Showing 21001 words to 24000 words out of 126557 words

Chapter 8 - MIJIN MALAMA Book 2 Complete by Nimcey Sarauta .txt

yanzu ku gaisa" Majeederh ta marairaice ta ce "Uncle ni ban son auren please" Wata kyakkyawar tsawa ya daka mata jiki na rawa ta miƙe zata fice ya ce "A haka zaki? Idanu buzu buzu duk a jime" Ta ce "To ya ganni a haka" Uncle Bello mamakin Majeederh yake kwana biyu ta sauya ga saurin kuka ga magana kai tsaye, ko mene dalilin sauyawar nata? _Only God knows!_
A hankali ta shiga parlourn bakinta ɗauke da sallama cikin siririyar muryarta, ta shiga kanta a ƙasa bata yadda sun haɗa idanu da Mai martaba Ajlaal Sultaan ba. Shi kowa yana zaune hakimce saman kujera ya ɗan kishin giɗa, jikinsa da wata farar jallabiya ya ɗora hirami a kansa sai ƙamshin perfume ɗn Jean Paul Gaultier sai lumshe idanunsa yake, tunda kuma ta shigo yake kallon fuskarta a karo na farko har ya gaza ɗauke fararen Idanunsa duk da irin basarwa ta Mai martaba, maganarta ya dawo dashi daga tunaninsa da take cewa "Gani" Kamar bai jita ba haka ya yi shiru yana mai da idanunsa tare da rufewa, Malama Majeederh ta ɗago kai tana kallonsa tana mamakin girman kai irin na Mai martaban, ko da yake ba laifinsa bane jinin sarauta dake yawo a jikinsa ne. A hankali ta ce "Gani" ba tare daya buɗe idanu ba ya ce "Kewa?" Ya ja numfashi ya ce "Suwa suka kira ki?" Ta ce "Ohk Maybe mistake ne" Tana faɗin hakan ta miƙe tsaye har ta je bakin ƙofa ta ji ya ce "Haw...wah" Cak ta tsaya a hankali ta dawo ta zauna, ya gyara ya zama yana buɗe ido calmly ya ce "Mun gani, mun yaba, muna son aura" Majeederh ta kasa Kallonsa sbd kwarjini ganin haka yasa ya ɗan gyara murya ta ce "Ƙhulud? ba zan iya mata haka ba" A hankali ya ce "Su waye haka? Oh Fulani kawai amincewar ki muke nema" Ta ce "Zan yi tunani" Ya jinjina kai he can't stop himself wajan kallon riskarta Bai ce komai ba tasan ɗin bazai tanka ba, har zuciyarsa yake son Majeederh amma yanzu tunani kala daban daban ya shiga kansa, ya miƙe yana tafiya a nutse sai da yaje ƙofa ya ce "Kuyi tunani mai kyau". Yana faɗin hakan ya fice ta bisa da kallo koman shi a nutse yake, ta jima kafin ta miƙe tana fita entrance na gidan taga Aliyu tsaye shi da yayansa Almustapha sun saka kaya iri ɗaya, Almustapha ne kawai yake magana amma hankalin Aliyu na kan Majeederh tayi kamar bata gansa ba, Almustapha ya ce "Assalamu alaiki" Ta tsaya tana amsawa can ƙasa bayan sun gaisa da Almustapha Aliyu ya ƙarasu inda take ya ce "Kin gama guje gujen?" Ta kame fuska bata ce komai ba ya marairaicewa fuska ya ce "I will ask for your help again and again, Hawwy, help my heart and accept me as your husband" Tayi shiru yana sauke numfashi murya kamar mara lafiya ya ce "Don Allah, don Allah ki taimaka mini ina son ki Jiddatul-khairy, bani da zaɓin zuciya sama dake tunda na fara haɗuwa dake har yanzu bani da ishasshiyar lafiya, bana cikakken bacci, bana cin abinci sosai wlh ko maƙiyina a duniyar ba zan so ya kamo da irin wannan son mai zautar da mutum da son kai shi kushewa ba, i loves you ina son ki" Wani irin tausayin Aliyu ya kamata domin kaf cikin su tafi tausayin shi yana da wata kalar zuciya mai sanyi da son kyautatawa mutum a hankali ta ce "Baka taɓa cewa kana so na ba sai yanzu?" Ya girgiza kai