Showing 45001 words to 48000 words out of 117648 words
Chapter 16 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt
ya yi wujiga-wujiga da shi. Ta saki d’an murmushi idanunta cikin na sa. Ya d’auke kai duk da matuk’ar kyau da ta yi masa. Ji ya yi tamkar ya rungumota gaba d’aya. “Ya Hammad sannu da aiki, ai da ka sani ka kira ni na dafa, ka ga ka wahalar da kan ka.” Bai kula ta ba ya cigaba da juye abincin a plate yana d’ora forks biyu a kai. Sai da ya d’ora a tray sannan ya dubeta “Ki ciro kaza a oven ki had’o da fruits d’in can.” D’aga masa kai kawai ta yi. Ya fice ya dire abincin sannan ya shige bedroom d’insa. Wanka ya yi ya fito daga shi sai riga armless da three quarter wando rigar ja ce wandon fari tas sai ya yi kyau sosai.
Tana zaune k’amshin turarensa ya sanar da ita zuwansa. Ta lumshe ido tana jin tamkar ta tashi ta rungumeshi. Turaren nan ya dad’e yana yi mata gizo a hanci da sanya ta fad’uwar gaba ashe dai zata mallaki mai turaren. Daf da ita ya zauna har suna gogar juna amma ya k’i matsawa don ya fi so su saba ta saki jiki da shi ba ya son ta dinga nesa da shi. “Ka yi hak’uri idan maganar da na fad’a d’azu Ta b’ata maka rai” Ya d’ago yana sauke idanunsa a kanta “Kin damu da b’acin raina ne?” Samun kanta tayi da d’aga kai tana sunkuyar da kai “To idan ba kya son b’acin raina daga yau kada ki sake min irin waccan maganar ko tambayata wacece ke? Idan lokaci ya yi zaki sani abu d’aya na sani aure na dake ba haramun ba ne halak ne kuma a gaban shaidu aka d’aura da hotuna da vedio da komai.”
K’asa ta yi da kanta tana wasa da yatsun hannunta. Zuciyarta ta samu nutsuwa ta tabbata iya gaskiyar sa ya fad’a mata. Hannunta ya kamo cikin wani salo ya ce “Yanzu kin amince za ki amshe ni a matsayin miji?” Ya fad’a yana shafa wuyanta da bata san da ta runtse ido cikin wani irin rawar jiki ta d’aga masa kai. Ya saki murmushi idanunsa akan abubuwan da suke tsone masa ido “Ki shirya tarbata da safe.” Da sauri ta rufe idanunta, saboda tsananin kunya da maganr ta bata “Ki yi hak’uri yau ba anan zan kwana ba, duk da ban so haka ba, amma ba yanzu nake son Nanna ta san na aureki ba, sai nan gaba a gaban kowa don haka wuni zan dinga yi anan na kwana a can.” Ji ta yi ranta ya d’an sosu amma da yake ta san mijin wata ta aura tilas ta runtse idanunta daga hakan. Sosai ya rungumeta a jikinsa Allah ya sani a dole zai koma wajen Nanna ji yake dama su dawwama da Hamda a haka sai dai ba yarda zai yi. Nanna ta cancanci y darajata ko bakomai ai uwar yaransa ce. Ya mik’e yana jan ta tsaye. Manna mata kiss ya yi a goshi “Kada ki ji tsoro ba abinda zai sameki kin ji my wife.” Ta lumshe ido tana jin wasu hawaye na shirin zubo mata da gaske ta amince Hammad shine mahad’in gangar jikinta.
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Har bakin k’ofa ya ja hannunta ta raka shi sannan ya nuna mata yarda zata kulle k’ofar kasancewar ta mai password ce. Yana murmushi ya fice daga gidan da d’an sauri nishad’i fal zuciyarsa Na mallakar matar da yake buri.
Ko da ya isa gidansa ya dad’e tsaye a k’ofar gida cikin mota yana tunanin yarda za su kwashe da Nanna dama danginsa gaba d’aya idan aka gano ya aure Hamda. Tabbas ya san sai Nanna ta kusa zaucewa kasancewarta a bigiren mata masu d’an banzan kishi. Ya lumshe idanunsa yana sakin murmushin hango tak’addamar da za’a buga, hakan kuma shine hanya d’aya da Ammi zata fito ta fad’i sirrin da take k’udundunewa.
