Showing 99001 words to 102000 words out of 126557 words

Chapter 34 - MIJIN MALAMA Book 2 Complete by Nimcey Sarauta .txt

hargitse Uncle B ya ce "Kasan Allah idan baka daina kiran Majeederh matsayin matarka ba, hukuncin da zan ɗauka akan ka mai tsauri ne" Yaya Bilkisu data fito ta ce "A'a yana da ikon faɗar haka saboda an ɗaura musu aure, bayani za ku yi masa yadda ya kamata" Ta zauna ta ce "General kasan ba a aure akan aure ko? An ɗaura maka aure akan rashin sanin mijinta na raye, kuma Allah ne ya ƙaddara babu rabon wahala da samun zunubi shiyasa bai ƙaddara ka ɗora mata idda ba har kawo yanzu, kuma idan an samu matsalar aure a irin wannan maslahar ba wani babbar maudu'i za a ja ba, idan mace tana son mijinta na farko shikenan sai na biyun ya saketa ta komawa mijinta, ko ma bai saketa ba ya zama dole ta koma, idan tana son ko wanne sai a bata zaɓi na zama da wanda take so" Yaya Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya cike da tausayin General ta ce


"Kalaman Majeederh a kullum sun isa su sanya ka fahimci irin son da takewa mijinta, a tarihi na soyayya ban taɓa ganin kalan tasu ba, shi yasa nake musu uzuri da rashin kunyar su a wani sa'ilin, ka yi haƙuri ka amshi hakan matsayin ƙaddara, kana son Majeederh wannan ra'ayinka ne, Majeederh bata son ka Khalil take so wannan ƙaddarar ka ce, our destiny depends upon whether we live in harmony with God, following His moral teachings, baka da ikon sauya ƙaddararka, rashin samuwar Majeederh hakan na nufin Zuleehart ita tafi dacewa da rayuwarka ita ce alheri ga duniyarka"


