Showing 42001 words to 45000 words out of 117648 words

Chapter 15 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

da kayan barcinsa pyjamas samfurin ck ya tsaya gaban mudubi ya taje sumar kansa sannan ya feshe jikinsa da turare. Duk abinda yake tana kallonsa tana wani sake birgima duk don ta ja hankalinsa tsaki ya ja a zuciyarsa ya ce “In an girma a san an girma wannan rigar ai bata dace da ke ba, da suturce jikin kika yi may be da na fi sha’awarki. Duvet ya d’auka had’e da kashe mata wutar d’akin ya fice. In dai shine ba zai kulata ba sai ya koya mata hankali ta fannin da ya san bata iya jurewa sai ta kusanceshi. Sau tari yana mamakin yanayin halitta irin ta ta. Tana da zafaffiyar sha’awa.


Kwanciyarsa ya yi ana parlourn zuciyar Nanna a tunzire ta biyoshi don ba k’aramin shiri ta yiwa wannan daren ba ta banki magunguna son ranta duk don ta kautar da hankalinsa tasa ya mayar da Hamda campus. Yana jin motsinta ya rufe idonsa ruf tamkar mai barci. Ga mamakinsa sai ya ji ta yaye duvet d’in rufe jikinsa da shi. Tana tsaye daga ita sai banzar rigar da ta k’ak’aba wa kanta. Ya so tuntsirewa da dariya sai ya gimtse bakinsa “Lafiya?” Ya furta yana tsatstsareta da ido “Anan zaka kwana?” “Eeh” ya amsa mata direct “Amma fa kai nake jira.” “Sai ki daina jiran nawa ki je ki yi barcinki tunda ni ai ba kiga ina jiran naki ba.” Ya sake mayar da kansa ya rufe. Gwiwa a salub’e ta juya ta koma d’aki hankalinta a matuk’ar tashe. Da kyar ta samu barci ya yi awon gaba da ita. Shima d’in ba wani barci yayi ba tunani sun sha masa kai ta yarda zai yi da matsalar Hamda.






__________________________




Kamar yarda ya ce mata kashegari da kansa ya kawo mata envelope shak’e da dollars a ciki. Ya mi’ka mata “Ga sadakin ki don zuwa yanzu na tabbatar kin gamsu da cewa auran da zan miki shine gatanki. Ango kuma zai zo anjima.” Shiru ta yi tana juya kud’in a hannunta kafin ta mik’a masa “Ka ajiye min a wajenka zan karb’a” ya karb’a kafin yace “Be ready around 5:00 pm idan ya dawo daga office zai zo.” Ta gyara zamanta had’e da d’aga masa kai.




Tunda k’arfe biyar d’in ta kusa ta ji k’irjinta na sake nauyi fargabarta na k’ara yawa, da gaske tana jin tsoron had’uwa da mutumin da aka ce shi zata aura. Ta dai yi wanka amma ko mai da kyar ta shafa ta zira wata simple gown had’e da mayar da gashinta baya ta yi rolling kanta. Yanayin garin da alama zai karb’eta don ta sake wani fresh fatarta ta sake bayyana taushinta. Tana zaune a k’asan carpet Kamla a jikinta, don ita sam ta kasa rabuwa da ita duk da jan kunnen da Mom ta yi mata tana son Hamda sosai. Ya turo k’ofar ya shigo idanunsa a kansu sai ya gan su tamkar wasu ya da k’anwa. “Fito ga bak’on ki can a garden, ki kuma kiyaye mutuncinki bana son zubar da martabar d’iya mace.” Hannunta cikin na Kamla suka fito kirjinta na sake nauyi tamkar an d’ora mata dutse.


Tun daga nesa ta hangoshi zaune akan kujerar da take gark’ame a garden d’in. Sanye yake cikin farar shadda k’al da ita kansa da hula zubin zannan bukar. Ta sake damk’e hannun Kamla a karo na biyu jikinta ya fara rawa ji take tamkar ta juya sai dai juyowar da ya yi ya sata saurin k’arasawa ba shiri, saboda ya riga ya ganta ba amfanin guduwar.


