Showing 57001 words to 60000 words out of 117648 words
Chapter 20 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt
nata. A kunne ya rad’a mata “Ki bari mu samu nutsuwa mana rashin jin mahad’insa ne fa ya saki zazzab’in.” Ta girgiza masa kai “Ni dai ka k’yaleni tunda muka taho fa baka kulani ba sai yanzu da ka bankawa matarka maganin barci. Ni baka damu da b’acin raina ba kenan idan na ga kuna had’a jiki itace ka damu da na ta b’acin ran. Ni muna zuwa Nigeria zaka sake ni nima na auri mijina ba mijin wat….” Ji tayi kawai ya cafki lab’banta yana bata wata irin zafaffiyar sumba kamar zai cire leb’en.
Son ransa ya yi da lab’ban kafin ya saketa cikin wani irin yanayi ya ce “Hamda so kike son ki ya kashe ni? Ba ki san yarda nake jin kaina ba ko a duk lokacin da kika had’a kanki da auren wani. Please ki daina.” Turo bakinta ta sake yi zata sake masa tsiwa still ya sake kame bakin yana tsotsa yana d’ago kansa ya ga Nanna ta nufo wajen tana daf da su………..
To fa! A yi min hak’uri please a k’aidata ga wanda suka karanta me Zan yi da ita? Sun san bana posting saturday sai Allah ya kaimu Sunday.
Jikar Nashe taku ce, ina alfahari da ku.❤️❤️❤️❤️❤️🙏
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Cizar baki tayi bak’in ciki ya turnik’eta jin k’ofar a kulle take gam da alama sai da ta murza key d’in sau biyu. K’arar bugun k’ofar ne ya farkar da Hammad da guntun barcin da ya fara surarsa. Da sauri ya mik’e yana isa corridor d’in mamaki fal fuskarsa da yaga Nanna ce a tsaye tana aukin buga k’ofar da alama ma kamar bata cikin hayyacinta “Wai Nanna meye haka ne? Kin san kuwa k’arfe nawa yanzu ki ke aikin buga k’ofa. Idan ta bud’e me zata miki me yasa ba kya son zaman lafiya ne?” Jijjaga jiki take tana masa kallon sama da k’asa “Eeh mana, ka ce haka ni kuwa na san k’arfe nawa. Uku har da Rabi na dare ko ba haka bane? Kuma ina sane nake buga k’ofar so nake ta fito ta sanar da bi uban me ku ke aikatawa a b’oye? Don haka siddan ba zata dinga wannan karairayar jikin ba, da duk wanda ya gani ya san da wata manufa take aikataw so take ta ja hankalinta kanka ko ma ka riga ka kai kanka wajenta idan ban da haka ta yaya da aurenta zata dinga maka d’abi’ar karuwai. Ko da yake uwarta ma da auren ubanka a kanta ka nemeta har ka yi cikinta….” Wasu taurari da ta gani shi yasa ta shanye maganar ta tsaf a mak’ogaro mari fa? Sosai ta dinga shafa wajen tana jifansa da kallon mamaki yaushe rabon da ya mareta tun farkon aurensu lokacin yana kan ganiyar cutar da bata tantama hauka ya yi a lokacin. Sai ga shi yanzu a cikin hayyacinsa ya sake marinta. Idanunta a jirkice ta d’ago tana kallonsa “Ni ka mara?” “Na mareki d’in, kuma ko yanzu kika sake alak’anta ni da waccan maganar zan sake zuba miki mari. Tunda ke ba ki san kara da kawaici ba. Sau nawa na ja kunnenki akan maganar amma kin yi burus da jan kunne na kullum sai sake maimaita min zance mafi muni a kunnuwa ki ke.” Da kyar ta janye jikinta daga wajen ta shige d’akin zuciyarta tana tunzira da b’acin rai gani take idan ta cigaba da tsayawa a wajensa komai ma zata iya aikata masa.