Ya fice daga motar yana sakin ajiyar zuciya. A falo ya ga Nanna zaune ta ci kwalliya kamar bata so da gaske ta yi kyau sosai ya d’an zuba mata ido ita kuma sai sakin murmushi take don yau dai kam hankalinta a kwance yake kamar tsumma a randa. Tana murmushin ta ce masa “Har ka dangana ta ga gidan mijin?” Ya d’aga kai yana jifanta da na sa salon murmushin da kai tsaye za’a kiransa na mugunta. Ta mik’e ta koma hannunsa had’e da zaunar da shi kusa da ita ba k’aramin missing d’insa ta yi ba d’an kwanakin da suka yi ba sa tare. Shiga jikinsa ta yi sosai kafin ta ce “Yanzu hankalinka ya kwanta ka aurar da y’ar so. Na san zan samu kulawa da duk ka banzatar da lamarina.” Ta fad’a tana wasa da sumar kansa. Ta nan ta ke karya lagonsa ya kuwa hau lumshe ido yana amsar sak’onta. Har cikin ransa tunanin Hamda yake ina ma itace zaune daf da shi haka tana wasa da sumar kan sa. Ganin ya amshi sak’onta kamar yarda take so ya sa ta sake ba da k’aimi kasancewar yara basa nan sun yi barci yasa ta samu sake ta dinga yi masa abubuwan da suka lula shi duniyar Hamda. Da sauri ya mik’e suka shige bedroom.
________________
Hamda kuwa tana jin tashin motarsa ta rufe k’ofar tana sakin wata irin ajiyar zuciya had’e da zubowar wasu siraran hawaye da zata iya kiransu kai tsaye na zafin kishi. Tana da tsananin kishi ita kanta ta sani shi Yasa sam bata so auren mai mata ba. Amma ba zata ja da hukuncin ubangiji ba za ta yi ta addu’ar Allah ya sauk’ak’a mata. Jikinta a sanyaye ta shiga ta gyara kitchen d’in da komai na cikinsa ya zama fari. Tsaf ya fito yana walwali tabbas Hammad ba k’ananan kud’ad’e ya kashe a gidan ba, gaba d’aya ya d’auke mata nauyin komai da ya kamata ace uba ne ya yi.
Parlourn ma komansa fari ne da adon black kad’an. Ta sake gyare parlourn sannan ta koma d’aki wanka ta yi ta tada sallolinta nafiloli kafin ta yi shirin barci ta kwanta. Sai dai me tana kwanciya tunanin Hammad ya fad’o mata yanzu haka yana can sun tsunduma wata duniyar shi da matarsa hakan ya sa ta runtse ido zuciyarta ta yi nauyi saboda b’acin rai. Addu’a kawai take akan Allan ya sauk’ak’a mata.
*******************
An ci nasara sosai Bakin Didi ya bud’e bayan yawan addu’oi daga bakin manyan malamai na karya sihiri sai dai harshen ya d’an karye kad’an maganar bata fita yarda ya kamata. Mijin Asma’u ya tabbatar musu komai zai daidaita insha Allah.
Da asuba kawai suka ji Didi tana kiran Atma’u wai Asm’au. Mama Asma’u ta yi saurin bud’e ido cikin farin ciki take duban Didi tana fad’in Alhamdulillah Didi na ke ce kika yi Magana.” Didi ta d’aga mata kai tana sakin murmushi ta ce “Ni te Atma’u Alhamdulillah Na ta mu lafiya.” Didi dai (s) d’inta ta d’auke gaba d’aya shi yasa take mayar da ita (t) Asm’au ta kama hannunta tana dariya Alhamdulillah Didi ta lumshe ido tana farin ciki itama da maganar da ta fara. Ashe ba k’aramar k’una wad’anda ba sa magana suke ji ba tabbas ta na tausaya musu a kuma yanzu take sake jajanta musu ubangiji ya sa hakan ya zama kaffara a garesu kuma sanadin shigarsu aljanna. A tsawon lokacinnan tana da abubuwan cewa da yawa sai dai ba halin magana rubutun kuma ba wai ta k’ware a hausan bane.
