Showing 6001 words to 9000 words out of 117648 words
Chapter 3 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt
shiga ta yiyo sannan ta ɗauro alwalarta ta saka tsaleliyer atamfarta da Didin ta ɗinko mata kaya ne kala goma dama ta saba duk sanda zata zo sai tayi mata don ta san kafin tazo nata sun mutu tunda ba wata sutturar arziki uwar take barinta ta saka ba.
Idan ka shigo gidan ma zata zaka yi ƴar aiki ce, Saboda tsabar yarda zaka ga kayan sun ƙojale don tsufa ga kanta da baya samun cikakken gyata fatarta ma don dai Allah yayi ta cikin jinsin mutane masu taushin fata ne, da duk wahala bata jemewa tabbas da ba ta kai haka kyauba.
Tayi kyau sosai ɗinkin kuma ya zauna a jikinta tamkar ba daga ƙauye aka ɗinko mata su ba. Ta cukuikuye gashinta ta danna cikin ɗankwali don rabon da ta tajeshi har ta manta balle ta saka man kitso, ko wanke shi tayi haka take barinsa.
A gefen Didi da take lazimi da jug ɗin furarta a gefe ita ma ta tada sallahrta cikin nutsuwa. Sai da ta idar tayi addu’ointa Didin Ta tura mata cup cike da fura tace “Maza kwankwaɗeshi tas ki bani cup don na san waɗannan mashiriritan kafin su kawo abin karyawa sai goma ta gifta shi yasa wannan karan zan saka ya kawo min kayan abincina kaf da kaina zan dinga girki ba zan iya zaman jira ba, girkin da sai an ga dama sannan ake yin mai daɗi ko a zabga mai da maggi to bana ba dani ba kowa ta riƙe banzan abincinta."
Ita dai Hamda murmushi ta saki kawai tana kai cup ɗin furar bakinta. Ta shanye tas zuciyarta cike da farin ciki. Har zata kishingiɗa ta kwanta sai kuma ta miƙe ta ce "Didi baki ba ni labarin ba." "Ƴar nema ashe kina so bari mu ɗan runtsa tunda yau ba islamiyya sai na baki anjima yanzu kam idanuna har yaji yake.” Duk da ba haka ta so ba haka ta hakura don ta san idan ta matsa Didin zata iya cewa ta fasa.
________________________________
Ammi na fitowa ta ga parlournta tsaf sai baza kamshi yake da sauri Ta isa bedroom ɗin ƴan matanta don a tunaninta su suka yi sharar tunda Ta san Hamda na can ɓangaren Didi turus tayi ganinsu sheme suna barci har Muneerahn da take zaton ita tayi.
Jikinta a sanyaye ta juya don ta tabbatar Hamdan ce dai tayi, wani abu ya Tsirga a ranta mai kama da tausayin uwa ga yaranta, sau tari tana tunanin sassautawa Hamdan sai dai tuni shaiɗan yake rinjayar zuciyarta wajen tunanin Hamdan a matsayin wata tashin hankali ce wanzuwarta a rayuwarta, mutuwarta a zahiri ita tafiye
Mata alheri shi yasa take takura mata ko don wataƙil zuciyarta ta buga ta rasu ta huta da baƙin cikinta, don tabbas idan Hamda bata mutu ba nan gaba kaɗan akwai tashin hankalin da bata so ya afku tana da rai wanda zai zamo tamkar tozarci ne mai girma a gareta da zuri’ar D’an Borno gaba d’aya.
Ta sha auna kashe Hamdan a ranta sai dai tana fasawa gudun fallasuwar asirinta da kuma tonuwar sirrin da ta riga ta bisne a cikin ƙasa.
Ta ja ajiyar zuciya bayan ta zauna ta nutse a cikin kujerar three seater ɗinta samfurin royal da take girke a babban parlourn, idanunta akan tv tamkar mai kallon labaran da ake yi sai dai gaba ɗaya zuciyarta ta Lula can tunanin wani zamani da ya shuɗe.
_____________________________
Barci sosai su kayi bayan idar da sallahr walahar akan faffaɗar daddumar Didin mai laushin tsiya da take ambula mata turare kullu yaumin don son tsaftace wajen ibadartata da yake can kusurwar ɗakinta.
