Showing 18001 words to 21000 words out of 126557 words

Chapter 7 - MIJIN MALAMA Book 2 Complete by Nimcey Sarauta .txt

you okay?" Tana kuka sosai ta ce "how can i be okay? Majeederh na yi ɓari cikina ya sake zubewa Bestie i lost my unborn" Majeederh ta ce "Subuhanallah! Sorry Dear Allah zai kawo wani" Latifa ta ce "Ykk? Yanzu dai lafiya kuke da his Excellency?" A hankali ta ce "Allhamd" ta ce "To ma sha Allah" suna gama wayar Latifa ta miƙe ta nufi bedroom ɗin Aliyu ta same shi yana bacci a hankali ta shiga ɗaukan shi photo da sauri ta fice daga ɗakin, zata yiwa Hassenatou sending sai ta fasa ta ce "Bari idan na dawo na tura" Kai tsaye wajan Turzum ta nufa ta same shi kamar kullum ya ce "Me kike so?" Ta ce "Kawai a raba auren nan, tana can hankalinta kwance maganar da nake maka gidan jaridar da nake aikin sun kureni, to akan me zata na jin daɗi ni ina wahala?" Ta ƙara girgiza kai ta ce "Impossible, ni burina ka san duk yadda kayi ka aura mata wannan gantalallen yaron, tunda shi ne wulaƙantacce tun da babu wanda ya san asalin shi wasu cewa suke ɗan bashi ne wasu kuma kidnaping" Turzum ya sakin wata dariya sosai kafin ya ce "To uwar azzalumai, mene sunan yaron?" Ta ce "Wai Abraham Denial David" Turzum ya ce "An gama, shi ne wannan?" Tayi saurin kallon ƙwaryar ta hangi Abraham zaune shi ɗaya a gefen titi ya yi jigum bakinta na rawa ta ce "Shi ne, wallahi shi ne" Turzum ya ce "Ki ɗauka ya zama MIJIN MALAMA" Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Yanzu zan fara bacci da yawo nasan watarana abincin da zasu ci sai ta fita bara" Bayan ta gama ta fito tana ƙoƙarin tura tura pictures ɗin wasu mutane suka taho da gudu akan babur tare da fisge wayar da jakar sukai gaba, wani irin ihu Latifa tayi tana binsu amma ina sai ihu take ita kaɗai tasan mene a cikin jaka da wayar, wani tashin hankali ya ƙaru tana zuwa ta samu Aliyu ya babar mata latter ya tafi Cairo for 3days... Uncle Isma'il ne ya kalli Abbu wanda tunda suka shigo parlourn bai ce musu komai ba, Uncle Isma'il ya gyara zama ya ce "Nura ya kawo kuɗin auren Aaliyyah na amsa, a matsayinka na uba nake faɗa maka domin zan sanya ranar auren" Abbu ya kalli yayan nasa cikin ƙasa da murya ya ce "To" Uncle Bello ya ce "Yanzu kana nan akan bakan ka na tsinewa Majeederh? Akan wanne dalili? Sbd gudun abin duniya wanda kuma mugun kalamanka suka jefata cikin wannan yanayin" A hankali Abbu ya ce "Please Bello bana son hayaniya bana gane komai for now" Uncle Isma'il ya ce "Ko dai ka gane ko baka gane ba matsalarka ce, tunda ka zaɓa mata miji Abuturab akan ya zama MIJIN MALAMA ba tare da sanin tana so ko a'a ba, kana hana matarka zuwa wajanta, ba komai watarana sai labari" Yana faɗin hakan ya fice Uncle Bello ma ya bi bayansa, a entrance na gidan suka ci karo da Raihana riƙe da trolley tana ya Uncle B ya ce "Ke kuma fa?" Ta ce "Uncle ya yi tafiya ne wai wata uku zai ni kuma ba zan iya zama ba gsky" Ya jinjina kai ya ce "Ohk ai Ruma ma na ciki" A hanya Uncle Bello yake faɗawa Uncle I yana ta sakawa ai masa roƙan Allah akan Alpha.... Da asubar fari bayan idar da sallah Majeederh na zaune tana azkar kamar daga sama