Showing 120001 words to 123000 words out of 126557 words

Chapter 41 - MIJIN MALAMA Book 2 Complete by Nimcey Sarauta .txt

ita, ta hanyar wani Gandiroba mai bala'in son kuɗi ta kalle shi ta ce "Amma Sir Khalil ya tsaneka" Ya girgiza kai ya ce "I knew my son more than anything, nasan waye shi yana so na, nasan kalar son da yake mini I just need your help" A hankali ta ce "Name?"
"Ya yafe mini, na yi regretting komai bani da tabbacin zan bar gidan nan ko a'a, idan har na bari to tabbas zan dawo ga iyalina idan ban bari ba to zan zauna a nan har zuwa mutuwata" Latifa ta ce "Sir kun yarda zaku mutu kenan?" Ya kalleta da mamaki a fuskarsa sosai sai kuma ya ce "Mun sani, a littafinmu ai mun san mutuwa gaskiya ce duk wani wanda ki kaga yana aikata abu wanda yake ba daidai ba ya sani, son kuɗi ta rufe idona na banbanta kuɗi da iyalina, wanda a yanzu ba kuɗin kuma iyalin nawa nake buƙata su nake son gani, amma bani da confidence na zuwa inda suke bani da confidence na neman yafiyar su" Ya ɗan saurara sai kuma ya ce "Ina son Gimbiya so mai yawa, komai nata birgeni yake amma rashin kishi da masifar son kuɗi nake son sadaukar da ita ga wani? Wanne irin miji ne ni?" Ya runtse idanunsa a hankali hawaye masu zafi suka shiga gangaro masa kafin ya ce "I am ashamed, I have failed as a father" A hankali ya lumshe idanunsa tears running down his cheeks"I made a mistake and I regret doing all the things I did in the past, dama lokaci ya bani dama na tariyo bayana domin gyara goben da bani da tabbacin kyanta, duk da ban kasance musulmi ba, amma nasan abubuwa masu kyau wanda littafinmu ya zo da shi" A hankali Latifa Omar ta ce "Kana cikin lokacin ka Sir, zaka iya amsar shahada, idan ka yi believing da addininmu" Ya girgiza kai ya ce "Da alama bani da rabo, ban ji son hakan a raina ba, Musulunci bai cancanta dani ba"
"A'a Sir!" Latifa ta faɗa a ɗan gaggauce ta ce "Addinin Musulunci mai sauƙi ne, ga ma'abota soyayyar shi, baya da wariya wajen bambance wanda zai shige shi, kyakkyawar niyyar da tsarkakkiyar zuciya kawai ake buƙata, abu mafi wahalar shi ne da wacce kalar zuciya kake son musulunta? A nan kuma sai ka saurari zuciyarka abinda duk kayi imani da shi, to shi ne daidai kayi amfani da damarka domin baka da tabbacin kawai anjima ko gobe" Da sauri ya ce
"Ina son musulunta ƴata, tsoro ne kawai ya hanani ina ganin kamar addinin ba zai amshe ni" Murmushin jin daɗi Latifa tayi, ya yi alwala a wajen aka bashi kalmar shahada yana faɗa idanunsa na cika da hawaye duk duniya yanzu iyalansa yake buƙata, Gimbiya, Khalil, Clara, Zizi, Badi, da kuma Kiristi ko mutuwa ce ta ɗauke shi a cikin su, Latifa Omar ma kukan take sosai zuciyarta babu daɗi, envelope din daya bata ta ɗauka ta nufi part ɗinsu na mata a asirrince ba tare da ankarewar kowa ba. Cikin dare zuciyar Mr President ta buga ko motsawa bai ba Ubangiji ya zare ran shi a ranar daya karɓi shahada, daman haka ne idan kakan aikata aikin ƴan wuta, idan Ubangiji ya soka da rahama kana dab da mutuwa ka koma aikin ƴan aljanna, idan na ƴan aljanna kake kaso taɓewa sai ka koma na wuta, su Latifa na kwance aka dinga tashin su ana fita ta wata ƙofa har suka fice daga cikin prison aka sanya su a wata ƙatuwar mota tare da ɗaukan hanya da su.