Bak’i ne sosai sai dai ba za a ce masa mummuna ba.
Yana da kyansa da kuma kamalarsa ji ta yi Kamla ta ce “La Uncle Musty.” Suka had’a ido ba shiri ta ce “Ina wuni?” Yana murmushi ya ce “Lafiya lau Amarya ya shirye-shirye?” Ta gyara zamanta tana kallonsa yana jan Kamla da wasa.
“Amma dai zahirin kamarku da Kamla har ta b’aci.” Ya furta yana tsareta da ido. “Sai dai ki yi hak’uri auren mai mata sai ka runtse ido ka kawar da kai daga abubuwa da dama.” Ba tace komai ba sai dai gabanta ya tsananta bugu da ta ji ya ce yana da mata. Sun d’an dad’e suna hira sama-sama kafin ya yi mata sallama ya tafi. Zuciyarta ta d’an samu nutsuwa kuma ta amince zata iya zaman aure da shi don ba shi da makusa. Musamman da ta ji ya ce Ba gida d’aya zan had’aku ba kowa zata zauna a gidanta.”








______________


Bayan kwana uku kuwa aka d’aura mata aure. Tana zaune Hammad ya shiga d’akin kullum anan zaka sameta rakub’e a carpet don Nanna ta hanata sakewa.


Ya bi d’akin da kallo kafin ya tab’e baki ya ce “Ki had’o kayanki mu je na raka ki gidan ki ga ango can yana jiranmu.” A take wasu irin hawayen bak’in ciki suka fara zubo mata. Wannan fa shine irin nata auren kamar auren y’ar tsana, ko a labari bata tab’a jin irinsa ba. Didi ta sha yi mata addu’a “Allah ya kaimu bikin ki na gwangwaje.” Ashe bikin nata ba wanda zai halarta Sai mutane da ba sufi uku ba. Anya kuwa mijin zai ga k’ima da mutuncinta? Da kansa ya shiga tattara mata kayanta shi kansa a yanzu tausayinta yake sosai amma bakomai insha Allah hakan alheri ne a wajenta. Ya durk’usa gefenta kawai sai ya tsinci kansa da share mata hawaye da tafukan hannunsa. Cikin kunnenta ya yi whispering voice d’in sa “Khairan Insha Allah, just pray.” Wani sanyin jiki ya ziyarceta sosai kalaman nasa suka yi tasiri a zuciyarta ta lumshe idanunta cike da kasala ta mik’e. Da kansa ya yafa mata mayafin abayar da yake jikinta ya sake fesheta da turare yana yi yana jifanta da murmushi “Ki dage wajen biyayya ga mijinki a yanzu shine farincikinki kema kece farin cikinsa.. ina tabbatar miki son da yake miki baya yiwa kansa. He loves you more than anything.” Jikinta a sanyaye ta bi bayansa yana janye da trolley d’inta.


A zaune a parlourn tana cika tana batsewa ta zuba musu ido har za su wuceta ya ja ya tsaya had’e da kiran Hamda “Maza ki yi mata sallama ta kuma sawa aurenki albarka idan ta ga dama. Yau sai ki zuba ruwa a k’asa ki sha ta bar miki gidanki ita ma ta tafi nata gidan mijin.” Da sauri ta d’ago tana kallonsa “Aure ka yi mata?” Ya d’aga mata gira yana sakin murmushin ganin yarda ta saki fuska nan da nan alamar lamarin ya yi mata dad’i “To fa! Wa aka lik’awa ko da yake ba hurumina bane, ko dai wa ka aurawa ka sanar da shi wacece ita idan ya ga zai iya zama da ita to don kada daga baya su ga ka ha’incesu.” Harara kawai ya zabga mata ya nunawa Hamda hanya. Nanna ta yi mutuwar zaune sai dai farin ciki fal ranta ko bakomai dai yau ta tabbatar mugun mafarkinta na Hamda da mijinta bai tabbata ba. Don ta kasa yardarwa zuciyarta Hamdan y’arsa ce. Ta saki murmushi da d’an dariya tana kiran wayar aminiyarta.






Musty da abokinsa suka tarar don haka suka shiga bayan motar.