taga mutum ya shigo hankalinsa a tashe ta yi saurin miƙewa tsaye kafin tayi magana ya miƙa mata envelope ya ce "Idan gari ya yi haske ki je gida na miki saki ɗaya, ki yi haƙuri amma wallahi Allah ina son ki, Allah da Manzonsa su ne shaidata i don't even know what comes over me, ina abu madly kawai na ji bani da nutsuwa idan ban sake ki ba, i don't mean to hurt you anymore, wlh ina son ki kuma ki saka a ranka watarana zan dawo" Tunda ya fara magana take kallonsa jikinta sai rawa yake da kyarma lura da yanayinta ya sanya ya jata jikinsa ya rungumeta sosai idanunsa cike da hawaye ya ce "I so much loves you Jiddo, i love you with all my heart and soul amma wallahi idan ban sake ki ba zan samu salama a raina ki yafe mini" Sai a lokacin kuka ya ƙwace mata ta ce "Me ya sa? Wacce irin ƙaddara ce wannan Abuturab? Me ya sa zaka wulaƙantani gabaɗaya watanmu nawa da auren, zaka sanya na shiga jerin matan da za'ana lissafin yawan auren su, me na yi maka haka don Allah ka yi haƙuri kace wasa nake Innalillahi wa'inna ilahir!" Wani irin kuka take kamar zuciyarta zata fita jiya ta gama waya da Uncle ta ce lafiya lou suke amma yanzu ta koma ta batun saki? Jikinta har jijjiga yake shi kansa Abuturab kukan yake ya rungumeta sosai a jikinsa Allah taga zuciyarsa na son Jiddo ɗinsa Ubangiji shi ne shaidar shi "I am sorry, please Hawwa'u ki yafe mini" Kamo fuskarta ya yi trying to kiss her for the first time tayi saurin janye jikinta, babu abinda ta ɗauka sai wayarta ta yi waje, securities basu hanata fita ba, tana zuwa titi ta samu napep ta shaida masa inda zai kaita, tayi shiru sai ajjiyar zuciya take saukewa har suka ƙarasa gidan Uncle Isma'il ɗin mai napep ya dinga magana firgigit ta ce ta dawo tunaninta tana sakkowa ya ce "Kuɗin fa?" A hankali ta ce "Bari na amso" Ganin yanayinta ya ce "Kiyi sadaka da su sbd Manzon Allah" Ta ce "Ngd" Uncle Isma'il na zaune shi da Anti da Jawaad da Sona daman sun saba kullum da sanyin safiya sai sun haɗu waje ɗaya, da sauri ya miƙe tsaye ganin Majeederh kamar an cillota Ya ce "Hawwa'u lafiya?" Ta kasa cewa komai sai jan numfashi da take ya amshi envelope ɗin hannunta, wani irin baya ya yi zai faɗi Jawaad ya riƙe shi ya zube yana faɗin "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Abuturab ya cucemu amma babu komai kansa ya cuta, laifinmu ne da muka bashi ƴar mu bayan bai cancanta ba, laifinmu ne da muka bashi ke bayan baki dace dashi ba, wlh tallahi zai san ya yi da ɗan halak" Ya kalli Majeederh ya ce "Da zarar kin yi idda ki sanar dani" zuciyarta tayi mata nauyi sosai da ƙyar ta ce "Bani da idda" Uncle Isma'il da Anti suka kalli juna, tuni Jawaad ya fice daga cikin Parlourn shi da Sona da mamaki Anti ta ce "Kina nufin tunda kika je babu abinda ya haɗaku?" Majeederh tayi shiru Anti ta jinjina kai ta ce "Ya cika tantiri a ƴan iska shi no 1 ne, kenan bai yarda dake ba all this day's? Kenan ƙyanƙyamin haɗa jiki yake dake" Uncle Isma'il ya yi murmushin takaici ya ce "Wallahi wallahi a gobe zan ɗaurawa Majeederh aure da duk wanda na yi niyya" Da sauri ta ce "Uncle please na haƙura da auren" Ya wani kalleta ya ce "Ba zaki ƙare rayuwarki