Showing 111001 words to 114000 words out of 117648 words

Chapter 38 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

kwalli da ta saka sai man leb’e da ya sake bayyana silb’in lab’b’anta da tudunsu da suka dace da kewayayyiyar fuskarta.


A kitchen take a tsaye tana dama kwalba da nonon da take hannunta, tana yi tana bin wak’ar da take saurare a wayarta, hankalinta gaba d’aya ya tafi akan kwalbar da take sha Tana lumshe ido bata san da wanzuwarsa a wajen ba har sai da ta ji k’amshin turarensa ya kama hancinta rad’am tuni ta tattaro duk wani rashin Mutunci ta yi masa masauki a fuskarta…
[1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: Babu fara’a ko walwala sam take kallonsa lamarin da ya girgiza shi saboda bai tab’a karo da irin kallon da take binsa da shi ba a fuskarta, da gaske ya hango fushinta sosai da b’acin ranta a k’wayar idanunta, gwiwoyinsa gaba d’aya suka sare sai yanzu yake tunanin tabbas abinda ya yi d’in sam bai dace ba kuma dole ya fusata ta tun tafiyarsa tsawon sati biyu bai kirata ba ba Kuma sak’o ko wani abin ya sani shi kansa ya tafka babban kuskure kuma Hakan bai dace da duk wani namijin k’warai ba.
K’ok’arin saka k’wayar idanunsa yake yi Cikin idanunta sai sai dai hakan ya gagara dalilin ta k’i ba shi dama, k’arshe ma d’aukan cup d’in kwalbar ta tayi ta nufi k’ofa da sauri dalilin aman da ya taso mata, da ta tabbata na k’amshin turarensa ne da ya nemi wargaza mata ya kuma cukuikuya mata kayan ciki. Cike da k’warin gwiwa ya janyota ta fad’o jikinsa idanunsa akan k’irjinta da abubuwan k’irjin da suke tsole masa ido tun farkon shigowarsa da ya yi ka tari da su sun cika sun batse kamar suma fushin suke da shi. Ya d’ora kansa saitin k’irjinta yana jin yarda zuciyarta take harbawa da sauri, ba tare da wani tunani ba Hamda ta wanke shi da aman da ya cika mata ciki, da sauri ya d’ago yana kewaye idanunsa a kanta kafin ya kaiwa bakinta kiss ba tare da k’yamar komai da ya fito daga cikinta ba, ji yake tamkar ya mayar da ita cikinsa, don tsananin yarda zuciyarsa take bugun sonta. Murya a dashe cikin kunnenta ya ce “Welcome d’in kenan K’albeey.” K’asan rigarta ya zura hannunsa yana shafa shafaffuyar mararta “Baby na ya zo kenan?” Rintse idanunta ta yi duk da tana amsar sak’on na sa hakan bai hanata janye jikinta daga nasa ba tana kallon yarda ta masa kaca-kaca da amai ta ja jikinta zuwa sink d’in kitchen d’in sosai take jin jiri don yau ba ta d wadatacciyar lafiya, da kansa ya iso ya fara tsaftace mata bakinta yana fad’in “Sannu please no more fushi kin ji K’albeey.” Ta lumshe ido tana sauraran yarda yake bin sassan jikinta da sumbata kamar zai aikata komai a kitchen d’in jikinsa har rawa yake yana fallasa shi ta hanyar nuna masa yarda ya yi missing d’inta. Ta yi saurin janye jikinta kafin murya a shak’e ta ce “Kada ka sake tab’a ni, ka damu da ni ne? Wato sai ina gabanka sannan kake tuna ni a matsayin matarka idan kuwa kana tare da matarka sai ka manta ka ajiye wata mata Hamda, nima yanzu na san ciwon kaina ina tabbatar maka ba zan zauna bak’in cikin d’a namiji ya kashe ni ba, ka je ka san me yi wuwa.” Daga haka ta fice da sauri daga kitchen d’in sakamakon hawaye da yake shirin zubo mata. Jikinsa ne ya yi sanyi sosai shi kansa sai yanzu yake da na sanin abinda ya mata ga wutar sha’awarta da ta kunno masa ya dinga lumshe ido yana neman mafita kafin ya saki ajiyar zuciya ya fita parlourn Didin sai dai abin haushi Didi tana zaune ta kasa ta tsare ba damar ya samu ya shige ya rarrashi y’ar dangerr tasa. Cije leb’e kawai ya yi ya fice daga gidan, wayarta ya dinga kira amma tana ji ta yi burus da shi, lamarin sa ba k’aramin haushi yake bata ba ji take kamar zuciyatta ta tarwatse ta lumshe ido duk ita kanta tana jin wata irin muguwae sha’awarsa hakan ba zai saka ta sake amincewa da shi ba har sai ta tare kamar yarda Ammi ta gargad’e ta ta bari duk magungunan su gama kama jikinta tukunna. Ta yarda da zarar ya kusanceta zai gigice ya manta kansa ya kuma mallaka mata duk wani gurbi na zuciyarta ta yarda ba zata barwa wata macen gurbi ba ko kad’an. ( Anya kuwa Ammi Anan ba ‘a tafka son zuciya ba, shi fa namiji mijin mace hud’u ne, to za dai mu gani idan ita kuma Nannan zata yi sake a k’wace mata miji, don wasu matan haka suke zama sakarkaru idan an musu kishiya sai kishi ya rufe musu ido su rasa kula da mijin har wacce ta shigo ta yi wuf ta mallake musu shi. Don haka Mata mu dage, Soyayya fa ba k’arya ba ce kuma So ba ya tsufa kullum ki dinga updating soyayyarki a zuciyar mijinki ta yarda ko ya auro wata zai raina ta ta kulawar har ki ji yana fad’in me ma ya kai shi auren?😀)




