Showing 69001 words to 72000 words out of 117648 words

Chapter 24 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

ta su ba yawa ba ce da ita.” Ban yarda da shi ba gani nake son kansa ne kawai idan ya ga na yi fushi da shi sai ya tattara dukkan nutsuwarsa a kaina ya shiga k’okarin lallai sai ya fahimtar da ni su yara mata da kike gani da zarar ka aurar da su, sun bar k’ark’ashinka kenan sun koma k’ark’ashin kulawar mijinsa ta ya zan bawa Najwa damar kula da dukiyata idan ta saba da kud’i kuma ta k’i aure fa. San da suka gama secondary school ba yarda ban yi ba ya tura Najwa K’asar England karatu amma ya k’i bud’ar bakinsa sai ce min yayi dama Namji ce amma ba Zan tura mace wata k’asa karatu ba. Wannan kalami nasa yasa na yarda na amince ita mace bata da wani value a idon iyayenta maza. Ba su d’auketa komai ba. Hakan yasa na k’udirce a raina ko ta wace hanya sai nima na haifi namiji.


Kady ta fad’o min a rai don haka na shirya tsaf na ce Umar zan je gidan Kady. Yana kallona ransa a b’ace ya ce “Har ga Allah Sakna bana son huld’ar ki da Kady don dai ba yarda zan yi dake ne, ke ban isa na hanaki ba dama Sadiya ce na san ina ce mata ta daina kaza zata daina.”
Murya a cunkushe ina jan tsaki na ce “Sadiya ka ce ita taga zata iya rayuwar gidadanci, ni rayuwa mai y’anci zan yi irin yarda na ga yarda ake yi a gidanmu, bata yarda zan zamewa miji kamar baiwa.” Girgiza kai kawai ya yi duk da alamunsa sun nuna ya ji haushi amma ya shanye b’acin ransa, sau tari hakan ce take kasancewa bai isa ya ce min ga abinda yake so ba na bi, kullum ra’ayi na nake bi fiye da nasa. Na fice ina jinsa Yana cewa “Allah ya shirya min ke Sakna, son ki ne ya yi min yawa shi yasa nake kasa d’aukan mataki a kanki.” Ni kad’ai na saki murmushi ni da kaina na San da damar son da yake min nake zabga masa rashin kirki shi kuma yake kasa hukunta ni ba irin Sadiya ba da take karb’ar hukuncinsa a koda yaushe.






Kady da murmushi ta tarbeni tana fad’in “Mhmd Mhmnn manyan mata ka ga ta Umar ba da kanki a sare. Mai tsoron cin amanar Umar.” Murmushi na saki kawai ina zama na ce “Biko na zo kwana biyu na ga ba na ganinki.” Kady ta girgiza kai “Ina kuwa za ki ganni a gidanki in je mijinki yana min wani gani-gani shi yasa na janye jikina da ke.” Na gyara zama ina tab’e baki “Ni ba wannan ya kawoni ba, zuwa na yi akan zancenmu na kwanaki.” Dariyar shak’iyanci ta yi sosai kafin tace "Kin ga uwar bari kenan wa ya gaya miki Borno gabas take ina jinki ya ake ciki?" fuska a had'e na ce "Ba fa waccan maganar ta kawo ni ba,
sam ba zan iya wannan kwamacalar ba, Buzu mai gadin mu na hango a yanzu shine nake ganin kamar zai cika min burina.” Tsawon lokaci tana min wani irin bahagon kallo kafin ta ja ajiyar numfashi ta ce “Allah ya kyauta, amma wannan tunanin naki kamar ya gurb’ata ta ya zaki iya had’a jiki da mai gadi?” Na runtse ido jina jijjiaga kaina “Dole na kawar da maganr duk wata k’azanta kady, in dai burina zai cika. Haihuwar d’a namiji shine cika makin farin cikin rayuwata.” Baki sake take kallona kafin tace “Mhmn, to yanzu ta ina ki ke tunanin za’a fara?”
Na gyara zama kafin na ce “Sai na gyarashi tukun, ya zama mai tsafta na kuma jik’ashi da Naira kafin na bijiromasa da buk’atata, amma fa ta hanyar aure ba zina ba….. sak’ek’e take kallona kafin ta ce “Aure kuma? Kamar yaya?” Na saki murmushi kafin na ce auren dai da kika sani mai suna aure.” Tsaki ta ja ta ce “Shi kuma auren Umar d’in ki kaishi ina?”




