Showing 96001 words to 99000 words out of 117648 words
Chapter 33 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt
ta k’arasa wajenta sai dai madadin zaman a jikinta kamar yarda ta so zamanta ta yi a gefe yarda ta saba, “Ina kwana Ammi” ta fad’a cikin sanyin jiki. Ammin sai da ta ja fasali da ajiyar zuciya kafin murya a raunane ta ce “Lafiya lau Hamda, kin tashi lafiya?” A karo na farko Hamdan ta ji abin banbarakwai don bata saba ji ba, ta saba jin Ammin ta amsa mata cike da kyara da hantara, sai ta ji bakinta ya yi nauyi ya kasa amsa tambayar Ammin, ta mayar da kallonta kan y’an uwanta da suma suka zuba mata ido cike da k’auna, tabbas dama su ta shaida suna sonta don ba su tab’a nuna mata tsana ko kyara ba, gaishesu ta yi Munira na tsokanarta “Amarsun Y. Hammad da alama dai Didi ta fara miki gyaran jiki, Ammi itama ki bata kayan gyaran jikin da naga kin ware kince nata ne, tunda dai duk sun yi aure sun bar ni. Har da k’anwata.” Nasma ta ce “Ke kika so Munirat idan banda haka mutum nawa ne suke cewa suna sonki.” Munira ta girgiza kai tana mik’ewa ta ce “Na barwa Hamda girman sai na je yi mata zaman dab’aro.” Wata irin kunya ce ta kama Hamda ta mik’e ba tare da ta ce uffan ba ta yi hanyar waje. Sai jikin Ammin ya yi sanyi ganin har yanzu Hamdan ta kasa sakewa a cikinsu, jikinta a sanyaye ta dubi Munira da ta d’ebo kayan sai ta yi turus ganin Hamdan har ta fice, ajiyar zuciya ta ja kafin ta ce “Munira bi ta da kayan can ki mata bayanin yarda zata yi amfani da su, amma don Allah ta kula da su kin san dai kud’in da na kashe wajen had’a su.” Ta fad’a muryarta a raunane tana jin haushin yarda Hamdan ta kasa sakin jikinta da ita, ko da wannan kad’ai a ka hukuntata abin takaici ne.
A falo ta same su Hamdan na shafawa Didi man zafi a k’afa, Munira ta yi sallama cikin siririyar muryarta. Sai da suka amsa sannan ta shiga, bayan ta gaishesu ta sauke idanunta akan Hamda “Muje ciki Ammi ce ta aiko ni in miki bayanin kayan nan.” Wani irin kallo Didi take mata kamar ta ga abin kyankyami, ta mayar da kallonta kan Hamdan da take k’ok’arin mik’ewa ta ja wani dogon tsaki kafin ta ce “Ammo ce ta aiko ki ba Ammi ba, ni za’a kawowa kinibibin banza, wato ta ga uban yarinya mai kud’i ne shine za’a zo a kanainayeta, to wallahi ki gayawa Sakina ta fita idona, uban me ma ta baki ki kawo mata, wato yanzu zata nuna min ita ta haifi y’ar bayan da ta banzagatar da lamarinta, zube kayan mu ga wace uwar ce a ciki?” Munira gaba d’aya ranta ya b’aci jin abinda Didin ta fad’a duk da ta san gaskiya ta fad’a amma ai Ammin ta yi nadama me yasa ba za’a bar abinda ya wuce ya wuce ba, ita kuwa Hamda zuciyarta fara k’al ko bakomai Didin yau ta biya ta, da Ammin me ta sani nata ita kam ko ina zata bugi k’irji tace Didi ce babarta, sai Abbu shima ba zata mance kulawarsa gareta ba. “Ki ke kallo na ko duka na za ki yi? Zube kayan nan naga me aka k’unshe za’a je a bata, tun yanzu wato za’a fara koya mata bak’in halin asiri, to wallahi ba zan yarda ba eehe.” Asma’u ce ta kashe maganar ta hanyar cewa “Haba Didi, duk me ya kawo haka? Ya za’a yi kice sai sun ware kin ga abinda ke ciki.” “Ki kiyayani Asma’u babu ruwanki ta bud’e naga me yake ciki? Na sani ko maganin mallaka ne ta bata a mallake min jika kamar yarda aka mallake ubansa.” Cikin takaici Munira bata san sanda ta zazzage kayan ba ta ce “Ga shi nan, kayan gyaran aurene da ake bawa duk wata mace idan za’a mata aure, wannan ki dinga sha da yoghurt wannan zuma ce wancan kuma turaren tsuguno ne, sai kuma tace a gaya miki ki dinga shafa wancan a fuskarki every morning kafin ki yi wanka na gyaran fuska ne kafin a sallace a fara muku gyaran jiki.” Didi ta ja tsuka “Zancen banza zancen wofi, ce mata na yi ba zan siya mata kayan gyaran ba, tun yaushe ma Asma’u ta fara mata kinibabbiya kawai, d’auki ki mayar mata.” Asma’u ta yi saurin cewa “A’a Didi, ba za’a mayar ba, ko wanne da irin aikinsa wannan na san na can garinsu ne, ki ce mata an gode.” Asma’u ta kwashe kayan ta na mayarwa leda, Munira ta juya ranta a b’ace ta fice daga falon.