Tsararrren gidan da yake unguwar Smethwick B66 madaidaicin gida ne mai matuk’ar kyau. Daga cikinsa babban parlour ne da d’akunan barci guda uku sai kitchen babba da kuma toilet a kowanne d’aki da parlourn.


Har Cikin d’akinta Hammad ya rakata wanda ya gaji da tsaruwa sai zabga k’amshi yake. Ta zauna a d’ofane a gefen gadon tana jan duk addu’ar da tazo bakinta. Saboda yanayin fad’uwar gaban da take ciki.


Yana ajiye trolley d’in ya juya da sauri ya fice yana jin karayar zuciya na tausayinta Na son kama shi kamata ya yi ace mata ne suka rakota kamar kowacce Amarya sai dai ita bata samu gatan hakan ba.






Tana jin rufe k’ofarsa ta bud’e fuskarta daga lullib’in da ta sha idanunta kuwa har tashi suka yi saboda kuka. Ta bi d’akin da kallo ba kowa sai k’arar a.c . Ta share hawayenta tana tunanin lokacin kuka ya ‘kare yanzu kamata ya yi ta fuskanci yarda zata inganta rayuwarta ta bawa mijinta kula ta kuma samu isashshen karatu ta yarda zata bawa Ammi mamaki, duk da ba ta jin zata sake mata kallon uwa.


A hankali ta ji ana knocking hankali a tashe ta ce “Waye?”duk da ta san mijinta ne daga can k’asa ta ji muryarsa ya furta “Your lovely Husband.” Hannu na rawa ta yayimi mayafi ta sunk’e kanta kafin ta murza mabud’in k’ofar idanunsu suka gauraya da juna yana mata narkakken kallo da ya kusa sanyata sakin fitsari a wando, don kallo ne da yake bayyana tsantsar soyayya da narkar da zuciyar duk wanda aka yi wa. Ganin tana neman zame masa mutum mutumi yasa ya jawo tattausan hannunta ya damk’e cikin nasa had’e da busa mata sassanyar iskar bakinsa da ta cakud’e da ta mount wash d’in da ya kuskure bakinsa yana murza hannunta idanunsa cikin nata har a lokacin ya ce “Bar kallo na kamar ba ki sanni ba, Da gaske ni ne mijinki Hammad!”




To fa! Hausawa na cewa laifin dad’I ya yi k’arewa anan na kawo k’arshen free pages nagode da bibiyata da kuka yi tsawon wannan lokacin. JIKAR NASHE TA KU CE..”
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Hannunta ne sosai ya fara rawa tana k’ok’arin matsawa daga daf da juna da suka yi. Tunani take anya Yaya Hammad bai samu matsalar k’wak’walwa ba ya za’a yi yace shi ya aureta shikkenan daga matsayin wa ya koma Uba, daga uba kuma ya koma miji lamarin kamar almara. Har a lokacin idanuns cikin nata suke ya gagara sauke su, damar da ya dad’e yana jira kenan. Tana k’ok’arin zamewa ya sake janyota jikinsa “Kada ki hanani kusantar jikin da yake halaliyata da gaske ni ne mijinki ki nutsu sosai zan gaya miki abinda kika dad’e kina son ji. Ba ni da alak’a ta jini ko d’aya da ke.” Ya kama hannunta ya zaunar da ita a gefen gado still hannayensu cikin na juna yana murzarsu a hankali ganin a rud’e take ya sa a hankali Cikin wata irin murya ya fara magana a kunnenta tamkar ba ya son wani ya ji “Da hankalina Hamda, da gaske nake miki ba ni da alak’a ta jini da ni da ke. Duk da labarin ba mai dad’in ji bane zan sake tabbatar miki ke y’ar halak ce kuma y’ar sunna da mahaifiyarki ta bi son zuciyarta domin samar da ke. Na San za ki fara tunanin wace irin magana ce wannan ana aure akan aure ne? Ba ni da wannan amsar Hamda amma da kunne na ji sanda ake jaddada ke y’ar halak ce y’ar sunna.” Zuwa yanzu rikitar da take cikin kwanyar Hamda ta bi gaban a misalta da gaske ta shiga cikin rud’u don haka kallon Hammad take kawai zuciyarta na d’agawa da sauri da sauri har hakan yana bayyana ta saman rigarta. Jin ta take tamkar a wata duniya ta mafarki da take fatan ta farka nan kusa a kuma sanar da ita mafarkin da ta saba ne mafarkin aurenta da Hammad. Ta yi mafarkin nan ya fi a k’irga a rayuwarta tun bayan dawowarsu da suka had’u take mafarkin sa a matsayin mijinta mai nuna mata zallar soyayya da gaske Didi take a duk San da ta rungume pillow a cikin barci to ba kowa take rungumewa ba sai Hammad har
Hakan ya rinjayi zuciyarta a zahirance idan har za ta ga Hammad to za ta ganta rungume a faffad’an k’irjinsa ya nuna mata zallar soyayya. Ta fi alak’anta hakan da shaid’anu ko aljannu da suke suffanta mata Hammad d’in a matsayin mijin da ya dace da ita da zarar hakan ya faru ista’aza take yi a ranta ta kuma runtse idanunta tana jin bugun zuciyatta.




