Showing 75001 words to 78000 words out of 117648 words

Chapter 26 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

masa. Abbun ya d’ago muryarsa a k’asa sosai ya ce “Idan ba zaki iya ba, Ai gwara ki kirawo wanda zai yi, kin barni sanyi yana dukana.” Sai sannan ta lura da rawar sanyin da yake. Hakan yasa ta d’au towel d’in ta fara shirin tsaftace masa jiki ba nuna tausayawa bakomai balle kwantar masa da hankali, wanda a condition d’in da yake bai kamata ace ta nuna masa b’acin ran ba, ta yarda Sakna ta yi mata fintink’au kenan.








**********


Idanunsa a lumshe hannayensa zube bisa k’uncinsa ya yi nisa cikin tunanin da yake, yayinda Hamda take barcinta peacefully bayan ya taimaka mata ta yi wanka. Da gaske lamarin Mahmah yana tab’a zuciyarsa ya rasa ta yarda zai b’ullowa lamarin.


Turo k’ofar da Umma Asma ta yi, shi ya farkar da shi daga zuzzurfan tunanin da ya tafi. Sai dai tana ganinsa ta san tunani yake. Da murmushi a fuskarta ta ce “Sannu Hammad, mun bar ka da jinya,
Sai yanzu hankulanmu suka kwanta Yaya ya farka da lafiyarsa sai dai hannunsa da k’irjinsa da suka yi masa nauyi.” Hammad ya ja ajiyar zuciya yana gyara zamansa, cike da k’warin gwiwa da jarumtar da ya arowa kansa ya gaisheta. Ta yi tsam da ranta tana sake karantar yanayinsa kafin ta ce “Me ya faru ne? Na ganka a wannan yanayin?” Nutsuwa ya yi sosai kafin ya sanar da ita abinda Mahmah ta ce, kafin ya gama tuni duk wani annurin fuskarta ya b’ace b’at, mamakin sauyin Sadiyar take yi, matar da aka santa da kyawawan halaye ta yaya lokaci guda ta rikid’e ta koma haka? Ta ja ajiyar numfashi kafin ta dafa shi “Ka kwantar da hankalinka Hammad, babu abinda zai faru insha Allah, amma a yanzu dai Kada a tursasa mata ta zo tana maka furuci mara kyau, ka bar Hamdan a wajen Didi kafin komai ya lafa, don na san uwarta ba zata rik’e ta ba, tunda har yanzu ma bata zo dubata ba, ka barta a wajen Didi na san ta yarda Zan b’ullowa Didin insha Allah ba za’a samu matsala ba.” Ya amince da shawararta ba don zuciyarsa ta so ba, sai don sanin cewa a yanzu hakan shine mafita a gareshi da Hamdan ma gaba d’aya, takaicinsa d’aya yarda Zai yi kewar Hamdan kafin komai ya lafa. Daga haka ya mik’e ya je duba Abbu ya bar Umma Asma tare da Hamdan da take sauraransu kamar mai barci Sai dai tun shigowar Umman ta su ta farka daga barcin kuma komai suka fad’a a cikin kunnenta. Ina ma Allah Zai bayyana mata ubanta da duk talaucinsa ta bi shi garinsu ta huta da yarda ake ta walagigi da rayuwarta.






____________




Cikin masifa da gadara ta zube idanunta cikin nata, ranta a matuk’ar b’ace take sake jifansa da duk kalaman da suka zo saman harshenta. Da gaske haushinsa take ji sosai tun bayan da ya bayyana Hamda a matsayin matarsa. Kasancewarta mai Tsananin kishi ya sa take sake bayyana haukanta tuburan, yana zaune yana kallonta cike da takaicin rashin mutuncin da take zuba masa “Wallahi dole ka saketa, idan kuma ka k’i sai na bayyanawa duniya Kamla ba y’ata bace a can waje ka je ka yi cikinta ka kawo min ita a ranar da aka haifeta tare da kafa min sharad’in da ka San dole ba Zan k’etare shi ba, ka ce lallai sai na rik’eta na kuma sanar da duniya ni na haifeta idan ba haka ba a bakacin aure na, don haka a yau nake son sanar da ni wacece Kamla?” Idanunsa a firgice ya d’ago yana watsa mata wani banzan kallo…






