Showing 60001 words to 63000 words out of 117648 words
Chapter 21 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt
da ya shirya tsaf yana combing kansa ya kalleta “ke ba zaki watsa ruwan ba ki fita mu ci abinci.”
Ta mik’e had’e da fad’in wash wallahi am too tired shi yasa ka ganni haka muje ka d’an mammatsa min jiki na a toilet mana.
Ya wurga mata wani kallo kafin ya ce “Wasa kike amma? Ni tausar kika yi min? Ni da kika bi kika nuk’urk’usa a jirgi.” Murmushi ta saki ta shige toilet d’in tana fad’in idan ban nuk’urkusa ka ba wa kake so na mannewa?” Ya bita da murmushin dama so yake ta shige kawai ya nufi d’akin Hamda. Sai da ya kulleta ta k’ofar baya sannan ya nufi d’akin Hamdan.
A takure ya ganta cikin duvet a gado sai kakkarwa da rawar d’ari take. Ya k’arasa gadon ya jata jikinsa sosai yana b’alle botiran rigarta. Jikin ya yi zafi sosai don haka ta kasa katab’us d’in k’watar kanta duk da haushin sa da take ji. Tana ji ya shige toilet ya d’ebo ruwa a wata roba da k’aramin towel a hannunsa ya sake hawa gadon. Sai da ya zare rigar jikinta kaf sannan ya shiga tsoma towel d’in a ruwa yana bin sassan jikin yana gogewa tas ya goge jikin kafin ya gama kasala ta shiga bibiyarsa ji ya ke tamkar ya kusanceta amma kuma tausayinta ya kamashi ganin bata da lafiya. Tsaf ya shirya ta cikin riga da wando na barci. Ya kawo hijabi ya zira mata ya mik’ar da ita tsaye murmushi kawai yake wurga mata. “Gwara a saka hijabi wad’ancan abubuwan su daina gigita min hankali.” Ta d’auke kanta kawai ya sake dawo da fuskarta suka yi facing juna ta lumshe idanunta bata san na san idanun su yi mata tasirin da zata sauke fushin da ta d’auka da shi. Duk da yanzun ma kaso mafi rinjaye a fushin ya zagwanye ya bi rariya tunda ya fara murzar jikinta da towel. Ji ta yi kawai ya kaiwa idanun sumbata a tausashe cikin dasashshiyar murya mai gigita hankalin d’iyoyi mata ya ce “Ko ki saki fuskar nan ko kuma mu koma gado a yi mai gaba d’aya ta inda dole ki sake fuskar ko ba kya so.” K’in bud’e idon ta yi balle ta saki fuskar sai ma hawaye da ta sakar masa “Ni ka kyaleni bayan ka fi damuwa da farin cikin matarka fiye da nawa ai ina kallo a jikinka tayi barci a jirgi.” Dariya ce taso k’wace masa ganin lamarin na Hamda azimin ne. Kishi ne kawai yake nuk’urk’usar zuciyarta idanunta still a runtse suke kuma ba su fasa fitar da ruwan ba. Ji tayi kawai ya d’auke ta cak. Daidai lokacin da bugun k’ofar Nannan ya tsananta ya fice da ita falo yana tsotse tsinin hancinta.
Ya direta a saman three seater sannan ya sake sumbatarta yana fad’in “My Daru Baby.” Sannan ya koma ya bud’e k’ofar d’akin da Nannan take ta bugawa kamar zata b’alleta.
Yana bud’e k’ofar tana binsa da wani irin kallo. “Ban gane rufe ni a bedroom ba me kake aikatawa?” Idanunsa ya d’auke a kanta ba tare da yace komai ba ya juya ya shige cikin kitchen don muddin ya tsaya fes zata karanto yanayin da yake ciki a cikin k’wayar idanunsa. Famfo kawai ya kunna a kitchen ya sakarwa kansa ruwan sanyi ba mamaki ya dawo hankalinsa daga duniyar da ya fad’a. Ta dad’e tsaye a k’ofar kitchen d’in hannunta rik’e a k’ugu tana k’are masa kallo. Shi kuwa bai bi ta kanta ba, sai dai sanin cewa tana wajen ya sa shi tsuke fuskarsa tamau ya cigaba da juye ruwan shayin da ya dafa a flask. Sannan ya had’o komai a tray ya saka abincin da ya siyo musu a microwave ya d’umama duk tana tsaye kafin ta saki ajiyar zuciya ta juya hankalinta ya d’an kwanta ganin ashe girki ne ya d’auke masa hankali. Amma kuwa zata ci uban Hamda tunda ga ta kwance a falon tana jin bugunta ta gagara zuwa ta bud’a mata.