ya ce "Ba zaki gane ba, ki fara amince mini zan yi miki bayani amma ko Latifa darajarki take ci" Ta kalle shi sai ta ce "Thank you, yanzu ma taci gaba da cin darajata" Ya yi saurin durƙoshewa gabanta ya ce "Ki duba Allah ki tausaya mini, zan nuna miki cewa baki asara ba, zan baki farin cikin da kika rasa zan nuna miki so da ƙauna, ban miki al'ƙawarin fari na har abada ba, amma daga gareni zaki ta samun kwanciyar hankali, Ina son ki ina tsananin ƙaunarki, zan ma kira Hajia da Papa su baki hakuri, ga Yayana Almustapha he's here to ask ur help, zan kira Anti Biba, Anti Rahmerh, da Antin Turkey su baki haƙuri kada ki wofintar dani Please" Idanunta ya cika da hawaye Almustapha ya ce "Plx Malama Majeederh a baya bana son tarayyarku amma yanzu na amince bana ƙasar ma sbd ke na dawo ki tausayawa Abokina aminina my younger brother idan wani abu ya sameshi ba zan yafe miki ba" Majeederh jikinta duk rawa yake ta ce "Am sorry ba zan iya auran mijin Latifa ba, wlh duk duniya zata haɗu ban iya auren mijin Bestie yadda Abbu ya haramta a gareni haka Aliyu, Am sorry" Tana faɗin hakan tai cikin gidan Aliyu zai bita Almustapha ya yi saurin riƙe shi sai kawai ya faɗa jikin yayan nasa yana wani irin kuka kamar zuciyarsa zata fito..... Anti ce tsaye waya kare a kunnenta ta ce "Yawwa duk yadda za ka yi kai ka sani ka tabbatar Abraham bai auri Majeederh ba, ka sanya masa soyayyar Sona a zuciyarsa, kamar yadda Alpha ya tattara kayansa yabar garin yace baya so kasan duk yadda kayi kasa Abraham yace baya son Majeederh, ai kace mini shi ɗin ɗan babba mutum ne? Yana da nasaba mai girma ga uban dukiya?" Magana akai ta cikin wayar can ta ce "Good, sau biyu aikin ka na bani matsala gashi Kuɗi dai ina baka sosai kamar hauka, nace ka saka Majeederh ta zaba karuwa ta ƙarfi da yaji amma kace ba zai ba, saboda ƙarfin addu'a da azkar ɗin da take, hakan yasa ƙaddara tazo ta sauƙi maimakon ta zama karuwa sai akai rapped nata, kuma....," Da sauri ta ajjiya wayar ta ce "Jawaad how many zance ka daina faɗo mini without my permission eh?" Ya ce "Sorry Maa, dinner is ready" Ta haɗe fuska ta ce "Fice ka bani waje kai ta abu kamar zautacce" Ya fita zuwa dining room. Majeederh ta fito sanye da duguwar riga wacce ta bi jikinta sosai fuskarta fresh kana ganinta kasan akwai damuwa a tattare da ita dan dai jaruma ce kawai, kai tsaye ta nufi dining room ɗin cak ta tsaya ganin Abraham zaune ɗare ɗare akan kujera suna ta tafka uban musu da Jawaad Uncle Isma'il kuma na zaune yana ta musu dariya wannan yace shi ne babba wannan ya ce shi ne babba. "Majeederh ƙarasu mana" Tsit Abraham ya yi kamar bashi a wajan ya zaro wayarsa ya shiga dannawa fuska haɗe babu alamar fara'a kafin ta zauna Uncle Isma'il ya ce "To Antin bata ƙarasu ba, ki zuzzuba mana abincin" Ta yi jim sai kuma ta zubawa Uncle Isma'il ta zubawa Jawaad ta zuba nata kaɗan, tana neman wajan zama Uncle Isma'il ya ce "Wa zai zubawa Ibrahim ɗin?" Ta ce "Uncle.." Ya ce "Ranki zai ɓaci" Ta miƙe ta nufi gefen tare da ɗakko plate ta shiga zuba masa, shi dai Khalil wayarsa kawai yake dannawa Uncle Isma'il na kallon tulin abincin data zuba masa tare da nama da yawa ta ciccire albasa da tumatir "Ya kika cire masa kuma?" Tana ajjiye spoon ta ce "Baya ci" Kallonta Uncle