Showing 66001 words to 69000 words out of 117648 words
Chapter 23 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt
kwance yake, balle ta ki matsalar ma mai sauk’i ce, shin ba shi da k’ani?” Wata zufa ta shiga karyo min murya a sark’e na ce “Yana da shi mana.” Ta tab’e baki “Yana da aure?” Na d’aga mata kaya “Ya yi aure da matarsa da yaransa biyu maza” “Shikkenan kin ga ta yarda za ki samu namiji kenan.” Cikin tsoro da firgici na ce “Kamar yaya Zina kike so na aikata?” Ta girgiza kai cikin tabbatar min da zancenta “Zina mai tsafta kenan Zinar cikin gida, hankalinki kwance zaki haifi d’a namiji, ki kuma ajiyeshi a gidan a zuwan d’an gidan ne ya d’ebo kamanni da komai na mutanen gidan, ta yarda ba mai tuhumarki.” Murya har rawa take wajen ce mata “Kady ba zan iya ba, ta ina zan iya janyo hankalin Gadanga?” “Ta kissa da kisissina da zarar kin haihu a lokacin za ki fara kai masa hari idan ya k’i ta lislama sai a biyo masa ta bayan gida. Duniyar nan fa yanzu haka take.” Na yarfe gumin goshina ina girgiza kai idan har na yarda da batunta tabbas abinda zan haifa zai zama JININ D’AN BORNO…
(Ku yi hak’uri idan na samu sauk’i zan k’ara muku yawan typing d’in ciwon kai nake fama da shi ina barar addu’arku. Nagode)
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Cije leb’ena na yi kafin na ce “Zan jingine auren nasa, ta hanyar da shi ma ba zai tab’a zata ba.” Daga nan na gaya mata shawarar da na yanke. Sakin murmurshi ta yi tana dunk’ule hannunta da d’aga min alamar jinjina ta ce “idan haka ne, tabbas sai na ce k’wak’walwarki ta fi tawa ja, kutmelesi ta yaya ki ka yi wannan tunanin? Kin ga shikkenan za ki haifi halastacciyya y’a inda ko nan gaba maganar ta tashi za ki sanar da jama’a da ubanta. Amma fa kin san dole a samo shaidu.” Na jijjiga kai “Shaidu ba matsala ba ne, yanda nake tunanin zan saka Umar ya sake ni cikin sauk’i shine abin ji, amma zan shirya tafiya Jordan don na samo shawara mai b’ullewa.” Ta d’aga kai “In dai shawara ki ke nema, ba sai kin je jordan ba, ki ba shi abin maye ya sha a lokacin sai ki tursasashi sai ya sake ki ki sa kuma ya rubuta a takarda, ta yarda duk bala’insa bai isa ya k’aryata ba, daga nan sai ki ce masa za ki yi zaman iddarki.” Na d’aga mata kai kafin na ce “To ta yaya? Zan zauna a gidansa har sai na yi zaman idda na samu ciki na haife sannan zan koma wa aurensa.” Ta yi jim kafin ta ce “Dole ki san yarda ki ka tsara ki ka sako Ummeey a maganar ita ce zata zame mana garkuwa ta hanyar ce masa za ki yi zaman y’ay’anki, amma fa ki tabbata saki uku ya yi miki, ki yi masa duk tijarar da zata saka dole sai bayan kin haihu kin d’aura aure da wani ko na awanni ne sannan ya sake ki shi kuma ya mayar da ke, duk da auren kisan wuta ba kyau amma a wannan gab’ar dole haka za’a yi, tunda kin san ke ba auren kisan wutan za kiyi ba, already da aurenku da buzu, idan ya rasa wanda zai zab’o sai ki ce ke kina da shi, sai mu gabatar da buzu mai gadi, daman mijinki ne kin ga bai zama auren kisan wuta ba.” Na jinjina lamarin kafin na amince da hakan za’a yi. Yanzu buk’atar yanda za mu shawo kanta da Umar ya sake ni kawai.