Fitowar sa ta sa ta zauna a kujera tana jifan Hamdan da kallon tsana. Ina ruwan ganni gaho don Hamdan sam bata san ma tana yi ba. Wani barci ne mai dad’i da tarin nutsuwa ya sureta. Tana yi tana shak’ar k’anshin turaren Hammad da yabi ya manne mata a fata. Duk duniya ba k’amshi mafi soyuwa a wajenta kamar k’amshin turaren Hammad. Da zarar ta ji shi take afkawa cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa.
Jin shiru har sun fara cin abincin bata motsa ba ya tabbatar da tayi barci. Hakan yasa ya dinga kiran sunanta da son ta tashi sai dai ko gezau ba tayi ba. Ya tabbata kuma tana jin yunwa. Don haka ya shiga bubbuga gefen kujerar da take. Hamda da taji shi cikin barci ta mik’e tana sakin wata irin mik’a da ta saka shi runtse ido ba shiri ya d’auke kansa. Nanna kuwa tamkar ta zunduma ihu ganin yarda hallitun Hamda suka bayyana b’aro-b’aro ta cikin Hijabi. Kasancewar Hijabin mai roba ne. Bata san sanda ta saki tsaki ba. Duk da Hammad d’in ubanta ne amma sai ta ji wani matsanancin kishin yarinyar ya kamata musamman ganin yarda gogannata ya runtse ido. Cikin takaici ta ce “Ke jaka ko da yake matsayin ubanki ai bai kamata ki zauna haka a gabansaba babu suturar arziki. Mik’e ki koma d’aki ki sauya kaya.” Hamda ta bita da kallo tana sakin murmushi sai kuma ta mik’e tana jin jiri cikin wata salon tafiya ta nufi d’akinta. Nanna ta sake jin zuciyarta ta buga ganin yarda Hamdan take juya hips da butt d’inta. Gashi wannan karan Hammad kasa hak’urin d’auke kai ya yi ya bita da kallo yana d’an cijar leb’ensa a zuciyar sa ya ayyana tabbas yarinyar nan idan ba a yi wasa ba nan gaba kad’an zata zautar da shi.
Nanna cikin wata iriyar murya mai alamar kuka ta ce “Na shiga uku ji fa kallon da kake bin ta da shi ko zaka bita ne ka turmusheta kamar yarda ka turmushe uwarta har kuka samar da cikinta.” Wani kallo ya wurgeta da shi kafin ya girgiza kai ya had’e ransa ya mik’e ya haye kujera kwanciya kawai ya yi ya lumshe ido zuciyarsa na wani irin bugawa muradinsa kawai Hamda. Zuciyarta Nanna ta shiga yi mata sak’e-sak’e don haka ta k’i tashi daga falon ta fara tunanin anya ba komai tsakanin Hamda da mijinta zubin yarda yarinyar take karairaya kamar dama tana yi ne don ta ja hankalinsa. Menene ma dalilin kulleta a d’aki d’azu? Kuma ta zo ta samu yarinyar kan kujera idanunta a lumshe take ayyana kada fa su raina mata hankali don haka zuciyarta a tunzire ta mik’e ta nufi d’akin Hamdan. Don idan ta tabbatar da zarginta tabbas zata iya cirewa Hamdan wata gab’a a jikinta… direct ta danna k’ofar d’akin bakinta na fesar da wani irin hucin b’acin rai.
To fa!