Murya can ƙasa yana kallon Yaya Bilkisu ya ce "How do i know my destiny?" Yaya Bilkisu ta taɓa kafaɗarsa cike da ƙwarewa irin tata ta tsohuwar ƴar boko ta ce "Destiny can never be figured out it can only be revealed by trusting and following what feels right, a Karan kanka za ka ji wannan abun kana son shi ne har zuciya, to wannan abun shi ne ƙaddararka, da yawanci abinda mukewa mugun so ko tsana shine yake kasancewa ƙaddararmu" Ta kama hannunsa domin haƙiƙa son wanda baya sonka jarabta ce, ko da iya haka nan Ubangiji na iya yi maka azaba da laifukan ka. Ta ce "Your destiny is determined by your decisions, abu ne mai sauƙi cire Majeederh daga ranka idan ka nutsu ka fahimci dalilin daya sanya kake jinta a ranka, wanda kake so shi ne wanda kake jin motsin shi a zuciyarka a kullum, wanda kake so shi ne wanda ko sunan shi aka kira sai zuciyarka ta girgiza, wanda kake so a kullum shi ne zaka ji ko yana nesa dakai kake jin shi kusa da zuciyarka, wanda kake so da gaskiya shi ne wanda zaka sadaukar da komai saboda da shi, yana da kyau ka sadaukar da soyayyarka ka Khaljeed sau ɗaya kawai su samu nutsuwa da farin ciki"
Hawaye na zuba a idanunsa yana kallon Yaya Bilkisu muryarsa na rawa ya san ba zasu gane su fahimta ba a hankali ya ce "Can i change my destiny? Ta dafa shoulder ɗinsa ta ce "
"Why not? Wata ƙaddarar daman mu ke ɗorawa kanmu, wata kuma jarabawa ce daga Ubangiji,In simple terms, your destiny is decided by your karma. Every human has the power to change his destiny by changing his karma, karma means “Action" Ya yi shiru a hankali kuma ya tashi yabar parlon yana zuwa daidai ƙofa ya yanke jiki ya faɗi a sume. A gigice sukayi kansa ganin jini na fita ta hancinsa da baki, haƙuri da juriyar da Maman Alpha keyi ta ƙare ta fashe da wani irin kuka na tausayin ɗan nata, tasan Soyayya jarabta ce kuma addu'ar Zuleehart dole ta bisa saboda ya cutar da ita bisa yardar da tayi masa, a mota aka saka shi zuwa hospital.
Innati ta sake kallon Yaya Bilkisu ta ce "Balkisa sake miƙo mini ruwa don Allah don Annabi, wanda yafi na ɗazu ɗan iskan san yi" Har dare suna hospital Majeederh na son cewa Khalil zataje amma tana tsoro tana lura da yanayinsa a sama yake, kuma yanzu jinin sarautar ke aiki a jikinsa, yana zaune hakimce a tsakiyar gadonta daga shi sai red ɗin gajeren wando, cinyoyinsa masu ɗauke da kyawawan gargasa a bayyane a tanƙwashe su jikinsa babu riga gefen cinyarsa Alhassan ne ke kwance yana bacci bayan ya gama fashe mata plate da sauyawa ɗaki kama, Khalil na kallon faɗan da takewa Alhassan hadda tsawa shi dai bai kulata ba, saboda bai san yadda ta kula dasu ba tsayin shekaru biyu, ga kuma ciki daya ƙara mata masifa. Hannunta riƙe da ƙaramin cup mai ɗauke da black tea da Honey ta zauna gefen gadon tana ajiye cup ɗin akan table ta kalle shi taga hankalinsa yana kan system sai ba tayi magana ba, ganin kallon ya yi yawa ba tare daya kalleta ba ya ce "Uhm" Can ya kalleta suka haɗa ido sai kuma ya kalli system clamly ta ji ya ce "Meye MATA A YAU?" Jee ta juya idanunta ta ce "A ina kuma?" Ya juya mata system ɗin yana matsawa kusa da ita ya ɗora kansa a cinyarta kamar mai jin bacci Alhassan ya dawo dashi ƙirjinsa Jee ta ce "Oh wani program ne a Arewa24, naga sunyi inviting nawa tun last week" Ya yi shiru Ta shafa kansa a nutse ta ce "Ban zuwa ai" idanunsa rufe ya ce "Uhm, kuma na yi Accepting request gobe" Tai jim domin bata ɗauka zai amince ba, ta ci gaba da juya yatsun hannunta a cikin sumar kansa ya yi saurin riƙe hannunta ya ce "Kina son taɓa ni? Zaki jama kanki? Mun samu yaro mai wayo fa" Jee tayi dariya cike da kwanciyar hankali ta ce "Photocopy ɗinka ne, harsu haura katanga da fashe cups da yake da su plate da ɗan banzan ci" Ya mirgina gabaɗaya ya kalleta yana kwaɓe mata fuska kamar zaiyi kuka ya ce "Kuma ni ne ɗan banza? Ba na daina ci ba?" Ta shafa fuskarsa zuwa kwantaccen sumar ƙirjinsa ta ce "Hucewa salamun Ranka ya daɗe" Ta faɗi hakan tana kifa fuskarta a tashi tana ƙoƙarin kissing ɗinsa suka ji an banko ƙofa a gigice an shigo Maman Alpha na kuka sosai wanda ya sanya Majeederh miƙewa shi kansa Khalil zuciyarsa ta girgiza ta zube a gabansu da ƙarfi ta ce "Alpha is dead"


Allah ya a nuna mana Monday Lafiya, labari yana ta jana bana son skipping shi ya sa yanzu nake tunanin sai shekara zuwa shekara zanna new book, gashi dai a 2023 shi ne kawai Novel ɗin da nayi, kuma an hanani na ƙara samun costumers sai fitar mini da littafi ake kamar bani da gata😂bana son fiye surutu wlh tallahi ƙimata ta zube amma dai ba komai..... 08119237616
[26/09, 7:48 am] Sdy Auwal Gstc: *Ina masoya littafan Arewabooks? Marubuta da makaranta? Ga dama gare ku, duk wani littafi da yake tashe a Arewabooks saka same shi a page ɗinmu na*


*How to be successful writer in Arewabooks?* Ga marubuta


*How to read a romantic and love story?* Ga makaranta. Akwai tarin kyaututtuka ga wanda yafi kowa comment, akwai certificate and award ga littafin da yafi popular a arewabooks, kawai kuje kuyi following, da like na shafinmu na👇🏼 facebook
https://www.facebook.com/arewabooks1