Bugun ƙofar da ake yi ne ya farkar da su daga barcin Hamda ta miƙe don taga waye itama Didin miƙewa tayi tabi bayanta da hanzari don bata da jiki ko kaɗan shi yasa bata jin nauyin jikinta.
Saliha ce mai aikin Mahmah ta shigo hannayenta ɗauke da manyan warmers bayanta kuma Humaid ne yake biye da ita da flask ɗin tea. Didi ta dinga amsa gaisuwarrsu tana girgiza kai haɗe da duba agogo "Ba shakka, wannan abincin da mai za'a kirashi kenan na safe ko na rana? Kai jama'a ayi mata da shegen lalacin tsiya, to ni ba zan yarda da wannan tujarar ba bari wanda ya ajiye su yazo na faɗa masa ya jawa matansa kunne dama kada wacce ta sake ɗora sanwarta dani, su riƙe abincinsu can, zan dinga yi da kaina naga acan gwarzon ma da kaina nake yi to name za’a dinga wahalashsheni Allah na tuba abincin ma da ba ɗanɗanon arziki."
Ta faɗa tana buɗe coolerr abincin faten dankali ne da ya sha busashshen kifi da alayyahu sai ɗaya coolerr farfesun cow-tail ne ɗayar kuma gurasar larabawa. Baki ta taɓe,dan ta tabbatar dai abincin ba makusa sannan ta ce Hamda ta kwaso plates ta zuba musu.
"Ku tashi kuje ku ke kallona kamar kun samu akwatin kallo, kai kuma me ya hanaka zuwa makaranta." Humaid da yake duk a tsorace da faɗan tsohuwar ya ce "Hutun independent day muke." kallo ta watsa masa kafin ta ce "Wani abu ne kuma indafadan?" Ba Humaid kaɗai ba har ta Hamda sai da ta tuntsire da dariya Didi Ta ce “Kaji min aikin banza faɗar tawa kuke wa dariya? Aikin kawai to turancin faɗar annabi ce da sai na iya? ka tashi kaje kace ina son ganin ubanka tunda gaisuwar ma sai na roƙa." Humaid ya fice yana dariya Ƙasa-ƙasa a zuciyarsa ya ce "Drammer Queen"
Abincin suka ci sosai kafin Hamda ta kai kwanukan kitchen ta ɗaurayesu sannan ta dawo.
Man zafi ta ɗauko tana shafawa Didin a ƙafarta. Didin ta ce Alhamdulillah tunda ciki ya ɗauka bari na baki labarin asalinmu ciki da bai, da yarda aka yi auren uwarki da ubanki ba bisa son raina ba.....”
_____________________________
Asalin kakanku haifaffen garin maiduguri ne kasuwanci ya kawoshi kano Ƙauyen Gwarzo, inda anan Allah yayi arzikinsa yake kuma anan ya had’u dani ya aureni har muka hayayyafa duk a Ƙauyen Gwarzo. Haihuwata sha huɗu sai dai a ciki huɗu ne suka rayu mahaifinki Umar ne babba sai Aliyu kafin na haifi Aliyu kuwa yara uku na haifa tsakaninsa da mahaifinki sai dai basu zo da rai ba.
Daga Ali gadanga ƙusar yaƙi sai Gwaggonku Asma'u da take zaune a can ƙasar dubai da mijinta daga ita kuwa haihuwa biyar nayi ba rai kafin na haifi autata lauratu wato Ammanku Ta Janbulo daga nan ne fa haihuwar Ta tsaya min bayan nayi biyu ba rai. Ni kad’ai ce wajen kakanku Usmanu dan Borno bai sake aure ba duk da baloƙoƙon da danginsa suke masa wajen son ya ƙara auren acan gida borno har mata aka bashi amma yace ya yafe ni kad’ai na isheshi tunda ina yi masa duk abinda yake so baya son yazo ya had’a tashin hankali a gidansa yana zaune lafiya.