Tun daga lokacin na d’aura d’amabar yi wa Umar rashin mutunci, ba lamarin da yake bak’anta masa kamar yarda na yi shakulatun b’angaro da shi a rayuwar auren mu, a kuma duk sanda aka yi magana na kan sanar da shi danginsa ba sa so na ni na gaji da shi ya sakeni kawai. Na sha fad’a masa magana musamman akan mahaifiyarsa, amma ko gezau sai dai ya dinga min hawaye yana cewa na taimakeshi ni ce rayuwarsa.
Ranar muna zaune da daddare na fece wanka sai zabga k’amshi nake, chewingum ne a bakina ina masa taunar rashin arziki. Kawai Umar ya shigo wata ajiyar zuciya ya saki zatonsa daidaitawa nake son mu yi, ni kuwa a zuciyata na yi alk’awarin dole ne ma Umar yau ya sakeni kuma a cikin hankalinsa ba ba wai a maye kamar yarda da muka shirya ba. Ya zauna gefen hannun kujerar da nake yana jifana da murmushi, abin ya tab’a zuciyata amma na share na tsuke fuskata ina cigaba da taunar chewingum d’in da nake. Ya shiga nuna min yarda ya yi kewata amma idona cikin nasa na dinga zabga masa rashin mutunci, ga shi a yanayin da muke dole ya shiga damuwa saboda ya yi nisa ba ya jin kira. A tsawa ce na janye jikina na ce “Umar ban san kai tantirin mara zuciya bane sai yanzu, Haba mutum sai ka ce bunsuru na ce bana sonka bana sonka ka k’i yarda, to yau zan sake jaddada maka idan ka cika d’an halak cikin uwarka da ubanka ka sakeni kuma saki uku ba d’aya ba.” Tunda nake ban tab’a ganin zallar b’acin ransa kamar na wannan ranar ba, fuskarsa ta had’e sosai sai hucin bak’in ciki yake murya a shak’e ya ce “Ko kece Hurul aini na sake ki saki uku..” Ya yi furucin wasu hawaye na zubar masa a k’unci, ya mik’e ya zira rigarsa. Sai na ga kawai ya durk’ushe ya kife kansa a kujera ya saki wani irin rikirkitaccen kuka. Buga kansa yake yana fad’in “Why? Why? Sakna?” Ni kaina a yadarance na saki kukan ina rungumeshi Umar ka sakeni? Saki fa Umar?” Tsam ya rik’e ni a jikinsa sai saukar da numfashi yake yana “Na shiga uku Sakna, ban san me ya shiga kaina na aikata ba, ke kika jawo Sakna.” Ji na yi numfashinsa ya yi d’if alamar ya d’auke. Da sauri na mik’e ina jijjiga shi “please Umar kada mu yi haka da kai don Allah ka tashi.” A diririce cike da firgicin lamarin na shige toilet d’in d’akin na d’ebo ruwa na watsa masa. Sai ga shi ya kawo numfashi mai nauyi, idanunsa cikin nawa ya mik’o min hannu, muryarsa can k’asa ya ce “Allah yasa mummmunan mafarki nake, ba a zahiri abubuwan da na gani Suka faru ba.” Cikin yaudararrun hawaye na shiga gyad’a masa kai kafin na ce “Mai afkuwa ta afku Umar ka sake ni har saki uku? Yanzu mai Zan ce da dangina? Musamman wad’anda dama suka tabbatar min nan gaba sai ka cutar da ni, mahaifiyata dama a kullum burinta kenan ka sakeni, ga shi yanzu ka aiwatar da hakan, duk abinda ka ji na gaya maka ko nake maka, wallahi ba har cikin zuciyata bane, duk na yi ne don in tabbatar da son da kake min. Sai ga shi ka yi abinda muka haramta da juna har abada ko na ce sai na yi wani auren mijin ya sake ni sannan ka ke da damar mayar dani.” Wani irin hawaye Umar ya saki, yana sake ja na jikinsa. Ni kuwa don in sake tunzira shi na ce “Wallahi ka ban mamaki, daga gwaji ta yaya kake zaton ni zan k’i ka? Alhali saboda kai na rabu da dangina da k’asata na zo nan inda ban san kowa ba. Na tabbata yanzu Ummeey ta ji labari ba zata bari mu komawa auren mu ba, cewa zata yi na tattaro na taho. Haka kaima idan Didi ta ji labarin shikkenan ta samu abinda take so.” A gigice Umar ya rungumeni k’am a kunne ya dinga rad’a min “Me yasa kika min