Ta mik’e sosai ta gyara zamanta “Atma’u kira min d’an Ki Hammad a waya, tun da abin nan ya faru nake cewa a kira min shi a waya tun k’i” Asma’u ta d’au waya ta shiga kiran layin Hammad a waya da layinsa na Birmingham.
Tsawon lokaci yana jin kiran idanunsa sauke akan wayar sai dai ganin daga family ake kiransa ya gagara d’aukar wayar musamman ganin Gwaggo Asma’u ce take kira daga layinta na Nigeria ya tabbatar ta je Nigeria kenan. Kimarta da take gani yasa ya kasa burus da kiran a karo na uku da ta sake kiran ya janye Nanna daga jikinsa had’e da kara wayar a kunnesa murya can k’asa ya ce “Hello Mama ina yini?” Asma’u ta saki ajiyar zuciya yau da aka ci sa’a ya d’aga wayar “Mun wuni lafiya? Yau ka ga damar d’aga wayar kenan? Yanzu Hammad yaushe ka zama yaro mara jin magana har haka? Ka
Saka k’afa ka yi tafiyar ka ka bar mahaifiyarka cikin damuwa ka kyauta mata kenan?” Tsit ya yi da wayar a kunnensa gabansa yana wani irin duka sai yanzu ya tuna irin b’acin ran da ya baro Mahmah a cikinsa “Ka kyauta ina tabbatar maka idan Sadiya ta rasa ran ta to bak’in cikin ka ne ya kasheta ga Didi zata yi maka magana.” Ta fad’a tana manna wayar a kunnen Didi “Hello Hammadu a duk inda ka ke ma kayi gaggawar dawowa gida ka warware k’ullin da bahaguwar matar uban ku ta k’ulla maka don na tabbatar akwai lauje cikin nad’i.” Murya a cunkushe ya ce “Insha Allah zan zo ko next month amma kin san fa Abbu ne ya kore ni ba tare da ya ji ta bakina ba.” “zancen banza zancen wofi, zancen Umaru har wani abin kamawa tallamamme da mace ta riga ta gama da shi. Ai ni na tabbatar da cewa Takina na haifawa Umaru Allah ya taimaki Utmanu kakanku ba ya raye balle bak’in cikin Ummaru ya kashe shi. Ka zo idan ka ta mu hutu don Tadiya ma uwarka a cikin matsananciyar damuwa take.” Ya ce “To Didi zan zo, amma ya naji maganarki kamar ta y’an koyo kin mayar da S T?” Ya fad’a yana tuntsirewa da dariya daga can Didi ta ce “Ai tuni na tan Umaru ya haifi d’an banza to Tadiya ka yiwa dariya ba ni ba.”
Shi dai katse wayar ya yi yana sakin murmushi tare da kallon Nanna da ta tsatstsareshi da ido saboda tana cikin morar jikinsa wayar ta dameshi da kira fuska a d’aure ta ja blanket ta d’an rufe jikinta don tana lura da kallon da yakewa k’irjinta ita kanta sau tari tana jin haushin yarda k’irjin ya zube ya lalace tilas ma ta nemi magani, don ta lura hakan na son jawo mata matsala da ai ba haka yake mata ba san da K’irjin yake a gyare tsam da shi. Murmushi ya d’an saki tare da d’an janyota jikinsa don ya lura matse take sosai kada ya shiga hak’k’inta.
Didi ta kalli Asma’u Ta ce “D’an banza ni dama na san sharrin Takina ne, ai kuwa watan jin kunyar Takina ya kama.” Asma’u dariya ta yi kawai zuciyarta na sauka daga b’acin rai da yake addabarta ko bakomai yanzu ta hak’kak’e Hammad ba shi ya yi cikin Hamda ba.