Jikar Nashe ce.✍🏽✍🏽📄


❤️❤️❤️❤️❤️🙏
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Babu alamar razana ko firgici a fuskarsa, ya sake dubanta ido cikin ido ya ce “Nanna kenan, ba na shakkar ki gayawa duniya ni na yi cikin Kamla na haifeta,
Kamar yarda ban ji kunya ba da aka danganta ni da Hamda, sai dai Zan sake tabbatar miki waccan maganar da na kafa miki sharad’i a kanta tana nan ban janyeba, don haka idan kin shirya karb’ar takardar sallama rubutawa ba zai zame min aiki ba.” Daga haka ya saka kai ya fice ya bar Nanna da wani irin tsoro da tashin hankali, ita kanta ta San ba ta da muhimmanci a wajensa, idan ban da haka me yasa a koda yaushe ba ya jin shakkar furta mata zai iya rabuwa da ita. Ta saki murmushin takaicin yarda ya mayar da ita wawuya ya fice ya barta. A tunaninta zai ji tsoro idan ta yi masa barazana da fallasa waccan sirrin madadin haka sai ta hango dakiyarsa da juriya akan lamarin. Ta tabbata ko fad’an ta yi ba zai damu ba.
Ta zauna a gefen gadon d’akin Mahmahn tana cigaba da tattara kayanta gidansu take son zuwa taga Dida tunda ta zo ba su had’u ba.
Mahmah ce ta tura k’ofa ta shigo d’akin idanunta akan Nanna da ta lura da zallar tashin hankalin da ya mamaye fuskarta, ta d’auke kai ba tare da ta tambayeta ba, don itama hankalinmata ba a kwance yake ba. “Ina zaki? Na ga kina tattara kaya?” Murya na rawa tana ji tamkar ta rusa ihu ko ta huta da nauyin da k’irjinta ya yi, cikin rawar murya ta ce “Gida zani Mahmah.” Tsawon lokaci ta d’auka tana nazarinta tabbas ta hango damuwa kwance a k’asan ranta kuma kamar tana k’okarin b’oye mata wani abin. Ta dafata “Nanna bana son ki saka damuwa a ranki, insha Allah auren Hamda da Hammad kamar na saka an warwareshi da son zuciyarsa ko babu, don nima ba zan so ki yi boranci a gidan aurenki ba, hakan ba zata faru ba insha Allah, kuma zuwa gida a wannan k’adamin ba kama ki ba, kin san dai kina zuwa Dida zata isheki da tabayoyi k’arshenta idan ta ji shirinmu ta ruguza mana tsari da wa’azinta da nasihar da ta saba, don haka ki bari mu aiwatar da komai kawai ta ji labari idan komai ya kankama.” Nanna ta ja ajiyar zuciya tana jin kamar ta gayawa Mahmah waccan sirrin tana tsoron furucin Hammad a kanta, don haka ta ja baki ta tsuke tana jan ajiyar zuciya, shawarar Mahmah itace abar d’auka gwara ta kasa ta tsare har sai ta ga abinda ya turewa buzu nad’i. Zaman aure da Hammad yanzu ta fara, kuma ba zata amince ta yi boranci a gidansa ba. Don haka ta dire jakar had’e da mik’ewa ta ce “Bari inje can sashen namu tunda kin saka an gyara.” “Yauwa maza je ki, kada ma ya samu damar da zai sake zuwa wajen waccan yarinyar, ki tabbata kin janye hankalinsa.” Ta fice tana jin k’warin gwiwa a ranta.






*********
Hamda jiki ya yi sauki har likita ya bata sallama. A kuma rana d’aya aka sallemesu da Abbu bayan an d’ora shi akan magani an kuma zayyana wa iyalinsa dokokin da za su kiyaye masa. Ammi dai tuni ta janye jikinta daga asibitin ganin ba wanda yake marabtar ta har gwara ma Gadanga, amma idanun Didi ma tsoro suke bata, ranar k’arshe da ta zo ta tabbatar mata idan ta sake zuwa a take a wajen zata saka Gadanga ya saketa wannan ne dalilin da yasa su Najwa suka hanata komawa zuwa asibitin. Su dai suna zuwa kuma har Hamda sun je sun duba zuciyoyinsu cike da tausayin yarda ta zamo bare a cikinsu ga shi bata samu tausayin uwa ba. Munira ranar a wajenta ta wuni.