Ana shan ruwa ya shiga falon Didin, don yau Nanna bata nan a gidansu zata sha ruwa, fuskarsa a d’an had’e take don haushin Hamda yake ji kamar me? Ace mace ta yi banza da mijinta kuma ta ganshi amma ta d’auke kanta, ko gaisuwa a haka za suyi ta su rayuwar auren kenan bai isa ya sata ba, bai isa ya hanata ba?
K’ananan kaya ne a jikinsa na companyn Ck da suka matuk’ar amsar gogaggiyar fatarsa, sosai ta yi kwalliya fuskarta fal annanshuwa musamman aminyarta ta sun iso ita da yayyanta maza guda biyu. Riga ce doguwa a jikinta da ta fitar da duk wani shape na jikinta, sai hula irin ta turban d’in da ake ya yi ta d’an zameta ta yi baya, kwantaccen gashin da yake gaban goshinta ya bayyana bak’i sid’ik da shi, ta yi kyau sosai duk da ba kwalliya ta yi ba, idanunsa ya sauke cikin nata cike da takaicin yanayin shigar da take jikinta ga kuma Maza a wajen, ransa a b’ace ya dinga hurga mata harara. Didi tana ganinsa ta ce “A’a ka daina fushin ne ka shigo?” Sake tsare girarsa ya Yi sosai Yana amsa gaisuwar da suke masa ya kalli Didi “Ban da matata mai k’aunata bata nan, ban ga mai Zai kawo ni nan ba.” Asma’u ta guntse dariyar da take shirin kamata don ta lura sosai Hammad yake Jin haushin hanashi keb’ewa da Hamda da aka yi. Hamda kuwa ranta a b’ace bata san sanda ta d’ago ta wurga masa wani kallo ba ya yi kamar bai ganta Ba Kafin ya kalli Sa’ada ya ce “Yarinyar kirki zubo min abinci maza ki kawo min shiyyata.” Ya saka kai ya fice ji yake kamar ya mak’ure Hamda ya hukuntata da y’ar banzar shigar da ta yi. Didi tace “Zancen Banza, abincin ma ka yi masa zuciya mana yaro Sai cin tsiya.” Sa’ada na shirya abincin ASMA ta kalli Hamda ta ce “Maza ki rakata ku kai masa k’afarki k’afarta kuma.” Hamda ta d’aga kai alamar amsawa ko Umma Asman bata ja kunnenta ba, takaicin maganar da ya jefeta da ita ba Zai saka ta zauna ba, ya tafi can wajen matar tasa, ina ruwanta….