Jikar Nashe taku ce
❤️❤️❤️❤️❤️🙏
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: “Me ka dawo yi Cikin zuri’ata bayan tuni na zareka daga cikinta..” Tuni kowa ya d’ago ana kallon Abbu fuskar kowa b’aro-b’aro da mamakin furucinsa musamman wad’anda ba su san zancenba don ba kowa bane ya sani a cikin family daga Abbun sai Ammi Didi da Mahmah. Sai kuma Asma’u Sadiya da Gadanga sai ahalin Hammad. In ban da su babu wanda ya San wannan badak’alar da take faruwa a dangin. “Ka fice min daga gida kafin na yi mai gaba d’aya na tsine maka.” “Ta tabbata da a yi tsinanannu biyu a zuli’alku don kana tine mata ni ma don tine maka.” Didi ta fad’s fuskarta taf da jin haushin furucin Ummaru “Kai Umalu na lula baka tan zulu ba, to bali nima na fito maka a mutum kamar yalda kake so. Idan banda shashashanci an tab’a yanke shari’a ba a ji ta bakin mutum biyu duka ba. Wato ita ce mai gaskiya da ba zata fad’I k’alya ba.” Ta nuna musu wajen zama. Hammad ya zauna ransa a had’e kowa ya zuba masa ido. Suma su Hamdan suka zauna Didi ta sa aka zuba musu abinci. Hamda kuwa ta samu abincin ta fara ci sosai don abincin ya yi Mata. Sinasir ne da miyar taushe da ta ji naman rago da kabewa.
Ammi kuwa gaba d’aya zufa ta ke duk da sanyin a’cn da yake kwarara a falon. Da gaske a tsorace take ga shi kanta ya k’ulle ta rasa ma tunanin da zata yi. Duk addu’ar da tazo bakinta take ja. Tabbas Hammad ya shammaceta a lokacin da ta manta da waccan matsalar sai ga shi ya dawo mata da ita bagatatan. Ta runtse ido ji take a lokacin notunan kanta suna shirin kuncewa saboda matsanancin tunani da ta zurfafa.
Kowa ya yi tsit baka jin k’arar komai sai ta cokula. Zuciyar Sadiya Asma’u da Lauratu yau fes ranar da suka dad’e suna jira yau gata tazo. Hammad abincinsa yake ci cike da nutsuwa duk da kallon banzan da Abbu yake zabga masa bai damu ba sai ma sakin murmushin k’asan kumatu yake yau zan shayar da Abbu ruwan mamaki shine abinda yake ayyanawa a ransa. Kuma dalilin murmurshin nasa kenan.
Sai da kowa ya yi nak, ga wanda suka ci abincin fa kenan sannan Didi ta juya ta kalli Hammad da yake fad’in Alhamdulillah bayan ya saki gyatsa ta ce “Hammad ya bayan saduwa? Ya kuma aka ji da wannan abu da ya falu?” Ya gyara zamansa a k’asan daddumar kafin ya ce “Bayan saduwa sai Hamdala abubuwan alheri da dama sun faru Hajiya Didi ciki kuwa har da aurena da Hamda.”
D’aukacin mutanen da suke falon ba wanda gabansa bai fad’i ba da jin furucin Hammad da ya zo musu bagatatan. Harta Didi sai da ta runtse idonta ta bud’e sannan ta tabbatar abinda take ji ba mafarki ba ne. Shi da Hamda da suka san lamarin ne kawai babu alamar gigita a fuskarsu. Amma d’aukacin mutanen da suke falon idanunsa a waje yake alamar firgici da razani a tatttare da su. Tunaninsu d’aya ne tabbas Hammad ya samu tab’in kwanya idan banda haka ta yaya zai ce wai ya auri k’anwarsa da suke uba d’aya.
Nanna kuwa suman zaune ta yi tana jifan Hammad d’in da wani irin kallo. Ita dai gata nan a zaune ita ba sumammiya ba ita ba farkakkiya ba.
K’arar marin da Gadanga ya zube a k’uncin Hammad ne ya dawo da su suman wuncin gadin da suka yi. Idanunsu akan Hammad da ya rik’e kumatunsa yana jifan gadanga da wani irin kallo da murmushin takaici murya a shak’e ya ce “Me yasa zaka mareni?” Gadanga cikin zafin rai ya ce “Marinka na yi saboda ka dawo cikin nutsuwarka, ka yi mana filla-filla ka sanar damu abinda kake nufi da aurenku da Hamda, tunda ba a garin gab’a-gab’a muke ba. Kuma ko a kafirai ban yi zaton sun yarjewa kansu Auren y’an uwansu da su ke uba d’aya ba.”