Suna komawa gida Najwa da ta zo daga Abuja ta saka Ammin a gaba da nasiha akan lamarin Hamdan, “Don Allah Ammi ki tausaya mata, ki daina nuna mata k’iyayyar da kike mata, zafin zai mata yawa ki tuna fa ba laifinta bane Ammi, duk ke kika jawo mata wannan matsalar sannan kuma ki kasa janta a jiki ki nuna mata kulawa.” Ammi ta d’auke hawayen idanunta, a karo na farko ta kalli idanunwan babbar y’arta ta saki ajiyar zuciya ta ce “Ni kaina Najwa a yanzu ina takaicin yarda na bazangatar da lamarin Hamda na yi kuma d na sani matuk’a da gaske, amma zallar kunyar Hamda ce ta sa na kasa kusantar ta a yanzu. Kunyarta na ke ji Najwa ban san ya zan mata bayani ta fuskanceni ba, na dad’e ina cutar da ita, cutar da ko d’an rik’o ba zaka yiwa ita ba, tunda nake Hamda bata tab’a jin d’umin jikina ba, ban tab’a mata wanka da kaina ba, balle tsarkin fitsari ko kashi, zan iya k’irga sau nawa na bata mama na ta sha, ban tab’a kallonta na mata magana mai sanyi ba, kullum sai hantara da cin mutunci, da musgunawa, idan bata da lafiya ban san ya take ta warke ba tunda bana kaita asibiti, duk da haka a kullum cikin kyautata min take ko bata da lafiya bata fasa yi min aiki, ni da kaina na san ban kyauta ba Najwa ta ya zan gyara tsakani na da ita?” Kuka ne sosai ya kece mata, Najwa kanta kukan take irin wannan ranar ta dinga gujewa Ammi tun a lokutan baya da take gallazawa Hamdan ga shi ta zo a cikinsu ba wanda Ammin ta bari ya kyautawa Hamdan don a lokacin ma ta sha fad’a musu bata k’i Hamdan ta rasa ranta ba sanadiyyar bak’anta mata da ke. Kuka sosai su ka yi kafin Najwan ta share hawayenta ta dafa Ammin kafin ta ce “Ki nuna mata soyayya, ki jata a jiki ki bata kulawa ta yarda za ki goge wancan bak’in fetin da kika sakawa zuciyarta duk da goguwar tasa zai zama aiki ne ja.” Ammi ta share hawayen, numfashinta da kyar yake fita saboda yarda take kukan sosai abubuwa goma da ashirin sun cakud’e mata, ga rashin ragayyar da ta hango a idanun Abbun ga fargabar sakin da Didi ta ce sai an mata, idan da abinda ta fiso a rayuwarta to rayuwar aure da Abbu ne, jikinta a sanyaye ta mik’e tana jan istigfari a zuciyarta.






