Showing 114001 words to 117000 words out of 126557 words

Chapter 39 - MIJIN MALAMA Book 2 Complete by Nimcey Sarauta .txt

haɗe fuska tana tura bakinta a hankali muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce "Bad boy" Yana cire ribbon ɗin kanta ya ce "Yhhhh, but untill on bed" Ya tura yatsun hannunsa cikin sumar kanta, gabaɗaya ya manta azumi ya kai ya gama kunce masa lissafin kansa, gently Jee ta zura hannayenta a ƙasan hannayensa ta rungumesa sosai ƙirjinsu manne a hankali ta ce "Man" Bai ce komai ba, sai dabara da ya yi mata yana ɗagota a hankali ya fara unhooking bra ɗin tayi saurin riƙe shi tace "Not now" A hankali ya ce "Saboda ke kika biya sadaki?" Da sauri ta ce "Sadakin da ba a bani ba?" Ya yi saurin sakinta tare da ja baya ya yi zuru domin da gaske shi bai bada sadaki ba ya yi kalar tausayi ya ce "Don Allah?" Ta hararesa tana miƙewa tare da ɗaukan abayarta sai a lokacin ya fahimci dabara take masa ya miƙe yana shafa kansa kamar zai nufi upstairs sai ya sunkuya gabaɗaya ya yi sama da ita ya ce "Yaushe ki kai wayon yiwa Ibrahim dabara? Ke kina jin idan nayi niyyar abu zaki hana? Shuka sai da ban ruwa" Ta yi murmushi kawai ya ce "I love you, and I'll always love you Jee" Ta mintsine shi ta ce "No is the man without a woman" Ya girgiza kai kawai can ya ce "Muje mu gaisa da wannan mala malan naki, naga how big they are yanzu?" Jee mamakin rashin kunyar Khalil take gabaɗaya baya jin nauyin sakin magana. Suna shiga bedroom ɗinsa ya saketa ta zauna saman kujera ya nemi waje a gabanta ya durƙusa hannunsa akan cinyarta yanayinsa ya sauya a hankali ya hargitsa sumarsa ya ɗago kai ya kalleta itama shi take kallo ya ce "You didn't tell me Hawwa'u?"


"Me?" Ya kwaɓe fuska yana ƙara haɗe hannayensu waje guda ya ce "Kina so na, tun sanda bana ji" Tayi dariya mai kyau ta ce "Oh, yanzu ji kake?" Ya ɗan yatsuna fuska ya ce "Be serious Maa" Ta zame hannunta ta ɗora a kansa a hankali ta shiga tura hannunta cikin tulin sumarsa cikin murya mai laushi sosai ta ce "Me ya sa zan faɗa? Bayan lokacin ko auren baka san ma'anar shi ba? Kana ji da rigima, dukan jama'a haura katangar Abbu?" Ya yi shiru kamar mai nazari while he keeps his eyes on her, tasan kuma dole ya karanto gaskiya a hankali ya yi dariya sosai yana girgiza kai ya ce "Kawai kina tunanin ban isa gona ruwa da ƴa ƴa shuka ba, kina tunanin kayan aikin noman sun yi kaɗan ko?" Ta zare ido sosai ta kasa cewa komai ya zauna sosai saman carpet yana lumshe idanunsa jin tana yamutsa gashinsa kamar babu laka a jiki ya ce "Da gaske kin zalunce ni, kuma ki gaggauta neman yafiya" Ta ranƙwashe shi a ka ya ɗaga mata gira ya ce "Ni nasan ko niyyar gado ne ni, ko motsi lafiyayye ne wlh, kuma da kin faɗa mini komai I'll fight don na aureki, I'll fight for my love, zan iya sadaukarwar da komai just to be with you Sexy mama, ni nasan ban cancanta da ke ba, bani da qualities na mazan da suke so...,"