Shi ma tsaki ya ja ya koma falo. Ya zube a kujera madadin barcin ya yi gaba da shi sai ya ji tas idanunsa sun washe. Dama da ya ya samu
Ya yi barcin tunanin Hamda ya hana shi sak’at sannan ta zo ta sake caza masa kai da kalamai mafi muni da ya tsani ya ji a kunnuwansa alak’anta shi da matar ubansa. Ya runtse idanunsa gobe dai zai fasa b’aragurbin k’wan zai ga da wani ido Nanna zata dube shi, yana zaune anan har ya ji kiran sallah ya tashi ya fara nafilfili kafin shigar lokacin Sallah.
Daidai lokacin itama Hamdan sallah take ga yunwa ta addabeta kuma bata san fita falon balle ta had’u da Nanna ko d’azu duk masifar da aka buga tana juyo su daga cikin d’akin bud’ewa ne ba zata yi ba don bata shirya karb’ar tijarar Nanna ba. Idan ta matsu da son jin amsoshin tambayoyinta ta rutsa mijinta ta tambayeshi ita ba ruwanta.
Sai da ta ji wajen ya yi tsit alamar sun kwanta bayan sun yi sallah sannan cikin sand’a ta fito daga ita sai y’ar riga iya cinya cikin sand’a ta bud’e kitchen d’in bata san ta yi dogon motsin da wani zai ji ta. Sai dai ina duk abinda take yi idanunsa a kanta. Ya saki murmushi kawai ganin yarda gashinta ya mimmik’e sai ka yi zaton aljannah ce.
Tana tsaye a kitchen d’in tana warming d’in abinci da cup d’in
Madara a hannunta tana sha da sauri da alama yunwa take ji. Ji ta yi a jikinta alamar wani yana kallonta. Ta juyo a tsoarace zata saka ihu ya manna jikinsa da nata had’e da rufe mata baki ruf. “Ya jikin na mu?” Ya rad’a mata yana shafa k’asan mararta “Wannan babyn me yasa yake wahalar da mu ne? Tun ban gama cin amarcin ba. Mhmn” wani shock ne ya zuyarceta ta bud’e ido sosai alamar tsorata kafin ta juyo su yi facing juna “Baby fa na ji kace?” Ya d’aga mata gira yana jifanta da murmushi had’e da shafo mararta “Tabbas na yi ajiyar k’wai anan ko nace k’waya k’wayai baki ga yarda kika yi fresh ba?” Jikinta ta zare daga nasa “Ina ni sam ba ni da ciki ina y’ar yarinyata da ni zaka ce min ina da ciki.” Gefen kunneta ya d’an ciza kad’an yana shafa kumatunta still a kunne ya sake rad’a mata “Y’ar yarinya kuma ta iya amsar sak’o ba?” “Ni dai ka tafi kada matarka ta zo ta ganka.” Matsarta ya sake yi sosai “Menene don ta ganni ina ce halak d’ina ce sai
Na ce matata ce.” Hamda ta tab’e baki “Ji sai ka ce gaske mutumin da ko magana baka iya yi min a gabanta.” Hannunta ya murza sosai Kafin ya ce “Ba tsoro bane, zallar mamaki nake son na shayar da zuri’ar D’an Borno. Wanda labarin aure na da ke gobe zai girgiza su kin ga tilas Abbu zai tuhumi Ammi Uban da ya yi cikin ki.? Hawaye ya kawo idonta kafin ta shige jikinsa cikin kuka ta ce “Please Yaya Hammad Are you sure ni ba shegiya ba ce?” Bayanta ya hau shafawa “Da gaske ke ba shegiya ba ce da ubanki Hamda, kuma duk family sun San shi.” Ta sake k’ank’ameshi “To wanene?” Ta fad’a da d’an shashshekar kuka Hammad ya saki hucin ajiyar zuciya a kunnenta kafin ya ce “Ko ma waye tilas gobe za ki Ji shi. Na riga na d’aukar mata alk’awari da bakina dai ba Zan tona mata asiri ba. Sai dai tun a lokacin na tabbatarwa kaina Zan aureki wannan dalililn shi Zai tona mata asiri tunda dai wa Ai ba ya auren k’anwarsa ko? Don haka tul fil azal da son aurenki da tarin k’aunarki na girma a zuciyata tun kina k’’aramarki.” Ya fad’a yana juye mata abincin “Maza ki je ki ci, ki tabbatar kuma kin koma barci gobe I yanzu na tabbatar ba shamakin da zai hana ni kwana dake a jikina ko?”