Jikar Nashe


❤️❤️❤️❤️❤️🙏
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Na raunana ganina a kansa sosai, bisa son tilas na nuna masa ni d’in ma a cikin matsananciyar kewarsa nake “Ka yi hak’uri Umar, kamar yau ne zaka ga na haife cikin nan mun komawa auren mu cikin yardar ubangiji.” Ya girgiza kai cike da sakin wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya ce “Shikkenan, Allah ya raba lafiya, yasa wannan karan ki haifi namiji tunda na san shine burin zuciyarki.” Na amsa da ameen cike da farin cikin jin addu’ar da nake so daga bakunan mutane masu albarka.


Daga lokacin na shiga rainon cikina, duk da kullum Umar a lissafe yake da watannin cikin, ganin yana son ya titseyeni akan ya kamata cikin ya isa watanni bakwai amma ya ga baya girma.” Hankalina tashe na samu Kady da zancen ita ta ba ni shawarar mu samu wani likitan mu siyeshi ya gillara masa k’aryar cewa akwai matsalar da tasa dole watannin cikin suke komawa baya, don haka zai iya k’ara watanni uku ko fi akan lokacin haihuwarsa. Likitan ya tsara shi sosai ta yarda ba ta inda zai yi ya musa tunda ba aikinsa ba ne. Kady duk da haka ba ta amince ba, sai da tasa muka dangana gidan Malamai ta sa aka rufe bakin Umar akan zancen cikin, sannan aka rufe bakin Hammad ta yarda duk sanda ya tashi tona asiri zai ji ya kasa. Na amince da shawararta da tunanin duk duniya ba ni da aminiyar da ta zarce Kady, a dai wannan lokacin.




Tun cikin yana wata uku na je scanning, sai dai likita ya tabbatar min bai zama lallai a wannan lokacin a ga abinda Zan haifa ba, ma’ana jinsin mace ko namiji, na bari ya shiga wata na biyar tukun.




Munafukin likita shi ya dinga shirga min k’aryar namiji zan haifa tun bayan da yaga zuciyata ta d’anfaru da son haihuwar namijin. Na dinga shirye-shirye na sakankance da hakan a zuciyata. Har mafarki nake da suffar jariri namiji mai kyau da zan haifa.


Abin haushi, mamaki da takaici, ranar haihuwa da na tashi sai na haifi mace, duk da Didi ta b’oye min a sanda aka yi haihuwar. Sai cikin dare lokacin na farka daga barci ta isheni da kuka na yi tunanin pampers ne ya dameshi, ina zare masa na ga mace ce, Allah ne shaida ta k’iris ya rage ban yi cilli da ita ba. Zuciyata ta tunzira ban san sanda na saki wani irin kuka ba. Hankalina tashe na tafi da ita wajen Didi don bana jin zan shayar da ita.




Daga wannan ranar na tsani mai gadi na ji babu amfanin zamansa a gidan tunda ya kasa ba ni farin cikin raina, tabbas idan ina ganinshi wata rana zuciyata zata iya fashewa musamman idan ina tuno yarda muka had’a jiki da shi. Sai na ji na tsani kaina. A kashegarin ranar da na haihu ne na samu Umar da zancen mai zai hana a sirrance mu yi auren da Buzu sai ya sake ni a take a wajen ko kashegari idan ya so sai a sallameshi ya koma garinsu da alheri mai tarin yawa.


Abbu kuwa babu ja ya amince da buk’atata, dama yana tunananin wanda zai aura min a sirrance kuma ya amince ya sakeni ba tare da duniya ta ji ba.




