Showing 96001 words to 99000 words out of 126557 words
Chapter 33 - MIJIN MALAMA Book 2 Complete by Nimcey Sarauta .txt
yi sallama ta shigo, suka kalleta Maman Alpha ta haɗe fuska, Latifa ta shigo tana tura wani tsohon mutum a wheelchair, suka dinga kallon mutumin Abbu kamar ya ganeshi sai kuma ya manta ina ya san shi. Maman Alpha ta ce "Mene ya kawo ki yau kuma? Maza tashi ki fita" Tana kuka ta ce "Don Allah ku saurareni, hakan zai sanya ku ƙara fita daga duhun da kuke ciki ta wani ɓangaren" Maman Alpha za tayi magana Uncle Bello ya ce "Bari muji meke tafe da ita ko?" Latifa Omar ta ce "Banga laifinku ba, na cancanci ko wane irin hukunci, son zuciya da kwaɗayi da kuma baƙin ciki ya jani zuwa cikin kabarina tun kafin lokacin mutuwata, ban kasance ƙawa Aminiya ta gari ba, duk abinda ya samu Majeederh ni ce sila amma ba komai ya zama laifina ba" Ta kalli Abbu ta ce "Abbu ka tuna wannan? Wani Alhaji Bashir da kuka yi maganar auren Majeederh akan Deal? Zai baka kuɗi ka bashi auren Majeederh?" Su Uncle Isma'il gabaɗaya suka kalli Abbu shi kuma ya dinga kallon Alhaji Bashir, Latifa Omar ta ce "Shi ne wannan, ga nan ya karɓi nasa hisabin duniyar, ka hana shi auren Majeederh bayan ka amshi kuɗin shi, akan gurɓatacciyar zuciyarsa ya sace Majeederh tare da reping nata, hakan ya faru ba tare da saninta ba, domin an gusar mata da hankali" Tayi ƙasa da kai ta ce "Maman Alpha idan kin tuna sanda bamu ga Majeederh ba tsayin sati har tace mana farkawa tayi ta ganta a asibiti to a lokacin akai reping nata, babana ya shirya hakan" Gabaɗaya suka kasa magana, Yaya Bilkisu ta ce "Ke mene haɗin ki da shi? Bayan Malam Umaru babanki?" Ta ce "Ni Adopted child ce, nima Shegiya ce bana da uwa shi kansa bai san wacece babata ba, yana da yara sunfi 30 yayi amfani da arziƙin shi ya yaudari ƴan mata da zawarawa da yawa, rabin yaran shi duka sikila ne kamar yadda Baby Khalil ya kasance sikila, Mijin Malama baya da alaƙa da baby khalil banda ta Kasancewar shi ɗan uwa, suna kama ne da Dr Ibrahimul-khalil saboda kasancewar, shi da Majeederh are cousins, baby khalil is my younger brother" Abbu ya kasa motsi, bai taɓa baƙin cikin kasancewar shi uba irin yau ba, yana ina duka hakan ke faruwa ne? "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" A fili ya ce
"Nawa ne kuɗin" Latifa Omar ta ce "Ba kuɗin ake buƙata ba yanzu, yafiyar Majeederh ni da mahaifina muke so, abubuwa sun mana yawa, duniya ta juya mana baya sai data bari muka gama jin daɗinta, naci amanar aure data mijina gashi yanzu nida haihuwa sai kallo amma yanke mini mahaifa, duka abubuwan dana shiryawa Majeederh ya dawo kai na, hatta aurenta da Khalil ni ce sanadi nayi zaton bashi da kowa, a gari kawai yake yana gantali, shi da gang team sai nayi zaton zata sha wahala idan ta aure shi, ashe bokana ya rufeni bai faɗa mini asalin waye Dr Ibrahimul-khalil mijin Malama ba" Innati ta miƙe tana dungure kan Latifa ta ce "Annamimiya, algunguma ƴar maza mai warin zina" Kuka kawai take, Alhaji Bashir baya motsi saboda paralyse shi kansa kuma sikila ɗin ce da shi. "Na yafe miki, dake da shi, but it's over between us" Latifa ta ce "Na sani, kinfi ƙarfina kin mini nisa, don Allah don Annabi ki bani baby khalil na riƙe na dinga kallon yaro a gabana ko zan ji daɗi" Majeederh ta ce "Allah ya sauwaƙa, ki ɗauka bashi da haɗi daku, zan ma nesanta shi daku" Maman Alpha ta ce "Ai yara kike so? Sanda kike ta zubar da kyautar da Ubangiji ya yi miki bakya tunanin zaki iya son haihuwa Nan gaba? Hoooo ƙaaasa! An yafe muku tashi kuje" Fita sukai jiki a sanyaye Abbu ya dafe kansa dake juya masa.