Shigowarsu Kamla ne ya sa ta bud’e idonta da suka mata nauyi ta zubesu a kansu, cikin farin ciki ta dinga ware musu hannayenta tana hugging d’insu d’aya bayan d’aya. Musamman Kamla da tun lokutan baya take jin tana mata wata iriyar k’auna da bata san dalilinta ba, ashe ita d’in jininta ce. Sosai ta rungume ta tana shafa kanta “Welcome Iyalan Birmingham ya kuka baro garin naku?” Khairi da bata cika son magana ba murmushi ta yi tana shafa gefen kumatunta “Anty Hamda are you married? Da gaske ne Daddy ne Husband d’inki.” Hamda ta lumshe ido zuciyar ta na tsoron amsawa Khairin bata sani ba ko ta taya uwarta kishi. Idanun Khairin cikin nata tana sakin murmushi ta ce “Am very much Happy Anty Hamda ke da Daddy kun dace sosai perfect match.” Ta fad’a tana rungumeta a gefen jikinta. Itama Hamdan rungumeta ta yi kafin Abul Khairi ya ce “And now is my turn, Anty Hamda and Kamla siblings ne da gaske haka Daddy ya ce mana, gobe Mommyn Kamla zata zo gari from turkey.” Tsit d’akin ya d’auka Hamda tana mamakin yarda yaran suka sake abinsu da alama duk Babansu ya zauna ya warware musu komai. Ta shafa kansu murya a sake ta ce “Allah ya yi muku albarka.” Ta fad’a tana sakin ajiyar zuciya mai k’arfin gaske, da ta tafi da duk wani tsoronta da shakkar yarda yaran za su d’auketa idan sun ji maganar, suma murmushi suka saki zuk’atansu fal da murnar dawowarsu cikin ahalinsu gaba d’aya.




___________


Rashin sukunin zuciya ya haifar mata da zazzafan zazzab’i cikin dare ga haraswa da take yi akai-akai musamman abin ya had’u ya had’ar mata da rashin cin abinci sai ta galabaita sosai.
Tun Sa’ada na ganin kamar hakan ragwanci ne da lalaci har ta tabbatar da tabbatuwar ciwon. Ganin tana shirin shid’ewa ya sa Sa’ada ta fita a kid’ime kiran su Didi. Duk da barci ne a idanunsu bai hana su tahowa da sauri ba. Suma ganin yarda yanayinta yake ya tashi hankalinsu da sauri suka shiga kiran Hammad don ya kawo musu agaji.


