Showing 51001 words to 54000 words out of 117648 words

Chapter 18 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

d’in. Ta yi saurin janye wa “Please Yaya Hammad sanyi” cikin mamaki ya saka hannunsa a jikinta ya ji zafi rad’au da sauri ya ce “Kai me ya sameki yanzu-yanzu?” Ba bakin magana sai kakkarwa take tana k’ok’arin sake k’udundune jikinta. Shiga cikin bargon ya yi ya jata jikinsa sosai ya rungumeta yana lalubar kiran Doctorn da zai zo ya duba ta. Shafa gashinta kawai yake yana sake gaya mata wasu dad’ad’an kalamai “ sannu kin ji zuciyata mhmn ni ne ko? Ki yi hak’uri sweetie ba zan sake ba.” Shi kansa wasu abubuwan bai san yana fad’a mata su ba. Jin sa a jikinta ya d’an lafar mata da zazzab’i sai dai bata daina jin zafin da take ji a k’asanta ba.




Da kansa ya shigo da Doctor d’in ya bata magani har da allura da sai da ya matseta sosai a jikinsa yana hura mata kunne sannan ta yarda aka yi mata allurar.
A jikinsa barcin wahala ya d’auketa yana ta aukin shafa bayanta kamar k’aramar yarinya. Shi kansa barcin ne ya d’aukeshi cikin annashuwa da tarin farin cikin da bai tab’a risksr kansa a ciki ba.




Kiran sallar azahar ne ya farkar da su. Ita ta fara tashi ta bud’e idanunta da suka yi mata nauyi kad’an ta zubesu akan fuskarsa mai tarin haiba da nutsuwa. Ta saki murmushi tana ji tamkar ta sa hannu ta ja pointed nose d’insa. Sai ta ga ya bud’e idon ya zuba mata idanunsa cikin nata yana sakin murmushin ya jata jikinsa “Kwanta ki huta Nuri ta” ta k’udundune kanta a k’irjinsa a hankali cikin matsananciyar kunya ta ce “Sallah” Da sauri ya mik’e yana duban agogo sam ya manta da d’auko su Kamla a makaranta. Shi ya ja su Jam’i suka yi Sallah sannan ya kalleta ya ce “Bari in d’auko yara a makaranta mai zaki ci in siyo miki.” Girgiza kai ta yi kawai ta ce “Bakomai zan sha tea”


Da kansa ya je kitchen d’in ya had’o mata tea mai kauri ya kawo mata. Da kyar ta runtse idonta kafin ta shanye. Ganin yanayin jikin nata yasa ya yiwa Musty waya akan ya taimakeshi ya d’auko su Kamla cikin dariyar shak’iyanci ya ce “Ka tafka tsiyar kenan an samu y’ar shila.” Tsaki Hammad ya ja kafin ya ce “Allah ya shiyeka saura idan ka je d’an banzan surutunka ya sa ka gaya mata na yi aure ba yanzu nake son ta sani ba.” Musty ya ja tsaki “Ni fa ban ga dalilin b’oye mata ba, ka sanar da ita kawai Malam ai ba ita take aurenk ba.” Bai jira abinda zai ce ba ya katse wayar Hammad ya dafe kansa tunani fal ransa kada Musty ya jik’a masa aiki shi ba yanzu yake son sanr da ita ba.






Musty na parking Nanna ta fito daga gidan mamaki da fargaba fal ranta saboda hakan bata tab’a faruwa ba wani uzuri bai tab’a saka shi k’in d’auko mata yara a makaranta ba. Ta daure ta k’arasa cikin fargaba ta ce “Lafiya Musty ina the Dear na na ga kai ka d’aukosu” “Yana wajen amarya mana"




Kash!
Ga dai Musty zai jik’a aiki y’an normal group mu tara gobe




Vip da special mu had’u anjima.




