kada Aljana ta aureka (ALLAH YANA GANI)". Bai furta komai ba ya miƙe ya nufi part ɗinsa idanunsa rufe yana jin wani irin zazzafan zazzaɓi na rufe masa jiki.
A can Ikot Ekpene Prisons Mr President ne zaune shi da Latifa Omar bayan ya samu kaɗaicewa da