irin wannan wasan Sakna? A lokacin da kika san ba zan iya controlling kaina ba, kin san rashin kusantarki babbar masifa ce a wajena, please ba wanda za mu gayawa ya zama sirri a tsakaninmu, idan kin gama idda a sirrance zan d’aura miki aure da mutumin da na tabbata a ranar ma zai iya sakin ki na mayar da aurenmu ba tare da kowa ya sani ba.” Na yi d’an jim har farincikin da yake cikin zuciyata ya bayyana b’aro-b’aro akan fuskata na k’ank’ameshi sosai a kunne na dinga rad’a masa na amince ya zama sirri a tsakaninmu amma ranar girkina ya zaka yi?” Ya runtse idanunsa yana dafe k’irjinsa kafin ya ce “Dole zan nisanci garin nan har ki ka gama idda, ina dawowa a d’aura mana aure, don ba zan iya controlling kaina idan ina ganinki ba Allah ya sani. Auren kisan wuta ba bu kyau amma da mu aikata Zina gwara mu aikata waccan b’arnar. Allah ka yafe mana don girman zatinka.” Ya fad’a yana saka kansa a cikin tafukan hannayena sai ga shi na ji yana wani irin gigitaccen kuka, mai tada hankali. Kafin ya mik’e cikin kasala da mutuwar jiki ya fice daga d’akin yana waiwayena. Nima hawayen ne suka zubo min masu zafin gaske sai na ji kamar ban kyauta ba dama ban aikata son zuciyata ba, amma buk’ata ta da haihuwar d’a namiji shine ya janyo komai. In dai Zan samu cikar muradina to komai na yi gani nake dai-dai ne a lokacin.
Daga ranar muka shiga wata irin rayuwa ni da Umar, ya zama ba shi da walwala ko kad’an. Sannan ya shiga neman visa ba ji ba gani. Idan ba ku manta ba shine lokacin da ya tafi Dubai ya yi zaman sa a can sai dai ya aiko da kaya a siyar masa idan an had’a kud’in a aika masa. Tsawon watansa hud’u a can.
Ni kuma a lokacin ni da Kady muka shiga farautar mai gadi duk da jira nake na gama idda sannan na bayyana masa k’udirina. Amma fa ina yawan yi masa d’inki sannan na dinga sanar da shi bana son k’azanta. Don haka ya rage k’azantar.
Daren da na gama idda, a daren na kira shi na bijiro masa da buk’ata daga ni sai Kady a zaune a falon har rufe k’ofa muka yi.” Tsawon lokaci ya d’auka shiru kafin ya d’ago ya yi min kallon cikin ido. Kady ta kafeshi da ido cikin tsare gira ta ce Saduwa d’aya za kuyi ka zabga mata saki uku bayan mun tabbatar da cikinka a jiKinta.” Na gyara zama kafin nima na d’ora da cewa “ Tun bayan da ka sanar min, yawaitar maza a zuri’arku, na tabbata Allah ne ya kawo min kai don na samu namijin da nake so, amma fa ta hanyar aure ba hanyar zina ba.” Kady ta sake tsareshi da ido kafin ta ce “A gobe muke so komai ya wakana saboda nan da sati biyu Alhajin zai dawo, ban dama an rufe dubai d’in da tuni a yau zai dawo a mayar musu da aurensu. Abinda muke so kafin ya dawo ya zama da tayin cikin namiji a mahaifarta, inda da zarar ya bijiro mata da maganar auren kisan wuta zata sanar da shi ai da cikinsa a jikinta, ka ga ba aure kenan har sai bayan ta haife. Amma fa duniya zata d’auka yes cikinsa ne. Tunda ba kowa ya san da sakin ba, kai ma kuma ya zama sirri a wajenka, don bayyanar sirrin kamar fansar da ranka ne, kuma tunda muka gaya maka sirrin mu ya zama dole ka yi mana abinda muke so. Sannan albishir d’in da zan maka bayan kwasar ganimar jikin tsaleleliyar mace akwai kyautar miliyan biyu cus da zamu maka ka tattara ka koma garinku.” Ya share zufar goshinsa kafin ya d’an saki murmushi ya tabbatar mana da ya amince. A daren ranar Kady da ni da wasu maza a wani k’auyen k’aramar hukumar k’araye aka d’aura mana aure. Sai da muka amshi sunayen shaidun saboda ko nan gaba magana za ta tashi sannan muka taho.
