Showing 117001 words to 117648 words out of 117648 words

Chapter 40 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

jegon Ammi kuwa bata zo ba, ta yi kara da alkunya. Hakan yasa lokacin da wata aminiyar Ammin ta zo bayan ta gaida Didi ta ce “Saknan bata zo ba ne Hajiya Didi?” Didi an tab’o mata inda take so ta gyara zama tana mele baki idanunta akan Sadiya ta ce “Ina za ki ga Sakna anan, ita da ba ‘digon jinin fulani ma a jikinta ta yi kara da alkuny duk da Hamdan ba ‘d’iyar fari bace, wasu fulanin dai ai suna jawa fulani tsiya wallahi Allah dai ya yiwa Sakna Albarka, kuma ina nan in ga wanda zai canjawa yarinyar nan suna daga nawa da na ra’da mata, mutane ba Allah a ransu y’ar kujerar makka dai ake wa to kuwa bana ko Kamalu ya bayar da kujerar sai na hana, naga dai mutum da ba son auren ya ke ba.” Mahmah murmushi kawai take tana mamakin Didi haka kawai sai a tafi a barta daga ita sai Hamda Lauratu na wajen aiki sai yamma take zuwa ta tafi da safe ita kuma sai ta fansheta tunda Saknan ba wasu y’an uwa ba ne da ita anan. Ita kuwa Umma Asma sun koma k’asar su can inda suke dama hutu suka zo. Turo k’ofar da Hammad ya yi ne yasa Didi yin shiru don lallab’ashi take kada ya ce ya canja takwarar da ya mata saboda ta san yarda baya son ko ka’dan a tab’a Sadiya. Idanunsa a cikin na Hamda da take bawa Babyn Nono hannunsa rik’e da na Kamla da Khairi, ya zauna a gefen gadon yana gaishesu ‘d’aya bayan ‘d’aya kafin ya juyo kan Didi ai kuwa tana washe baki ta ce “Yauwa Hammadu ya kamata ka gayawa duniya sunan yarinyar nan.” Hammad yana k’unshe dariya ya ce sunanta UMMA Asma mana. Wata zabura da Didi ta yi sai da kwanukan wajen suka tarwatse bata damu ba ta ce “Ai wallahi ka yi a banza ni zaka yaudara to ko Usmanu Uban Umaru bai isa ba balle kai ‘dan Umaru yarinya tilas sunana zata amsa ba fashi.” “Tabbas kuwa Hajiya Didi” KK da yake shigowa ya sake tabbatr mata yana dariya don duk yana jin drammerr da ake yi ya ce “Hammad na fa lura ka raina min uwa zan maganinka yarinya dai tabbas sunanta Hadizatul Kubra Didi ba, kuma ba wata inkiya da zamu mata Didi za mu dinga kiranta da shi don kada sunan ya b’ata.” Didi ta ranga’da gu’da ta ce “Madalla da alherin ka gareni Kamalu D’an Kabiru jikin Mu’dallabi yaron albarka.”




Bayan fitar kowa daga ‘dakin ya rage daga Hammad sai Hamdan ya k’arasa wajen ta ya zauna sosai a jikinta yana lek’en fuskar yarinya a kunne ya ra’dawa Hamda ba sunan Didin ne ake gudun sawa ba Allah yasa kada ta yiyo rigimar Didi da masifarta.” Hamda ta shafa gefen kumatunsa tana murmushi kafin ta ce “In sha Allah komanta Halin Didi ba zata ‘dauka jajirtacciyar mace mai son zumunci ibada ga kyauta Allah Ameen.” Ya ja karan hancinta kafin ya ce “Jallah ya miki albarka ina jiran twins next year maza su ci sunan Kamalu da Umarun Didi, Allah yasa Didin tana da rai a lokacin.” Ya fad’a zuciyarsa cike da alhinin ranar da za’a ce masa Didi ta mutu suna son Didi sosai sai dai sun san tabbas Didi ta zo gangara duk da ance ba a san Gawar fari ba. Fatanmu dai Allah yasa mu cika da imani ya ji k’an magabatanmu.




Tammat.




(Darasin cikin littafin: kowane ‘da Allah ya baka namiji ko mace ka gode masa. Sannan a dinga kyautatawa mutum zato ba kowacce mace don ka ga tana zaune da mijinta lafiya kace asiri ta yi ta mallakeshi ba, akwai hanyoyin mallakar miji ba boka ba malam. Ku yi amfani da alherin cikin littafin ku yi watsi da sharrin da yake ciki. Y’ar mutan makwarari ke cewa Shukran lakum. Allah ya sada mu da alherinsa.❤️❤️❤️❤️😭🙏)

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login