a haka ba, dole ki yi farin ciki kamar kowa dole ki rabauta da miji mai son ki da ƙaunarki, Majeederh buɗe kunnenki da kyau zan baki zaɓi, da Mai martaba Ajlaal Sultaan, da Barrister Aliyu Sufyan, da kuma ɗan abokina Junaid wakike so?" Da wani irin sauri ta ce "Ajlaal kuma Uncle? Mijin Ƙhulud? Aliyu mijin Latifa? Wlh Uncle duk duniya ko zan mutu babu aure ba zan taɓa auren mijin Bestie ba ai cin amana ne" Anti ta ce "Ji shasha? Bashi ne ya ce yana son ki ba? Ko Ubangiji ne ya haramta hakan?" Majeederh na kuka sosai ta ce "Mijin Latifa? Bani da Aminiya sama da ita..." Sai kuma ta saki kuka sosai Uncle Isma'il ya ce "Tashi ki je, ai Ajlaal ɗin jiya ya nemi appointment dani nace masa kin yi aure to Allahamdulillah ba zai taɓa komawa Saudiya ba sai dake, na yaba da halinsa nutsuwarsa da nagartar shi ya faɗa mini yadda ya jima yana son ki tun a Misira" Zatai magana ya daka mata tsawa ya ce "Ban waje, wallahi sai na nunawa Abuturab ni ma ɗan iska ne kuma ɗan yau, zan nuna masa baki rasa mijin aure ba" Yana faɗin haka ya miƙe tare da ɗaga waya ya fita.... Majeederh ta kasa sukuni ita dama a barta ba wani aure daga sakin nata zaa ƙara ƙaƙaba mata wani auren? ta rushe da kuka har gari ya gama haske tana kuka sosai, tunda Uncle ya fita kuma bai dawo ba gashi har wajan huɗu na yamma, tana zaune abin duniya ya yi mata zafi aka buɗe Ƙofar tare da shigowa Sona ce ta ce "Anti wai kizo ana kiranki a parlour" muryarta bata fita ta ce "Waye?" Ta watsa hannu ta ce "Ban sani ba" Tana faɗin hakan ta fice da sauri, Majeederh ta jima kafin ta ɗauki vail tayi rolling kanta tunda yanzu ta daina saka liƙab, a hankali a sanyaye tayi waje ba zaka taɓa cewa tayi 35yrs a duniya ba, tana shiga parlourn taga ba taga kowa ba, a hankali ta sake dubawa tsaye ta ga mutum ya juya mata baya yana sanye da wata gezner ɗin shadda amy green ta amshi jikinsa sosai ta haska fatarsa hannunsa ɗaya zube a aljihu ɗaya kuma yana rungume da Baby Khalil dake bacci abinsa a hankali ta ce "Kai ka ke kira?" Domin bata gane waye ba zuciyarta na bata maybe Junaid ɗin ne ya kwaso yaƙunannun ƙafafuwan shi, jin shiru yasa ta saki tsaki domin kwana biyu faɗa take ji sosai ta juya zata shige ta ji sautin kamilalliyar muryarsa mai taushi da ratsa kunne mai cike da nutsuwa da Ilhama ya ce "Amincin Allah ya tabbata ga ruhin Ibrahimul-khalil......
*Like i always say and always emphasize, things are not always what they seem, Duk abinda kake zargi karka yanke hukunci a kansa sai kayi bincike, ba ko wacce kishiya ko stepmom take kansa cewa azzaluma ko macuciyya ba.. Akwai masu zuciyar musulmi wanda babu tsatsa a cikinta, akwai soyayya ta gaskiya akwai ta algus, akwai mai tsayawa a rai akwai mai gundira..Never and never judge a book by it's cover idan kuma ba haka ba you might spend the rest of your life regretting... Kuyi ta turo ƙudundunanniyyar dubu ɗaya amma kuna bawa mutum dubu ɗaya as free🤓to ai ko ɗan-gote akewa haka ya tafka zabgegiyar asarar balle Sarauta. Ni ba zan zagi ko Allah ya isa ba, ba kuma zanta surutu ba akan abu ɗaya ba, balle bakina ya yi tudu a barni da siyan mansileta.*




#Who is the husband?...