Jikar Nashe ce.
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Sosai hantar cikinsa ta kad’a da tambayar k’wakkwafin da ta jeho masa. A hankali ya yi k’ok’arin matsewa ta hanyar jan hancinta “Idonki bai lura bane, sau tari ina tafiya da kaya office na dawo da wasu musamman idan lokacin damuna irin wannan ya kama lokacin ruwan sama. Turare kuwa may be hancinki ne ya ji.” Ta d’an saki ajiyar zuciya kad’an duk da ba wai ta amince da abinda ya ce bane zuciyarta tabbas tana wasiwasin lamarin. Cikin tsare gira sosai ta ce “idan ma wani abu ne a ranka ka tattara shi gefe ka ajiye don ba zan amince ka yi Aureba balle na yarda da kwamacalar had’a shimfid’a da
Wata mace.” Ya bi idanunta da kallo ya tabbatar iya zallar gaskiyarta ta fad’a tabbas nan gaba kad’an ashe za a kwashi drama don ruwa da iska ba mai saka shi rabuwa da Hamda ko a da ma balle yanzu da ya kwankwad’i zallar madarar dad’i daga gareta.
Murmushi kawai ya sakar mata yana sauka daga gadon. Burinsa ya je yaga Hamda sai dai ya san bai isa ba a wannan lokacin don haka tilas ya hak’ura.






Sai yamma bayan ya d’auko yara daga makaranta. Sannan ya sake shirinsa bayan ya yi wanka ya sameta a d’akinta. Zaune take a gaban mudubi tana sake tsantsarawa kanta kwalliya sam Nanna bata gajiya da kwalliya lamarin son kwalliya a jininta yake. Ya saki murmushi yana k’arasawa bakin mudubin. Ta jikin mudubin ta dinga masa kallon mamaki. Yana k’arasawa ya dafa kafad’unta yana kallon kansu ta jikin mudubin murya a raunane ya ce “Kin yi kyau sosai M. Khairi.” Bakinta ta d’an turo kad’an kafin ta tab’e bakin ta ce “Sai ina kuma naga ka fece wanka?” Ya shafa gefen kumatunsa ya yi kalar tausayi “Am sorry dear, kin san abinka da d’an k’wadago yau ma kwanan office d’in Zan yi.” Wani kallo ta jefe shi da shi na kada ka raina min hankali sannan ta d’auke kanta fuska a d’aure ta ce “Dear bana son fa rashin gaskiya, shekararka nawa a office d’in baka tab’a aikin kwana ba sai yanzu ka tsiro min da zancen aikin kwana.” Wuyanta ya murza a hankali cikin kwantar da murya ya ce “To ya zan yi? May be nextweek ma za mu wuce Nigeria insha Allah, ina tunanin su Khairi ma a gidan Musty zan bar su.”
Baki sake take kallonsa ta ce “Nigeria kuma? For what reason duka-duka how many days rabonmu da k’asar ni sam wallahi ko sunanta bana son ji balle shiga cikinta nan kwana kusa.” Ya girgiza kai cikin mamakin furucinta ya ce “Me yasa? Ke da k’asarki ta haihuwa?” Ta girgiza kai “Abinda ya faru ba k’aramin girgiza ni yayi ba shi yasa sam bana son sake ziyartar k’asar nan kwana kusa” yana jan jelar gashinta mai tsananin sulb’i da k’yalli ya ce “Ya zame miki dole ki je don kira ne daga Umma Asma’u na gaggawa akan wancan maganar da kike gudu, na fi son a yi komai a gabanki ki zama ready nan da 5 days.” Daga haka ya saka kai ya fice yana fad’in take care. Idanu kawai ta bishi da shi zuciyarta cike da d’imuwa gani take kamar a tsukun lokacin a canja mata shi ganin yarda yake walwala da farin ciki tamkar sabon Ango da sauri gabanta ya buga da tsoro dafatan kada Allah ya k’addara mata ganin ranar da za’a yi mata kishiya. Ta girgiza kai tare da runtse ido ita kanta bata hasasho kalar haukan da zata yi ba.