Na biya da shi yarda zai dinga zuwa gyaran kai da hak’oransa. Kady sai tsiya take min.
Bayan kwana biyu Buzu ya dawo tas da shi. A kuma lokacin ne aka yi wata mutuwa a Gwarzo duk gidan suka tattara suka tafi. Na had’a musu har yara na suka tafi da su.
Wannan damar na samu na kira buzu mai gadi na muka keb’ance a d’akina. Bayan na saka shi ya datse gate d’in gidan. Sai dai a rashin sani da tsautsayi sai ga Hammad ya dawo ranar kamar an turo shi sabida ba ya dawowa daga kasuwa da rana. Shi kuma ya riskemu a d’akin wanda ban san dalilin da ya kai shi d’akina a ranar ba. Sai ganinsa kawai muka yi, a lokacin ya turo k’ofar d’akin. Cikin gigitaccen yanayi ya saki ihu, ihun da yaja hankalinmu muka mik’e a firgice ina jan bargo. Buzu yana neman hanyar guduwa….
Jikar Nashe taku ce
❤️❤️❤️❤️❤️🙏
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Cikin Tsoron lamarin na dinga girgiza kaina kafin na mik’e idanuna cikin na Kady da take min kallon shashasha “Ai shikkenan ki je idan kin yi shawara zaki nemo ni da kanki. Kawo wayarki na saka miki numberta” na mik’a mata wayar kasancewar lokacin wayar hannu ta d’an fara zaga gari. Ta daddanna ta saka min numberrta sannan ta rungumeni kad’an ta ce “Allah ya raba lafiya, ni fa farkon ganina da ke na zata ba kya jin hausa wallahi. Sam ba ki yi kama da y’an k’asata ba.” Na jijjiga kai “kin canka daidai ba ni da kowa a Nigerian nan duk dangi suna jordan aure ne ya kawo ni nan.” Ta ce “Ayya insha Allah yanzu kuwa Zan zame miki y’ar uwa in dai kin karbeni da mutunci.” D’aga mata kai na yi kafin nace “Why not? Ina maraba da ke, ni ko sunanki ma ban sani ba muna ta surutu.” Ta girgiza kai “Muna magana mai amfani zaki ce ba surutu ba, sunana Kadija amma an fi kira na da Kady.” Na fad’a mata sunana nima ina tafiya ta rakani har bakin mota in da driver yake jirana.
Tun daga lokacin muka d’inke da Kady ta zame min abokiyar shawara, na ji dad’in had’uwa da ita k’warai da gaske. A hankali ta dinga tunzira zuciyata har na amince da abinda ta ce, muka fara shirin yarda za mu farwa Gadanga da zarar na haifi cikin jikina na yi arba’in zamu fara saka shi a tarko.