________________
Tun asuba da ta farka ta kasa komawa dama barcin da kyar ya d’auketa. Hakan yasa ta mik’e ta gyara gidan tsaf sannan ta fesa wanka aka kuma yi shigar wata doguwar riga mai d’an banzan kyau rigar ta bi ta kwanta a jikinta had’e da fitar da duk wata sura ta y’a mace da take jikinta. Mayafi ta samu ta d’an yane kanta da shi don ita kanta ta ji kunyar shigar tata. Sai zabga k’amshi take haushinta d’aya rashin irin humrorin Nanna balle turaren wuta sai air freshners da humidifier ta bi ta bad’e gidan da su.
Kafin 8:00 ta gama komai har chips ta soya da kwai sai black tea da gasasshen kifi. Tana zaune ta tasa abincin a gaba sam ta kasa ci kishi ne yake nuk’urk’usar zuciyarta. Ta jiyo dirin motarsa da sauri ta gyara zamanta.
Tsawon mintuna biyu ya shigo cikin parlourn fuskarsa fal murmushin farin cikin ganinta. Tana sunne kai ganin yarda ya tsaya yana bin sassan jikinta da kallo tace “Ya Hammad ina kwana?” Shiru bai amsa ba hakan yasa ta d’ago da niyyar sake gaisheshi tunaninta ko bai ji ba. Take kuwa idanunsu suka sarkafe cikin na juna yana jifanta da wani irin narkakken kallo. Ya mik’a mata hannu alamar ta zo jikinsa. Nok’e kai ta yi cikin matsananciyar kunya duk da tana buk’atar hakan. Hannu yasa ya mik’ar da ita tsaye ya manne jikinsu sosai tamkar zai mayar da ita ciki. A kunne ya rad’a mata “K’auyis kawai, ni bana son gaisuwar y’an k’auye haka Nanna take gaishe ni duk Safiya.” Ya fad’a yana manna mata sumbata a lab’ba. Saura k’iris ta fad’i saboda yarda jikinta yake shaking ga haushin maganar matarsa da ya soko mata. Ta yi kicin-kicin da fuska kamar ta fashe da kuka.Sam bai lura da ita ba balle ya san ta na yi. Shi kansa gani ya yi k’afafu nasa sun kasa d’aukansa shi yasa ya sunkuce ta zuwa bedroom Sai dai yana direta ta hau janye jiki tana kuka da had’a shi da Allah akan ya bari ba ta so. Ya runtse idonsa jin kukan nata ya yawaita kawai ya kyaleta yana ji shima kamar ya saka mata kuka. Da kyar ya shige toilet ya sakarwa kansa shower.
Ko da ya fito tuni ta fice daga d’akin tana mayar da numfashi ta tsorata da lamarin sosai don haka tayi masa haka idan ban da haka ita mai son ta faranta masa ce.
Ko da ya fito kallo d’aya ya yi mata ya zauna daga gefe yana zubawa tray d’in abincinta ido da alama ko Ci ba ta yi ba. Ya d’an ja tsaki a ransa ya ce haka auren k’ananan yara yake ban da haka lokacin Nanna da kanta ta dinga uzzira masa. “Abincin ma gudunsa ki ke?” Ta d’ago kai tana jin kunyar had’a ido da shi “Bar kallo na sai kace cinyeki na ce miki zan yi kika zauna kina zunduman ihu, daga yau ba zaki sake gani na ba sai kin nemo ni da k’afafunki dad’inta ina da inda zan sauke buk’atuna da ko ban shirya ba za’a biyoni cikin farin ciki da kwanciyar hankali.” Ji tayi zuciyarta na wani irin tururi ta mik’e da sauri ta shige d’aki tana sakin kuka. Hammad ya saki murmushi ya san kishi ne yake damunta. Ya mik’e ya bita. A tsakiyar gadon ya sameta tana kuka ya saki ajiyar zuciya ganin yarda yau murararn ya ga dirarru kuma lallausun cinyoyinta. Bai hau gadon ba gudun kada ya sake janyowa kansa “Ki tashi ki je ki rufe gidan zan fita.” Wani irin juyi ta yi da ya saka shi bin ta gadon bai shirya ba. Ina nan lamarin ya fi gaban wasa ganin idona na shirin makancewa da azama na juya na bar d’akin. Ina mamakin yarda Hammad ya murje idanunsa yake aikatawa k’aramar yarinya son ransa.