Majeederh bata san lokacin data hantsilo daga kan gadon ba, tana ture kan Khalil, jikinta na rawa sai a lokacin ne take jin duk wata soyayyar shi matsayin ɗan uwa yana ratsa jinin jiki da tsokarta. Ta kasa magana sai kallon Maman Alpha take da wani firgitaccen tashin hankali, wanda ya kasa ɓoyuwa daga zuciyarta, gabaɗaya zuciyar buɗewa take a hankali ta shiga aikinta a gaggauce. Ƙirjinta tana jin kamar an ɗora mata dutsen dala da Gwauron Dutse saboda yadda take fusgar numfashi da ƙyar, ƙwaƙwalwarta na buɗe a gaggauce tana amsar saƙon, cikin yanayi na firgici da hali na gigita da manta kai. Khalil ya zura farar tattausar Muslimi thobe jallabiya ɗinsa, ta bi jikinsa ta kwanta kasancewar jikinsa ya buɗe ya ƙara cikar da zati da haibar shi ya ƙara bayyana a fili yadda maɗaukakan jama'a zasu gani su fasalta yanda kamalar ta kwanta a fuskarsa. Gashin kansa duk a barbaje baya son ya yi cutting ɗinsa gashi bai je saloon ba, ya ɗan juya sai yaga wani ƙaramin white ribbon siriri ya ɗauka ya tattare gashin ya ɗaure ya sauka a wuyansa, duk ya cuccure kamar Indomie, ya ɗauki p.cap ya ɗora a saman kan shi, babu abinda kake iya gani sai jajayen laɓɓansa masu kauri da taushi, sun ɗan jiƙe da damshin yawun Jee, sai fararen Idanunsa da suke jiƙaƙƙu kamar wanda hawaye ya kwanta a cikinsu, sun yi wani laushi a lumshe irin yanayinnan na kasala, asalin blue eyes ɗinsa da ba kowa ke lura dasu ba ya fiddo saboda yadda ya ɗan buɗe idanun yana gyara zaman agogon Rolex akan wrist ɗin shi, yanayin suffar Khalil ta cikakkun baƙaƙen ƴan America ɗin nan ne, a fusge kuma laushin fatarsa da ɗan duhunta kamar ta ƴan Etopia ko Mali, Khalil
baƙi ne sosai irin dark-skinned ɗin nan wacce har Shinning take, amma kana kallonsa kasan cewa hutu da jin daɗi sun zauna masa, saboda yadda dark-skinn ɗinsa tai fresh gwanin sha'awa _His elegant black skin_ sai sheƙi take cikin light blue ɗin hasken da yake ɗakin six-packs ɗinsa a bayyane ya bubbuɗe ta cikin jallabiya ɗin, ga Round face wacce saje da gemu suka yi covering ɗinsa,sexy eyes masu fitinannan ɗaukan hankali, ko namiji shakkar idanun yake balle mace, ba ruwansa da kowa amma wanda ya shiga inuwar shi a nan yake sanin asalin haukan Khalil, yana da rauni akan mata,baya son cin amana, ƙarya, da munafurci.


"Mu..mu..mutuwa?" Ya furta a rarrabe kamar bagware, yana fiddo idanunsa waje cike da razani, yama rasa cikakke kuma ainahin kalaman da zai amfani dasu wajen yiwa Maman Alpha magana ɗin. Majeederh ta kama hannun Maman Alpha ta ce "Ya..yaya..? Daman bai dawo ba gida ba? Karki ce mini ya mutu" Maman Alpha ta kama hannun Majeederh ta riƙe cikin nata idanunta na zubar da wasu azababbun hawaye wanda yake da cin zuciya ta ce "Ko wanne bawa mai rai a nan duniya, al'amarinsa na wanzuwa ne bisa tsarin Ubangiji, Alpha ya rayu a cikin uwa mai kyakkyawar zuciya na tsayin wata tara da kwanaki, tun kafin zuwan shi duniya Ubangiji maɗaukakin sarki ya zartar da ikon shi akan yadda rayuwarsa zata kasance a duniya" Ta sauke ajiyar zuciya tana ƙasa da kanta, Khalil duk baya fahimtar wannan farsafar zancan, mai wahalar fahimta azancin maganar na kalaman da akai amfani dasu sun dunƙule a kansa ne. A hankali Maman Alpha ta sake cewa.