A hankali Khalil ya juya kujerar da yake zaune, bluetooth a kunnen shi yana jin komai dake faruwa, domin a jiya sai daya sanya wata na'urar ɗaukan sauti a gidan, ya kuma saita ta, idanunsa sukai jajur. John ya ce
"Mene amfanin ɓoye kanka ne? Yana da kyau su san mijin malama is still alive" Khalil baiyi magana ba, sai jijiyoyin kansa da suka fito tare da yin ɗoɗar a saman goshinsa, idanunsa sukai jajir John na lura da yadda naman jikin Khalil ke rawa, gargasar jikinsa ta mimmiƙe tsaye tana zubewa. Har John zai yi shiru sai kuma ya ce "Mene amfanin zuwa Orphanage ɗin nan kace zaka yi rayuwa cikin yaran da kake taimakawa?" Khalil ya miƙe tsaye yana dafe kansa John ya miƙe ya ce "Ko wajan Ummie ne ka....," Bai ƙarasa maganar ba yaji Khalil ya ɗauke shi da mari ya damƙi wuyansa ya haɗe da jikin bango duka jikinsa rawa yake idanunsa sun firfito waje da ƙarfi ya ce "Shut up!" Sai kuma ya saki John Khalil ya dafe kansa a gigice ya ce "My head" Daidai nan Faɗimatu ta shigo da basket kyakkyawar yarinya cikin kamilalliyar shiga, John ya ce "Wife stay right there" Faɗimatu ta kalli John wanda sunan shi tuni ya koma Othman Zannur. Ta ce "Dear Yaya Khalil na kawowa abinci fa" John ya ce "Wife i said ki tsaya nan ko" Ta tsaya tana kallon Khalil durƙushe, John ya kama hannunta suka fice tare da rufe ƙofar, babban Orphanage ne, gidan marayun ya haɗu Khalil tun yana asalin bad boy ɗinsa ya gina, Faɗimatu a gidan ta tashi itama har zuwa lokacin da John ya aureta, yara ne sosai a gidan Khalil na mutuwar son su kamar rai haka kowa na Orphanage ɗin. Khalil ya jima zaune kafin ya miƙe tsaye ya ɗauki bottle water ya zubawa tsakiyar kansa, kamar ya kira Zaytoon ko Mai martaba Ajlaal haka yake ji, amma ya ɗauki niyyar sai ya yiwa kowa hauka duk wanda ya shiga rayuwar Majeederh dame ƙoƙarin raba shi da ita more especially GENERAL ALPHA BELLO KHAN. tsayin wata guda kenan kullum Khalil yana zuwa bedroom ɗin Majeederh, sai asuba yake guduwa ya razana Uncle Bello hade da General, Majeederh kuma taƙi yarda ta tare, ta yarda zata rayu da ruhin Khalil tunda yana sanyata cikin farin ciki, kuma har yanzu a tunaninta a mafarki yake zuwar mata, tayi wani irin kyau haske da ƙiba Maman Alpha har mamaki take, cin abicinta ya ƙaru shi da kan shi Khalil ya fahimci haka, har wata guda ba wanda ya san labarin Khalil na raye! Even his mother, Aaliyyah bata ƙasar ma bakiɗaya ita da Barrister Aliyu ya ɗauketa sun barwa Latifa gidan.
Yau ma kamar kullum Khalil ya hauro ta katanga ya sanya fararen kaya voyel ne fari tas da shi, kai tsaye direction ɗin da zai kai shi bedroom ɗin Majeederh ya nufa, ya zuge glass ɗin window ya diro, abinda bai taɓa gani ba ya gani, ya ganta kwance ta rungume Alhassan dake ta kuka zai sha tea cikin dare tana bashi kuma ya tarwatsa cup ɗin saboda ya ji haushi, baccin da ya yi kenan bai sha ba, Khalil ya zubawa fuskar Alhassan idanu ganin wata mahaukaciyar kama da suke da yaron, nan da nan ya fara loosing control ɗin shi, so da ƙaunar yaron ya wanzu a zuciyarsa, ya ƙarasa bakin gado ya zauna, a hankali ya kifa kansa tare pecking kumatun Alhassan yana buɗe idanu yaga yaron ya kafe shi da Idanu, sai kuma ya ɗauke shi ya rungume yaron kamar yasan babansa ne ya ƙanƙame shi yana sauke ajiyar zuciya, sun jima haka kafin Khalil ya goya yaron abayan shi dake Alhassan ɗan fitina ne irin babansa ya ƙanƙame shi, Khalil ya kama window ɗin ya dira yana jin Alhassan yana kyalkyala dariya a haka ya fice da yaron goye a bayansa...