Sunkuyar da kanta ta yi ita kanta tana kewarsa sosai fiye da tunaninsa.
Ya rakata har d’akin da cup d’in shayinta sannan ya juyo ya koma falo makwancinsa.
_______________
Barci ne sosai ya d’aukesu don sai kusan sha biyun rana suka mik’e shima da kyar. Hamda ta samu kanta da wanka har da gyaran gashi ya kuma yi mata kyau sosai ta murza wet lips a bakin nata mai k’amshin strawberry.
Zama ta yi a gefen gadon sam ba ta son fita don haka ta yi zamanta tana aukin game a wayarta tunda ya ce sai after magriba za su je gidan. Yau fes ta tashi zuciyarta fresh take jinta. Ba mamaki hakan yana cikin farin cikin yau duniya zata san wacece ita? Ita kanta zata san wanene mahaifinta don haka take zakwad’in zuwanta gidan.
Nanna kuwa fes ta fito cikin hamshak’iyar shiga, zazzafan lace ta saka gold hannu da wuya sai zabga k’amshi take duk da zuciyarta ba dad’i tana jin haushin Hammad haka dai ta daure ta shiga kitchen don samar musu abinda za su ci su yi bud’a baki tunda ya kafe shigar dare za su yiwa gidan nasu.
Girkin cin mutum biyu kawai tayi. Yarda ta ke jin haushin Hamda bata jin zata iya yi mata abinci. K’amshin girkin ya ziyarci hancin Hamda ta ji babu abinda take son ci irin abinda aka dafa. Don haka cikin dakiya ta fito falon. Fuskarta ba yabo ba fallasa ta sauke ganinta akan Nanna. Da itama ta tsuke fuskarta tun bayan ganin fitowar Hamdan. Hammad dai yana zaune a gefe yana kallon yarda suke musayar kallo kamar za su amayar da wuta a bakinsu. Hamdan ta kalleta kamar an mata dole ta bud’e bakinta da kyar ta ce “Maman kamla ina yini an sha ruwa lafiya?” Idan kai da baka wajen ka amsa to Nanna ma ta amsa. Hamda ba ta damu da rashin amsawarba ta k’arasa dinning d’in saboda yawunta ya gama tsinkewa da abincin Nannan duk da ba wata tsiya bace illa indomie da k’wai ta sunkuci plate d’in da Nanna ta zubawa Hammad abinci ta yi hanyar bedroom d’inta. Da sauri Nanna ta ce “Kan uba, ke kin isa in dafa abinci ki ci.” Zata bita Hammad ya rik’eta idanunsa narai-narai ya ce “Haba Nanna please mana, ki barta ta ci kina ga laulayin ciki ta ke.” Idanu ta zuba masa murya a dashe ta ce “Kai ya aka yi ka san laulayin cikin ta ke?” Ya basar da maganar ta hanyar janyo plate d’in da ta zuba nata abincin ya d’ebo indomien da fork cikin salon da ya san yana gigita ta ya kuma saukar da fushinta ko wane iri ne ya ce “Ha, kin ji Sweetie na.” Kamar k’aramar yarinya kuwa haka ta bud’e bakinta sai dai takaicin Hamda na nan a zuciyarta.
Sai da Hamda ta ci ta yi nak sannan ta saki hamdala tana murmushi hango idanun Nannan cikin masifa. Zamanta ta yi a d’aki ta k’i fita har san da Hammad ya k’walo mata kira. Tsaki ta yi ta mik’e tana nad’e mayafinta da d’aukan hand bag d’inta. Ta sake feshe jikinta da turare sannan ta maka Glass samfurin Gucci a idanunta wanda ake kira No respect.
A wajen gidan ta sameshi yana magana da mai gadi. Nanna kuwa ta hakimce a gaban mota. Hamda ta bud’e bayan motar ta shiga. Tare da cewa Nanna “Sannu Maman Kamla.” A zafafe ta juyo zata fara mata masifa kenan Hammad ya shigo don haka ta had’iye fad’an nata.