**********


Didi na kishingid’e a falonta ita da Lauratu tana matsa mata k’afafunta. Umma Asma da Hamda suka yi sallama cikin falon, a firgice Didi ta mik’e tana kallon Umma Asma da Hamdan fuskarta a had’e ta ce “Asma’u lafiya ko?” Murmushi ta yi jikinta a sanyaye ta shige gaba had’e da cewa Hamda “Shigo mana, Ki ka ja kika tsaya, ko nan d’in bak’onki ne?” Da kyar ta ja k’afafunta ta isa gefen kujerar da Didin take ta d’an rank’wafa da niyyar gaisheta.
Didi ta watsa mata wani kallo ciki-ciki ta amsa gaisuwar ta ta had’e da cewa “Maza ki wuce wajen uwalki, Ai yanzu ba ki da mahalli anan, to fisabilillahi fa, me ye had’i na da ke? Da d’in ma da ki ka ga na jaki a jiki na zata jinin Umalu ce, amma yanzu tunda na gane ba bu abinda ya had’aki da Umalu ma balle kuma ni, son ki a likkafa ki ja sillan k’afafunki ki yi wajen uwalki kafin shi Umalun ya San yalda zai yi da ita, tunda ina nan na zuba ido tai Takina ta bal gidan nan wallahi.” Jikin Hamda a sanyaye ta mik’e da niyyar barin wajen, Umma Asma ta saka baki ta kira sunanta “Hamda, maza wuce cikin d’akinki.” Ganin babu Wasa a fuskar Asmaun Yasa Hamda ta shige ainahin d’akinta na b’angaren Didin. Didi ta saki baki tana kallon d’iyar tata cike da mamaki ta ce “Ba Shakka, Shin Asma’u yaushe kika maye gulbin uwata ba ni da labali? To wallahi ki je ki fice kin da waccan k’anwal shegiyal kafin na had’aku na ci muku mutunci, zancen banza zancen wofi me ya had’ani da ita?” Asma’u fuska a d’aure ta ce “Abinda ya had’aku shine Auren Hammad da ta yi, don haka tilas ba ta da Inda ya fi nan, don Allah Didi ki tausayawa yarinyar nan ki rik’eta, ni fa na san Didin mu mai hak’uri ce, yara nawa kika rik’e a gwarzoma balle wannan da dama ta taso a wajenki kin san dai ballagazar uwarta ba rik’eta za ta yi ba, ga Sadiya da shashanci ta ce Hammad sai ya saketa to ina ki ke so ta je? Ki tuna fa d’a na kowa ne, kuma hakan da za ki yi sai ya zama silar shigarki aljanna.” Didi ta saki ranta musamman ganin yarda Asma’u ta ke sake kambama lamarin tausayi da jin k’anta sai ga shi tana sakin murmushi ta ce “Allah na tuba dama ni me ta yi min? Da Allah ya rufa mana asili ma uwal ta hanyal halal ta samal da ita, zan lik’eta amma ki tabbata kin ja kunnen d’an ki wallahi ba shi ba hanyal nan d’akin kada in ga k’afafunsa dama anan, lokaci na ne nima yanzu wallahi sai na mulza kambuna, ai ni ya yi min daidai da ya rama min abinda ubansa ya yi min ya je ya yi aule ba tale da Sanin kowa ba, ki gaya masa ba shi ba sashen nan te ya take neman aule daga falko idan na ga dama na ta Tadiya dole ta amince ya d’au matalsa idan na ga ba a kyautata min kuma wallahi na bawa wani aulenta.”




Jikar Nashe ce✍🏽✍🏽📄




❤️❤️❤️❤️❤️🙏




Afuwa insha Allah yanzu yara sun samu hutu daga gobe za ku dinga ganin dogon posting nagode.
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Dariya sosai Didi ta bawa Asma’u, ita dai ta yi farin ciki da Didin ta amince da Zaman Hamdan a wajenta, ba ruwanta da abinda za ta yiwa Hammad wannan tsakaninsu ne su gyarota a can. Lauratu kuwa haushi abin ya bata, sam bata so Yayarta tata ta jajib’o musu Hamdan ba, ta so a barta a hannun uwarta ta ga yarda zata yi da ita sai dai bata furta ba ta ja baki ta tsuke ganin sam Asma’un ba wasa a fuskarta.