[1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: Didi ta dinga zarar Super exclusive da Hkg lace masu matuk’ar tana mik’a musu, bakinta washe sai fara’a take, yarda ta bawa kowa haka ta mik’awa Ammi tana muzurai, Ammi murmushi ta yi bata bi ta kanta ba, ta tabbatar yanzu lokacin Didin ne na yin duk yarda ta ga dama, kuma bata da power ko ikon da zata hanata hakan, ita yanzu burinta Hamda ta saki jiki da ita kamar kowane d’anta. Shi kuwa Hammad gaba d’aya baya cikin nutsuwa, ransa duk ya dagule ganin yarda idanun Hamdansa ya nuna tana cikin damuwa, da zarar sun had’a ido kuma take zuba masa harara.
Ana gamawa kowa ya mik’e, ganin duk iyaye duk sun fita yasa ya kalli Hamda fuska a d’aure don kada ma Didi taga fuskar da zata kawo masa wargi ya ce “Mu je waje ki karb’i sak’o” Didi ta watso masa ido “Ba zata ba, idan sak’on Allah da annabi ne a kawo mata nan mana, in dai ba sak’on tsotse-tsotse da lashe-lashe ba, nema kake ka bud’ewa yarinya ido kamar yarda ka bud’ewa waccan matar taka ido.” Duk zantukan Didi akan kunnen Ammi, gaba d’aya hankalinta tashi ya yi abinda Didi dama take koyawa Hamda kenan gudun miji, lallai Didi bata d’orata a kan turba mai kyau ba, har zata koma ta yi magana sai ta tuna kwararaton Didi don haka ta fice jikinta a salub’e tana ayyana ya zama dole ta ga Hamda kafin tasa Mijinta ya fara jin haushinta. Hammad kuwa a zafafe yake kallon Didin murya a cunkushe ya ce “Raina ni kike so ta yi? Ina cewa ta zo kina ba zata zo ba?” Didi ta gyara zama tana tab’e baki “Ai na san zuwan ba na Allah da annabi bane, ka yi gaggawar kawo lefe kafin na yarda ta dinga bin ka.” Ya gyara zama idanunsa cikin na Hamda da taga tsagwaron b’acin ransa a ranar kalar wanda bata tab’a gani ba, kamar ya mik’e ta bi shi amma idan ta tuno abinda ya ce mata sai itama taga gwara ta bi ta Didin ta kyaleshi wato yau a rashin matarsa yake nemanta kamar yarda ya ce. Idanunsa jajur ya ciji leb’ensa had’e da mik’ewa ya yiwa kansa alk’awarin sai ya koyawa Hamda hankali kafin Didi ta saka raini ya shiga tsakaninsu, ba zai yarda ba duk son da yake mata ba zai bari ta raina shi ba.
A zuciye ya mik’e ya fice daga falon, Umma Asma tana d’aka bata san duk wainar da ake Toyawa ba, sai Sa’ada da takaicin Hamda ya sa ta mik’e ta shige d’aki tana mamakin wautar Hamda, mijinki yana binki yana lalla’ba Ki har ki bari fushinsa ya sauka kan fuskarsa tana jiye mata ranar da Hammad zai sauke kwandon fushinta a kanta, banda shashancin Hamda y’an matan yanzu da idanunsu yake a waye ita kuwa Didi na nema ta zamar da ita y’ar zamaninsu banda wauta yanzu wa ke gudun namiji.