She looked at him with surprise and excitement baki buɗe take kallon Khalil She couldn't believe that he was in front of her, because he was different from the Khalil she knew before, da sauri ta rufe bakinta tare da ɗauke Idanunta tana haɗe fuska sosai domin har cikin ranta bata ƙaunar sake ganinsa a rayuwarta. Abraham dake tsaye rungume da Baby Khalil ya ɗan ja baya kaɗan yana ƙare mata kallo frm head to toe, ta sauya bakiɗaya ta rame sosai idanunta ya faɗa, sai siririn hancinta da tsukakken bakinta da duk ya bushe, shap ɗin jikinta na nan daram musamman faffaɗan waist ɗinta dake kwance, ya ɗauke idanunsa a hankali kuma ya miƙa mata Baby Khalil ɗin, ta watsa masa harara mai nuna yadda take tsananin tsanar shi, shi dai bai ce komai ba kallonta kawai yake, because He has nothing to say, no words in his mouth. Ta saka hannu ta amshi ɗanta tana sauke ajjiyar zuciya ta rungume shi sosai, Abraham dai yana tsaye hannunsa zube cikin Aljihu Majeederh ta kasa yin shiru da bakinta ta ce "Stay away from me and my son, ban ce kada ka sake dawowa gare ni ba? Ka fita daga rayuwarmu tun kafin nayi maka baki, kasan kamar uwa nake wajanka da nayi maka baki zai bika" Ya yi ta kallonta Calmly ya ce "Ohk" Ta juya zuwa bedroom ɗinta sai kuma ta ƙara juyawa taga ba ita yake kallo ba wayarsa ya zaro daga aljihu yana dannawa a nutse ta ce "Ka fita daga gidan nan, kayi nisa damu, kuma ɗana bashi da alaƙa dakai hakƙin uba na yafe" bakinta dake motsawa ya zubawa idanu a hankali kuma ya miƙe tsaye yana mayar da wayarsu zuwa aljihu, walking slowly ya nufi inda take fuska ɗaure bata taɓa ganin fuskarsa haka ba, ta juya zata shige bedroom ɗin ya yi saurin cafko hannunta tare da bayar da ita baya zuwa jikin bango ya saka hannunsa a both sides ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious yana fita daga jikinsa, ya dinga kallonta ba tare da yace komai ba, tama ɗauka yabar wajan ta buɗe idanu a hankali taga fuskarsa dab da tata kamar zai haɗe fuskokin nasu, tana ɗaga idanunta taga bakinta kawai yake kallo tayi saurin ɗauke fuska gefe ɗaya, silently bakinsa na fidda ƙamshin Spraymintt mouth freshener ya ce "Ohk, kuma nace wajanki nazo? da wani mitsitsin bakin ki" Majeederh dai bata ce komai ba, domin bata son duk abinda zai haɗata da shi. Ya ƙara matsar da fuskarsa dab da nata murya can ƙasa ya ce "Kuma da zaki ce ba ruwana ɗana ke ki kai cikin? Ki biyani cikina da ƙwayayen haihuwata sai na bar miki shi" Cikin fusata ta ce "Ka matsa ka bani waje before I lost my temper" Ya dinga kallonta sai kawai ya juya da sauri tare da barin parlourn, yana fita tana sauke ajjiyar zuciya mayataccen turaren shi duk ya addabeta, ta shige bedroom tana zama saman gado idanunta akan Baby Khalil daya kwaɓe fuska Exlty yadda Abraham yake abinsa tun yana ƙarami ta lumshe idanunsa tana jin soyayyar ɗan ta har cikin zuciyarta, gabaɗaya yanzu bata son aure tana son ta rayu haka tunda Allah ya nuna mata ɗanta na cikinta, ta fahimci babu komai a cikin aure sai tashin hankali ba soyayya babu kulawa. Anti ce ta shigo ta sameta tana jijjiga baby khalil dake kuka yana harba ƙafa Anti ta ce "Au ke ya kawowa?" Majeederh ta kalli Anti bata ce komai ba ta ce "Ai tun safe Abraham ke gidan nan a part ɗin Jawaad ya dameni wai ina ɗan shi, na faɗa masa yana gidan Uncle Bello babu jimawa sai gashi