__________________


Cike da nishad’i da walwala ya kutsa kansa cikin falon. Bakinsa d’auke da wak’ok’in soyayya na larabci. A kwance ya ganta fuskarta a had’e duk da ta sha kwalliya cikin wasu matsatstsun English wears da suka bayyana tsantsar kyawun dirin jikinta. Amma sam fuskarta ba walwala idanunta kuwa sun nuna alamar ta sha kuka don sun d’an kumbura. A tunaninta tunda ta ji shiru ba zai dawo ba duk da dagewar da tayi ta tsantsara masa girki mai rai da motsi. Amma ta ji shi shiru tun safe daga cewa bari ya kai y’an makaranta ya dawo. Zama ya yi daf da ita sosai yana janta saman jikinsa “Me ya faru Nuri?” Ya rad’a mata a kunne “Ko missing d’ina kika yi?” Samun kanta ta yi da d’aga masa kai tana k’udundune kanta a jikinsa. Ya saki murmushi yana k’ok’arin d’aga fuskarta ta runtse ido kafin ta ce “Ni ka kyaleni bayan ba ka damu da ni ba ka yi tafiyarka ka bar ni.” Murmushi ya ja yana kaiwa lab’b’anta sumbata tuni ya kashe bakin tsiwar ta yi muk’us kafin ya d’ago yana jifanta da murmushi “Tarbar da ya kamata ki yi min kenan, amma kin tsaya shagwab’a. Idan mace ta yi missing mijinta kyakykyawar runguma take kai masa ba k’ananan mita ba. Ni haka matata ta saba min.” D’if ji da ganinta suka d’auke saboda tsananin kishi ta zare jikinta a hankali ta koma gefe idanunta na shirin zubar da ruwa. Yana murmushin ya sake damk’ota, tana tirjewa ya d’aga ta cak “Bari na je na baki hak’uri a d’aki mana. Kin ga idan na tada miki da mikin jikinki kya tuna ni mijinki ne ki dinga girmamani.” Bakinta ta turo tana kicinyar k’wace jikinta ta sauka da kyar tana tirjewa da bubbuga k’afa “Haka kawai sai ka dinga min zancen matarka ka san yarda zuciyata take ji.” Kallon mamaki yake binta da shi ya kuma tabbatar iya gaskiyar furucinta kenan. A yarda yake hangowa ma kamar Hamda ta fi Nanna kishi ashe akwai aiki ja a gabansa. Cikin tsokana ya ce “Tab, amma fa Nuri kin d’auko da zafi ki aure mata miji kuma ki dinga kishinta? Ita kuma ya kike so ta yi? Da kika kwace mata ni ya zama dole ki rage kishin nan don har yanzu Nanna bata san na aureki bane da kin gane kalar kishinki bakomai bane akan nata. Shekarar mu kusan nawa ko gado ba ma rabawa sai ta kama dole ko haihuwa ta yi bana yarda mu raba d’aki. Kullu yaumin manne take a jikina.” Wannan karan Hamda ji ta yi kamar kanta yana son darewa biyu da sauri ta runtse idonta cikin b’acin rai ta ce “Ka san da haka wa ya ce ka aureni me yasa baka bari zunnuraini ya aureni ba? Ko kuma ka kyaleni na samo mijina ba mijin wata ba.” Da sauri ya d’alle bakinta cikin jin zafin furucinta ya kuma manne ta da jikinsa yana ganin kamar wani zai kwace masa ita. Haushin lafazinta ne ya sa ya dinga datse leb’ensa ya kuma kakkafe ta da idanunsa “Kada ki sake min kwatankwacin wannan furucin. Shi kansa Zunnurainin ji na yi kamar na harbeshi san da na ganku kuna zance. A zuwansa na biyu kuwa da kaina na sameshi na ja kunnensa akan cewa an miki miji ya ja mutuncinsa. Ta yi lamo a jikinsa tana jin yarda yanayin bugawar zuciyarsa ya sauya ashe shima dai yana kishinta ba ita kad’ai take kishinsa ba. Shafa kanta ya yi ya jishi cunkus alamar yau bata taje ba.
Ya ja gashin sosai kafin ya ce “Dole gobe da kaina na kai ki saloon a gyara gashin nan ya yi tauri da yawa ba irin na Nanna bane mai taushin gaske.” Da sauri ya rik’e bakinsa dariya na shirin kama shi ganin yarda ta yi da fuska ya ja karan hancinta “Seriously gashin Nanna ya fi na ki kyau ko don ita tana gyarawa ne. Ke ma ki dage da gyara don ina son inji gashin mace yana sulb’i. Bata san sanda ta kai wa hannunsa cizo ba cikin takaicin maganganunsa sannan ta fad’a jikinsa tana shirin saka kuka ya yi mata abinda tilas ya sata had’iye guntun hawayen shagwab’arta.