"Stop, bana so" Ta furta muryarta na rawa sosai ta kalle shi ta ce "Me ake buƙata a zaman auren Man? So da ƙaunar juna, yarda da amincewa, riƙe gaskiya da amana, kishin juna, kulawa, kyautatawa, i love you, and you love me too, ci, sha, sutura, magani duka kana bamu ka faɗa mini Qualities ɗin da suka fi wannan?" Kallonta kawai yake without blinking,yana jin kansa wani daban Majeederh ta shafi fuskarsa zuwa gemunsa ta ce "The most important thing in your character is your honesty" Shi a ransa yake jin bai yarda ba kawai taimaka masa tayi da kuma ƙarfa ƙafan da ya yiwa rayuwarta "Are you sure?" "Yes, of course Aby-Alhassan" Ya kwaɓe fuska ya ce
"Ni ban so" Ta ce "Sai me?" Calmly yana saka idanunsa cikin nata ya ce "Say my name, ina son ji" Ta ɗauke ido tana miƙewa tsaye sai kuma ta juya sosai ta ce "I can't" Ya miƙe tsaye shima yana riƙe ƙugu kamar yadda tayi yadda yake sakin jiki da iyalinsa ba zaka taɓa yarda yana da azababben miskilanci ba ya ce "Kina son ɗaukawa kan ki zunubi, yanzu dai ki zaɓa" Ta juya Idanu alamar tana ji ya ce "Ko kice Ibrahim, ko yau a casar bugun dawar da zamuyi Kiyi riding nawa" Ta zare ido sai kuma ta yi saurin ɗauke kanta ya juya ya kalleta sai kuma ya nufi waje ya ce "Zoki ban abinci"
Washegari da safe Khalil ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda gezner dark blue ɗinkin jamper da babbar riga, bai saka hula ba sai sumar kansa daya ɗaure zuwa ƙasan wuya, bai saka babbar rigar ba ya bar iya half da wando hannunsa ɗaya zube cikin Aljihu ɗayan kuma yana danna wayarsa da ɗan sauri yake sakkowa daga kan steps ɗin benen sumar kansa na tashi sbd iskar dake kaɗawa ta Main parlour, yana sakkowa Alhassan ya miƙe da sauri ya ce "Aby" Al'hussain ma ya miƙe baby khalil na tsaye gabaɗaya shaddar jikinsu iri ɗaya ce, Baby Khalil ya fara miƙawa Abyn nasu hannu yana durƙusawa ya ce "Assalamu alaika Aby" Khalil ya amsa yana bashi side hug twins ma suka miƙa masa hannu har sun saba da gaisuwar musabaha, yana tsaye da yaran yana jin abubuwan da kowa ke cewa bugun zuciyarsa da ya ji ya sauya yana tafiya da sauri yasan she's here, tana tsaye kuma shi take kallo ya ɗago kansa suka haɗa ido, farar lafaya ce a jikinta mai bala'in tsada ta kwanta jikinta sosai, ta ɗaura wani siririn liƙab hatta flat shoe ɗin ƙafarta fari ne, har wayar hannunta wacce Khalil ya sauya mata fari, gabaɗaya tayi shigar da Khalil ke so yana ƙaunar farin abu, a fili ya furta "Allhamdulillah!" Ya yi saurin ɗauke tunanin da yake sanda ya tuna azumi suke, ya sunkuya ya ɗauki Al'hussain, Alhassan ya fara kuka ya ce duk kukansa ba zai ɗauke shi ba wlh, yau mai halin matarsa zai ɗauka Majeederh ta yi murmushi ta ɗauki Alhassan tana rungume shi, a tare ita da Khalil suka kama hannun Baby Khalil, Alhassan ya ce "Baby" Khalil ya buɗe ido ya ce "What? Baby?" Ya juya ya kalli Majeederh ya ce "Mimi ɗanki ake cewa Baby fa?" Ta ce "Haka suke faɗa, amma zasu koma faɗin Yaya K" Ya jinjina kai suna fita driver ya buɗe musu jibgegiyar mota yaran a tsakiya, Kspider da Jee suna baya, suna ɗaukan hanya yaga tana buɗe Azkar a hankali ya ce "Ki faɗa a fili, I'll repeat after u" Haka akai har suka nufi gidan Abbu, suna zuwa suka samu Aaliyyah da cikinta ya fara girma sosai suka gaisa da Mami Abbu kuma baya nan, kasancewar jirgi baya jira suka tafi gidan Uncle Bello tunda Uncle Isma'il ba kowa a gidan, Jawaad ya dawo gidan Uncle B da zama, Sona kuma tana gidan Abbu. Tun a ƙofa suka fara jiyo maganar Innati