"Sister ina za a kaimu?"
Latifa ta tambaya a tsorace, wacce ta tambaya ɗin ta ce "Haka ake mana duk sati ko duk wata, sunan an kawo mu nan da niyyar gyaran hali ko yanke mana hukuncin zaman gidan kaso gabaɗaya har mutuwa ko mu yi shekaru mu fita, amma an mayar damu saniyar tatsa" Latifa ta ce "Pardon! Ban fahimta ba" Ta ce "Ina nufin yanzu haka kaimu wajen wasu manyan gari za a yi su kwanta damu, bamu da wani option wanda ya a shige obey, yanzu hatta ƙwayoyin maye da ake karɓewa wajen mutane sune suke amsa, to da irin haka taya rayuwa zata gyaru? Wani ma laifinsa bai kai matsayin da za a kaisa prison har haka ba...," Ta kasa ci-gaba da maganar saboda kukan daya ƙwace mata... Saukar yamma duk Khalil sukai Majeederh tunda jirgi ya tashi ba taga Khalil ba sai yanzu da suka sakko, ya kasa haɗa Idanu da ita, kunyarta yake ji sosai bai san mene ya sanya ya kasa controlling kansa a lokacin ba, ya kama su twins Yaa K na tare da Majeederh daman already ta faɗawa Zaytoon zuwan nasu sai dai bata shaida mata da Khalil bane, motocin Palace a jere wajen biyar, a nutse Gimbiya ta fito daga motar tana sanye da wata milk ɗin alkyabba wacce ta amshi jikinta sosai, fuskarta a kame kamar kullum, sai Clara wacce take tsaye a gefenta ta saka baƙar abaya tare da zagaye fuskarta da veil, sai Rohaan, ɗaya motar Zainab da Badriyya ne suka fito gabaɗaya cikin abaya iri ɗaya, Zizi da Badi. A kusan lokaci ɗaya cikin daƙiƙa guda idanun Gimbiya dana Clara wacce itama ta musulunta ta koma Fatymerh ya sauka akan Khalil duk yadda Gimbiya ta kai ga jan ajinta da riƙe kanta kasawa tayi, ta saka hannu ta murje idanunta still Khalil take gani tsaye yana mata murmushi ga yaransa da matarsa zagaye dashi, Jee ta nuna kamar babu komai, Gimbiya komai nata ya tsaya ta kasa yarda ko gasgata abinda take gani da ɗan sauri cike da nutsuwa Khalil ya nufeta yana zuwa ya rungumeta, suka sauke ajiyar zuciya "Ummie" Ya furta a taushashe tana jin muryarsa mai cike da kamala ta rungumesa a jikinta tare da sakin wani irin raunataccen kuka tana cewa "Khalil? My son.....
[11/2, 20:11] Ummu: *MIJIN MALAMA*
*_Arewabook@Nimcyluv 106_*


Innati ta sharce majina ta ce "Ƙarara baki babu linzami a dinga Sakin tsurar zance? Dafa a makarantun islamiyya ya faɗi haka a gigice zasu dinga salatin Annabi, ana kaɗa zunubin can wani wajen, ƴar bulala ɗari da tamanin ɗin nan yi masa ita za su yi"
Majeederh ta yi shiru, Aaliyyah sai dariya take ta ce "Ni a shawarce da islamiyyar kika mayar da shi Innati" Ta yi caraf ta ce "Waa? Ubana daya mutu zai dawo kenan ashe, yanzu da an yi magana ya ce Mijin Malama? Haka Kululu take? Asstagafirullah!" Aaliyyah ta ce "To Allah ya shirya shi" Da sauri ta ce "Amin don nabiyyun rahamati, idan ba zai shiryu ba Allah ya ya fe masa" Ta juya ta kalli Majeederh ta ce "Mijin naki batsa ya yi fa? Ko ba ki ji bane?" Kafin ta ce komai Ƙhulud ta shigo da plate wanda yake cike da zallar gasasshen nama.... Washegari aka Raɗawa yara suna Hawwa'u Ibrahim Khalil da Fatima Ibrahimul-khalil, wanda suka ci sunan Fulani da Gimbiya ana kiran su da Noha da Soha, faɗar shagalin da akai ɓata baki ne, duk da cewar family biyun basu da cikakken yawa amma Majeederh ta samu arziƙi daga jama'a, hatta Barrister Aliyu Sufyan sai daya bawa babies gift Khalil dai bai ce komai ba, haka Akeeth wanda suka zama friends shi da Khalil, hatta P.a Hammad sai daya basu mahaukatan kaya wanda suka jone shi da Badi tun a Naija har zuwa matakin da zai aureta.