Sai ga shi yau a zahirance ba bad’inance ba ita ce daf da Hammad yana nuna mata kwatankwacin waccan soyayyar ta bad’ini.


Bai bar murza hannun nata ba, ji yake hakan da yake yana samar masa wata irin nutsuwa da shiga wata duniya da bai tab’a katarin kasancewa a cikinsa ba, ko don bai tab’a had’uwa da macen da yake wa kwatankwacin so irin na Hamda ba. Tun bayan zuwansa Nigeria da ya kyallara idanunsa a kanta ya ji matsananciyar k’aunarta ta kama shi irin k’aunar da take huda k’ashi da b’argo fatansa kawai a kullum hanyar da zai bi ya mallaketa ya ji tattausan hannunta a cikin na sa hannayen ya ji wannan tattausa lab’b’anta masu tudu kad’an a cikin bakinsa ya ji shi yana murza dukka sassan jikin ta da ya tabbatar da cikar halittun ta ko ta ina, cikin tafukan hannayensa. Ya kwana da sanin cewa idan har ya ce zai aureta akwai rigima kwatancciya da zata b’ullo shi yasa ya dinga k’ok’arin danne duk wata zilamarsa. Sai yau da ta zama halaliyarsa mallakinsa ta amsa sunanta na Hamda Matar Hammad. Ya lumshe wasu hawayen farin ciki suna ziraro masa bai tab’a sanin ashe haka masoya suke ji ba sai yau da ya mallaki Hamda ashe tilas masoya su rud’e a lokacin da suka rasa abinda suke so. Yana son Hamda son nan da ake cewa So da zai iya aikata komai a kansa ciki kuwa har da sadaukar da rayuwarsa kacokam a kan ta.


Zame hannunta ta shiga yi saboda wani irin yanayi da Ta shiga. Da sauri ya sake damk’e hannun ya jingina kansa a saman kafad’arta bakinsa a cikin kunnensa ya ce “Please kyaleni Hamda kin san tsawon lokacin da na dad’e ina jiran wannan ranar.” Ta lumshe idanunta tana amsar sak’onnin da yake isar mata wata irin kunya ta kamata saboda yarda ya rikid’e mata sam ba kunya a lamarin sa yau ya ajiye Yaya Hammad d’in ya ajiye Daddyn da ta ce ta dinga ce masa ya koma mata Hammad d’inta na mafarki.


