Showing 126001 words to 126557 words out of 126557 words

Chapter 43 - MIJIN MALAMA Book 2 Complete by Nimcey Sarauta .txt

bi ta window ya shiga bedroom ɗin ta. Majeederh na tsaye tana ƙoƙarin kwanciya a gajiye take sosai kamar daga sama taga an diro ta window an kuma kashe switch na bedroom ɗin, tana ƙoƙarin yin magana aka rungumeta ta baya, a hankali ya manne mararsu waje guda a kiɗime ta ce "Who are you, wa..waye?" Yaƙi magana hannunsa ya sanya ya farke ƴar rigar baccin dake jikinta yana sake rungumeta tare da shinshina wuyanta ta ce "Waye?" Muryarsa na rawa saboda abubuwan da yake ji da ƙyar ya iya furta maganar cikin ƙasa da murya ya ce "MIJIN MALAMA".






Allhamdulillah!
Komai ya yi farko yana da ƙarshe, ba zan ce labarin nan ya yi 💯 hundred patient ba, duk iyawarka dole ne ka samu kuskure ta wani gefen, ɗan adam ajizi ne mu zama masu uzuri. Bana da ƙarfin qiwar cewa na iya, amma ina da yaƙini na abinda zuciya ke ayyana mini harna rubuta, ba zance Rubutana yafi na kowa ba, domin ban san kowa ɗin ba, abu ɗaya na sani nawa Al'ƙalamin a kaifafe yake musamman ta ɓangaren zanen ƙaddara, ban yarda akwai happily ever after ba, ba kuma zan taɓa gasgata akwai zama na har abada tsakanin ma'aurata babu wani tasgaro ba, ba zan lamunci rashin jarabta ba, domin ƙara gasgata imanin mutum ƙaddara take, ban yarda jarumi baya mutuwa ba, domin kullum akan idanunmu mutane sun sha mutuwa, Miji ya mutu, mata ta mutu,ko iyaye, kenan zanen ƙaddara na rubutun ƙagaggen labarin daya samu nagarta ga mai yinsa done zanen ya zo mana haɗe da sunan mutuwa, a zamantakewa dole mu yarda da Sadaukarwa kuma tilastawa kanmu fahimtar ba komai muke nema mu samu ba, ko da alheri ni garemu SOYAYYA a zane take da rubutacciyar Tawada a rayuwar ko wanne. Kullum mata sune masu rauni, kullum sune suke wahala a labari shin baza kuzo rawar ta sauya zani ba? Kullum cikin force marriage ake ba zaku so wani abu wanda ba wannan ba? Me ya sa kawai namiji ke ganin mace ya ce yana so, ita macen bata da zuciya ne?.... Mu tara a littafina na gaba.


Na gina labarin Mijin Malama akan tasirin Ƙaddara, yarda da ita a matsayin mutum Musulmi, illar da ƙawaye sukewa aminansu, da kuma sadaukarwa, komai girman tawadi'unka da ilimin Addinin da kake da shi Ubangiji na iya jarabtarka, haka JINKIRIN AUREN na zuwa ta hanya daban-daban.


Godiya.
Na gode sosai bisa jumirin bina da kukai tun daga farko har ƙarshe, godiya ga Arewabooks followers wanda bakwa gajiya da sanya kuɗinku wajan siya, ALLAH ya ƙara arziƙi wadata da imani y sanya kuci gaba da bibiyata a ko wanne littafi.


Tambaya?
1.Mene kuskuren labarin?
2. Dame ka ƙaru a labarin?
3. Mene yafi birgeka a labarin?
4. Mene saƙonka zuwa ga marubuciyar MIJIN MALAMA?
5. Wanne kallo ku kaiwa rayuwar Malama Majeederh Abdul'aziz Khan da Dr Ibrahimul-khalil?


6. Wanne salo kuke son na sauya a labarina zuwa gaba?.


Ina da labarai uku masu inganci ko wanne yana da amfani kuma sun sha banban da Mijin Malama na rasa wanne zan muku next faɗi zaɓi ka wanne kafi so?


1.JOURNALIST LATIF
{Allah yana gani}
2. RUHI BIYU
3. MUNAFIKIN MIJI
4. ƊAN MALAM


Yi comment da wanda ka fi so, wanda aka fi zaɓa shi za a fara yi, kuma zai fara sauka ne a Arewabooks.


COMMENT
FOLLOW MY ACCOUNT ON AREWABOOKS


NA'IMA SULAIMAN SARAUTA
NIMCYLUV
08119237616
Kuyi magana na yi adding naku group ɗina mu tattauna.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login