Hammad ya sake shafa k’uncinsa kafin ya girgiza kansa idanunsa cikin na Hamda da take jin marin da aka yi masa tamkar k’uncinta aka daka. Ya d’an sakar mata murmushi kafin ya ce “Gata nan ku tambayeta da aurena a kanta ko babu? Kuma ta tare a gidana ko a’a?” Da sauri Asma’u ta kama ta “Hamda gaya mana gaskiya shin abinda Hammad yake fad’a gaskiya ne?” Hamda ta yi k’asa da kanta tana d’aga kai alamar gaskiya ne. Jikin Gwaggo Asma’u na b’ari ta ce “Innalillahi wa inna ilaihirraji’una. Tabbas akwai lauje cikin nad’i idan banda haka ta yaya Hammad da iliminsa da komai zai je ya auri k’anwarsa sai kace wanda ya samu tab’in k’wak’walwa.” “Tab’in k’wak’walwa na nawa? Ku yanzu ku ka San haka ni tuni dama na sani kuma na tabbatar a cikin rashin hankalin ya je ya haikewa matata ga shi nan yanzu yazo ya sake tafka haukan ta hanyar auren k’anwarsa jininsa ku fice min da shi daga gidannan kafin na yanke hukunci mai muni don wallahi Zan iya sawa a b’atar min da shi.” Abbu ya fad’a cikin wata irin murya jikinsa na b’ari hannunsa na rawa yake nuna Gadanga “Fita min da shi Gadanga kafin na kashe shi ku zo kuna da na sani.” Daga haka ya zauna idaunsa suna jirkicewa suna canja launi saboda zallar bak’in ciki.
A firgice su Asma’u suke da jin furucin Abbu, suma kenan balle Sadiya da ta ji kanta ya zama kamar dutse hak’oranta sun fara rawa suna kakkafewa tsoro take ji sosai kada zancen Abbu ya tabbata ace Da gaske Hammad ya samu tab’in k’wak’walwa. Idan ban da haka ta yaya zai aikata wannan kwamacalar? Zuciyarta ce kawai take bugu.
Ita kanta Hamda maganar Abbu ta jijjigata, Idan ya kasance hakan ta tabbata ya zata yi da cikin da yake mak’ale a jikinta? Wace amsa zata bawa duniya don gane da tarin tambayoyin da za’a dinga mata. Ta runtse ido ta bud’e tana fatan taji Hammad ya ce wani abu amma bai ce ba, sai murmushi kawai yake yana wa kowa kallon k’asan ido.
Zuciyar kowa dakan uku-uku take. A zafafe Didi da ta gaji da jiran cewar Hammad d’in ta ce “Kai don ubanka ka fito ka yi magana ka wanke kanka, ka bar mutane a cikin duhu ko so kake zuciyoyinmu su buga.” Ya d’ago idanunsa cikin na Didi ya girgiza kai yana sakin murmushi kafin ya ce “Ai Abbu ya baku amsa tunda ya ce mahaukaci ne ni. Na yarda ni mahaukacin ne ayi min hukuncin da ya dace da ni musamman ga cikina na nan a jikin Hamda ku min afuwa..” A gigice Mahmah ta zuba masa marika har biyu a duk k’uncinsa. Ya rik’e k’uncin yana kallonta cike da tausayawa halinta da take ciki daga ganinta ka san zuciyarta bata aiki yarda ya kamata. Gani ya yi kawai ta zube a jikinsa tana fad’in “Ka fito ka fad’I gaskiya Hammad kada kasa zuciyata ta buga ka yiwa y’an uwanka asarata…” Muryarta na rawa cikin kuka da gigita take fad’a. Tausayin uwa ne ya ratsa shi ban da ita yau da ya k’yalesu su yi ta d’aukansa a mahaukacin. Ya kama tafukan hannunta ya sanya kansa a ciki kawai ya saki wani mahaukacin kuka da ya hargitsa duk zuk’atan mazauna wajen kada dai Hamda ta ji labari. Gaba d’aya ta yi firgai-firgai da ita.