Itama Hamdan jiki a salub’e ta mik’e ta bi bayan Sa’adan tana shiga ta zube a gefen gado tana jin wani irin feeling na son kasancewa da mijinta, musamman magungunan da take sha suna aikinsu yarda ya kamata a jikinta, kuma ta d’and’ana zak’in abin ta ji, don haka yanzu yake wahalar da ita, ta lumshe ido tana jin yarda duk tunanin Hammad ya dabaibaye zuciyarta. Sa’ada ta yi tsaki tana zuba mata harara ganin yarda ta cukuikuye filo ta janye filon “Aikin banza ga inda can zaki je ki samu nutsuwa kin zo kin wani k’ank’ame filo.” Ta d’an bud’e idanunta da suka mata nauyi tana kallon Sa’ada da gaske tana buk’atar nutsuwar amma tana gudun jarabar Didi, “Kin wani bi kin takure kanki saboda wannan tsohuwar da bata san annabi ya faku ba, da wannan azimin kin d’auki zunubin mijinki don wallahi na gano tsananin b’acin ransa, ki tashi ki je na tabbata Didi yanzu ta yi barci ki samu ku rage wa kanku zafi, wallahi ba zance kin je wajensa ba, kin san Umma a d’akin Didi take kwana ba ma zata zo nan ba sai asuba, idan kin fito ki saka Yaya Hammad d’in ya kirani da kaina zan bud’e miki k’ofa.” Hamda ta d’an saki ajiyar zuciya “Ba zan iya ba Sa’ada bar shi kawai.” “Kada Allah yasa ki iya d’in, Allah yasa shi yana da wata matar ko a darennan zai iya zuwa can gidansu ya d’auko a barsa idan matsuwar tasa ta kai ke ce abin ji da ba abinda za ki iya sai rungumar filo.” Wani abu ne ya tokare wa Hamda ta dinga kallon Sa’ada a wani irin yanayi tana jin takaicin maganarta kishi mai girman gaske ya fara k’ok’arin toshe mata numfashi, sai ta ji gaba d’aya Hammad d’in ma haushinsa take ji ba kuma zata je ba ya je ya nemi matar tasa. Sa’ada ta zuba mata ido tana kallon k’wallar da ta kwaranyo mata duk da k’ok’arin mayar da ita da take, a hankali ta ce “Kan uba ba dai tsananin kishin naki har ya kai haka ba?” Ta fad’a jikin Sa’adan tana kuka “Ya wuce haka Sa’ada, har addu’a nake ubangiji ya yaye min kishin nan amma kamar k’ara tunzira lamarin nake a zuciyata, Sa’ada irinmu ba su kamanci auren mai mata ba, gudun kada kishi ya ja mu mu fad’a halaka, Musamman Ina son Y. Hammad son da ban had’a shi da komai ba, ko sunan matarsa wallahi bana son ji, ji nake kamar na fasa aurensa.” Sa’ada ta d’an bubbuga bayanta alamar rarrashi, tana hango tarin matsaltsalun da za’a fuskanta a zaman Hamda da Nanna, murya a sauk’ak’e ta ce “Ki sake dagewa da addu’a, sannan kuma ki jajirce wajen kula da shi, ta yarda zaki kwance masa duk wata hadda tasa ya zama baya tunani da hangen kowace mace sai ke. Amma kina wannan abin kalar na k’auyanci ai Nanna tsaf zata samu riba a wajenki wallahi ta k’waceshi don duk son da miji yake maka matuk’ar baka amsa buk’atarsa a lokacin da ya zo miki wallahi fita ransa kike.” Hamda ta share hawayenta, “Farkon aurenmu ba haka nake masa ba, shi kansa ya sani yanzu ma ba wai maganar su Didi ba ce ta saka ba guje shi, haushi ya bani duk sanda muka had’u sai ya min maganar matarsa ni kuma bana so. Kuma ki gaya masa na fi son zama gidan Abuja kusa da shi, don wallahi ba zan yarda ya bar ni a kano ba, ya d’au matarsa su tafi Abuja ban yarda da wannan tsarin ba.” Sa’ada dariya ta yi sosai har tana rik’e ciki ganin yarda Hamdan take masifa ta ce “Ke da mijinki me yasa ba zaki gaya masa ba?” Hamda ta datse leb’enta ta ce “Ba zan sake masa magana bane, har sai na tare ba dai saura 5weeks ba.” Sa’ada cikin takaici take kallonta “Au nufinki har 5weeks za ku yi a haka yana jin haushinki? Cab a haka zaki mallakeshi? Ga waya nan yanzu ki d’auka ki kirashi ki bashi