Sarewar dake tashi a hankali wacce ta karaɗe Palace bakiɗaya cikin ƙanƙanin lokaci shine ya fargar da jama'a zuwa ga abinda yake faruwa acikin masarauta. Su Mami gabaɗaya suka fita domin bawa Idanunsu abinci Majeederh dake zaune kiɗan na ratsata jinin sarautar nata ya motsa ta miƙe a hankali tare da nufar waje, cak ta tsaya daidai window tare da ɗagawa idanunta ya sauka akan gwarzonta Dr Ibrahimul-khalil kuma Mai martaba Ibrahim Khalil na 4, a hankali ta dinga binsa da kallo jinin jikinta na tsinkewa ganin wani irin kyau da ya yi mata wanda bata taɓa ganin irinsa ba, farar jallabiya ce a jikinsa ƴar gasken, an ɗora masa jibgegiyar golden Silver ɗin Alkyabba mai mugun tsada, fuskarsa zagaye da rawanin hiramin daya ƙara fidda tsagwaron kamala da tarin haibar dake kwance a fuskarsa, baya murmushi ko kaɗan ya kame kansa idanunsa ya buɗe tare da lumshe su, komai ya gundire shi tashin hankalinsa bai shige kiɗan da ake masa a ka ba, da surutan jama'a. Jajayen laɓɓansa sun jiƙe da damshin yawu tunaninsa ya tsaya cak sanda ya gama tabbatarwar da kansa fa yau shi ne jagoran mutanen Saudiyya? Nauyi da hak'ƙin nasu yana rataye a wuyansa.


"Ya Allah" Ya furta a zuciya bisa mamakinsa kuma harshen shi ya ƙara nauyi fiye da ko wanne lokaci, jinkimar shi da kame kansa sun ƙaru fiye da ko wanne lokaci da rana na tsayin ranakun da ya yi a rayuwarsa, a hankali wata nutsuwa ke sauk'a tana mamaye jikinsa ya rage babu wani jini da ya yi saura a jikinsa sai na sarauta. Majeederh ta yi saurin ɗauke idanunta ganin ya bar sashin fada ya nufo cikin gidan kai tsaye sauran mutanen fada suka tsaya. Da sauri ta shige bedroom ɗinta tana nufar gaban mirror, Khalil kai tsaye sashin Ummie ya nufa ya sameta zaune akan bed tana duba sauran turarrukan da aka kawo mata, idanunsa da suke yawo a kanta ya tabbatar mata da cewa shi ne, sabon Takawar Masarautarsu, ta ɗaga kai suka haɗa ido ganin nasa ta yi jajur ta ce "Ranka ya daɗe?"


A hankali ya zame rawanin kansa ya ƙarasa wajenta ya ɗora kansa a cinyarta, yana sakin ajiyar zuciya sun jima haka kafin ya ce "Me kika fahimta a labarin rayuwata Ummie?" Ya ɗan yi jim ya ce "Karki duba bangon labaran cikin littafin kawai"
Ummie ta ce "Idan zan fasalta rayuwarka dole na fara daga farko, bangon littafi shi ne abu na farko da jan hankalin mutane zuwa ga sanin abinda yake ciki, rayuwa dole ce ga dukkan mai rai dake wanzuwa a duniya, mutuwa gaskiya ce hisabi dole ne, a wannan littafin naka dole aga sunan Majeederh zane a ciki, kai tsaye zan iya basa suna MIJIN MALAMA, babu komai cikin littafin zai ZANEN ƘADDARA" Yana sake kwanciya kan cinyarta ya ce "Me hakan ke nufi Ummie?"


"Khalil rayuwa ba tabbas, zanen ƙaddara ne ya yi aikinsa cikin littafin nan, da kuma muhimmaci yarda da ita a matsayin mutum Musulmi, muna numfashi da ƙaddarorinmu a jininmu, kasan me yasa na ce sunan labarin littafinka MIJIN MALAMA? Na farko a ƙaddarorin Majeederh akwai farin jini wanda ya tara mata ma nema da yawa kuma a ɓoye dalilin asirin da akai mata, shi yasa ba a san da su ba, kayi rayuwa da ita kana ƙarami ka sake rayuwa da ita a karo na biyu, kuma a hakan kai ba Musulmi bane, bayyanar warwaruwar baƙin ƙullin daya shuɗe da rufewa ya sanya ma neman yin caa" Ta yi shiru can ta ce