Murya a dashe, muryarta da yake so sosai a dashe take kad’an ta ce “Please Yaya Hammad!” Da kyar ya bud’e idanunsa da suka canja kala a kanta kawai sai ji ta yi ya rungumeta tsam a jikinsa yana k’ok’arin zame mayafin da ta k’udundune kan ta da shi. “Ni fa ka kyaleni ba zan amince da kai ba har sai ka tabbatar min da gaske ba ni da alak’a ta jini da kai kada naje ko irin abinda ka yiwa Ammi zaka yi min...” Cikin wani irin sauri ya sake ta yana bin ta da wani kallo sai dai madadin ta ga alamun b’acin ran sa still soyayyarsa ta gani kwance a idanun. Ya ja ajiyar zuciya kafin ya mik’e ya bar d’akin gaba d’aya sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ji sam bata kyauta abinda ta yi masa ba. Ta lumshe idanunta farin cikin cikar burinta ya gama naso a zuciyarta da gaske Hammad shine mijin ta dad’e tana nema. Bata san sanda ta kai goshinta ta yi sujudar godiya ga Allah ba. Amma kafin ta amince masa ya zama dole ya gabatar mata da shaidu da kuma tabbatar mata ba su da alak’ar jini da shi. Ya kuma sanar da ita ta hanyar da aka sameta tunda ya ce y’ar sunna ce ita? Abin tambaya dama ana aure akan aure ne?


Mik’ewa ta yi tana sake nazarin d’akin, yana d’auke da babban gado family side ruwan k’asa mai adon silver. Kasancewar d’akin da girmansa daga gefe can dresser ne mai d’auke da cahinet ta zuba kaya sai wajen saka takalma da jakunkuna.
Kuma ko ina ta bud’e cike yake da kaya alamar da gaske Hammad ya shiryawa auren nan. Ta tsaya jikin mudubi tana k’arewa kanta kallo tana mamakin mai Hammad ya gani tare da ita har idanunsa suka rufe daga tarin matsalolin da za su shiga nan gaba ya aureta. Tana da tsayi sai dai ba can ba, ta fannin dirin jiki kam sai sam barka haka nan fuskarta ba za’a kira ta mummuna ba sai dai ba ta cikin kyawawa matuk’a ainun. Bakinta ya fi komai fisgar hankali a fuskarta don yana da kyau sosai kasancewarsa mara girma kuma mai d’an tudu ga su pink sosai suna kuma shining kamar an shafa wet lip. Ba ta da hanci mai tsayi na ta tudu ne da shi kuma a duk san da tayi dariya yana lob’awa kad’an sai lob’awar da take k’asan hab’arta. Cikakken gashin gira da na ido shine abinda ya ke sake fisgar hankalin mai kallonta. Da kuma yalwataccen gashin da ya kwanta a gaban goshinta. Tana da duhun kala sosai don ba za’a saka ta a layin farare ba sai dai tsaka-tsaki duk da bature ya ce black is black to tabbas itama Hamda ta yarda bak’ace sai dai fatarta mai kyau ce ainun fiye da ta wasu fararen. Ajiyar zuciya ta ja kafin ta shige toilet ta sake wanka sosai duk wani lungu na jikinta sai da ta sake tsaftace shi. Don ta san jikin nata yanzu ba mallakinta bane ita kad’ai.


Ko da ta fito tsaf ta tsane kanta da towel kafin ta saka hand dryer ta busar da shi. Ta shafa oil ta taje shi sosai sai ga shi ya mik’e sai k’yalli yake. D’aureshi ta yi a tsakiyar kanta sai ga shi ya zama kamar doughnuts.


Ba wata kwalliya ta yi ba, powder kawai ta murtsika a fuska ta shafe bakinta da wet lips mai k’amshin strawberry. Brush ta saka ta taje gashin girarta sai kuma Ta d’an zizara eye liner. Sosai ta fito tsaf da ita bayan ta zira wata doguwar riga pink colour. Madadin ta fita kuma sai kunya ta kamata ta tada sallah kawai kasancewar magriba ta yi. Ko da ta idar nan ta yi zamanta idanunta akan tv amma zuciyarta na ga Hammad ganin har lokacin bai sake shigowa ba, ta san fushi ya yi. Kawai sai ta samu kanta da ganin rashin kyautatawarta ta mik’e cikin mutuwar jiki ta fita parlourn.


Baya parlourn amma ta ji alamunsa a kitchen don haka kai tsaye ta nufi kitchen d’in.


Yana tsaye da ludayin miya a hannunsa duk ya yi kaca-kaca da kitchen d’in wajen dafa noodles da kwai sai fruit da ta gani a gefe an yayyanka. Dariya ta so kufce mata ganinsa da rigar girki a jiki (Apron)

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login