Haka suka gaji suka zuba masa ido duk da surutun da suke masa yasa auduga ya toshe kunnensa ya ce ba zai ƙara aure ba. Ni nan da kike gani na macece mafaɗaciyar gaske da ba na barin ta kwana in dai ka takaleni ka taɓo masifa bana shiga shirgin kowa amma fa bana yarda a taka ni. Hadizatu nake mutane da dama suna kirana wargi kike dai-dai Ƙugun kowane ɗan iska. Shi yasa duk garin Gwarzo in dai kika je kika ce kina neman Didi matar D’an Borno to kin gama samu na saboda shaharar da nayi a masifa, wanda bakomai bane sai zallar fad’ar gaskiya da mutanenku basa so yanzu.
Ko iyayenki Shakkata suke, saboda bana sakar musu fuska kamar yarda Kakanku yake sakar musu. Ba yabon kai ba dole Kakanku ya kasa aure sabida na riga na siye zuciyarsa da girki tunda shi in dai cikinsa zai d’auka to kin gama masa komai, idan kinga masifarsa to ya dawo gida ban gama abinci ba. Sannan ba yabon kai ba ina da tsafta dai-dai gwargwado, ga kwalliya kamar me don idan na cab’a kwalliya irin Ta mutanen da baki ga yarda yake zama yayi ta kallo na ba, na tabbata da yanzu zan yi wannan kwalliyar wasu ma mahaukata za su d’aukeni. Idan kuwa kika shigo gidana ba abinda zaki fara jiyowa sai k’amshin turaren wuta da na tsinke d’an Borno, don sana’ata kenan duk da ba wani ciniki nake ba kasancewar jama’ar garin mu basu damu da k’amshi ba. Ke na fa zabga iyayi ina yarinya Wani suna suke kira na da shi Delu iyayi har na haihu Umaru ya cigaba da kira na wai Delu, bisa tilas na koya masa cewa Didi shikkenan sai sunan ya bini. Idan kakanku yayi fushi wuyartana shafe baki na da jan jambaki nayi d’igo-d’igo a gefen k’uncina na ja siririyar jagirata, na bad’e fuskata da hoda pankeke shikkenan zaki ga ya daina fushin yana bina da ido yana fad’in Indiyana ni kuma kaina yana kumbura duk da ko a layin bak’ak’en India ba za’a saka ni ba, gashinta k’ak’k’arfa ne irin na hausawa, haka nan ba wani idon arziki gareni ba ga ni bak’a kamar yarda kika ganni d’in nan, amma don son ran kakanki yake kira na Indiyana ni kuma ina amsawa Cike da izzar nafi sauran mata, duk da wani ko a k’afa aka k’ulle masa ni ina tabbatar miki sai ya kunce ya arce ni da y’ar dab’as... wata dariya ce ta kufcewa Hamda, ganin duk suffofin da ta zayyana
Haka zubinta da fasalinta yake, sam bata da tsaho ko kad’an...
Hajiya Didi tamu....
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE
YA ABIN YAKE ?
LIttafin Nazeefah Nashe.
08033748387
Follow me on ArewaBooks
@nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e
✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽
ELEGANT ONLINE WRITERS
(Haɗin kai shine takenmu.)
Page 5
Ina macen datake fama da ciwon mara in mijin yana saduwa dake kirinka jin xafi to kixo kimallaki female care
Ina masu fama da basir constfree tea yana magnin basir yana gyara fata tayi kyau
Royal jelly ya gyara mace yafito mata da shafe dinta kama daga breast hips duwawo
Fat bunner yana rage kitse ina wanda kitse ya mata yawa a jiki kigarxayo kimallaki naki 09131164861
Gamai bukatan yin register xai iyayi yasaya afarashin company
Company ght zakiyi registered akan 4500 kikawo mutun biyu suyi siyaya company zatabaki 36000 inbaki shiryaba karkimin mgn ngd
****************************
_Mu d’in ba wasu masu wadata
bane sai dai muna cikin ni’imar ubangiji, don bamu rasa ci ba, bamu rasa sha ba, Kakanku a tsaye yake sosai akan iyalinsa ta yarda duk abinka baka isa ka hango gazawarsa ba, ya tsaya sosai musamman ga karatun iyayenku, burinsa a kullum bai wuce yaga sun samu nagartaccen ilimi ba, na boko da na muhammadiyya, Musamman Babanki Umar. Sanda ya gama secondary School Allah ya taimake shi har jami’a yaje can zaria inda yayi karatunsa a ‘bangaren Zane-Zane kasancewarsa mai hazaƙa wata rana kawai yazo min da labari mai dad’i wai Gwamnati ta d’au nauyin karatunsu ‘kasar waje can ‘bangaren larabawa ‘kasar Jordan zasu je su yi babban degree a can. Mun yi murna sosai sai dai Kakanku ya ce bai isa ba, ba zai tafi ba sai da aurensa, amma mahaifinku ya turje ya kuma kawo uzurin gwamnati tace ba zata d’au masu mata ba saboda ba zasu d’au nauyin mutum sannan su d’au nauyin iyalinsa ba, har da ce mana sunce sai dai ya hak’ura Haka dai dole muka k’yaleshi ya tafi ashe tafiyar zata zame mana jangwamgwam domin dai a can ya had’u da alak’ak’an uwarki ya aura.