Shima a lokacin ba barci yake ba gaba d’aya hankalinsa a tashe yake ga wata iriyar zafaffiyar sha’awarta da take neman kassara masa garkuwar jiki. Duk da ga Nanna a gefensa amma gaba d’aya ba tata yake ba, gangar jikinsa Hamda take muradi abin tamkar wani maganad’isu tabbas d’iyar Ammi ta yi gadon Ammi abin a jininsu yake, kishi da irinsu kuwa akwai tashin hankali don kullum sababbi suke komawa dal da su da zarar miji ya d’an yi kwana biyu bai kusancesu ba sai ki ga sun koma sun rufe ruf kamar ma ba’a tab’a aikata komai da su ba, samun irinsu k’alilan ne a cikin mata, don haka da zarar mutum ya auri irinsu to fa kowace irin mace zai aura ba zai tab’a kwatanta ta da wannan matar tasa ba, ki dage ki zama irinsu y’ar uwa.😀




Wayar ya kara a kunnensa kafin ya ji kwararaton Didi tana sanar da shi rashin lafiyar Hamdan. Ai kafin ya k’arasa ji ya yi wurgi da wayar da sauri ya mik’e ya fice ba tare da ya amsa kiran da Nanna take masa ba. Gabansa ne kawai yake fad’uwa yana fatan kada wani abu ya samu Hamdan. Kafin ya isa sashen Didin kuwa ya saka mai gadi ya bud’e masa k’ofa.


A tsakiyar gadon take zube, numfashinta yana fita sama-sama, wannan karan idanunsa rufewa ya yi ruf ya ma manta da wata Didi tsam ya rungume Hamdan a jikinsa yana manna mata kiss kafin ya sunkuceta bayan ya zira mata dogon hijabi da sauri yake furta “please Hamda bud’e idonki don Allah kada ki rufe…” wasu irin maganganu ya dinga furtawa da har ya bawa Umma Asma kunya. Didi kuwa bud’e baki kawai ta yi tana kallonsa rud’anin da take ciki game da ciwon Hamdan ya sa ta kasa furta ko da kalmar ‘A’ sai mayar da ajiyar zuciya kawai take.




Sosai asibitin suka yi iya bincikensu kafin su sanar da su cikin jikinta ne yake galabaitar da ita ga shi ta saka damuwa a ranta, tun a gaban likitan Didi ta fara furta “Subhanallahi, ciki kuma to a gidan uban wa hakan ta faru? Yanzu fisabilillah yaron nan sai da ka bi yarinyar nan ka turmishe ka mata ciki? Ni dai ban tab’a ganin jarababbe irin ka ba wallahi Hammad. Allah yasa ba a gado na aka je aka aikata wannan ta’asar ba. Masifa!” Didi ta furta tana watsa masa kallo. Hamda kuwa wata irin kunya ce ta kamata da sauri ta lumshe ido tana jin kunyar duka mutanen wajen Tabbas Hammad ya kaita ya baro yanzu kuma kowa ya san ta yarda ta je ta samo cikin. Didi ta k’arasa bakin gadon idanunta akan Hamdan ta ce “Munafuka bud’e idonki da kyau ki kalleni ashe kin san ciwon da kike yo ni da na san laulayin ciki ne da mai zai saka na rakoki da lokacin da ne dai da an saka miki wak’a a dandali ace kin samu ciki ba’a kaiki d’akin mijinki ba. Jarababbu ku dai ku je ku nanik’i miji ku samu ciki mhmmn za ki dawo gidan ki sameni.” Ta juya ta fice tana ta sababi. Umma Asma dai dariyarta kawai take shek’awa ganin yarda Didi ta d’au lamarin.