"Ku kawo ruwa mai ɗan iskan sanyi, ina ƙara Saa guda macewa zan yi, wannan azumin Allah ka yafe Ubangiji ka cika kabarina da gwala-gwalan lada Allah ka yafe mini zunnubaina, a bani ruwa ana taɓa cikina lotsewa zai ƙwaranƙwasa" "Karya azumi kuma?" A hargitse Innati ta ce "Waye wannan kamar ana tashin hankali zai shigo kai tsaye ba sallama?" Majeederh ta ƙarasa shigowa ta zauna tana cewa "Ina yini Innati?" Innati tayi banza ta sake cewa "Ina yini?" Tana ƙanƙance Idanu ta ce "Ibro ka rabani da munafukar matarka, bani ba ita ni ta munafurta" Khalil dai na tsaye idanunsa zube akan majeederh shi har yanzu ya kasa fahimtar wanne kalar so yake mata? Innati ta miƙe tare da ɗaukan kwano ta kwaɗawa Majeederh aka ta ce "Algunguma, irin wannan ranar nake jira gashi tazo, babu tashin hankalin da bamu gani ba akan bakya so da ƙaunar Ibro" Majeederh ta runtse Idanunta cike da baƙin cikin kalamanta a baya kuma tayi nadama yanzu duk wanda ya furta haka ma haushinsa zata ji wallahi Innati ta ce "Ba dole ki runtse ido ba? Wannan azababbiyar ƙaryar ta bugawa a jaridu a haɗa? Ina har Aljanu ki kayi wai Allah ya kashe Ibro ki huta, kika dinga suma kin tsane shi baki son shi? Yanzu ubanwa kika bajewa tika tiki ya ƙunsa miki ciki? Ɗan gwaninin yaron ko? Shi ne ya buga miki iska?" Majeederh ta rasa me zata ce sai kawai ta fashe da kukan takaicin Innati, Khalil ya dinga riƙe murmushin shi ya ƙarasa kusa da matarsa yana bata side hug ya ce "To ke ina ruwanki ne? Idan ta tsane ni ina son ta ai?"


Innati ta fashe da matsanancin kuka hankali tashe ta ce "Asstagafirullah! Allah na tuba bana iya bacci idan na tuna a gidan nan aka bunka iska ta biyu, a gidan nan aka dinga lalata, bani da nutsuwa ana tsokala tsinke a kunnena wuta za a tsokano saboda tashin hankali" Uncle Bello da yake shigowa ya ce "Ibrahim ku tashi ku tafi kar ku yi missing Flight ɗinku" Majeederh dai kuka take, Alhassan ya cika ya yi fam ya kafe Innati da ido, Baby Khalil ya kalli Abynsu ya ce "Aby mene buga iska?" A harzuƙe Innati ta ce "Ubanka Ibro shi ya bugawa babarka iska, ya ƙunsa mata ciki wallahi tallahi" Da wani sauri Majeederh ta miƙe tana yin waje domin Uncle Isma'il ya ce har yanzu Alpha na asibiti kuma karta kuskura ta je, ta jima tsaye kafin taga Khalil ya fito shi da Jawaad da yaran tana ganinsa ta buɗe ƙofa ta shiga saboda wata matsananciyar kunya data lulluɓe mata jiki, bata taɓa jin kunyar mijin nata Dr Ibrahimul-khalil irin yau ba, bata son ma haɗa Idanu da shi, shigowa motar ya yi bayan ya saka yaran tana ganinsa ta rufe ido sarai ya ganta ya share, a haka suka nufi airport, Uncle Isma'il tuni ya sanya ayi masa binciken gidan su Zuleehart