Harabar gidan a cike take da alama ahalin gidan suna nan. Don dama duk yawanci da azimi goma ga azimi a gidan ahalin d’an borno suke shan ruwa. Sai a sannan zuciyar Hamda ta shiga matsanancin bugu. Ta kasa fita daga motar har sai da Hammad ya bud’e idanunsa cikin nata murya can k’asa ya ce ko sai na fito da ke?” Ta watsa masa wani kallo mai nuni da kamar zai iya? Ya girgiza kansa had’a da d’aga yatsansa d’aya daga yau ne dai gobe kowa ya san matsayinki a wajena.”
Jikinta a sanyaye ta fito ta bi bayansa. Ahalin d’an Borno Nanna suka fara gani kafin Hammad ya yi sallama shima ya shiga sai Hamda. Aka kuma ci sa’a kowa da kowa yana falon Didin saboda ya fi kowane falo girma a gidan. Mutanen gurin cak suka yi da mamakin ganinsu musamman Ammi da cikinta ya yi wata irin hautsinawa cikin tsananin firgici ta sauke kallonta kan Hammad. Didi kuwa da fara’a ta dinga cewa maraba lale da mutanen bilningam maza Ku shigo. Inye Hamdede haka kika zambad’a kyau daga zuwanki k’asar mutane…. Abbu ya d’ago a zafafe ya sauke mugun kallonsa akan Hammad cikin tsawa ya ce….
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Hankalinsa ne ya kai k’ololuwar tashi. Yana k’ok’arin zame Hamdan a jikinsa ita kuma ta sake cukuikuyeshi don ita ma ta gano tahowar Nannan ta tsakankanin kujera. Farin ciki ne ya kama shi ganin Nannan jiri ya d’ebeta ta rik’e kanta ta dafa wata kujera da take daf da ita ta zauna had’e da rik’e kanta. Ya saki ajiyar zuciya kafin ya zame Hamda daga jikinsa ya mik’e. Hamdan ta bi shi da kallo me nuna zallar haushin abinda ya yi mata sai kuma ta yi k’wafa ta mayar da kanta kujera tana cije gefen leb’enta da ya riga ya zame mata d’abi’a. Hammad ya shige ba tare da ya lura da kallon da Hamdan take masa ba. Abu d’aya ya sani ya san zuciyarta na nan tamkar ta buga don fushi.
A gefen kujerar Nannan ya tsaya ya dafa kafad’arta, da kyar ta d’ago idanunta da suka mata nauyi cikin jin barci ta ce “Ina kaje ina ta nemanka?” “Shi yasa kika taho jiri na kwasarki sai kace ni d’in k’aramin yaro ne balle na ce tunani ki ke zan b’ata.” Ya fad’a cikin jin haushi da katse masa hutun da ta yi. Idanunta Dishi-Dishi ta dinga binsa da kallo har ta ga ya koma mazauninsa. A hakan duk da tana jin jiki sai da ta sake mik’ewa ta bi bayansa tana zuwa ta sanya kanta a cinyarsa ta k’udunduna a jikinsa kamar wani zai k’wace mata shi. A haka barci ya sake awon gaba da ita. Shi kuwa Hammad gaba d’aya ya raba hankalinsa kan Hamda da barci ya yi awon gaba da ita.
Cikin takaici ya sake zame Nanna da barcin ya d’an fara mata nauyi amma sai yaji ta sake rik’e shi gam murya a cikin barci take ce masa “please Dear na fi samun nutsuwa da barci mai dad’i a cikin jikinka.”
Cikin takaici ya zabga matsakaicin tsaki kafin ya mayar da kansa jikin
Kujerar a hankali shima barcin ya yi awon gaba da shi.