"To me zamu ce da Ubangiji banda godiya ga ni'imar shi? Daman wanda bai godewa ni'imar Allah ba to zai godewa azabar shi, Alpha ya jawa kansa, tun a haihuwar Bilal yaci ace jirkitacciyyar ƙwaƙwalwar shi mai wassafa masa muggan abubuwa wanda zasu gurɓata goben shi, fahimtar shi Zuleehart kyauta daga Allah ce, kuma ita ce ni'ima a gare shi, ni, ke, Khalil, Alpha kowa na duniya yana rayuwa a cikinta bisa yardar Allah, kowa na rayuwa da kalar tashi ƙaddarar, wacce Ubangiji ya samar da ita tun kafin zuwanmu duniya, hakan rubutacce ne, kuma halataccen rubutu ne akan allon da ba zaiyi ƙarya ba, hannun da ba zai rubutu ba daidai ba, zuciyar da bazata cutar ba, kyakkyawan rubutu ne kamar rubutun tawada a jikin dutse wanda baya goguwa balle ya zama shuɗaɗɗe, barin Alpha garin nan, aurenki da Khalil, dawowar Alpha, mutuwar khalil, aurenki da Alpha, dawowar Khalil a matsayin rayayye gabaɗaya yana zane jikin Lauhul Mahfouz, wata ƙaddarar mune muke janta, wasu siya musu akayi, i believed cewa General ba alheri bane ga duniyarki shi yasa abinda ya faru, bai wakana ba sai ana ranar aurenku" A kiɗime Majeederh na damƙe hannun Maman Alpha muryarta na sarƙewa da ƙyar da iya cewa.
"Fahimtar dani meke faruwa? Ina jin kamar na yi ba daidai ba!" Maman Alpha ta ce "Majeederh alfarma nake nema, amma kafin nan kizo muje hospital ɗin" Majeederh ta juya ta kalli Khalil bai kalleta ba, ya ɗauki key d'in motarsa wanda alama ne ya kewa majeederh ta shirya, doguwar riga ta saka ta ɗauki mayafi tayi rolling, wani fitinannen kallo Khalil ya yi mata ba tare da ya ce komai ba yana ɗaukan Alhassan, wajan wardrobe ta nufa ta ɗauki hijab har ƙasa ta saka, ta nufi wajan Al'hussain a ɗan hankali ya ce "Madam, ur niƙab" Tayi jim domin bai taɓa nuna sha'awa akan niƙab ba, ta ɗan hargitsa kayanta ta ɗauka ta saka, ya dinga kallonta from head to toe kafin ya nufi waje ta ɗauki Al'hussain dake kusan lokaci ɗaya yaran suke bacci, suka jero gwanin sha'awa suka samu Maman Alpha a motarta, gabaɗaya suka kwantar da yaran a baya da wani irin gudu Khalil ke jan motar har tsoro ta ji, ta manta komai nasa a gaggauce yake yinsa, kuma ya saba da tseren mota tun sanda suke kasawa da ƴan sanda. Lokaci kaɗan suka ƙarasa shiga cikin hospital ɗin kai tsaye kuma Emergency, a reception suka samu Yaya Bilkisu dasu Widad da Du'a su nata kuka, jikin Majeederh ya yi sanyi zuciyarta ta karaya, Uncle Bello ya kalli matarsa ya ce "And who gave you the permission? Me kike ƙoƙarin yi?"
"Ni uwa ce, zuciyata ba zata ɗauki halin da ɗana yake ciki ba, zan nema masa abinda kai ka kasa nema masa bayan kana da ikon yin haka" Uncle Bello ya ce "Idan taƙamar shi ɗan uwanta ne kin manta ya suke da mijin nata? Ko kema son zuciyarki zaki gwada ne?" Maman Alpha ta cillawa Uncle Bello dairy ta ce "Ka duba, General shi ne ya sakawa Majeederh suna tun ranar da aka haifeta, babarta Fulani tayi Supporting nasa, ya nemi ta bashi Majeederh zai kula da ita, a nan Fulani ke cewa ba kulawar Majeederh ta bashi ba, har duniya ta naɗe ta mallaka masa Majeederh, ta bashi ita matsayin matar aure ya yi mata wannan alfamar, ya amshi batunta wanda ita ta kasa gane ribar tasa ce, sai dai ashe kashin dankali ne, General yana jin zai sadaukar da komai wajen ganin ya auri Majeederh ya cika mafarkin Fulani, da al'ƙawari na muradin zuciyarsa" Ta goge hawayen fuskarta ta ce "Kun kasa fahimta, nima a bincike na gano hakan gabaɗaya bedroom ɗin shi pictures d'inta ne tana ƙarama har zuwa girma, ba wanda ya taɓa faɗawa hakan wanda dalilin hakan akai masa asiri, after all these things he did, didn't he deserve to be Majeederh's husband?"