a can Ghana accra ɗin. Zuwan su airport ba wahala bayan an musu komai passengers sun fara shiga, Khalil na sallama da John yaga wani ya tsaya kusa da Majeederh kallon su yake, a tsorace Majeederh take kallon mutumin fuska rufe ya miƙa mata envelope babba fara tas sai wani ƙaramin rose dake maƙale a jiki ta ce "Waye kai?" Ya ce "Sanin ko waye ni bashi da muhimmanci, domin bani ne wanda yake zuwa gareki ba, ni ɗin Manzo ne, bi ma'ana ɗan aike, Boss Ubangida shi ne wanda ya aiko ni.....,"
"Ok da kai da ubanka yake ko wa?" Khalil yama kasa ƙarasa maganar ya nufi kan mutumin "Ni fa ɗan aikene, ko a zamanin jahiliyya ɗan aike baya laifi kuma..," Wani mugun naushi da Khalil ya sauke mutumin shi ne ya hana shi ƙarasa maganar, ya damƙi wuyansa tare da yi masa gware nan take jini ya ɓalle, Alhassan me zai yi ba ihu ba yana tsalle yaga ubansa na faɗa, mutumin ya ɗaga hannu ya ce "Ka saurare ni please, zan faɗa maka ko waye" Bai bashi damar magana ba ya damƙi hannun ya karya Ihun azaba ya saki da wani irin fitsarin wahala, ya ce "Ka tsaya ka ji" Khalil ya sake kaiwa bakinsa naushi haƙori ɗaya ya fita ya saka hannu ya zare ribbon ɗin kansa a kausash ya ce "Bana buƙatar reasons, ka zama shaiɗan mai raba aure ko?" Ganin Khalil na ƙoƙarin yin kisa yasa majeederh cewa "Man...," Wata masifaffiyar tsawa ya daka mata tare dayi mata nuni ta kama yaran su nufi jirgi, polices ɗin wajen suka tsaya domin babu wanda bai san waye Khalil ba, ya kalli mutumin ya ce "Kai kayi kaɗan wajen siyan soyayyar Matana, Ubangidan naka ya fito muyi gaba da gaba, zan tafi Saudiyya idan ɗan halak ne shi cikin uwarsa da ubansa ya biyoni zuwa Palace ga i.d card nan" Yana faɗin hakan ya cilla masa I.d card ya nufi cikin jirgin bai yarda ya nufi wajen Jee ba domin sai yanzu yake jin nauyin tsawar da ya yi mata, yana shiga cikin jirgin mutumin ya nufi mota jiki jina jina da jini, yana shiga wanda ke cikin motar ya ajiye azkar ɗin hannunsa ya ce "Sorry" Mutumin ya ce "Boss Ubangidana Akeeth ni zan baka haƙuri" A hankali Akeeth ya girgiza kai ya ce "Ka yankar mini ticket na zuwa Saudiyya now, I'll follow him....
[11/2, 20:11] Ummu: Khalil ya sake rungume Gimbiya yana jin kamar ya shige cikinta ya huta wani irin kewarta ta saukar masa tare da mamaye jikinsa, ƙofofin zuciyarsa suka bubbuɗe da soyayyar Ummien nasa, idanunsa sun yi jajur saboda yadda a karo na farko tun bayan sanin wace mahaifiyarsa ya ji tana kuka, a hankali hawayenta masu zafi suke sauka a bayansa wajen wuyansa, ta ƙanƙame shi da kyau kamar zata sake yin cikinsa ta haife shi, a hankali a kuma nutse tana babbuga bayansa tana shafawa saboda jin yadda yake sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri, wata na korar wata.
"Ummieeeyyy" Iya abinda bakinsa ya furta kenan, saboda bashi da ƙarfin zuciyar da zai faɗi abinda yake saman harshensa a yanzu, ya sake rungumeta, wata gamsasshiyyar nutsuwa na sauka a jikinsa, sai yanzu ya ƙara tabbatar uwa, mahaifiya rahama ce, dole wanda ya rasa tashi ya zubar da hawaye.