Tsawon lokaci ya d’ago ya zube idanunsa cikin na Ammi. Wani irin kallo yake mata da yasa kowa ya mayar da hankalinsa kanta. Kallon nasa ne yasa jikinta ya dinga rawa alamun gaskiya ya bayyana b’aro-b’aro a fuskarta tun kafin ya yi magana idanunsa suka fara bata tsoro. Yana murmushi ya nuna ta da yatsa “Ki sanar da su gaskiyar yarda abin yake? Alk’awari na d’aukar miki ba zan gayawa kowa ba. Kuma na cika miki alk’awarinki don haka da bakinki ki sanar da su yarda ABIN YAKE?” Tun kafin ta fara magana wasu suka tabbatar da rashin gaskiyarya zuk’atansu suka fara saukuwa daga b’acin ran da suke ciki. Idanu suka zuba mata suna jiran cewarta. Ammi ta yi k’asa da idanunta tsoro ya cika ta fal, bata san yarda Umar Abbu zai fassara lamarin ba. Bata san kuma da me mutanen wajen za su kalleta ba idan ta gaya musu gaskiyar yarda abin yake. Ta share zufar da ta karyo mata kafin cikin rawar murya ta kalli Abbu ta fara magana….
Jikar Nashe taku ce ✍🏽✍🏽
❤️❤️❤️❤️❤️🙏
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: “Ka gafarce ni Umar, ha’k’ik’a na san na cuceka bisa son zuciya da sharrin shaid’an, sai dai hakan ya faru ne saboda d’amfaruwa da zuciya ta tayi na son haihuwar d’a namiji. Amma ina tabbatar muku Hamda d’iyar halak ce da aure na samu cikinta ba kamar yarda zuciyarku take hasashe ba.”
A tunzire Didi ta zuba mata ido cikin b’acin rai ta ce “Takina bana ton itkancin banza da wofi ta yaya zaki ce da aule kika haifi Hamda an tab’a aule akan aule ne? Ko a garinku haka ake ni dai ina gidan nan ban ji san da Ummalu ya take ki ba. Don haka ki tanal da mu yarda kika tamu cikin tegiyar y’alki”
Shiru Sakina ta yi zuciyarta na dakan uku-uku ta kasa cewa komai illa murza wani zobe da yake hannunta. Razani da firgici ne a cikin ranta shi yasa ta kasa d’aga kai ta kalli kowa. Musamman yarda take jin sautin kukan Abbu har nan inda take zaune. Alamar lamarin ya gama gigita tunaninsa. Tunda zata iya k’irga sau nawa ta ga hawayensa amma bata tab’a ganin yana kuka da shashshek’a ba. Hakan ya sake d’aga hankalinta yanzu ma kenan ina ga ya ji gaskiyar abinda ya wakana.
Asma’u a harzuk’e ta kalli Hammad cikin tsawa ta ce masa “Kai don ubanka tunda ta k’i fad’ar abinda ya wakana kai tunda ka san komai sai ka sanar mana.” Hammad ya hau girgiza kai yana tuno da ranar da zai iya kiranta bak’ar rana a tarihin rayuwarsa, a duk sanda ya tuna kuma sai ya zubda hawaye yake jin sanyi a ransa. Yanzunma hawayen ya share yana sakin murmushi kad’an ya ce “Ita zata fad’a muku da bakinta Umma, a tun lokacin da abin ya faru na tabbatar musu da ba zan fad’awa kowa ba alk’awari na d’auka bayan sun tursasani bisa son zuciyarsu, ta hanyar d’aukan hotona tsirara shimfid’e akan gadonta, da camera suka kuma wanko hotunan suka nuna min tare da tabbatar min idan maganar ta fito to wallahi za su alak’anta ni da cewa ni ne naje har d’aki na yi mata fyad’e. A lokacin hankalina ya tashi har aka dinga kaini asibiti kuna tunanin motsuwar k’wak’walwa ya sameni, da gaske ni kaina a lokacin gani nake kamar na haukace bani da nutsuwa ko kad’an. Shi yasa na uzzira sai da aka kaini Birmingham karatu saboda da zarar na rufe ido lamarin nake gani da kuma hotunana tsirara. Na san bani da mafita kuma ko na fito na fad’a alokacin suna nuna hoton nan ba wanda ba zai amince da cewa ni na haik’e mata ba. Shi yasa na bar maganar a ciki na har ta kusa zautar da ni banda Allah ya kiyaye Mahmah ta fahimci kamar sammu aka yi min ita