hak’uri, idan kuma ya k’i kice ya zo nan ni sai in fita falo na muku gadi.” Ta zunb’uro baki tana kallon wayar kamar zata kira sai kuma ta ajiye tana kallon hoton da Sa’ada ta saka mata a screen d’in wayar, Hammad ne yana sakin murmushi jikinsa sanye da jar rigar polo da facing cap a kansa, ta d’auke kanta murya a cunkushe ta ce “Rabu da shi ba.” Sa’ada ta wafci wayar ta danna sunan da ta mata saving na Hammad wato ‘k’albeey na’. Kusan bugu nawa kafin ya d’auka don ya san numberr Hamdan tunda tsohon layinta ta saka a wayar idanunsa a lumshe ya saka wayar a kunnensa ko a lokacin tunaninta ne ya cika masa zuciya, Sa’ada ta saka mata wayar a kunne ta mik’e ta fice daga d’akin “Ki yi magana ko na kashe, ana so ana kaiwa kasuwa.” Cikin takaicin furucinsa ta ce “Ni ba ni na kiraka ba Sa’ada ce.” Daga can ya saki wani zazzafan murmushi da taji sautinsa ya sake maye duk wani feeling da take ji, tsigar jikinta sai ta shi take “Ba ke kika kira ba Sa’ada ce to me yasa na ji muryar ki?” Wannan karan sai da ta runtse ido jin da salon da ya mata maganar, cikin wata irin Husky Voice, “A haka za muyi rayuwar auren kina gudu na? Saboda wata al’ada can, shi yasa yanzu na fasa kaiki Abujar ki zauna a Kano na tafi da mai kula da ni….” D’if ta kashe wayar tana sakin wani hucin b’acin rai Hammad kuwa murmushi ya yi ya tabbata ya sake tunzira zuciyarta ya rasa irin wannan kishi na Hamda ki auri mace da mijinta amma ya ga alama ta doke Nanna da kishi. Ya sake kiranta tsawon lokaci kafin ta d’aga “Ki kawo min abinci, wallahi yunwa nake ji babu abinda na ci, ko kin fi so na d’au azimin haka ga yunwa ga mutuwar sha’awarki da take neman kassarani please ki zo kin ji y’ar Aljanna ta, ba abinda zan miki.” “Ka tabbata?” ya d’aga kai daga can yana murmushi “Am sure ko kallonki ba zan yi ba.” “To na taho da Sa’ada?” “Kada ma ki fara idan ba so ki ke itama Sa’adan na fara son ta ba.” Da sauri ta ware ido ta ce “Sa’adan?” Ya d’aga kai “Yes, Sa’adan itama ba mace bace, idan ina yawan ganinta ai zan iya fara son ta.” Kashe wayar ta yi da sauri kafin ta mik’e dama ta yi wankanta tas kayan barci ne ma a jikinta sai ta zunbula hijabi had’e da ambula turare a jikinta had’in Humran da Ammi ta kawo mata ta cilla wani chewingum mai mugun k’amshi a bakinta.
Sa’ada na zaune a falo ta ga ta zo ta shige kitchen murmushi kawai ta saki, tana ji ta yi warming d’in abinci da peppe soup, sannan ta fito da kwandon abincin, Sa’ada ta bi bayanta tana murmushi tana shirin rufe k’ofar a hankali ta rad’a mata “Asuba ta gari Hamda yau za’a sha amarci kut balle kin sha uban gyara kece d’azu har da hanani kazar da Umma ta dafa miki, ai yau zaki gane kin ci kaza, ga zuma kika dinga lasa kina lumshe ido, zaki lumshe ido mai dalili ai yanzu.” Gabanta na fad’uwa ta dubi Sa’ada kafin ta ce “Kada ma ki fara rufe k’ofa yanzu zan dawo.” Cike da shak’iyanci Sa’ada ta ce “Ni kuwa na san haka.” Sai da ta wuce a hankali ta ce “Tunda Hammad d’in tsoranki yake ba.”
Cike da confidence ta tura k’ofar, ba kowa a falon sai k’arar T.v da yake kallon tashar saudiyya, ta ajiye abincin had’e da zama a falon tana tunanin ta inda zata fara nemansa, ga shi ta bar wayarta a gida, falon babu wadatar haske sosai, tsawon mintuna tana zaune kafin ta ji ya turo k’ofar d’akin ya fito sanye yake cikin Riga fara tas armless sai gajeran wando da ko gwiwa bai rufe masa ba. Ta saba ganinsa a haka amma yau kam da ta gan shi sai da gabanta ya buga. Yana murmushi ya zauna daf da ita kan kujera yana k’ok’arin shiga jikinta,