rungume da yaron, wannan mugun kamar da Abraham yake da yaron nan ya ɓaci kamar shi ne yana ƙarami" Majeederh ta haɗe fuska tamau ta ce "Plx Anti ki daina haɗa my son with someone else" Anti ta riƙe baki ta ce "Au haba? Dole ya amsa sunan Ibrahim Ibrahim, ko kuma Ibrahim I Khalil kuma kin manta ke kika saka masa sunan? Kuma dole a cewa mijin iya baba ba zaki hana duniya faɗar cewa ɗan Abraham bane" Majeederh ta ce "Ɗana tsarkake ne, shi daban wancan daban" Anti ta gyara zama sosai ta ce "To Albishirin ki Abraham ya musulunta, yama jima da zama Muslimi ya sauya gabaɗaya daga yadda kika san shi, ke banda ya sauya tunda yazo gidan nan ai wajanki zai fara zuwa amma ko sunanki bai ambata ba balle kuma yace kina ina, he just asked where's his son, kuma shi ma yasan ba zai sameki ba, da Jawaad yana basa labarinki bayan barinsa garin da kuma labarin mutuwar aurenk ko ƙala bai ce ba, ya kwanta tare da yin shiru kamar bacci, sallah bata taɓa shige shi akan lokaci da jami'i, so ki kwantar da hankalinki He didn't come because of you, he came because of his son, Stop the small talk and shrug" Anti ta miƙe tsaye har taje bakin ƙofa ta tsaya ta ce "Uncle yana kiranki" Gaban Majeederh ya faɗi ta ɗan marairaice ta ce "Plx ki ce bana jin daɗi" Da wani irin kallo Anti ta ce "Tell him by yourself" Tana faɗin hakan ta fice, Majeederh ta runtse Idanunta tana zuciyarta na bugawa sosai tasan rabuwarta da Abuturab alheri ne tunda ta roƙi Ubangiji ya zaɓa mata mafi alheri, bata son ta shiga layin matan da za'a dinga lissafawa Aure, bata ji daɗin aurenta da his Excellency ba, bata san farin cikin dake cikin aure ba, ta gama karaya tasan bata da rabo da farin ciki bata da rabo na ladan dake gidan miji. Da ƙyar ta miƙe ta nufi parlour ta samu Uncle Isma'il zaune shi da Uncle Bello suna magana a hankali suna ganinta sukai shiru,ta zaune ƙasan carpet kanta a ƙasa bayan ta gaishe su Uncle Isma'il ya ce "Hawwa'u" Ta kasa amsawa sbd fargaba ya ce "Kamar yadda na faɗa zan ƙara, wallahi wallahi Allah a gobe zan aurar dake, daman furniture's ɗinki da kayan kitchen da komai suna nan, abu ɗaya zan faɗa miki inma ki fitar da gwani a cikin su, Mai martaba Ajlaal Sultaan, Barrister Aliyu Sufyan, Engr Junaid, ko kuma Dr Ibrahimul-khalil, ko kuma na aura muki wanda ya fara zuwa ya saman wato Mai martaba" Majeederh ta rasa waye wani Dr Ibrahimul-khalil, idan ta auri Aliyu bata kyautawa kanta ba darajar Latifa a wajanta ta shige ta auri mijinta, idan ta ce Mai martaba kuma da wanne idanu zata kalli Ƙhulud Arzaan? Wacce ta ɗauketa matsayin ƴar uwa kamar Aaliyyah da Ruma da Raihana da su Sona, Du'a, Widad da Sahar? Idan kuma ta ce Engr Junaid bata san halinsa ba infact she don't even know who he is? Uncle Bello ya numfasa ya ce "Kina da lokacin daga nan zuwa Subhi, ki yanke hukuncin da kike ganin ya dace dake Hawwa'u, ki dai sani a wannan karan zaki rayuwa da wanda yake son ki ne, kuma a yau kowa zai zo ya sameki ki bashi lokaci ku tattaunawa, but am sure you'll like His Highness" Uncle Isma'il ya girgiza kai ya ce "Definitely" Ita dai bata ce komai ba suna zaune Jawaad ya shigo ya ce "Uncle na sauke shi a special parlourn gidan nan" Uncle Isma'il ya ce "Ok zata zo" Ya juya ya kalli Majeederh ya ce "Ga can Mai martaba kije

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login