Isma'il da Jawaad kawai sukai tana gamawa zata bar wajan a hankali ta ji muryarsa daidai kunnenta ya ce "Thank you" Ko su Uncle Isma'il ba su ji ba, Jawaad nata yi wa Khalil surutu daman haka yake shi kamar aku, Abraham daman baya wasa da cikinsa abinci kawai yake ci sai da ya cinye abincin tas ya sha ruwa ashe tuni Uncle Isma'il yabar wajan sai Majeederh dake ƙoƙarin tashi "Hawwa'u" Dam! Zuciyarta ta buga jin sunanta raɗau abakin Abraham, ta juya da sauri da tunanin ko bashi bane suka haɗa idanu ya harɗe hannunsa a ƙirji, Jawaad ya bar wajan tayi tsaki zata bar wajan ya ce "Kina barin wajan nan ni dake ne" Ta wani kalle shi ta ce "To sannu ubana" Ya girgiza kai ya ce "Ki zauna magana nake so mu yi, bana son kuma kai hannu jikin ki balle aja mini aya" Ta ƙara jan tsaki rai ɓace ta ce "Kai da jikina har abada yaro" Ya miƙe tsaye ya ce "Idan dai kika sake hannuna ya taɓa ki to ko Uncle I da Uncle B basu isa su ƙwace ki ba" Ganin yana nufuta yasa ta juya da sauri zata bar wajan ya saurin saka mata ƙafa kamar zai taɗeta ta faɗi da sauri kuma ya cafko gaban rigarta yana haɗuwa hatta bra ɗinta tayi kamar zata faɗa ƙirjinsa ya saurin ɗan baya ya riƙe waist ɗinta sosai ta ce "Zan baka abinda bakai tunani ba, sbd kai ɗan yau ne daman ance ka haifi yaro banda halinsa wlh..." Hannunsa yasa ya cafke lip's ɗin nata tare da murɗewa azabar da taji yasa tayi saurin riƙe masa ƙugu da duk hannunta jikinta idanunta ya yi rau rau sai da ya murɗe mata bakin son ran shi kafin ya saketa ai kowa lip's ɗin sukai jajur sosai suke mata azaba takaici yasa wani irin hawaye zubu mata, Abraham ya tallafo fuskarta kamar mai raɗa ya ce "It's hot?" Ta yi masa shiru ya ƙara leƙa fuskarta silently ya ce "What??" Sai kawai ta fashe da wani irin raunataccen kuka na zallar takaici jawota ya yi jikinsa ya rungumeta zata ƙwace ya ƙara matseta a jikinsa gabaɗaya baƙin ciki ne yasata kuka gashi bata da wani ƙarfin kokawa dashi ta runtse Idanunta taja jin yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi "Gobe za mu yi aure, ni ba zan wani tsaya roƙanƙi ba kamar su dole ya zame miki yarda" Da dukkan ƙarfinta tasa ta hankaɗe shi, ta ce "Wallahi na tsaneka bana ƙaunar ganinka dana aureka gwara na zauna ba aure ko na auri wani, ko bakai mini komai ba kayi mini ƙanƙanta da zama mijina ɗan cikina sbd kai baka da kunya wani ɗan mitsi-mitsi dakai har kai ka isa yin aure ba, wlh bana ƙaunarka" Tana faɗin haka ta shige Khalil ya zube yana riƙe kansa fargaba da tsoran rasa Jee ya wanzu a zuciyarsa... Da asuba Uncle ya tambayi Majeederh me ya yanke? Sai ta ce masa ta amince da Ajlaal shi take so, Sosai Uncle Isma'il ya ji daɗi domin shi ma Ajlaal ɗin ne ya kwanta masa, daga nan ya kira Aliyu ya bashi haƙuri akan ba zai taɓa yiwa Majeederh auren dole ba, daga nan ya kira Khalil har Parlour shima ya kura masa bayani akan ya bawa Ajlaal Sultaan auren Majeederh, Khalil kasa magana ya yi sai jikinsa daya ɗauki rawa da sauri ya fice ya nufi hotel ɗin da Mai martaba Ajlaal Sultaan ya sauka, sosai ya dinga neman afuwa akan Ajlaal ya haƙura ya bar masa Jee ɗinsa amma fur Ajlaal ya ce "Sorry, i wishe you all the best da zan iya dana bar maka ita, but muma muna sonta" Abraham kamar zai zauce wani zazzaɓi ya rufe shi, shikenan