Suka keb’e da Buzu ya sanar da shi k’udirinsa, Buzu ba wani jainja ya amince suka wuce masallachi na can wani gari aka sake mayar da auren mu da buzu, duk da dama da aurensa a kaina. Kashegari kuma ya dank’ara min saki Umar ya sallameshi ya tafi ba mu sake ganinsa ba, kuma ba mu san inda za’a same shi ba, abu d’aya na sani ya ce min shi mutumin Ethiopia ne wato k’asar Habasha. Ina rok’onku don girman zatin Allah ga duk wanda ya ji haushi ya yafe min sharrin zuciya ne da na shaid’an.”
Ta na gama bada labarin ta saka wani irin kuka. Duk jikin mutanen wajen saki ya yi, tsananin mamakin cukurkud’dden lamarin ya sa suka gaza cewa komai illa sakin ajiyar zuciya. Hamda kuwa kuka take sosai kamar ranta zai fice, duk da ta ji dad’i da ya kasance ita d’in halastacciya y’a ce ba shegiya ba kamar yarda take tunani. Amma tunaninta ya fi karkata akan ta yaya zata ga mahaifinta, mutumin da a labarin da Ummanta take bata bata ji ta anbaci sunansa ba, sai kiransa da Buzu da ta ji ana yi, buzaye nawa ne a Habasha in dai haka ne? Didi da ranta ya gama dugunzuma da ta’ajibin labarin Sakna ta dinga dubanta tana jijjiga kai, ta kasa furta furucin bakinta, lamarin ba k’aramin girgizata ya yi ba, wacce irin soyayya ce ta rufewa Umar d’inta ido har haka? Da ya kasa bayyana mata ya tab’a sakin Sakna tsahon wannan lokacin. Ji take tamkar ta shak’o shi ta yi ta jibga, ta fi jin haushinsa fiye da Sakina da dama bata amince da tsarin tarbiyyarta ba, idan ban da haka ta ya za’a yi ace, kai zaka zab’a ma kanka abinda ka ke so ka haifa sai kace a lokacin jaliyya. Hammad ma ya shiga jerin mutanen da Didi take jin haushi sosai ta yaya zai b’oye wannan babban abu haka? Duk da dai da yarinta a lokacin amma me yasa da ya girma bai fito ya bayyana musu gaskiyar lamari ba, ai akwai hanyoyin da za’a gane tabbas Hamda ba y’arsa ba ce, ya ja bakinsa ya tsuke ya barsu suna bulayi cikin duhu.


Fuskar Didi a had’e sosai ta zubawa Nanna da take ta kuka a wajen ido, duk da ta bi ta cika wajen da kwakwazon kukanta, cikin takaici Didi ta ce “Ke da halla yi mana shilu, mu ji da abinda ya damemu ke me ye ma na ki a ciki da za ki zauna ki b’are mana baki kina kuka? Wad’anda kuka ya kama ai bayan mu ne, da aka mayal y’an itka ba a damu da mu san komai a cikin gidan ba, kai Umalu ai te ka ja Takina ku yi gaba, a je a cigaba da Toyayya tunda Takina ta fiye maka ni Uwalka da na kawo ka duniya. Allah na gode maka da ka nuna min wannan lana tun kafin mutuwata. Ga dai Takina ga kuma tsiyal da ta shuka maka k’alshen Toyayya kenan, wanda na tabbata ba na haufi hak’kin Tadiya ne tun yanzu ubangiji ya fara mata takayya. Kai kuma Hammad ba abinda zan ce maka te Allah ubangiji ya yi maka abinda ka yi mana da ni da Uwalka, ka b’oye mana abinda ya kamata ace tun tuni mun tani ka bar mu muna ta yawon bin malamai muna a yi maka addu’a ashe kai lamalin da yake filgita ka kenan? Kai ka jiyo ka je kai da halinka.”


Ta juya ta kalli Ammi da take ta kuka kamar ranta da zai fita, musamman ganin har a lokacin Umar bai ce komaiba, tun da ya d’ago kai ya kalleta da jajayen idanunsa sau d’aya, ba bu kuma abinda ta gani a cikin kallon sai tsantsar tsana da bata tab’a gani a cikin idanunsa ba, tsawon zamansu a matsayin ma’aurata.