______________


Haka dai suka dinga zuba soyayyarsu har ana i gobe azimi don haka da daddare ya zaunar da ita kusa da shi murya k’asa-k’asa ya ce “Please mu yi magana ta fahimta, gobe azimi gaskiya ba zan iya jurar ganinki da rana na kyaleki ba. Ba tare da na ji wani feeling a raina ba. Ina gudun karyewar azimina don haka zan dinga zuwa bayan magriba na tafi da asussuba na sanar da Nanna aiki na ya koma na dare so ba ni da fargaba ta wannan fannin.” Runtse idanunta ta yi tana jin kunyar kalamansa don duk da a lokacin ta d’an fara sakewa da shi. “Nan da 3 days za mu tafi Nigeria insha Allah, dad’in da na ji ma ba ku fara lectures ba har ma je mu dawo ma da izinin Allah.” Ta d’an d’aga kai tana jin yarda k’irjinta yake bugu a duk sa’ilin da aka ambaci Nigeria.




Haka dai suka dinga morewa amarcinsu kafin ranar tafiyarsu ta zo. Da kansa ya kai su Khairi gidan Abba Musty kuma sam ba su damu ba murna ma suke don da sa’anninsu a gidan kuma school d’in su d’aya. Ga Abba Musty da son yara.




A daren ranar a gidan Nanna ya kwana. Don haka Hamda kwan ta yi tana sallah da addu’ar kada Allah ya kawo abinda zai rabata da Hammad. Ubangiji yasa zamansu ya d’ore har aljanna. Tuni ta shirya akwatinta tsaf.


Da safe kuwa da kyar ta mik’e don tafiyar rana za suyi. Wanka ta yi sosai ta sanya wata doguwar riga mai masifar kyau light purple ta yane kanta da mayafin rigar. Kyau kam ta zuba shi a ranar da duk wanda ya kalleta na tabbata sai ya sake jiyowa ya kalleta.




Tun a mota Nanna da taga yayi parking a k’ofar gidan ta kalleshi “Me za muyi anan ko mota zaka ajiye? Wai gidan ma waye tukunna?” Fuskarsa a d’aure ya ce “Wace tambaya kike so na amsa miki? Ko gidan ma waye ai yanzu zaki gani.”
Ya fad’a yana ficewa daga motar. Wannan karan madadin ya bud’e da key kamar yarda ya saba sai ya danna door bell



Hamda da take zaune mamakin waye ya kamata ta mik’e a hankali ta bud’e k’ofar. Kallo d’aya ya yi mata ya d’auke kai “Oya ki yi sauri ki fito muna mota.” Daga haka ya juya. Hamda da take tsaye turus ta yi tana kallonsa tana mamakin dalilin canjin fuskarsa ko don ya d’auko Hakimar tasa ne?






Jikar Nashe ce…
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Ya dad’e a bakin k’ofa yana knocking kafin Nanna ta mik’e zuciyarta a tunzire ta bud’e k’ofar. Idanunsa cikin nata ya hango tsananin b’acin rai kwance a fuskarta.
Ko kallo na biyu bata sake yi masa ba ta juya da sassarfa zata shige ciki da sauri ya jawo hannunta ya damk’e sosai ta yarda ba zata iya gudu ba. Ya rutsa ta a bango sosai ta yarda ba zata iya wani motsi ko gudu ba. Ya kuma kakkafeta da ido kaifin idanunsa da suke yawo a jikinta ya sa ta runtse idanunta tana jin hakan yana tasiri a ranta ya kuma sauya bugun zuciyarta a lokaci guda. Hammad ya san ta kan zuciyar mata yana siye zuciyar mace ko bata shiryaba balle ita da soyayyarsa ta game zuciyarta gaba d’aya bata jin zata iya sharing d’insa da ko wace mace shi yasa da ta kwana ita kad’ai a gado d’aya lamarin ya gigita ta dan hakan sabon abune a wajenta. Bai tab’a faruwa ba a tsawon zamantakewar su ta aure. Ganin ya kwantar da b’acin ranta ta hanyar da ba ta zata ba ya sashi sakinta yana mayar da
Numfashi kad’an ya ce “ina yaran su fito na yi dropping d’in su kada su yi late.” Ta so ta sake yi masa mita sai dai ta san shi mutum ne da baya son ya lallab’aka ka botsare don shi idan ya tashi rigimarsa ta fi tata. Jikinta a sanyaye ta juya duk da hancinta ya juyo mata k’amshin turaren da ba nasa ba a jikinsa. Amma ta bar abin a ranta don ba yanzu bane lokacin magana zata yi bincike da kanta idan kuwa ta tabbatar da wata ce take tarayya da mijinta a waje tabbas mai raba da ita sai lahira. Ta fad’a zuciyarta na matsanancin bugu saboda tsananin kishi. Ganin irin kallon da
Take masa ya tabbatar masa rigimar tana nan jira take ya dawo ta sauke masa ita kwando-kwando murmushi kawai ya saki a zuciyarsa ya ce dama kin adana rigimarki nan gaba kad’an zata yi miki amfani.