[24/09, 8:05 am] Sdy Auwal Gstc: *MIJIN MALAMA*
*BOOK 2 PAGE 96*
Arewabooks:
Facebook:
Instagram:
Tictiok:
Wattpad:
Okadabooks:
*Searching Na'ima Sulaiman Sarauta, to find out my account in all social network.*
*If you want to talk to me directly, find me on Instagram or Facebook👑*
Da sauri cikin wata kakkausar murya General Alpha ya ce "Ƙarya kake! Cikina ne a jikin Hawwa'u ba naka ba, Liar, maƙaryaci" Lokaci guda suka kalli direction d'in sashin da General ɗin ke tsaye, domin babu wanda ya hankalta da zuwan nashi cikin parlourn. Ba wanda ya furta ko alifun balle ya ja doguwar maganar da zata ɗauki hankalin jama'a, ko wanne a parlon wani razanannen tashin hankali ne ya mamaye masa zuciya, rashin madafa da sanin abin yi, akan aure biyun dake bisa mace ɗaya! Mene GASKIYAR LAMARI? Wake da haƙik'anin samuwar cikin na Majeederh? Wani abu ne mai kama da kunya a sa'ilin da akai yunƙurin binkan asalin uban, ALLAH YANA GANI, shi zai basu haske wajan fahimtar abinda ke cikin duhu.
"Ni ne wanda yake da nasaba da cikin Hawwa'u, saboda ita ɗin mallakina ce She's my wife, kenan babu doubting a ɓullowar ciki a jikinta? Tunda tana iya yiwuwa na kaɗaita da matata" Babu shakka,ko tsoro a fuskar General! Yanayin fuskar shi na tabbatar da asalin abinda ya bijiro daga ƙasan zuciyar tasa ne, bisa rikiɗewar ƙaryar daya shirya zuwa sahihiyar gaskiya wacce ya yi mata rajista da kansa. Uncle Isma'il ya juya ya kalli Dr Khalil wanda yake danna wayarsa haɗaɗɗiyar iphone 15 promax wacce aka launcher ta, not too long ago. Idan kaga yadda Khalil ke acting da basarwa ba zaka ce shi ake ƙaryatawa ba, ta hanya ɗaya zaka san kalaman sun ratsa zuciyarsa yadda gargasar hannunsa ke mimmiƙe ita kaɗai tana zubewa, Abbu bashi da hurumin magana domin batu ne akan ƴarsa daya shafi ɗan, ɗan uwansa, ita kuma Majeederh ya shafi mijinta da kuma jininta, dole ya zuba Idanu yaga yadda al'amarin zai wakana, baya da magana tun fil azal dama.
"General zauna, maganarka ta sanya firgici ina son kar mu shiga hak'ƙin Ubangiji, duk da cewa bamu da masaniyar Ibrahim yana raye, ALLAH YANA GANI"
General ya zauna yana jin wani ƙarfin quiwa da ganin alamun nasara, wacce da ita zaiyi amfani wajen kassara zuciyar ta uban girman kan nan da tsaurin idanu.
“Ya akai cikin ya zama naka? Shin bayan aurenku yaushe ka samu nutsuwar keɓewa da Majeederh? Tunda kasan mun san cewa taƙi yarda tayi accepting naka matsayin mijinta ko? Ya akai hakan ta faru?" General ya yi shiru can zuciyarsa yana tunanin "What should I do?" Majeederh kuma mamaki da tu'ajjubin lafiyayyiyar ƙaryar da General ya shimfiɗa take, wanda ya hanata magana sai kallon shi da take.