Didi ta yi tsaki “Kuka ma ai yanzu ki ka fala shi Takina? Kin cuci yarinyar nan yanzu ina za’a gano wani Buzu mai gadi mutumin da ko cikakken tunanta ba wanda ya tani a gidannan da Buzu kawai ake kiranta, Garin Habasha da fad’i ta ina za’a fara lalubar wani gidan Uban maza ko ba Abu rijalun ki ka ce sunan mahaifin buzun ba? A Habasha wani gari? Wace jiha? Wace unguwa? Duk ba ki tani ba, kin cuci yalinyal nan, ki ka dinga gallazawa yalinyal nan akan laifin da ba nata ba, wallahi Allah te ya kama ki da laifinta, ko da ki ke uwa a wajenta ai ba ‘a ce ki cuceta ba.Umal ka yi shilu ka balni ina ta magana ni kad’ai ban ji ka yanke hukunci ba?” Bai d’ago d’in ba, don ba ya jin zai iya musamman yarda k’irjinsa ya yi nauyi ga wani bugu da zuciyarsa ta keyi, idanunsa dishi-dishi suke gani, yana daga zaunen amma jiri yake ji. Sai gani suka yi ya zame ya kwanta idanunsa sun kakkafe gaba d’aya. Salati mutanen wajen suka saka musamman Gadanga, a rud’e shi da Hammad suka sungumeshi suka fita da shi. Zuwa lokacin Hamda ma ta saka wata iriyar k’ara sabida wani irin ciwon mara da ya turnuk’o mata, take a wajen jini ya b’alle mata. A rud’e Asma’u ta yi kanta tana kiran sunanta, amma ina tsananin azaba ya sa ta kasa motsi sai nuni da ta yi mata da jinin da yake zubo mata da sauri ta k’ark’ashinta. Umma Asma’u ta saka salati tana kallon Mahmah Sadiya ta ce “Taimaka min mana Sadiya ina ji fa b’ari ta yi.” Sadiya fuska a cunkushe don dole ta kamata haka kawai ta tsinci kanta da rashin farin ciki da auren Hammad da Hamda. Suna fita Hammad yana k’ok’arin jan motar da zai kai Abbu asibiti shi da Gadanga, ya ga sun fito da ita da sauri ya tsaya yana tambayar lafiya?” Umma Asma ta ce “Je ka kawai, zamu taho da ita bleeding take ina jin ta samu miscarriage” Hammad ya runtse idonsa ya ja motar cikin rashin kuzari. Asma’u kuma ta shiga motar tana kallon Sadiya da take shirin juyawa ta shiga gida ta ce “Mahmah ya haka ne? Taimaka ki shigo mu kaita mana.” Ta zubawa Asma’u ido kafin ta ce “Ko Abbun ban bi asibiti ba balle ita, ki kira uwarta ta kaita.” Daga haka ta shige sashenta. Ta bar Asma’u sake da baki tana kallonta.


A sashenta ta samu Nanna tana ta wani irin kuka da take da tabbacin kukan takaicin Hammad ne yake nuk’urk’usar ta. Ta ja tsaki a fili ta ce “Nanna ki saurara min kada ki sake b’ata min rai, idan za ki kwantar da hankalinki ki kwantar, Hammad dai ni na haifeshi nake kuma iko da shi, don haka in dai Nono na ya sha ina tabbatar miki sai ya saki yarinyar nan, ba ta yarda za’a yi na bari ya zauna da y’ar Sakna bayan d’aukan tsawon lokaci da suka yi suna cutata ita da Umar, lokaci ya zo nima da zan rama Wallahi Hammad sai ya saki yarinyar nan, in dai kin ga sun cigaba da aure to tabbata bana duniyar nan…”


Nanna ta saki wata ajiyar zuciya kafin ta kumshe idonta, hawayen sauk’in zuciya yana ziraro mata, ta hango gaskiyar Mahmah ta cikin idaniyarta, alamar zancen da take har k’asan ranta. Ta saki murmushi na tarin farin ciki, ta yi alk’awarin Hammad na ta ne ita kad’ai har abada!