ya rasa Majeederh ya rasa Ƴar Madara ya rasa Maluma da ƙyar yakai kansa gida.... Gidan Uncle Isma'il ya cika da ƴan uwa hadda Mami su Raihana da Ruma kowa na family Abbu ne kawai babu, kowa jira yake ji waye MIJIN MALAMA? Tunda duk basu san shi ba... A Masjid ɗin dake layin gidan Uncle Isma'il ake ɗaurin auren abun mamaki manyan mutane sosai ta ko'ina kamar wanda jima ana sanar da ɗaurin auren, cikin masallacin cike yake sosai da mutane, Aliyu Sufyan Alhassan yasha wata dakakkiyar shadda yana zaune gefe, ga Mai martaba Ajlaal ango ya shafa farar shadda sai ɗaukan idanu take, abin mamaki hadda Abuturab wanda da gayya Uncle Isma'il ya kira shi, Jawaad na gefe daga can ɓangaren Abraham ne durƙoshe yasha wata shadda fara tas kusan iri ɗaya data Mai martaba jikinsa duk rawa yake zuciyarsa na bugawa amma ya yi imanin Jee ba rabon shi bace Maybe Allah ya haɗa su don ya rabauta da addinin musulunci bawai dan ya zama mijinta ba hakan yasa ya haƙura...... Manyan mutane da liman ne suke magana a hankali Abraham ya miƙe da sauri zai fice daga cikin Masjid ɗin daidai nan Liman ya ce.....








💃💃Ko waye zai zama MIJIN MALAMA?
Idan na so mugunta da kuma jan labarin.... Sai kawai na ɗakkowa Akeeth na bashi auren Malama Majeederh ai shima namiji ne? Idan kuma nagarta nake so sai kawai bawa Sheykh Ajlaal Sultaan? Idan kuma dangantaka nake so sai kawai Alpha ya dawo ranar auren a bashi ita? Idan kuma ramuwar gayya nake so sai Majeederh ta auri Aliyu.... Idan soyayyar gaskiya nake so da kulawa, da kuma dole ki so ni ko zaki mutu love by forch madly love sai kawai na bawa Ibrahimul-khalil, Abraham bad boy auren Majeederh.... Na tsaya da typing tunani kawai nake🤔🤔🤔to ita matsalar ma Abraham yaro ne wai ya yi ƙarami bai isa aure ba.... Congratulations TEAM MAI MARTABA AJLAAL SULTAAN🥰
*#Unexpected*


Cak Khalil ya tsaya saboda abinda kunnenshi ya jiye masa His whole body was shaking, his heart was beating hard, he couldn't believe what his ears were hearing because of surprise. Ya juya a hankali yana kallon direction ɗin limim da kuma bakinsa, a ƙoƙarin shi na son fahimtar meke faruwa? Ya runtse idanunsa tare da riƙe jikinsa Ya Allah What is happening here? why should his ears lie to him? Ya tambayi kansa a zuciya, a hankali kuma ya sake ware idanunsa akan Liman ɗin wanda yake cewa "Ma sha Allah, aure ya ɗauro bisi amintattun shaidu, da kuma amincewar ko wanne ɓangaren, an ɗaura auren Ibrahimul-khalil Denial David da Hawwa'u Abdul'aziz Khan akan sadaki 500k Naira dubu ɗari biyar" At that time, Khalil looked like a madman, especially the way he looked at the imam without even blinking his eyes, abin yake ji da gani kamar a mafarki yake gilma masa kamar reflection wanda ya saba ganin kansa ciki, ya juya ya kalli Mai martaba Ajlaal Sultaan suna haɗa idanu yaga yana yi masa dariya, da sauri ya kalli Uncle Isma'il wanda shi ma Abraham ɗin yake kallo suna haɗa idanu da Uncle I ɗin Abraham ya kwaɓe fuska sai kuma ƙafafuwansa suka ɗauki rawa, cikin nutsuwa Takawa ya miƙe ya isa wajan Abraham dake ƙoƙarin sulalewa yana zuwa Abraham bai tsaya jiran komai ba ya rungume Takawa yana sakin wani irin raunataccen kuka mara sauti wanda Mai martaba ɗin ne kawai yake jinsa, ya kuma ƙanƙame shi kamar zai