_______________________




A zafafe ya mik’e a d’akin taron yana watsa idanunsa cikin nasu, idanun da suka kad’a suka yi jajur tamkar garwashi.” Mutumin nan ya yaudaremu tsawon lokaci muna fama da yarda za mu kawar da shi a doron k’asa sai ga shi ya zo mana da wata maganar banza wai yana da zuri’a, to ya zama dole a wannan karan mu kawar da KK daga doron k’asa kafin mu bi ahalin nasa suma mu murk’ushesu.” Yarda yake maganar a hassale zai tabbatar maka abin ya dad’e yana ci masa tuwa a k’warya. D’aya daga cikinsu shima ya mik’e kafin ya ce “Ya zama dole kuwa Yaya, amma ta wacce hanya kake ganin za’a bi?” Ya ja ajiyar numfashi kafin ya ce “Duk da gidansa akwai security ya zama dole mu samu wata daga cikin y’an uwa ta koma gidan ta tare ta yarda za mu samu mu cimma burin mu kai tsaye, ko da ta hanyar gubar iska ne da za’a saka a d’akinsa da zarar ya shak’eta zai shek’a lahira ko kuma mu kashe duk wasu cameras na d’akinsa ta saka masa wuta a d’akin cikin dare….






To fa
jikar Nashe ta kuce!




08033748387
[1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: Tsayuwarsa a gabansu shi ya bawa cikinsu damar sakin wani irin rugugin sauti na razana da kid’ima. Daga yanayin kallon da yake musu tabbaci ne na cewa ya ji duk manak’isar da suke shirin k’ulla masa. Murmushi kawai yake saki mai nuna tsananin takaicin kasancewarsu zuri’ar mahaifinsa. Idan wani ne ya gaya masa hakan zata iya faruwa a rayuwa zai iya k’aryatawa sai ga shi zahirin lamarin kacokam ya faru a kansa, y’an uwansa da ya sani wanda suke uba d’aya su suke neman rayuwarsa bayan sun gama neman ta y’ay’an cikinsa duk akan wani banzan lamari wai dukiya da take k’arewa a duniya duk kud’in mutum bai isa ya tafi da shi lahira ba sai dai ya tafi da aikin ladan da ya yi ta sanadiyyar kud’in. Ya lumshe idonsa wasu hawayen bak’in ciki suka shiga zubo masa, bai san me yasa y’an uwansa suke k’insa har haka ba, duk da tarin kyautatwar da yake musu ba wanda ba ya cin moriyar arzikinsa mazansu da matansu, kai har ma da yaransu, akwai albashi da yake marasa k’arfin cikinsu duk wata ban da zakka da yake dunk’ulewa ya basu, hidimar biki shine kai komai ma shi d’in dai KK shine mai d’aukar kaso mafi tsoka a hidimar ahalin K. Mud’allab sai ga shi zuri’arsa ce ba sa so da shi kansa suke neman hanyar hallaka shi, anya kuwa ubangiji zai barsu da alahakin wannan bawa nasa, kaico wannan zamanin da son zuciya ya yi bake-bake a zuk’atan al’umma. Kukan ya ke sosai kukan da ya karya zuk’atan tsirari daga cikinsu suka riski zuk’atansu a cikin tarin da na sani, kunya matsananciya ta yi musu dabaibayi a zuciyoyinsu suka fara tunanin ta yarda zuciyarsa ta dinga ingiza su da bin son zuciyar wasu daga cikinsu.


Lamarine mai girma a wajen KK don haka ya kasa furta musu komai illa jan sawayensa da ya yi ya fice daga bigiren da suke. Zuciya bata da k’ashi a yau duk hak’urinsa zuciyarsa ta karye ba ya jin har abada zai sake dubansu da idanun rahma, bai tsanesu ba amma ya zama dole ya nisanci mu’amala da su, duk kuwa da yake musu zahirinsa da bad’ininsa Allah ne shaida amma tunda su sun kasa fuskantar haka ya zama dole ya bi da su ta hanyar da karatun rayuwa zai fahintar da su, shima d’an zamani ne mai kuma madafan iko tunda yana da kud’i ya tabbata ko k’ara zai kaisu shine a sama, amma ba zai aikata haka ba, ko bakomai suna amsa sunan mahaifinsa ne K. Mud’allab albarkacin wannan sunan da yake rab’e da nasu ba su cancanci tozarci ba, sai dai zai bar su da halinsu ta hanyar yanke duk wata alak’a da su. Alhamdulillah tunda yanzu yana da zuri’a yana kuma da Ahalin Didi da ya mayar da su tamkar nasa ahalin madallah da ubangiji buwayi gagara misali. Da kansa ya fisgi motar da mugun speed ya bar harabar gidan, don dole escort na sa suka bi shi suma a guje, zuk’atansu cike da tunanin dalilin tashin hankalin da
Suka ga uban gidansu a ciki, fatansu dai ya zama komai lafiya.