"Kasan zaka sameta matsayin mata? Kasan zaka yi rayuwa da ita? Kasan zata haifa maka wannan zuri'ar?" Gently ya girgiza kai ta ce "Why? Me ya sa baka sani ba?"
Ya yi jim kana ya ce "Ina ganin ban cancanta ba Ummie, akwai wanda suka fini nagarta, shekaru, sanin daidai ga ilimi babban dalilin da bata so na" "Good" Ummie ta furta tana shafa kansa ta ce "Bata auri Alpha ba ƙaddarar su ce haka, Ubangijin bai ƙaddara zata aure shi ba, ta auri Abuturab bata zauna da shi ba, ranar data aure shi, shine ya fara amsa sunan Mijin Malama, da Allah ya ƙaddara wa Majeederh aure da yawa to duk wanda ta aura sunan da zai amsa kenan MIJIN MALAMA daga bakin jama'a, dalili a nan ita ce _MALAMA_ akanta labarin littafinka ya fara rubuta “headline” kasha wahala wacce ta kai ka zuwa matakin da kake a yanzu, dalilin Malama kayi rayuwa bisa saka hannun Ubangiji da yarda haɗi da amincewar shi, dalilin Malama ka samu tarbiyyar daka rasa wajen iyaye, dalilin Malama ka fara sanin daɗin Ahali, dalilin Malama ka fara karatu, Allah ya ƙaddara zaka kasance Musulmi ko wacce ƙaddara mai kyau ko mara kyau akwai sanadi, dalilin Malama ka musulunta, dalilin Malama kasan asalin iyayenka, dalilin Malama kasan waye Mahaifinki" Ta jinkirta ta ce "Idan baka amsa sunan MIJIN MALAMA ba waye zai amsa?" Ya riƙe numfashi da kyau yana riƙe hannun Ummie ya ce "No one has been as lucky as Ibrahimul-Khalil, the son of Ummie, the husband of Hawwa, the father of Alhassan and Al'hussain, the king of Saudi Arabia"


"Ma sha Allah, rayuwa cikin farin ciki no more challenges, babu wani tashin hankalin da zai ƙara zuwa ya rusa farin cikin, Ibrahimul-khalil, Ɗan Ummie, mijin Malama, uban Alhassan da Al'hussain sarkinmu na yau da gobe Takawa Khalil" Ya ɗan sauk'e numfashi yana jin wani abu na tsarga masa, a hankali ya miƙe ya fice tare da nufar sashin Queen Majeederh, takunsa bisa duga-dugensa wanda ke nuna tsantsar lafiyar gangar jikinsa dana zuciya. Tsaye ya ganta ta juya baya tana kallon makaken photonsa wanda Fatymerh ta maƙala yanzu, ya ɗaga kansa ya kalli photon a karo na biyu ya sake ware gajiyayyun idanunsa akan frame gabaɗaya ba a jima da yin photon ba, har an yi frame? Aikin Rohaan ne da dukkan alama photon daya gama zaga internet ko wanne sarki gwamna da manya suna posting a twitter akan taya sabon Sarkin Saudiya murna. Ta juya ta kalle shi shima ita ɗin yake kallo cike da sahihin so wanda yake fitowa daga ƙasan zuciyarsa idanunsa ke bayyanar da motsin ji, na daga tafiyar gudun zuciyar tasa, komai nasa ya bubbuɗe. A nutse yake bin jikinta da kallo kayan sunbi jiki tare da zama daram, ya kalli ƙirjinta daya sake cikowa hakan ya haifar da dagulewar riƙon da ya kewa yanayinsa a fili, rauninsa ya bayyana, ya zubawa yatsun ƙafarta dake shimfiɗe zane da ƙunshi kallo, ya juya idanunsa zuwa faffaɗan mazaunanta da suka buɗe sosai asalin dirinta ya bayyana, baya jure kallon idanunta. ganin bashi da niyyar motsawa ta nufe shi tana tafiya jikinta na rawa wanda ta ke yinta cike da gayya hannayenta ta buɗe tare da zagaye shi ta rungumesa tsam a jikinta, hot tears na bin kuncinta, full of love and passion for her husband, she hugged him again, slowly take magane "Ma sha Allah, Alhamdulillah ina taya Takawa murna, Ubangiji ya baka wuyan ɗauka da sauk'e hakƙin jama'a, na yi farin ciki sosai Takawa" Khalil ya kasa cewa komai saboda jinkansa yake kamar ba Khalil ba, wani daban ne, nauyin kansa ya masa yawa, He believes that any success that a man will get in life, it does not happen without a woman by his side, dalilin Majeederh ya cimma burikansa, duk wani long and short terms na goals ɗinsa ya yi Achieving dalilin Malama ba zai taɓa manta sunan Mijin Malama ba, a shekarun da basu shige huɗu ba ya samu cikar victory ɗinsa, me zaiwa Ubangiji banda godiya? Ba zai taɓa butulce masa ba ga tarin darajojin daya bashi.
Majeederh ta ɗan bubbuga bayansa a hankali tana shafa kansa ta ce "Ba lokacin ƙunci ko damuwa bane yanzu a gareka ba Takawa, lokacin farin ciki ne ka zama mai godiya a koda yaushe Sarkina" Ya sauk'e numfashi he needs a shoulder to lean on and cry, he feels like he's going to cry but he can't, ya sake matseta a ƙirjinsa, naman jikinsa na rawa zufa na yanko masa laɓɓansa na karkarwa saboda maganar da yake tattarowa cikin tsananin wahala yana matseta a fusge ya ce "Thank you My Queen" Yana ƙara riƙeta ya ce "Thank you, thank you And i love you"