____________________


Cikin dare ta gama shirinta tsaf cikin wasu irin sihirtattun turaruka masu gigita d’a namiji ko bai shirya ba. Wani chewing gum mai masifar k’amshi ta cilla a bakinta ta tsaya gaban mudubin d’akinta tana sake turare sussulb’an gashin kanta da abin turara ga shi. Ita kad’ai take sakin murmushi bayan ta bi jikinta da kallo ta ga irin yarda yauk’akkar rigar barcin ta bi lafiyar jikinta ta kwanta luf iya kacinta gwiwa ta kuma fitar da duk wani shape d’in ta na halittun Y’a mace. Har a wannan lokacin saboda gyara da take wa jikinta halittunta suna nan tsaf kamar na wata budurwar shape d’inta da surarta sam ba su jirkita ba saboda yarda take maintaining d’in su.


Tattausan silifas d’inta ta saka sannan ta kawo dogon hijabi ta saka tana murmushin mugunta don tabbas yau mai kwatar Abbu a hannunta sai ya shirya. Ita kad’ai ta san bam d’in da ta had’a masa ta yarda duk umarnin da ta ba shi zai bi ba wani musu.


A falo ta sameshi yana kallon BBC london. K’amshin turarenta ne ya sanar da shi zuwanta ya d’ago yana sakar mata tattausan murmushi. Kafin ya yi aune ta cire hijabin ta hullar guntuwar rigar barcin da kad’an ta wuce gwiwa ta bayyana Santala-santalan cinyoyinta. Abbu kusan sumewar zaune ya yi don ta dad’e bata yi masa wannan shigar ba sai ya ganta tamkar ranar da suka fara tarewa a matsayin amarya da ango. Cikin tafiyar jan hankali da lank’wasa jiki ta k’arasa wajen sa tana sakar masa wani irin murmushi had’e da kallo mai rikitar da y’an maza sam bai san sanda ya yi mata masauki a cinyarsa ba bayan ya ji sunan da ta rad’a masa a kunne k’albeey barka da dare.




Karfe biyun dare ta sake gyara kwanciyarta a jikinsa tana rik’e da hannunsa ta ce “K’albeyy akwai fa abinda yake damuna.” Gashinta ya shafa sosai yana jin kamar ya mayar da ita cikinsa “Gaya min damuwarki ko ta mecece kin ji Dearling.” Ta sake narkar da idonta cikin nasa “Kalbeey me yasa Asma’u ta takurawa rayuwata? Ban san me nayi mata ba yanzu fa zuga Didi take a zuwan ni na yi mata asiri. Fisabilillah in rasa wacce zan yiwa asiri sai matar da nake wa kallon mahaifiya. Ni ban san me yasa y’an uwanka basa sona ba ko don na zamo bare a cikinku ni ba k’abilarmu d’aya ba.” Ta fad’a tana sakin wani irin kuka na tashin hankali. Ran Abbu kam ya kai k’ololuwar b’aci. Don ba abinda yake d’aga masa hankali irin ya ga Saknansa tana kuka. Ji yake kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login