Bai tsaya ko ina ba, sai a gaban Didi. Cikin tashin hankali ya shiga falon Didin. Idanunsa sun kad’a sun yi jajir ya zube gwuwoyinsa a gaban Didin ya dafa cinyoyinta yana sakin wata irin ajiyar zuciya mai bayyana mad’aukakin tashin hankalin da yake ciki. Didi addu’a kawai take ja a zuciyarta don idanun KK kawai zaka kalla ka san zuciyarsa a turnik’e take da tashin hankali. Ta hau shafa kansa tana bubbuga bayansa had’e da jawo masa addu’oin samun sauk’in zuciya ‘Allahumma la sahla illa ma ja’altuhu sahlan wa anta taj’alil hazna iza shi’ita sahlan.’ A hankali ya dinga maimaita wa kafin ya saki wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa ya zame ya kwanta a k’asan carpet d’in Didin had’e da yin matashin kai da hannayensa. Nauyayyan barci ne mai k’arfin gaske ya d’aukeshi. Didi ta saki ajiyar zuciya had’e da zuba masa ido cike da tausayawa ta tabbatar duk abinda ya gigita shi mai girman gaske ne tausayinsa ya kamata, ganin duk tarin dukiyarsa shima akwai ta yarda Allah ya jarrabeshi don haka duk wanda ka ganshi kada ka yi addu’ar zama irinsa saboda baka san tarin matsalolinsa da suke bad’inance ba, kowa da inda yake da nak’asu a rayuwarsa. Didi ta saki ajiyar zuciya had’e da Kunna masa sautin Alkur’ani a gefen kunnensa sannan ta mik’e ta shige d’akinta, jin KK take kamar jininta a zuciyarta take jinsa kamar yarda take jin dukkan ahalinta.






____________________


Sai Azahar Umma Asma ta bar asibitin ita da Ammi da ta zo duba Hamdan bayan bayyanuwar ciwonta, suka bar Sa’ada da Munira a wajenta, sabida jikin nata da sauk’i su kuma akwai abubuwan da za su yi masu mahimmanci tunda bikin dai saura kwana uku kacal.


K’amshin turarensa ne ya sanar da su wanzuwarsa a asibitin tun bai kai ga bud’e k’ofar ya shigo ba. Hamda ta runtse idonta don ita ta san shine, duk da tana jin haushinsa hakan bai saka ta k’i d’akin ganinsa ba, sosai take son ganinsa idanunsa suna bayyana mata zahirin k’aunar da yake mata.


Jallabiya ce fara tas a jikinsa mai gajeran hannu sai hula da ake kira hana sallah da ya saka a kan nasa. Idanunsa sanye ciki. Kyakykyawan farin glass. Da sallama ya shiga d’akin yayin da ya zube idanunsa a kan Hamda, da take sanye cikin tausassar doguwar Riga kalar ruwan hoda, ta tufke gashinta a tsakiyar kanta fuskarta ta sake haske ta yi fa yau da ita. Sa’ada da Munira gaishe shi kawai suka yi suka fice daga d’akin. Ya saki ajiyar zuciya kafin ya k’arasa gadon ya zauna sosai ya na k’ok’arin jan ta jikinsa, duk da burinta ne hakan ta jita kwance a jikinsa bai hanata janye jikinta ba fuskarta d’auke da wancan fushin da yake tsammanin ya wuce ashe da saura. Ya saki ajiyar zuciya had’e da kwanciya sosai a cinyarta ya lumshe ido kafin cikin kasalalliyar murya ya fara fad’in “Tarin laifi na a wajenki shi yasa na kasa furta miki kalmar hak’uri gani nake ba ni da wannan kalmar ki barni na nuna miki a aikace please my Hamda, wallahi bana cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ko barci bana iya yi.” Ya fad’a yana bud’e idonsa ya ware su a cikin nata idon, kallon da ya yi mata tasiri mai girman gaske don duk wani sassa na jikinta sai da ya amsa wannan kallon, soyayyarsa gaba d’aya ta yi hank’oro ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login