***********


Sadiya ce zaune a gefensa yana kwance a d’akinsa fuskarsa na bayyanar da damuwa b’aro-b’aro, so yake Yace Sadiyan ta matsa masa k’afa tunda ya tabbatar da Sakna tana nan da ba sai ya rok’a ba ma da kanta zata ja shi jikinta ta dinga matsa masa k’afar tana kuma lallab’ashi har sai ya yi barci, amma ji yarda Sadiya ta saka shi a gaba kawai da kallo fuska ko alamar murmushi babu balle ya hango tausayawa a cikinta, don haka yake ganin da kyar idan zai karb’i shawarar da zuciyarsa take ba shi na rabuwa da Sakna, duk da dai ya san ta yi laifin da dole ya bata saki ko d’aya ne. Ba ya azimi amma Sadiya bata damu da tambayarsa me yake son ci ba, da Sakna ce kuwa sai ta jere masa abinci kala-kala wanda ta San Zai ji dad’in cin su a matsayinsa na mara lafiya.
Ya saki nauyayyiyar ajiyar zuciya idanunsa cikin na Sadiya ya ce “Taimaka a samo min abinci kuma jikina na d’an ciwo ina buk’atar a matsa min.” Ba tayi musu ba ta mik’e dama ita haka take dole sai ya ce ta yi masa abu take yi ba ta san ta yarda zata kula da shi ba, shi kuwa mutum da duk da shekaransu har a yanzu yana son soyayya yana son kuma tarairaya daga wajen matarsa. Ya lunshe ido yana sakin tsaki kad’an zuciyarsa na tunano masa Sakna da halin da take ciki, ya tabbbata duk a inda take tana cikin damuwa.


*****
A d’akinta ta tsantsara had’ad’diyar kwalliya, sai baza k’amshin had’addun turarukan humra take da wanda ta turara jikinta da shi. Buk’atar shiri take da Umar ta kowane hali, ta kashe d’auri sosai irin d’aurin da ta san Umar ya fi so sannan ta jefa k’amsassan chewingum a bakinta, ita da kanta ta san lafiyayyen d’inkin ya zauna a jikinta. Tana gamawa ta d’auki tray d’in peppe soup d’in da ta yi masa na kifi ragon ruwa da ya sha kayan k’amshi. Sai kunun mard’am da ta yi masa.


Daidai lokacin shan ruwa ne ta san ba wanda zata gani a sashen nasa, don haka hankalinta kwance ta murd’a k’ofar tangamemen falon nasa. Shiru falon alamar yana cikin d’aki.


Da siririyar muryarta ta yi sallama kafin ta shiga cikin d’akin, kamar yarda ta yi hasashe kuwa shi kad’ai ne zaune a tsakiyar gado ya yi jigum da alama ya zurfafa a cikin tunanin da yake. K’amshin turarenta shi ya ankarar da shi wanzuwarta a cikin d’akin, da sauri ya d’ago ya sauke idanunsa a kanta. Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyarsa sai dai bai bayyyana hakan a saman fuskarsa ba, madadin haka ma had’e fuskar ya yi ya d’auke kansa daga kallonta. Ta saki d’an guntun murmushi had’e da isa gefen side bed drawer ta d’ora abincin, tana zama daf da shi. Bai yi auneba ya ji hannayensa cikin nata taushi da santsin hannunta yana ratsa shi, murza hannun take a hankali cikin kwarewa tana sake luguiguta shi, duk da k’ok’arin k’wacewa da yake ta hanashi damar hakan. Sai ganinta ya yi zube a k’asa ta d’ora kanta bisa cinyarsa cikin wata iriyar salon murya ta fara bashi hak’uri “Ka yi hak’uri sweetheart na san ni mai tarin laifi ce a gareka don girman Allah kada ka yarda a raba mu, tunda dai ba zina na yi ba ko mai ma na aikata da aurena na aikata shi please don Allah ka yafe min wallahi zuciyata ta kasa sukuni sharrin shaid’an ne.” Ta sake sakin wani irin kuka da yake jinsa har tsakiyar zuciyarsa, ji ya yi kaso hamsin cikin d’ari na b’acin ran da ta sabbaba masa yana zagwanye so yake ya kamota ya sanyata a k’irjinsa amma wata zuciyar tana hana shi, ita da kanta ta yiwa kanta masauki a jikinsa tana ba shi wani irin zazzafan kiss a k’uncinsa murya a dashe cikin kunnensa take sake rad’a masa please ka yafe min ka san kai ne rayuwata wallahi ba zan iya rabuwa da kai ba, son haihuwar d’a namiji ita ta jawo min gurb’acewar tunani. Luf ya yi a jikinta cikin wani irin yanayi na kissa da bata tab’a yin amfani da shi ba ta saukar masa da b’acin ransa. Daidai lokacin da Sadiya ta turo k’ofar ta shigo idanunta ya yi kyakykyawan gani, da sauri ta saki tray d’in da yake hannnuta hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login