Duk da zuciyata tana rawa da tsoro akan amincewar ko rashinta. Tabbas na san ba namijin da zai k’i ya kusanceni a yarda Allah ya kyautata min halittata. Amma ina tsoron bayyana hakan da Gadanga mutumin da ya zamo daga cikin jinsin mutane miskilallu, ta ya zan janyo hankalinsa? Kada na je ya tona min asiri don haka na k’udundune shawarar Kady na saka ta a gefe na shiga neman mafita da kaina. Ba k’ok’arin da ba tayi ba akan na amince da batunta sai dai na ce mata wallahi ina tsoro. Ta gaji ta k’yaleni had’e da cewa idan kin shirya d’aukan cikin namijin ki sanar da ni.” Na d’aga mata kai kawai.
__________
A duk shekara na kan zauna na yi kwalemar kayan bayarwa a d’akina, na kwashi kayan yara da yawa buhu guda da k’atuwar ghana must go, kuma duk sanda na tashi bayarwa masu yi mana hidimar gida nake bawa. Su yi ta godiya suna min addu’oi.
Wannan karon san da na had’a kayan sai na ji zuciyata tana son na bawa Buzu sabon mai gadin da aka kawo gidanmu. Shekararsa guda kenan kuma muna d’an d’asawa da shi saboda yawan kyauta da nake masa. Da na gama tattara kayan sai na sanya Najwa ta kirashi ya d’au kayan gaba d’aya idan ya tashi tafiya garinsu sai ya tafi musu da shi.
Da kirarin da ya saba min ya shigo falon. Cikin harahensu na buzanci “Idan ka ji Kiran Uwar larabawa alheri ne, wannan yaran da izinin ubangiji sai sun zame miki abin alfahari, farar mace mai farar zuciya. Na saki murmushi ina wasa da gashin Munira da take cinyata na ce “Buzu ka bari ka iya hausar kafin ka dinga Yi, ni wani abin ma idan ka fad’a bana ganeshi, tunda nima hausar ba wai ta isheni ba ne.” Ya yi dariya kawai yana kallon kayan da suke zube a gabana. Na ce “Buzu kayana ne da na yara na had’a na ji kace kana aike garinku sai ka aika musu da shi.” Bakinsa ya washe kafin ya ce “Kash ina ma Allah d’iyoyi mata ya bani da sun mori kaya, to tsiyar abin sai dai mutanen gari su mora. Yara na goma sha biyar daga iyayensu mata biyu amma kaf ba wacce ta tab’a haifa min mace duk da so na da haihuwar y’ar d’iya.” Sak na yi ina kallonsa jin furucinsa kafin na ce “Kana nufin kaf zuri’arka maza ne?” Ya d’aga min kansa cike da tabbatarwa “Wallahi Hajjaju nake gaya miki kaf d’insu maza ne guda sha biyar da su masha Allah, haka zuri’ar mu take da wuya ki ga an haifi mace daga yayyena maza har mata kuwa, ina ga d’iyoyi biyu ne mata a cikinsu, shima daga tsatson wata k’anwata, San da aka haifesu ba kiga irin murnar da ahalinmu suka shiga ba. Da zarar kin je Habasha kika ce kina neman gidan Abu rijalun to za’a kai ki gidanmu. Tunda ba b’oyayyu ba ne mu muna da sarauta a garin.” Na tsaya ina kallonsa baki na sake zuciyata da tunani iri-iri a cikinta. Ciki kuwa har da tunanin Allah ne ya kawo min buzu mai gadi don na samu d’a namiji daga tsatsonsa. Idan haka ne kuwa ya zama dole na yi wani abu kafin lokaci ya k’ure min. Na sallameshi ina masa godiya zuciyata cike da farin ciki. Shima ya fice cike da farin ciki.
Tun daga lokacin na gadarwa kaina zama na zurfafe bincike akan yarda zan samu Buzu mai gadi ya amince da buk’atata. Duk da ina k’yank’ayamin kasancewa da shi. Hankalina duk ya tafi akan tunanin yarda zan samu d’a namiji. Musamman ganin yarda Hammad ya girma kuma Komai Umar sai yace sai shi shine babba. Idan na kawo masa maganar Najwa ce babba sai yace ai Hammad shine namiji nan gaba ita kanta Najwan wa zai zame mata ba k’ani ba, musamman tazarar