Tafiyarsa da wata uku yayi mana aike akan ya samu mata zai yi aure a can. Ai kuwa na rufe idona na ce bai isaba, hakan ya tashi hankalinsa sai gashi ya dawo k’asar ba shiri lokacin watansa shidda da tafiya. Da Allah da annabi da saka malamai suyi mana wa’azi muka amince da yayi auren amma da sharad’in ni da kakanku zamu je muga tushe da asalin yarinyar. Bai wani damu ba ya ce mana ya yarda. Nan muka fara cuku-cukun tafiya kakanku ya siyar da gonarsa d’aya muka tafi har da k’aninsa da suke ciki d’aya wanda kuke kira Baffa Mamman.
Mun samu tarba Ta mutunci daga iyayenta,babu aibu sam a tattare da su dattawa ne sosai, don shi kansa Umarun a gidansu yake zaune kuma yana d’an aiki a kamfanin mahaifinsu mutumin kirki shima daga Nigeria yaje karatu sai ya had’u da uwarta mutuniyar Jordan d’in ta nuna bu’katar aurensa shikkenan zamansa ya koma can don haka da yaga Umar bahaushe ne ya ja shi a jikinsa,
ya shiga farin ciki, ko da yarinyarsa ta nuna tana sonsa take ya amince ya bashi aurenta.
Hankalina ya kwanta da naga ubanta bahaushe ne, kuma har kwatancen gidan su yayi mana a garin Niger (Minna) cikin unguwar limawa nan ce mahaifar Kakanku na wajen uwa, ta daina muku fankamar wai asalinta balarabiya ce, asalin uwarta dai.Kakanku ya ce zai bincika ya gani, ai Niger ba bak’on waje bane a wajensa.
Ba mu dawo ba sai da aka d’aura auren, amma jikina ya yi sanyi da na lura da uwar Sakina ce take kula da al’amuran gidan shi uban nasu ba shi da ta cewa sai abinda Ta d’aurashi a kai, kuma yarinyar da naji suna kira Sakna ni ce nan na mayar mata da sunanta Sakina har yanzu a garinsu Sakna ake kiranta, kaf halayen uwarta ne a tare da ita bata ganin mutane da gashi. Gaisuwa kanta sai taga dama take min gashi iyayen suna ji da ita tamkar masifa ko don itace babba.
Satinmu biyu muka baro garin daga nan umara muka wuce, na kuwa dad’e a d’akin Allah ina kaiwa Rabbil Izzati kukana akan aurennan na ubanki don sam zuciyata ba wai ta gama yarda da auren d’ari bisa d’ari bane, na yarda ne dai don Malam yafi ‘karfina.
Dawowarmu Nigeria muka dinga zuba idon ganinsu sai dai kamar mun shuka dusa ba amo ba labarinsu.
Hankalina ya tashi matuk’a da gaske ga gari ba kusa ba kuma lokacin wayar hannu bata zo ba iyakaci ta landline ce shima ba waje mai nisa ake kira ba.
Ganin tashin hankalin nawa ya yawaita hakan yasa Malam ya shiga addu’a da a lokacin ake kiranta addu’ar kiranye. A lokacin har aka yi bikin k’anwarsa amma bai dawo ba. Na haifi autata lauratu shima bai dawo ba.