"Ibrahim? Khalil yarona"
Gimbiya ta furta a kamalance tana jin dukkan wata damuwar zuciyarta na shekara wajen uku ta yaye nan take, zuciyar ta wanke tare da yin fari daga duhun damuwar da Mr President ya sanyata "Kana raye? Zan sake ganinka?" Yadda take maganar da ƙyar zaka san cewa ba ƙaramin ƙarfin hali tayi ba wajen furta kalaman, Khalil ya ɗago a hankali ya zubawa mahaifiyar tasa ido, shi mamaki yake wai ita ta haife shi? Ya ɗan yi Miskilin murmushi kafin ya ce "Allah bai ɗauki raina ba, ina tare dake, zan ji daɗin uwa Ummie" Sharr! Wasu hawayen suka sake sakko mata a hankali tayi murmushi mai laushi ta ce "Ya Allah!" Ta kama hannunsa tana tattaɓa shi ya riƙe hannunta ya ce "The real Ibrahimul-khalil is back, your son ɗanki ya dawo" Da sauri ta sake jawo shi ta rungume a wannan sa'ilin kasa riƙe kukan ta yi, ta sake shi bisa umarnin zuciya. Majeederh dake tsaye ta yi ƙasa da idanunta hawaye na zuba a cikin idanunta, lallai uwa! Daban take a cikin rayuwar yaranta, yadda Khalil ya narke jikin Ummie kaɗai ya isa ya fahimtar da ita yadda ya yi kewar mahaifiyarsa, ta rufe ido tana jin soyayyar mahaifiyarta fulani na ƙara sauka a zuciyarta ko wanne motsi tayi sai ta tuna da ita, bata san soyayyar uwa ba, babu rabon kuma zata samu ɗin Ubangiji ya fita sonta tunda ya ɗauke ranta ya barsu. Jin an kira sunanta a taushashe ya sanya ta ɗaga kanta Gimbiya ta gani riƙe da hannun Khalil tana kallonta alamar ita ke kiran nata, ta nufeta jiki a sanyaye da sauri twins da Yaa K suka mara mata baya, tana zuwa Gimbiya ta ce "ke fa ba Daughter-in-law ba ce, you're my daughter ko baki auri Khalil ba" Kunya ta kama Majeederhn ta sunkuyar da kanta Khalil ya ɗan shafa kansa speaking calmly a taushashe ya ce "Ummie ki rungumeta itama" Gimbiya ta kalli Khalil sai kuma ta ɗauke ido ta ce "Come closer dear" Ta haɗa su ta rungume a jikinta tana rufe ido a ranta ta ce "Alhamdulillah!"


"Brother" Clara kuma Fatymerh ta kira Khalil tana murmushinta irin na Ummie, Khalil ya kalleta sosai suke kama da ita bambancin kawai ita fara ce komai nasu iri ɗaya ne, nata zubin halittar na mace ne, shi kuma nasa namiji. Ta sake murmushi ta ce "Ko na ce Biyunina" Ya ɗaga mata gira da dukan kafaɗarta sai kuma yi yi mata rungumar gefe (Side hug) Kamar an masa dole ya ce "Sweetheart" Fatymerh ta yi murmushi ta ce "You're welcome Kspider" Ya lumshe idanu ya buɗe, ya kalli Zizi da Badi da suke ta kallonsa jikinsu duka a sanyaye sai ya miƙa musu hannu da gudu suka rungume shi suna cewa "We miss you alot Kspider, Welcome back to the kingdom, among your relatives and parents" Khalil ya yi guntun murmushi iya laɓɓansa kafin ya juya ya kalli Majeederh yaga harta shige motar da Ummie take, ya tsaya cak da mamaki domin basu saba haka ba Ummie ta kalle shi sai kuma ta ce "Me?" Ya ɗan yatsuna fuska ya juya zuwa motar da Fatymerh Clara ke ciki, ya tarar su Al'hussain na ciki ya kwanta a bayan motar yana lumshe idanunsa zuciyarsa na bubbuɗewa na fargabar abinda ya aikatawa Jee har ta raba mota da shi, har suka isa cikin Palace idanunsa rufe ko tari bai yi ba, yana jin wata sarewar Algaita na tashi mai sanyi da daɗin saurara sounds ɗin na musamman kamar yadda ko wacce masarauta kalar Algaita ɗinta daban yake, wanda Sarkin Busa ke yi ya gada kuma wajen iyaye da kakanni, Khalil ya tsani duka irin wannan shi kaɗai sai siririn tsaki yake jaa. Majeederh na fitowa daga motar ta bi masarautar da kallo wata kamala, nutsu izza da isa irin ta masu jinin sarauta na game jinin jikinta, a ranta tana yiwa Ubangiji kirari rashin sani ya fi dare duhu sau biyu tana zuwa cikin Palace ɗin nan ba tare da sanin cewa gidan grandparents ɗinta bane, ashe duk wata soyayya da Ƙhulud Arzaan ke nuna mata jininsu ɗaya,ita ɗin ƴar uwarta ce, Lillahi wahidur Qahhar, buwayi gagara misali banda Al'hakkamu waye zai yi wannan? Ta goge hawayen dake bin idanunta, yadda take tunani haka Khalil ke yin nasa shi da keɓantacciyar zuciyarsa, ya karɓi Musulunci wajen Uncle ɗinsa, ya kalli Mahaifiyarsa ba tare da sanin matsayinta a wajensa ba, ya zauna cikin danginsa ba tare da saninsu da nasa ba, komai yana zuwa bisa tsarin Ubangiji da kuma yadda yaso. Ya lula

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login