Jikar Nashe ce.✍🏽✍🏽




❤️❤️❤️❤️❤️🙏
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Da sauri Hammad ya fice jikinsa na rawa. Na mik’e ni ma da sauri ina nunawa buzu hanya. Cikin rawar jiki ya ce “Hajiya kada ya illatani.” Cikin masifa na ce masa “Ka wuce ka tafi, ba ni abinda zai maka zan yi maganinsa.” Ya fice da sauri jikinsa na rawa a matuk’ar tsorace yake.


Na kasa samun nutsuwa bayan na yi wanka na kira Kady da sauri cikin matuk’ar damuwa ba ce mata an yanka ta tashi, Hammad dai babban d’an gidannan ya kama mu dumu-dumu da Buzu.” Cikin k’arami Kady ta ce “Innalillahi, ya aka yi wannan katob’ara don Allah?” Na runtse idona kafin na ce “Tsautsayi, ni dai ki gaya min mafita.” Ta ja ajiyar numfashi kafin ta ce “Shikkenan, akwai mafita amma dole sai mun saka Hammad ya shiga d’akin ki. Mun d’ana masa tarko mai zafi tukun na inda tilas ma ya ja bakinsa ya tsuke, idan ba haka ba tabbas kina ruwa.” Na amince da shawararta, kuma na karb’eta d’ari bisa d’ari tunda ba ni da wata mafita da ta zarce wannan.


A ranar muka d’ana masa wannan tarkon, na isa d’akinsa da yake Boys Quaters, yana zaune hannayensa dafe da k’uncinsa, na kira sunansa ya k’i ya d’ago ya kalleni illa had’e fuska da ya yi, kansa a k’asa. “Ka taso mu je akwai bayanin da zan maka.” Funfurunfus yaron nan ya min banza. Ko kallona bai yi ba.


Jikina a sanyaye na bar b’angaren nasa, ina mamakin kafiya da taurin kai irin nasa, duk da lallashinsa da na yi. Ina zuwa na cewa Kady “To ya k’i zuwa, don ba kiga ba ko kallona bai yi ba, balle ya san ina wajen, kady ina tsoron kada yaron nan ya tona min asiri.” Ranta a b’ace ta ce “Tunda mun biyo masa ta sauk’i ya k’i, dole mu bi da shi ta zafi, kin ganni nan dama na shirya masa idan har ya yi kafiya, kuma kin tabbatar min ba kowa a gidannan bari na kira yaran da za su kawo shi nan ko bai shirya ba.” Ta d’auko wayarta tana kiran yaran da ta sabawa sawa su yi mata aiki. “Ku zo yanzun nan, aikin nan na ga dole sai da ku.” Ta katse wayar tana cewa “Ba su mintuna goma, za su kawo shi nan ta k’arfin tuwo, zai gane kafiyarsa ba ta da amfani.”


Muna zaune kuwa suka yi mata waya sun zo, da kaina na je na bud’e musu gate d’in, suka shigo kasancewar Buzu yana d’aki cikin tashin hankali, ya yi k’ok’arin ya tafi kuma na hanashi, na tabbatar masa ba abinda zai faru.


Su biyu ne, k’arfafa da su. Na kai su har d’akin Hammad. Duk da gani na da ya yi da su bai saka zuciyarsa ta rusuna ba, sai ma wani irin hucin b’acin rai da yake yi, yana jifana da kallon tsana. Da naga ba zai tafi ta dad’i ba da kaina na ce su d’aukeshi ko a kaine su kai shi d’aki na.


Haka kuwa aka yi, aka shimfid’e shi a gadona, su da kansu suka cire masa kaya, aka kuma d’aukeshi a haka yarda ya ke akan gado bayan sun shak’a masa abinda ya saka shi suman dole.


Bayan farfad’owarsa muka saka shi a gaba ni da Kady, anan nake sanar masa Ba zina nake ba da aurena da maigadi. Na ba shi labari tas tare da nuna masa vedion d’auren auren a camera Kady. Fuskata a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login