__________________
Cikin dare suka dira A airport d’in da ke garin kano Malam Aminu Kano International Airport. Hannun Nanna sak’ale da na Hammad. Ita kuwa Hamda da kyar take jan trolley d’inta ga jiri da take ji gaba d’aya yanayin ta ya canja kasala take ji sosai da alama kuma laulayin ciki ne. Wannan karan Hammad fuskarsa a d’aure ya janye Nanna daga jikinsa don ya tabbatar zuwa lokacin maganin barcin ya sake ta tana sane take sake narke masa a jiki uwa wata yarinya. Gurin Hamda ya je duk da banzan kallon da Nanna take wurga masa. Ya saka hannu ya janye trolley d’in da take ja da kyar ga wani amai da take ji yana taso mata. Idanunsa a kanta ya ce “Ya dai jikinne?” Kallo mai cike da harara ta wurge da shi kafin ta turo d’an guntun bakinta. Cikin mamakin lamarin shagawab’arta kawai ya ga ta saki hawaye yana gangaro mata ta kuma ya gaba da d’an sauri alamar bata son magana da shi. Murmushi ya saki yana jifanta da kallo. Sannan ya ja trolleynsa da nata ba tare da ya sake bi ta kan Nanna ba ya bi bayanta.
Taxi suka d’auka kasancewar ba wanda ya san da zuwansu sai Mahmah shi kuma ko su Humaid bai gayawa zai zo ba. Gidansu ya so wuce da su amma sai ya canja shawara ya wuce direct gidan Musty inda ya ajiye Hamda kafin su tafi. Ba’a gama gininsa ba shi kuma ba zai je gidansu a wannan daren ba mahaifinsa ya wulak’anta su. Sai da ya tsaya a Eatery ya yi musu take away ya siyi kayan tea sannan suka wuce. Nanna mamakin inda ta ga yace a nufa take don haka ta kalleshi ta ce “Me yasa ba zamu gidan naku ba? Za mu je gidan aro.” Ya girgiza mata kai kawai ba tare da ya yi magana ba. Shi a gaban motar yake yayin da ita da Hamda suke baya. Bakinta ta ja ta tsuke ganin kamar baya son magana. Ga shi ya yi kicin-kicin da fuskarsa.
Kafin ya sallami maigadi Hamda ta shige gidan abinta ainahin bedroom d’in da ta mallakawa kanta nan ta shige kawai ta zube a gadon tana mayar da nunfashin wahala ita kad’ai ta san yarda take jinta bata san kuma me ya sameta ba. Nanna kuwa a parlour ta zube takaicin Hammad ne yasa ta kasa magana tana bin parlourn da kallo duk da tsarin gidan ya yi mata amma ita bata ga dalilin da zai kawo su gidan ba. Ga Gwanar na iya har ta shige bedroom d’in wanda da alama shine babba a gidan. Bari ta zo ta ji su kuma a ina za su sauka?
Yana shigowa hannayensa ya zuba a aljihu sannan ya dubeta “Ya baki shiga cikin bedroom ki samu ki yi freshing up ba?” Ta girgiza kai “Ta ya zan shiga ciki alhali ban san inda zan shiga ba.” Mhmn” kawai ya ce yana tura d’ayan bedroom d’in wanda ya san Hamda bata cikinsa. Kuma shine k’arami don da alama ma d’akin yaran su Mustyn ne suke sauka idan sun zo. Nanna ta shiga cikin d’akin fuskarta a d’aure take bin gadon d’akin da kallo.
“Abu mafi dacewa dai kace da Hamda ta dawo nan, mu da muke mu biyu mu koma can.” “Saboda neman rigima? Ta riga ta shiga na ce ta fito.” Ya fad’a yana b’alle botiran rigarsa.
Nanna ta ja tsuka kawai “Amma ai nan gadon mu yayi mana kad’an?” “Sai ki bar ni ni na kwana da
hamda..”
Haka ya so ya ce sai kuma ya matse ya ce “Ba zai mana kad’an ba tunda dama duk fad’in gado da yalwarsa ba kya barina na sake nanik’ata ki ke.” Ya fad’a yana kashe mata ido da d’an murmushi ya fad’a toilet d’in da Mustafan tuni yasa mai kula da gidan ya sake gyara musu duk da dama ba wani shahararren datti ya yi ba tsaf Hamda ta gyara shi kafin ta tafi.
Tsawon mintuna ya fito d’aure da towel sai