shige jikinsa, shi tunda aka haife shi a duniya ba zai ce ya yi kuka a gaban mutane har haka ba,He couldn't shake himself from the state of happiness and surprise he was in, ya kasa yarda yau shi ne ya auri Maminsa, Jee ɗinsa, ƴar madara Maluma, Maminsa data raine shi ya rayo da soyayyarta yau ita ta zama mallakinsa ta zama matarsa, He just belong to him ya sani, ya rungume Takawa da kyau yana sauke numfashi da wata iriyar zuciya domin abin ya tsammace shi, tsammaci abinda bakai tsammani ba, ya fitar da rai da Malama Majeederh sai gashi yanzu igiyoyin auren shi sun rataya akan ta, Wow dear Ibrahimul-khalil you're lucky. Suna nan tsaye rungume da juna Takawa na sakin wani ƙayataccen murmushi yana bubbuga bayan Abraham, Uncle Isma'il ya ƙarasu yana murmushi ya ce "Yau naga abin da ya daman mazaje da kuka?" Jawaad dariya yake hadda riƙe ciki ya ce "Lallai yaro ya girma ya auri Maminsa" Khalil yaƙi ɗago kai balle ya tanka haka kurum kunyar Uncle Isma'il ta dirar masa a zuciya. Uncle Bello yana naɗa babbar riga zuwa sama ya ce "What did i miss?" Uncle Ismail ya ce "He's crying" Uncle Bello ya ce "Wanne irin kuka ba daɗin ji, baka son ta ne ko me?" Da sauri Khalil ya ɗago da rinannun idanunsa da sukai wani irin jaa ya yi baya kaɗan yana kwaɓe fuska a hankali ya ce "What, ban so fa?" Yadda ya yi maganar yana zare idanu zaka san maganar ya shige shi ance bai son Maminsa, Jawaad ya ce "Yaro an shigo matakin manya, an zama MIJIN MALAMA" Khalil ya yi murmushi kawai yana girgiza kansa har yanzu Shocked bai sake shi ba, muryarsa can ƙasa baya fita ya ce "Ban kula ka, ranar farin cikina" Uncle's ɗin sukai murmushi gabaɗaya Abraham ya sauya kamar bashi ne Bad boy ba, leader team na Gang ɗin su, har ya tsani kace masa Abraham kawai Khalil ko Ibrahim. Suna nan tsaye Barrister Aliyu ya ƙarasu fuskarsa ɗauke da murmushi ya kalli Khalil yana miƙa masa hannu ya ce "Congratulations brother in Islam" Khalil bai kalle shi ba, bai kuma miƙa masa hannu ba fuska sake ya ce "Thank you" Ganin hakan yasa Barrister Aliyu ya dunƙule hannunsa sai kuma ya fice daga cikin Masjid ɗin, Khalil ya ɗan matsa kusa da Takawa wanda suka magana da wani mutum yana ɗan jinjina kansa, Khalil sai zunguro Mai martaba Ajlaal yake amma bai kula shi ba, daga ƙarshe ya juya gabaɗaya ya sakar masa ranƙwa shi aka, Khalil ya shafa kansa daya cire hular ya ce "Auchhhii, it's hurt" Sai da suka gama magana Mai martaba ya kalli Khalil yana ware idanu a hankali ya matsa dab da kunnen shi ya ce "Why? How?" Sosai ya gane me yake nufi sai ya ce "Not here" Suna haka Abuturab ya ƙarasu tun kafin yazo Khalil ya yi saurin barin wajan. Waje ya samu su Uncle Isma'il da Uncle Bello su Jawaad hadda Engr Junaid suna ta yin pictures kowa da farin ciki a fuskar shi. Khalil ya tsaya yana kallon su, gabaɗaya keɓance kansa yake son yi domin ya yi farin ciki wayarsa ya zaro a aljihu yana ɗan daddannawa sai kuma ya mayar jin Uncle Bello yana cewa "Ibrahim mu shiga ciki ku gaisa da mutane" Ya ɗan kwaɓe fuska ya ce "No! Uncle zuwa yamma" Uncle Bello bai takura shi ba domin ya fahimci shocked ne ya masa yawa har yanzu kuma bai gama yarda dashi aka ɗaura auren ba, Motar su Ajlaal ya shiga suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login