______________
Didi tsaf ta shirya cikin shaddarta samfurin getzner ta kashe d’aurinta na tsofaffi ta zauna zaman dirshan a falonta. Yanayin fuskarta kawai zaka kalla ka san yau a shirye take ta ci zarafin kowa a gidan. Ta gutsiri goronta kafin ta cilla shi a baki ta ce “Atama’u kira min uban kowa da uwar kowa na gidannan da wanda ma ba ta gidan nan. A zo a ganni na tamu lafiya d’an bak’in ciki te ya mutu burina na ga ranar tonon atirin Takina.”
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Haka Mustyn ya so ya ce a zahirance sai dai ya tuna warning d’in abokinsa akan fad’ar hakan don haka ya guntse furucinsa had’e da sakin murmushi kad’an ya ce “Afuwa uwargida ya d’an shiga busy ne a office shi yasa ba ki gan shi ba.” Nanna ta saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa kafin ta ce “Ko da na ji, ai shikkenan ku wuce mu je gida kuma tun d’azu fa nake kiran wayarsa ta k’i shiga.”
Musty ya d’an saki murmushin sa kafin ya ce “aikin da yake yi ne mai mahimmancin gaske ne shi yasa ba ki gan shi ba.” Ta d’an tab’e baki ta ce “Allah ya taimaka ka gaisa min da madam.” Ya d’aga kai yana fisgar motar sa da sauri zuciyarsa fal da tunanin yarda za’a kark’e da wannan aure na abokinsa da kai tsaye zai iya kiransa auren Drama. Ya saki murmushi yana jijjiga kai tabbas Hammad akwai k’wallan shege. Ko da ya kira wayarsa still a kashe take.
__________________
Sai magriba sannan ya fara shirin tafiya gida. Bayan wuni da yayi yana jigilar ta da jinyarta da gaske ya lura Hamda raki ne da ita na gasken gaske. Gaba d’aya ta bi ta narke masa. Yanzun ma tana zaune tana ganin yarda yake shiryawa ya d’au kayan da ya zo da su ya mayar jikinsa sannan ya zauna a gefenta yana mata kallon k’asan ido murmurshi fal fuskarsa. Gefen kumatun ta ya shafa kafin ya ce “Nuri ta zan tafi. Gobe ki shirya da wuri za muje shopping kin ga saura 4 days azimi. Duk dama ina tunanin kafin sallah zamu wuce gida don Gwaggo Asma ta matsa sai na koma.” Shiru ta yi masa tana cono bakinta alamar zuciyar a kusa take. Ya matso da ita jikinsa sosai yana k’ok’arin lalubo k’wayar idanunta da ta runtse cikin muryar shagwab’a ta ce “Ni tsoro nake ji.” Ya bud’e ido yana kallonta sosai cikin mamaki da ganin hawaye na malala a fuskarta. Ya sa hannu ya share mata hawayen saman fuskarta yana mamakin rigimarta “Yanzu me kike son ayi? su nan garin fa ba su da aljannu balle ki ce tsoro kike ji ba abinda zai sameki fa.” Turo baki tayi kawai ta mik’e ta shige d’aki zuciyarta a tunzire gani take bai damu da ita ba, idan banda haka ta ya zai tsallake ya bar ta a condition d’in da take, don kawai ba ya son b’acin ran matarsa.
Ya dad’e rik’e da kansa kafin ya mik’e yabi bayanta waya a kunne yana neman layin Nanna. A karo na farko Hamda zata saka shi yiwa matarsa k’arya. Kafin ya shiga bedroom d’in Nanna ta d’au wayar ranta a b’ace ta ce “Yanzu Dear ina ka shige tun fitar safe?” Ya saki ajiyar numfashi kafin ya ce “Nanna am sorry aiyuka ne suka rincab’emin sai da asuba Zan dawo please take care ki rufe gidan.” Kafin ta ce komai ya katse wayar ya kasheta gaba d’aya sannan ya shiga d’akin a zuciyarsa ya