Kwatsam wata rana muna zaune da hantsi sai ga sallamarsu ina d’aga Kai suna shigowa da hakimar uwarku tana wani cin magani tana yatsina kamar ta shigo gidan da ake tsubire himulin kashi, ba mu bi ta kanta ba muka shiga murnar ganin Umaru da duk yayi ‘kiba ya zame min babban mutum kuma duk da a lokacin ko shekaru talatin bai rufa ba. Na shige rumfa ina musu lale marhabin ku shigo mana. D’aki na tsaf yake duk da dai ba kujeru amma malale yake da sabuwar leda sabuwa dal don mun fara shirin azimi daga gefe kuwa fanka ce Ta tsaye sai dadduma da tum-tum irin na gidan sarauta.
kuma bana mantawa a lokacin k’amshin turaren tsinke yake da na kukkunna a duk wata kusurwa da take d’akin, ya kuma sha Fenti da farar k’asa kamar yarda malam yake k’o’kari duk shekara a watan sallahr tsofi yake shafe gidan da farar k’asa.
Duk da wannan abin amma Sakina yamutsa fuska kawai take, ta d’ofana d’uwawunta akan tum-tum d’in da yake gefe sai sannan Umar ya kalleta ya ce “Ki gaisheta mana.” Fuskarta kamar ta zunduma ihu cikin gwarin hausarta da ko fita bata yi a lokacin ta ce “Ina kwana?” Ina murmushi na ce mata “Lafiya k’alau Sakina.” Ji nayi tana masa magana da turanci ban dai fahimci abinda tace masa ba amma tabbas naji ta ce Sakna da Sakina a cikin zancen nata. Sai naga yayi murmushi ya ce “Didi sunanta ba Sakina ba Sakna sunanta.”
Na kuwa daddage na jefe shi da umbola na ce nak’i nace Saknan ka gaya mata ba zance ba Sakina zance Au nan k’arata Ta kawo don rashin Ta ido? gaisuwar ma ina ce sai da kace ta gaisheni, kai Umaru!ni dai ka tak’aitan da ba ka auro mai jin hausa ba balle ta fahimci masifar da nake mata ja’ira fuska kamar jan k’osai.” Kallona kawai take tana ta’be baki ni kuwa na mik’e ina kallon Ummaru da yake ta guntse dariyarsa nace “Sai ka kawo mana bak’uwa ba sanarwa yanzu mai kakeso mu bata? Ga d’akin naku ma ba a gyare yake ba.” Na k’walawa Ali kira yana zuwa nace “Gadanga sai ka tattara kayanka ka dawo d’akin nan na tsakargida sai a gyara musu can d’in tunda d’aki ne da rumfa har da makewayi a ciki.” Ali cikin farin ciki ya shiga aiki ma’kota kuwa tuni aka fara shigowa ganin Amaryar Ummaru ana mamakin yarda ya auro balarabiya sai da nayi musu jan ido sannan suka fice na saka sakata a Zauren gidan ina sake tsinewa k’auyanci banda haka meye na dandazon zuwa ganinta abinda gobe zan saka ta zaga gida-gida su gaisa dasu.
Abincin da muka yi na rana shinkafa da miya da salak na juye musu kaf na bawa gadanga ya siyo kifi sukunbiya na saka musu, har da dafaffen k’wai wai duk don na karramata. Na zuba musu zo’bo mai sanyi har da fura da yake ina siyarwa k’aton firiza ne dani a tsakrgida, nake sararwa da mutane zo’bo da fura mai sanyi kuma cinikin ya kar’beni sosai.
Reras na jere musu langunan abincin har da cokula na sababbi gal dasu.
Umaru yayi saurin jan tray d’in abincin ya fara k’o’karin zuba musu, gani nayi tayi wuf Ta ri’ke hannunsa tana girgiza masa kai sai kuma naji tana ambaton hotel da nuna masa lokaci ta hanyar kallon agogo. Sai naga ya mayar da abincin ya rufe yana sakar min murmushi ya ce “Didi ai wucewa ma masauki za muyi mun riga mun kama d’aki a hotel.” Ban san sanda bakina ya zunduma masa zagi ba nace “Ba Otel ba Otalo kai har kayi kud’in da ba zaka iya ajiye iyalinka anan ba? to wallahi baka isa ba nan d’in da take ‘kyama anan zata zauna ba gidan uwar da zata je, ina kallo da ma tun d’azu kallon rainin da take wa gidannan to ka gaya mata nan kwana nan yini don uwarta ba inda zata je