"Ina magana? Bamu da cikakken lokaci" General ya ce "Uncle binciken sirrin ma'aurata haramun ne fah, faɗin yadda akai daidai yake da furta kalaman batsa a gabanku" Uncle Isma'il ya rasa bakin magana, General ya girgiza kai cike da tausayawa ya ce "Ita ta sani, tasan ni ne uban" Sai a lokacin Khalil ya ce "Ƴar Shaye-shaye ce ita, irinka da zata sani?" Khalil ya ajiye waya ya Kalli General sosai da kyau ya ce "Yadda Ubangiji ya tsarkake ni daga shiga gonar matar wani, haka ya tsarkake matata wani ya shiga gonata" Khalil ya saka hannu ya hargitsa kansa, a hankali ya miƙe hannunsa a bayansa like yadda Mai martaba Ajlaal yakeyi, tafiya yake sai kuma ya juyo ya kalli General ya ce "Kasan ko gaskiya za ta yi ajalina sai na faɗa, ban taɓa furta ƙarya ba da wasa ko akasin haka" Ya juya ya kalli Innati da Yaya Bilkisu ya ce "Ko sanda kuka ɗauka ni fatalwa ne, tarayya na gama yi da matata ita kanta zatonta mafarki take but it was reality" Kunya ta kama Majeederh tana jin kamar ta nutse, ya akai Khalil har ya yi mata wayo haka? Ta kasa kallon kowa, a hankali Abbu ya miƙe tare da ficewa,Yaya Bilkisu tayi tsuru da Idanu Innati ta hangame baki tana jin zunzurutun rashin kunya irin ta surukinsu Dr Ibrahimul-khalil Abraham. Uncle Isma'il girgiza kai kawai yake yana jin da ana mutuwar gaske a dawo Khalil ba zai taɓa sauyawa ba, hali zanen dutse, cikar mutum suffar shi, gaskiyar ka nagartarka.
"Maƙaryaci, ka shirya zancenka ne, amma ciki nawa ne" Khalil daya fara birkicewa yana ɗan nufo General shi kuma yana yin baya tare da riƙe kansa, ya ce "Haba? Ashe kai ne ka farke ɗinkin haihuwar da akai mata?" General ya ce "Ohho dai ai ni ba ɗan iska bane da zan dinga rashin kunya a gaban mutane, Majeederh is my wife dole mu kasance tare" Khalil ya fara tattare hannun riga idanunsa jajur ya ce "Ni Ibrahimul-khalil cikakken ɗan iska ne akan matata, tunda gashi daga dawowata na bata wani cikin, ka tabbatar ni da kai akwai bambanci nayi abinda ka kasa a shekara biyu, Loser!" Kunya ta kama kowa na wajan, Innati ta share zufa ta ce "Balkisa ɗakko mini ruwa mai ɗan iskan sanyi suma nake ji"
"Innati lafiyarki lau ba wata suma, sha ruwa ki nutsu" Ta fashe da kuka ta ce "To tsakani da Allah a nemo abu a toshe min kunnuwana" Khalil ya fara hauka jikinsa yana jijjiga, Yaya Bilkisu ta miƙe ta nufi wajen Khalil tana zuwa ya saka hannu ya ɗauketa cak! Ya nufi wani bedroom da ita ya kulle, ya dawo Gadan-gadan kan Alpha da sauri Majeederh ta shiga tsakiya yaƙi kallonta, domin ƙwayar Idanunta sune weakness dinsa masu raunata masa zuciya, ta saka hannu a hankali ta juyo da fuskarta tare da sanya idanunta cikin nasa, ya ɗan kwaɓe mata fuska ya kasa cewa komai,ta kama hannunsa ta ɗora a cikinta a hankali daidai shi ta ce "We're one single family, no one can separate us ok? Ni da kai jini ɗaya ne, ma'aurata ne, kai Mijin Malama ne, ni kuma Mrs Ibrahimul-khalil Ranka ya daɗe,mu ɗin masoya ne KHALJEED💖" Wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke yana damƙe hannunta cikin nasa, ya dinga kallonta shi kansa baya da zarafin faɗa mata yadda yake jinta a zuciyarsa.