"Love You too Takawa, Sarki Dr Ibrahimul-khalil" Ya saketa yana buɗe idanunsa ya zubawa lip's ɗinta idanu a hankali ya ɗan yi murmushin gefen baki cikin firgitaccen yanayi ya suɗe gefen bakinsa wasu maganaɗisun abubuwa suka shiga motsawa a duka jijiyoyin jikinsa, magana yake son furtawa gareta ɗin amma ya kasa, yadda tsakiyar goshinsa ke fidda zufa yasa ta fahimta ta ce "Takawa nawa, ni da yarana, Alhassan Singer kamar Aberdeen Abduljabar Abbas, Alhassan Footballer kamar Abu maleek, Yaa K Dr kamar Dr Abdul-hakeem Bukar Bello, Noha Lawyer kamar Moon, Soha matar malam ce kamar Danejo da Yaa Sheikh Aliyu.." Ya ɗan ware idanu sai kuma ya girgiza kai a taƙaice ya ce "Lahhh" Ta zauna kusa da shi tana kallon sai marairaicewa yake kansa ƙasa daya ɗago suka haɗa ido ya saka hannu ya shafi fuskarta ya ce
"Idanunki azaba ne ga Takawa" Ta ce "Ka fito ka ce kana buƙatar ka" Ya yi Miskilin murmushi bai ce komai ba a hankali ya kama hannunta ya ɗora a ƙirjinsa yana rufe ido sun jima kana ya ce "Blessing Woman, Allah ya saki Aljanna" Kasa magana ta yi sai kama fuskarsa da ta yi tare da fara masa wasu lafiyayyun sumbata.
Bayan wata uku akai bikin naɗa Takawa, tare da bashi sanda da Takofi sai wani haɗaɗɗen zobe. Soha da Noha sun yi wayo tare da yin wata ƙiba gwanin sha'awa yaran sun yi jajur dasu kamar na turawa, Yaa K ya sake girma amma jikin nasa sai addu'a ciwon sikila ya sa shi a gaba daman tafi wahalar da maza, ya kwanta jinya asibiti babu adadi, haka kurum hannunsu ya kumbura ba ciwo ba komai ya ja ruwa daga ƙarshe ya fara kure sai da suka je asibiti akace ciwon sikila ɗin ne ya ƙarya ƙashin hannunsa. Alhassan abubuwa suka faskara a halin babansa abinda ya manta ne kawai bai ɗauka ba, hatta zane sai ya ɗauki Ebook ya dinga zane har cewa yake ya zama Aby da Mimi. Da ƙyar Takawa ya tasaa Ummie a gaba da roƙan ta aure Uncle Isma'il Majeederh hadda kukanta, ita sam gani take raini ne ba don tana so ba ta amince. Rohaan ya yi caraf da Sona ƴar Uncle Isma'il. Lokaci ɗaya akai gagarumin biki na fidda raini ƙasa ta ɗauka suka tattara suka nufi Naija domin a can za'a yi bikin. Ummie da Uncle

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login