"Idan mutuwa gaskiya ce, hisabi wajibi ne, haka nan Soyayya ma gaskiya ce Ubangiji ke samar da ita a zuƙanta bayinsa, ba tare da sani ko tambayar su ba" Khalil dai kallonta kawai yake a hankali ya ɗauki wayarsa dake ringing shiru ya yi a hankali yana ƙasa da murya ya ce "Ko Latifa ne, arrest her directly ku kai ta prison" Yana faɗin hakan ya kashe wayar ganin Maman Alpha ta ja hannun Majeederh zuwa room ɗin da Alpha ke ciki ya miƙe tsaye walking slowly ya bi bayansu, rashin sanin abinda zai iya faruwa ya saka Uncle Isma'il da Uncle Bello da Yaya Bilkisu suka rufa musu baya. Cak Majeederh ta tsaya ganin gabaɗaya jikin General maƙale da na'ura musamman ƙirjinsa, cikin bakinsa ga oxygen ta hancinsa, sai wani green ɗin yadi da aka ja masa zuwa wajan cibiyar shi babu inda yake motsi a jikinsa kamar matacce, Maman Alpha ta juya ta kalli Majeederh sai kuma ta zube akan ƙafafuwanta tana riƙe ƙafar Majeederh ta ce "Alfarma nake nema a wajanki Majeederh, ba don na taɓa taimakonku a rayuwa ba, ba dan na wahalta miki ba, ba don na kasance cikin zuciyarku ba, yadda Ubangiji ya bayyana miki gaskiya akan Latifa da Hajiya Luba, yadda Ubangiji ya dawo da hankalin mahaifinki, yadda Ubangiji ya sadaki da dangin mahaifiyarki, kiji tausayina,kiji tausayin halin da ɗan uwanki yake ciki, ki duba girman Allah, kaɗaitar shi da buyawarsa ki sadaukar da soyayyar Ibrahim wa Alpha..." A gigice Khalil ya kalli Maman Alpha sai kuma ya cire p.cap ɗin kansa, tare da zare ribbon ɗin ya girgiza kansa gabaɗaya sumar ta wargatse ta rufe fuskarsa, a hankali ya yi kneeling down a gaban Maman Alpha shi ma ya dafa ƙafarta ya ce "I love you Maa, and i also respect you, ke uwa ce kina fahimta, ni i don't know how to explain yadda Ƴar madara take a raina, ki yi tunani idan na rasata ya Ummie na zata shiga? I love my wife ku barni da ita nayi rayuwar farin ciki don Allah...,” Kafin ya sauke Maman Alpha ta damƙe hannun Khalil tana kuka kamar ranta zai fita ta ce "Don Allah don Annabi Ibrahim, ba danni ba saboda girman da Soyayyar da kake ma Ummie ka barwa ɗana Majeederh bari na har abada....


[11/2, 20:11] Ummu: Follow my Facebook account👇🏼https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL


Ta bisa da Idanu kamar yadda yake kallonta gudun kada ya zaro mata wani zancan ta yi shiru, Khalil bai fasa kallon duk inda idanunsa yake son gane masa ba clamly yana ƙasa da murya ya ce "Yanzu ƴan uku zaki haifa ko?" Ta kalle shi ya ɗaga mata gira ta ce "Kawo kunnenka na faɗa maka" Ya matsa yana riƙota dragging her more closer to himself ya ɗora kunnensa a bakinta ta ɗan yi baya tare da saka hannu ta murɗe kunnen ya ce "Auchhhii" ya ɗan yi wani erotic and emotional sounds yana rufe ido a hankali ya ce "Faɗa mini" Ta ce "Eh, da Bad boy, Abraham, the one whose Love always tortures my heart.." Wanda kullum soyayyarsa ke azabtar da zuciyata. Idanunsa lumshe ya ce "Who? Waye?" Ta saka hannu ta shafa fuskarsa tana jan gemunsa muryarta na fita a hankali ta ce "My love, Ibrahimul-khalil" Ya buɗe ido ya kalleta sai bai ce komai, ba wanda ya ƙara magana har suka isa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login