"Hawwa'u!" General ya kira sunanta da ƙarfi ya ce "Cin amana? Akan shi zaki mallaka masa jinina?" Khalil ya sake damƙe hannun Majeederh kamar zai raba gida biyu naman jikinsa duka rawa yake. Maman Alpha kasancewarta barrister ta gama fahimtar komai ta ce "Ok a zubar da cikin kawai" Ta faɗa tana kallon kowa tana son ganin reactions ɗin su, a gigice Khalil ya kalleta idanunsa na shigewa ciki da ƙarfi ya ce "Maaa, cikin nawa za a zubar? Kamar cikin shege?" A fili kuma General ya sauke numfashi ya ce "Better! A zubar kawai kowa ya huta zanfi jin daɗin hakan" Maman Alpha ta girgiza kai ta ce "You are ashamed, You are a liar" Uncle Bello ya ce "Ka bani kunya, ka bani mamaki, daman tabarmar kunya da hauka ake naɗeta, kaga duk duniya ba abinda zaka sake faɗa mini na yarda, Firstly ka ce Majeederh na sonka har muka ɗaura aure, ashe ƙarya ne, secondly ka ce Zuleehart ba matarka bace nan ma ƙarya kake, thirdly, ka ce cikinka ne shi ma ƙarya ne, When will you stop lying? when will you be an honest person? you are nothing but a liar"
Innati ta saki baki sosai sai kuma ta ce "Tirr! Amma ka ji jiki sosai soja ƙarya zagin Allah ka bani kunya, ya akai kamar wannan yaron mijin Malama da yake tun farko Ahlul kitabb ya fika iya faɗin gaskiya?" Ta girgiza kai ta ce "ALLAH ya isa a gaskiya zaman jiran jin matsiyaciyar ƙaryar da kake zabgawa, yanzu da za'a zungura tsinke a kunnena wuta za a tsokalo" Uncle Isma'il ya kalli Khalil da General a hankali ya ce "Ku zauna" Khalil ya nemi waje ya zauna, Jee ta miƙe ta bar wajan, Uncle Isma'il ya fara ta kan Khalil ya furta.
"Da yawan lokaci dole ne ka koyi tanƙwara zuciyarka Ibrahim, ba komai ne zaka ce zaka fara duka ko faɗa ba" Khalil bai kalli Uncle ba, yana tunani to shi me ya yi? Bayan bai damu da hayaniya ba yaushe ma yake duka? Uncle ya sassauta muryar shi ya ce "Lokacin da ba ku da ikon sarrafa tunaninku, tunaninku da motsin zuciyarku na iya yin ta'adi. Kuna iya samun kanku kuna yawan jita-jita akan abubuwa da yawa, kuna shakkar kanku akai-akai, ko kuma kuna fuskantar matsala game da motsin zuciyarku. Bai kamata ya kasance haka ba! Kuna iya sarrafa tunaninku kuma ku maye gurbin tunani mara kyau na rashin kulawa tare da tabbatacce, daidaitattu. Bayan lokaci, za ku fara jin daɗin farin ciki, ƙarin daidaitawa, da kuma kula da yadda kuke ji da tunaninku, Khalil na san a haka Ubangiji ya halicceka sauya mutum ɗabi'a ko wani hali nasa wanda ya ginu a kai abu ne mai matuƙar wahala, amma ka dinga haƙuri Plx!" A hankali ya kwantar da murya kamar ba zai ce komai ba tsayin seconds kafin ya ce "Thank you!" Uncle Isma'il ya ce "Allah ya yi maka albarka" Ya ɗan yi jim sai kuma ya ce "Zamu tafi Palace" Uncle Bello ya ce "Yaushe?" Khalil ya ɗan shafa kansa domin sam ya gaji da magana wallahi "Gobe" Suka ce "Da wuri haka?Ina a nan za ku yi Ramadan gabaɗaya bai fi saura kwana uku ba a fara" Khalil bai ce komai ba, ya miƙe tsaye tare da ficewa daga parlourn.
Uncle Isma'il ya juya kan Alpha da yake durƙushe zuciyarsa kamar zata fito haka yake ji, shi kaɗai yasan wanne so ya kewa Majeederh ba kowa zai fahimci ko gane hakan ba, kalaman Zuleehart ne suka shiga yi masa amsa kuuwwa! A cikin kunnensa. Uncle ya ce "General kai da kanka baka ji nauyin Ibrahim ba? Ka dinga shirga ƙarya bisa son ranka? Saboda cikar burinka, duk lalacewar mutum idan ya riƙe gaskiya da amana wallahi yafi haiba da kamala cikin mutane nagarta ta ban mamaki mene ribarka akan yin ƙarya? Kasan hukuncin masu ƙarya bisa son rai ba don kare kai ba? Ka ji tsoron Allah tun kafin lokacin ya ƙure maka kaje ka nemi matarka" General ya ce
"I am sorry Uncle, zan gyara yanzu a bani matata" A